← Book details Matar Police Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 19

Sashe 6

Matar Police Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ta kyalyale da dariya kan ta tashi ta na" yauwa lantana ki ga ni fa yadda za ki na tafiya daga yau irin na manyan Mata, daura hannu za ki yi akwankwason ki kina tafiya kamar taliyar yan birni, kinga indai ki na mishi haka to fa ba zai kara aure ba, nima ranar da mukaje birnine naga ana fada a Talabijin."

Lantana ta ji maganar rashin karo kishiya tuni ta ta shi ta na kwaikwayon Jidda.

Kiransu akazo yi kan cewa angwaye sun dawo daga daurin Auren.

Wani mayafi Jidda ta dauko Wanda babanta ya aiko ma ta da shi ta lullube Lantana.

Suna fita antaro ana kallon Amarya mai irin adon yan birni.

Shi dai Adamu abokin ummaru hankalinshi na kan Jidda ita kawai ya ke kallo.

Ta na sane da shi suna hada ido za ta galla mishi harara tuni ya ke kawar da kan shi kasa.

Jiddatu ta ce,"Ummaru Amman zaka bar mu MU cigaba da zuwa makaranta da lantana ko? Kasan dai saura shekara daya mu gama."

Ummaru ya San halin Jidda sarai hakan ya sa shi saurin amsawa da Eh.

Yamma ta yi amfara zuwa daukan Amarya Jiddatu ta rankwashi kan Lantana "wawiya kin ki kiyi kuka ko? Ai ace mi ki Mara kunya ko kukan ya ki zuwa ki kakalo na karya."

Haka ba yadda lantana ta iya ta fara kukan karya ta na ihu.

Sunje har an wuce gidan ba a sani ba, tuni lantana ta cire ido amayafi ta na fadin, "An wuce gidan fa gashi cen wance da ke da dakalin ne."

🤣🤣🤣amaren zamani.

_*Karku manta fa har yanzu ba mu shiga birni ba🥳🥳🥳karku bari shiga birni ya kubuce ma ku, maza Ku hanzarta domin fara biyan 200 din Ku kacal*_

Urs Xayyeesherth
[11/13, 1:57 PM] Xayyeesherth: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation

°°°°°° _*MATAR POLICE*_ °°°°°°

*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*🤝

__________________________________________________________
_We Are Here To Educate,Motivate, And Entertain Our Readers._
__________________________________________________________

_*Matar Police kirkirarren labarine mai cike da barkwanci, fadakarwa,nishadantarwa tare da sabon salo na mussaman domin farantawa masoya littafaina*_

_*LABARI DA RUBUTAWA*_

_*AISHA MOHAMMED SANI (Xayyeesherthul-humaerath)*_

_LITTAFAN MARUBUCIYAR_
1- _BABU RUWAN SO_
2- _KUCHAKAR KISHIYA_
3- _WASA DA SO_
4- _AZZAWAJUL-MUKADDAR_
5- _JAMEEL (Nafseen)_
6- _KWADAYI 2020_

AND NOW *MATAR POLICE*

_LITTAFINA NA KUDINE INDAI KI NA SON CIGABAN ZA KI TURO KATIN 200 KACAL TA WANNAN NUMBER 08103080717 SANNAN KI YI SCREENSHOT DOMIN TUROMIN DA SHEDAR BIYA_

_*BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHIM*_

*_FREE PAGE 11/12_*

****************
************
******************

Sai da suka kammala gyaran gidannan tsaf kan Jidda ta bari su ka je gida domin cin abincin rana tare da shirin islamiya.

Ko da suka dawo tana nan ta na gilu-gilu lokacin Islamiya har ya fara kurewa, ga shi suna jin tsoron mugun malaminsu, ba abin su yi magana ba Jidda ta hau su da bala'i, kwaskwarima ta fara yi sannan ta dauko kayan kwalliyarta, "Ku zo nan kuna YI da kan Ku duk abin da na YI kuma Ku yi."

Da sauri kuwa Su Indo da lantana ansami garabasar kayan kwalliyi akafara, tuni ma sun manta da maganar sun makara.

Jidda na gamawa ta kalli Indo tare da dafka wani hamshakin tsaki ta ce, "Dilla chan Ke ba a kan gira ake sa kallin ba saman gashin ne wawiya kawai."

Karfa ta yi ta kara chaba mata girar da eye-shadow .

"Woo kin ga yadda ki ka yi kyau kuwa kamar yau aurenki, aradu in anzo bikin ki za aga tsiya a kauyen nan."

Karasa maganar ta yi cikin dare ta ce, "Ku tashi muje kan wannan masifaffen malamin ya fara."

Tafiyarsu su Ke su na ta dariya duk Wanda ya kalli Jidda su ka hada Ido sai ta galla ma sa harara tare da murguda baki.

Suna isa makaranta Malam ya yi suman tsaye ya ce, "lallai ma wato yau ba iyaka makaran Ku ka tsaya ba hadda kwalliyar Aljanu?"

Jidda ta fara murguda baki, "Ni dai Wallahi ban yi kwalliyar Aljanu ba Ehee, ni nasan ma haushi ka Ke ji matarka ba ta iya ba."

Mallam ya ce, "Ni kike maiwa da martani ko? Zan nuna mi ki ba ta iya ba kuwa, daga Ke yar yan korar na ki sai na yi maganinku yau."

Jidda ta ce, "Tab ni Wallahi an hana dukana kuma in ka dakeni za ka gani."

A fusace Malam ya dauko dorina domin ba Yau Jidda ta saba yi mi shi rashin kunya ba, ya na kyalletane sabida karatun ta.

Dukan su ya farayi suna kuka, mussaman Jidda ban da kararta ba abinda ake ji, Iya da ke gida ma sai da ta jiyota."

Tuni Iya ta zagaro kafa ko takalmi ba bu bare mayafi.

Jidda kuwa ta kidime"Wayyo mallam zai kasheni shikenan mallam zai kasheni, mallam Wallahi kashi na Ke ji ka barni na je na yi nadawo sai ka cigaba, mallam zan yi agun wallahi gashinan zai fito mallam, mallam zai fito."

Shi ko mallam kaman ana Dada tinzirashi ya cigaba da dukanta.

Yan makaranta kuwa ban da dariya ba abin da su Ke.

Iya ta shigo cikin masifa, "Wai wannan wani irin bala'i da masifa ne yarinya kowa ya na hassada da ita duk kun bi kun tsaneta son ko kowa kin Wanda ya rasa."

Ta fisge Jidda awajen mallam ta cigaba da fadin, "Gani nan sai ka hadamu ka daka ai ko in tsinemaka, in tsinewa kakan kakanka, ban da mugunta irin taka wannan yarinyar nawa ta ke yaushe ta kai duka wannan ko goyo abayama ba ta zarce ba bare amata duka da wannan tsimagiyar, kana nan da hanci kamar fantekar da ta yi wata ba waiwayeta ba, ba ki kamar tuwun dawan da ya shekara, to wallahi ahir din ka da jikata karkasa in maka baki domin gadon mu kambun ba ka."

Shi dai Mallam tunda Iya ta fara magana ya ja bakin shi ya yi tsint tare da saukar da kai kasa domin yasan ba abin mamaki ba ne Iya ta mai tijara cikin dalibansa ya gode ma da abin ya tsaya iyaka masifa ban da mari Dan in taso sai ta rama ma ta.

Cikin shagwaba da gulma Jidda ta ce, "Iya kuma fa na fada mishi kashi nkeji ya bar ni nayi Amman ya ki."

Iya ta dubeshi tare da zungure mi shi kai, "Kai baka kashin ne ko ko ba kasan yadda ya ke matsin mutum ba, nan nan naga kana yaro kullum in ka zo gidana wasa sai kasani aikin kashi ga kashinka da uban wari, yo ai ko ubanka ma lokacin ahe haka ya ke gadone abin."
Ta kyalyale d dariya.

Yara na son yin dariya Amman ba yadda suka iya suka gimtse.

Jiddatu ta ce, "To Iya ki tafi ni nama daina jin kashin ya mana karatun kawai."

Iya ta ce, "Shikenan yar lelena,kai kuma Audu ka ke ko mudi, ahir dinka ko kallon banza ban so akarayiwa Jidda, maza ka ma su karatu jikin lumana kasan ba mu son tashin hankali, Ah to."

Ta fice ta na kanun maganganunta, "Yo in ban da tsiyama har an iya ayi mana kallon banza sai inyiwa mutum baki ya ba ce aradu
, Ni fa tausayin yan kauyen nan ma na ke, kar in tafi komai ta barbare,da tuni na koma birni,Amman su ba sa ganin hakan, Oh ni Baba Kulu."

Iya na tafiya mallam ba yadda ya iya haka ya cigaba da ma su karatu ko hada Ido ya yi da Jidda saurin kawar da kai ya ke yana fadin, "A uzubillahi."

Ita kuwa Jiddatu sai kallon shi ta ke tana kyakyalewa da dariya.

Ana cikin karatu ta katse, "Mallam zan yi kashi."

Kawar da kan shi ya yi daga I donta ya ce, "To jekiyi."

Ta kara da cewa, "Kai baka jin kashin ne?"

Ya ce, "Eh."

Ta ce, "To ai shikenan ni dai zanje na yi kuma in ka na ji kaje ka yi karka ma na tusa a aji."

Yara suka tintsire da dariya sai da ya ma su tuzuren dole kan su ka kumshe dariyar.

Kuwa Jidda fita tayi ta yi wasanta son ranta kan ta dawo ajin.

Mallam Addu'a ya ke kawai lokacin ta shi ya yi ya kadasu gida.

Jidda sai kakale-kakale ta ke daga tace zata sha ruwa, sai ta zatayi fitsari.

Daga karshe dai lokaci bai ma yi ba mallam ya kadasu gida ya ce antashi, Jidda kuwa sai murna daman abin da ta ke so kenan ahanya su lekya gona su diba karas.

Tafiya su ke Jidda ban da tsokanar mutane ba abinda ta ke yi.

Indo ta ce, "Laa Jidda kin ga fa Mallam Ya'un ya na barci dadin ma diban kenan."

Lantana ta ce, "ai kuwa kin ga shikenan ma diba son ran mu."

Jidda ta ce, "Ku Je Ku diba ni zan tsaya anan inna tsokanarshi."

Tsinke ta dauka ta karasa wajen shimfidar mallam ya'u dai-dai kunnenshi ta tura ahankali..........

Urs Xayyeesherth
[11/13, 1:57 PM] Xayyeesherth: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation

°°°°°° _*MATAR POLICE*_ °°°°°°

*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*🤝

__________________________________________________________
_We Are Here To Educate,Motivate, And Entertain Our Readers._
__________________________________________________________

_*Matar Police kirkirarren labarine mai cike da barkwanci, fadakarwa,nishadantarwa tare da sabon salo na mussaman domin farantawa masoya littafaina*_

_*LABARI DA RUBUTAWA*_

_*AISHA MOHAMMED SANI (Xayyeesherthul-humaerath)*_

_LITTAFAN MARUBUCIYAR_
1- _BABU RUWAN SO_
2- _KUCHAKAR KISHIYA_
3- _WASA DA SO_
4- _AZZAWAJUL-MUKADDAR_
5- _JAMEEL (Nafseen)_
6- _KWADAYI 2020_

AND NOW *MATAR POLICE*

_LITTAFINA NA KUDINE INDAI KI NA SON CIGABAN ZA KI TURO KATIN 200 KACAL TA WANNAN NUMBER 08103080717 SANNAN KI YI SCREENSHOT DOMIN TUROMIN DA SHEDAR BIYA_

_*BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHIM*_

*_FREE PAGE 14/15_*

****************
************
******************

Rankwashi Jiddatu ta kaiwa lantana
Ta ce, "Mara kunya kawai, ni daman so na ke in Dan ba tsofin nan wahala Amman kin wani kofsa wawiya kawai ai sai mu shiga."

Su kuwa tsofin da ya ke sun San halin Jidda sarai kawai shigewa gidan su kai ba tare da sunce kala ba.

Ko zama ba su yi ba ana ajiye Lantana tsoffafin su ka bar indo da Jidda.
Chapter 6 · 0% Book details