← Book details Matar Damusa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 56 OF 58

Sashe 56

Matar Damusa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ransa a ɓace yake nuna ta da ɗan yatsarsa yana faɗin "zan kashe ki idan na sake jin dariyarki..."

Juyowa yayi yana kallon Angel a fusace, ai kuwa bata jira wani-wani ba da gudun gaske ta koma ɗakin mommy ta danna sakata, saboda gudun kar ya yo kanta...

kawar da kansa yayi yana kallon Ayush tana tsaye a tsakiyar benin bata ƙarasa sauƙowa ba,
ganin irin kallon da yake mata ne yasa ta kawar da kanta gefe, itama da gudu ta koma ɗakinta...

Adity ce ta tashi da gudun gaske ta nufi ɗakinta tana faɗin "tiger bai warke ba wallahi, mahaukaci ne.." ta danna sakata a ɗakinta..
da sauri zai bita ɗakin mommy tayi saurin riƙe hannunsa tana girgiza masa kai, ga kuma kumburarren baki😹,
itama Rumana ɗakinta ta wuce da ɓacin rai tana riƙe da goshinta,
mommy tace "toh daga yanzu zaka fara ganin alamar Auren mata uku ba wasa bane, gashi suna son saka maka hawan jini..."
kafin mommy ta ƙarasa maganar ya katseta da cewa "impossible ba macen da zata ɗora mun jinya, kuma wallahi a yau zasu tafi.."

Mommy tace "a'a ba yanda zasu je a yau har sai an kammala hidimar nan, kuma muje mu ɗakinka inaso yin magana da kai mai muhimmanci, kafin baƙi su fara hallaruwa zuwa anjuma kaɗan..."

Mommy jan hannun Junaid tayi suka nufi upstairs acan ɗakin Junaid zasu tattauna....

bayan sun shiga mommy zaunar dashi tayi a bakin gado itama ta zauna tana fuskantarsa, tace "Junaid dan Allah inaso ka nutsu kabar duk wannan haukar ka hangi abunda zai biyo baya, nasan kasan ciwon kanka kuma ka mallaki hankalin kan ka, kasan mai yake maka ciwo, waɗannan ƴanmatan daka tarasu ba wayewa bane sai tarin tashin hankali, kai kan ka hankalinka ba'a kwance yake ba nima kuma haka, dan Allah na roƙe ƙa Junaid kamun wata alfarma ɗaya..."

juyowa Junaid yayi yana kallon mommy sannan yace "ina jinki mom.."

tace "na tsara wani abu ne, inason wannan walimar da za'ayi anjuma ya tafi tareda baikon ka, ka zaɓi mace ɗaya acikin ƴanmatan ka ayi muku baiko da ita, sauran kuma duk ka watsar amma banda Ayush tinda ita ta rigada ta zamo naka, idan kuma ita ka zaɓa a matsayin matarka zanfi kowa jin daɗin hakan sosai amma bazanyi maka dole ba, ka zaɓa da kanka tin yanzu saboda a gaban mutanen za'ayi muku baikon..."

Junaid dogon numfashi yaja yana karkaɗa ƙafafunsa ya tsayar da eyes ɗinsa a guri guda kamar mai yin tunanin wani abu, yace "Mom ki ban lokaci zanyi tunani akai..."

Girgiza kai mommy tayi tana faɗin "babu wani lokacin da muke dashi a halin yanzu, ka duba fa yanzu ƙarfe 12 rana tayi kafin kuyi shirye-shiryen ku har lokaci zai ƙure, kuma dole sai anyi zaman shirya wacce za'ayi baikon da ita, bamu da lokaci kai ai kasan wacce tafi kwanciya maka a rai...."

Mommy dai har cikin zuciyarta tana so taji ya ambaci sunan Ayush, haka take binshi da kallo tana son jin sunan da zai furta..

yana motsa baki a hankali ya furta cewa "nifa mace biyu zan zaɓa, Adity da Yushert inaso ayi mun baikonsu a tare...."

turɓune fuska Mommy tayi sannan tace "Adity wacce ka gama dukanta yanzu?.."

yace "eah mom saboda a rayuwata inaso na ringa dukan mutum da zaran yamun laifi, toh kinga Adity a koda yaushe zan iya mata dukan fitar rai ita kuma Yushert bazan iya dukanta ba saboda tanada rauni kuma ina tausayinta sosai..."

Mommy jijjiga kai tayi tana faɗin "a'a wallahi baka tausayin Ayush, inda kana tausayinta da bazaka haɗata da wannan ƴar china ba, kawai dai kace kuna son zaluntarta ne.."

yamutsa fuska yayi sannan yace "to mom ya kike so nayi, ai ba'a guri ɗaya zan ajiyesu ba..."
Mommy ta katse shi da cewa "nidai ban yadda da wannan haɗin ba, idan Ayush ka zaɓa toh ita kadai ce, idan kuma Adity ce to kaje can ka Aureta ita kaɗai amma bazaiyu ka haɗa mun Ayush da wata ba..."

juyowa yayi yana kallon Mommy da dara-daran eyes ɗinsa yace "to kuwa idan na Auri Yushert zata sha duka ne a gurina, domin bazan juri raini ba, tana mun laifi zan ɗau hukunci yanda nayi wa Adity dukan na toh haka itama saina farfasa mata jiki, tinda nace zan haɗa ta da wacce ta saba da dukana kin ƙi yadda toh shikenam idan kin yarda da abunda nace zan Auri Yushert idan kuma baki yarda ba, zan haɗasu duk su biyun na Aura domin bazan taɓa barin wani ya Auri Yushert ba saboda ita ce first kis....." bai ƙarasa maganar ba ya dakatar tareda juyar da kansa gefe, saboda baya son furta wani abu domin yana matuƙar jin kunyar mom ɗinsa..

Mommy ce ta ƙarasa masa da cewa "itace mace ta farko daka sumbata? bazaka iya barin ta a wani ba? hmmm! nasan haka kake son cewa..."

dasauri Junaid ya juyo yana kallonta cike da mamaki, sosa sumar kansa yayi yace "mom baki ce kin amince da batuna ba, shin zaki Aura mun Yushert ita kaɗai da zarar tamun laifi na hukuntata da duka ko kuma zan haɗata da Adity inyaso koda tayi mun laifi zanje na hukunta Adity a madadinta ne kodai mekika ce?...."

Mommy kallonsa tayi tareda jan numfashi tace "na amince ka Auri Ayush ita kaɗai inyaso idan tayi maka laifi saika hukuntata, gwara kaiɗin ka zalunce ta akan Adity, nasan wata rana Allah zai saka mata kuma zakayi danasani..."

"please mom kefa kika ce babu lokaci, tinda kin yarda da yarjejeniyar mu shikenam aje a fara shiryata kafin lokacin da za'ayi mana baikon ya gabato, ni yanzu zan fara shiri ne..."
ya miƙe tsaye zai nufi toilet, ya kuma cewa "mom a ƙira masu girke-girke da kuma waɗanda zasu gyara parlour nan saboda naga duk sunyi kaca kaca da wajen,
Sannan kuma ƴan uwanki suna kan hanya ɗazu nayi waya dasu,
my phone yana can parlour kije ki zare mun sim ɗin na sannan kisa a kawo mun wata wayar na 5.5million...."

Mommy ce itama ta miƙe tsaye ta kama kunkumi tace "Ashe Babana dole nayi maka biyayya akan abunda kace mana, saboda kana sakaye da sunan mahaifina shine zaka wani bani order?.."
ta ƙarasa maganar tana harararsa..

juyowa yayi yana murmushi yazo gabanta ya haɗe tafukan hannayensa biyu sannan yace "please my lovely mom banida time ne yanzu abokai na zasu fara zuwa, help me mom..."

Mommy dariya ne ya kuɓuce mata ganin yanda yayi kalar tausayi tace "shikenam my son je kayi wankan ka, zansa a kawo wedding gown wa Ayush.."

Junaid hannu yakai saitin lips d'in mom yana fad'in "mom kinji rauni da yawa fa, gashi har ya kumbura waje, kije Kisha magani saboda wajen ya sa6e..."

Murmushi tayi sannan tace "bazan sha magani yanzu ba saboda yau na tashi da Azumi.."

Zaro eyes yayi waje tareda fad'in "Azumin na meye ne?.."

tace "zan godewa ubangiji na akan samun lafiyarka mana, amma inadai ba kid'e² zakuyi ba? domin banason harkar shaiɗanci..."

yamutsa fuska yayi sannan yace "mom kin dai san manya² mutane ne zasu halacci taron nan ko? kuma har da abokan mahaifina da kuma shuwagabanin mu na sojoji, yaushe za'ayi party kuma, just iya walima ne aci asha a godewa ubangiji, toh tinda kin kawo maganar baiko sai a haɗa ayi awajen taron..."

Mommy murmushi tayi tareda jan kuncin Junaid tace "Masha Allah my son, Allah ya maka albarka.."

shigewa cikin toilet yayi tareda faɗin "thanks nima kisa a kawo mun suit yanzun nan kafin na fito a wanka, na manta ban tanadar dashi ba, ni kuma bazan iya saka old ba..."
yana cikin toilet ya ƙarasa maganar,
Mommy da murmushi a fuskarta tabar ɗakin...

☆☆☆☆☆

Misalin ƙarfe 2 Doctor Hasheem yana zaune a ɗaya daga cikin kujerun falonsu yanata danna wayarsa, sai ga Laylah ta fito sanye da doguwar riga maroon colour na kanti har jan ƙasa take, mai dogon hannu,
rigar ya ɗameta ta sama breast cup ɗinnan ya zaunu ga daman dirarriya ce gaba ɗaya ta cike rigar, daga kunkuminta kuwa rigar ta baje sosai, taci ɗaurin ɗan ƙwalinta ta fitar da gashin ta tsakiyar ƙwalin, ta ɗauko gyale ɗan ƙarami kalan kayan mai tsantsi ta yafa a kafaɗarta, ɗan kunnen da sarƙar wuya tareda warwaron hannunta duk sunyi colour da kayan jikinta,
ga ta hau takalmi mai tudu sosai shima kalar kayan, ta lanƙayo ɗan ƙaramin handbag ɗinta, ɗayan hannun kuma tana riƙe da ƙatuwar infinix ɗinta, tana taku a hankali ta shugo falon tana ƙamshin turare gata sha makeup domin zuwa tayi akayi mata na kuɗi...

Doctor Hasheem kallonta yayi tareda miƙewa tsaye yana faɗin "wow my little sister kinsha kyau sosai, fashion girl ƴar wanka..."

murmushi tayi sannan tace "my bros ka tayani da Addu'a Allah yasa idan munje walimar nan Ogah Junaid ya faɗa cikin soyayyata, tinda har ya warke nasan zan burgeshi.."

shima Doctor Hasheem murmushi yayi sannan yace "toh Allah yasa.."
in short answer ya bata, ya kuma cewa "toh mu tafi ko kar lokaci ya ƙure mana, ina kina tareda gate pass ɗinki.."

ɗan turo baki tayi tace "Ina dai a kai ɗaya aka bawa, sai dai na maƙale a bayanka.."

yace "ok shikenam muje mu koh.."
har sun ɗan fara tafiya Laylah ta tsaya tana faɗin "Big bros Maimoon fa? yakamata kaje ka dubo ta kafin mu tafi karta ji mu shuru.."

jim yayi kaɗan kafin yace "ok wait for me.."
ya nufi can cikin gidan wanda yakeda rata sosai da compound ɗinsu, key yasa ya buɗe ya danna kansa ciki yana sallama,
Maimoon tana zaune akan katifa ganin shugowar Doctor Hasheem yasa ta kawar da kanta gefe, kwata-kwata ma bata son ganinsa,
zama yayi a bakin katifar tareda cewa "Maimoon har yanzu fushi kike dani? daman soyayya zata iya juyewa ƙiyayya? daman ba ƙaunata kike ba ashe...."

kafin ya ƙarasa maganar ta katse shi da cewa "please malam inason ganin mahaifiyata, na fahimce ka kai baka san ciwon rashin iyaye a kusa ba, shiyasa ka rabani dasu ka kawo ni nan saboda rashin imani irin taka..."
Chapter 56 · 0% Book details