← Book details Matar Damusa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 52 OF 58

Sashe 52

Matar Damusa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

kafin yayi magana wayarsa ta fara ring sound ɗaukar wayar yayi yace "kinga ƴar halak Rumana ce.." ya saka wayar a speaker ba tareda ya Kara a kunne ba yace "hello girl.."
ta ɗayan ɓangare kuma tana magana ta yaren french "Beb jiya na ƙira wayarka you didn't pick my call, Beb i really miss you too, naji labarin gobe kana hidima shine ko a gayyace ni, to yanzu ma zan sanar maka ne zan hau jirgi zanzo nigeria, hotel zaka kama mun ne ko a gidanku zan sauƙa? kasan banson hayaniya kuma mommy ta cika sa eyes..."

murmushi yayi sannan shima ya mayar mata da reply cewa "don't worry zaki zauna ne a gidan mu, kinsan bana son hotel ɗin nan.." shima ta yaren french ya yi maganar...
daga ƙarshe ya katse ƙiran.

duk tattaunawar nan da sukayi mommy ko kaɗan bata ji yaren ba,
sai murmushin da take ta zubawa..

ita kuma Ayush ta zauna kamar wacce ruwa ta cinye ta,
duk wayar nan da sukayi kaf daga A har Z Ayush taji, domin itama ta iya yaren french sosai, ta koya daga waran mahaifiyarta,

Mommy ce ta kalle shi tace "to ita kuma wannan mai ta ce?.."

yace "tace yau zata sauƙa a gidan nan,
kuma wannan kishi a waran ta ya ɓaci kinsan bature baya son haɗakar.."

Mommy tace "toh fah karfa kasa suzo suyita faɗa acikin gidan nan?."

yace "haba baza suyiba ai suna jin shakkata..."
yana danna wayarsa ya kuma cewa "bari na ƙira Adity tin kafin ta ƙirani saboda nasan ita ta cika raki.."
cikin sa'a wayar ta shiga bugu ɗaya ta ɗauka murya a kasalance tace "ka manta dani daman ina jiran ƙiranka naga an ɗora ka a media cewa gobe zakayi party ko?.." tayi maganar ne da yaren china,
amsa mata yayi da cewa "to sarkin complain, ya aiki, a wannan satin mutane nawa kika harbe da bindiga?..."
dariya tayi sosai saboda tasan indai tana cikin fushi to Junaid yasa yanda zaiyi ya faranta mata,
domin ita indai ta ɓangaren mugunta ne ta ƙwarai sosai batada aiki sai mugunta haka kawai zata ƙaƙulu faɗa don ta zalinci mutum, Adity ta iya faɗa sosai faɗanta kuma irin na chainoni,
ita ta sanar masa zata zo gobe kuma a gidansu zata sauƙa,
da haka suka kammala wayar ya katse yana dariya....

idon Ayush ne ya kaɗa ya yi jawur tsabar takaici da baƙin ciki da kuma ciwon kishi dake damunta, kuka ne yake shirin kuɓuce mata ta tashi da sauri ta nufi kitchen, tana zuwa kuwa ta tsaya a gaban gas tana rera kukan ta,
ita har ta fidda rai akan Auran Junaid yanda taga yana waya da ƴan matansa waɗanda suka fita class bama a nigeria suke bama, kuma yanada tabbacin Aurensu zaiyi tinda gashi da bakinsa yake faɗa, kuma tasan Junaid baya taɓa faɗan abunda bazai faru ba...

tana cikin rera kuka taji an zagayo hannaye ta gaban kunkuminta ya manne jikinta da nashi yana shaƙar ƙamshin wuyanta, yazo saitin kunnenta ya hura mata iskar bakinsa sannan yace "kina kuka akan meye?.."

shuru tayi bata bashi amsa ba,
ta tsayar da kukan tana ajiyar zuciya!
hannunsa ya cusa cikin rigarta ta ƙasi yana shafar ɗan ƙaramin tumbin ta yace "ko kinaso a ƙira miki Doctor Hasheem ne?..."
juyowa tayi da sauri ta hankaɗa shi baya a fusace tace "to tinda ni ba taka bace ai taɓa jikina ya haramta a gareka, baka sona toh meyasa kake son jikina? idan zaka so ni ka soni saboda Allah bawai dan tada sha'awa ba, ina Arnakun ƴan matan nakan suke ka bari idan sun zo saika cigaba da tada sha'awarka akansu daman can halinsu ne, ni kuma zan Auri Doctor Hasheem ɗin domin ya fika ƙaunata...."

Junaid fah ran maza ya ɓaci kawai rufe idonsa yayi sosai ya cizai gefen leɓɓensa na ƙasi, tinda yake a rayuwarsa mace bata taɓa tsayawa a gabansa tana faɗa masa maganganu ba sai yau, kuma hakan ma macen daya rainawa shekarunta, wacce a baya take matuƙar jin tsoronsa,
inda ace babu girman soyayyar Ayush a cikin zuciyarsa da tinin yayi ball da ita, da ba abunda zai hana yayi mata dukan tsiya a gurin nan,

Ayush tana huci tazo zata wuce ta gefensa ta fita taji ya riƙo dantsenta da ƙarfin gaske ya finciko ta sannan ya mannota saman faffaɗar ƙirjinsa suna kallon juna, numfashinsu ma haka yake ta gaurayuwa, cikin ɓacin rai yake kallonta leɓɓensa na rawa muryarsa cool yace "inda ace ɗaya ce daga cikin sojojin ƴanmata na take gaya mun wannan maganganun wallahi tallahi dana murɗe mata wuya...." ya ƙarasa maganar yana zaro mata disasshun idanuwansa waɗanda suka kaɗa sukayi jaa tsabar baƙin cikin da ya ƙunsa a yanzu..

ya kuma cewa "inda ace sha'awa ce take sa na taɓa jikinki wallahi tallahi da baki isheni kallo ba, saboda ni ƴan matan nigeria ma gaba ɗayansu a tafin hannuna suke, kinyi mun ƙanƙantar da zan taɓa jikinki saboda sha'awa,
Angel! Rumana!! Aditi!!! duk zasu zo zakuma ki gansu duk babu wacce shekarunta yayi ƙasa da shekara 30 a duniya, cikakkun ƴanmata, wayayyu, dirjajjun ƴanmata wanda class ɗinsu ya wuce yanda kike tsammani to su suke bibiyata kuma duk acikinsu babu wacce na fara cemata ina sonta, kafin su shawo kaina ki tambayesu irin wahalar da gwagwarmayar da suka sha kafin na amince musu da soyayyata,
kamar yanda kike kishi akansu to su basuda lokacinda zasuyi kishi akanki domin idan sukazo bazasu banbance ki da namiji ba, saboda su a wajensu ke ƴar jaririya ce,
idan kika ƙara tsayawa a gabana kina faɗamun maganganu makamancin haka saina......"
yasa hannu ya jawo ɗan ƙaramin lip ɗinta na ƙasi yana kallon cikin eyes ɗinta,

itama tin daya fara maganganunsa ta ƙura masa ido ko ƙibtawa batayi ba, ita kaɗai tasan irin raɗaɗin da take ji acikin zuciyarta...

lokaci guda kuma yasau murmushi yace "Doctor Hasheem ko? to kije ki Aure shi mana,
wai ma shin menene sha'awa? na daɗe ina taɓa jikin ƴanmatan ƙasar waje cikakku amma ko kaɗan ban taɓa jin wani abu a jikina ba.."
saketa yayi yana dariya tareda faɗin "wai sha'awa ce tasa nake taɓa jikinki, gaskiya kin ban dariya yarinya, ok tinda haka kika ɗauka ki jeki ni kuwa insha Allahu bazan ƙara kusantar ki ba, nigerian hausa fulani girls baƙauyawa...."

yana kaiwa ƙarshen maganarsa yayi ficewarsa daga cikin kitchen rai a ɓace domin ransa ya sosu sosai kawai jurewa ya yi...

ita kuwa Ayush tsabar baƙin ciki durƙusawa tayi a ƙasi ta fashe da wani irin raunannen kukaa...

*🤝 SDEENDTM DATA SERVICES🤝*
*MTN* . *Airtel*
1GB = ₦300. 1GB = ₦300
2GB = ₦600. 2GB = ₦600
3GB = ₦900. 3GB = ₦900
4GB = ₦1200. 4GB = ₦1200
5GB = ₦1500. 5GB = ₦1500

*GLO* . *9MOBILE*
1GB = ₦350. 500Mb ₦500
2GB = ₦700. 1.5GB ₦1100
3GB = ₦1050. 2GB ₦1600
4GB = ₦1400. 3GB ₦2000
5GB = ₦1750. 4GB ₦2500

*VALIDITY: 30DAYS/1MONTH*
For cable subscription or sell recharge card
Call this number or whatsapp
👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽
*🪀08066268951*
𝗔𝗦𝗠𝗘𝗘𝗧𝗔𝗛 𝗡𝗢𝗩𝗘𝗟✍️✍️

*typing📲*

🐅 *MATAR DAMUSAA*🐅
(the wife of a tiger)

*written and story*
*by*
*Asma'u Muhammad Auwal*

( *ASMEETAH NOVEL* ✍️)

*WhatsApp me 09065443871*

*BOOK ONE*⬇️
*97 to 98*

*MATAR DAMUSAA BOOK 2 PAY ONLY 200👌👇👇👇*

*ASMA'U MUHAMMAD AUWAL,*
*9065443871, OPAY BANK.*

*OR*

*ASMA'U MUHAMMAD AUWAL,*
*2267236949, ZENITH BANK*

*SHAIDAR BIYA TA WANNAN NUMBER*
👇👇👇
*09065443871*

https://chat.whatsapp.com/CYC0vxQRZ269ISx36l1Dmt

*NASARA WRITERS ASSOCIATION*
___________________________________
{{ *_Nasara abin so ga kowa, domin marubuta da cigaban rubutu, alƙalaminmu ƴancinmu._* }}
___________________________________

💫💫 *{{N W A}}* 💫💫

بِسْــــــــــــــــــــــمِ اللّهِ الرَّحْمَنِ الرَّحِيْم

𝐔𝐩! 𝐔𝐩!! 𝐔𝐩!!! 𝐇𝐮𝐫𝐫𝐲💃💃💃

𝐒𝐀𝐅𝐍𝐀 𝐆𝐑𝐀𝐏𝐇𝐈𝐂𝐒 𝐃𝐄𝐒𝐈𝐆𝐍.
ᴴᴼᴹᴱ ᴼᶠ ᴳᴿᴬᴾᴴᴵᶜ ᴰᴱˢᴵᴳᴺ
ᵂᴱ ᴰᴱˢᴵᴳᴺ ᴬᴸᴸ ᴷᴵᴺᴰ ᴼᶠ ᴰᴱˢᴵᴳᴺ ˢᵁᶜᴴ ᴬˢ:
LOGO* POSTER* BANNER* 3D MOCK UP LOGO* FLYER* STICKER* PRODUCT STICKER* I.V CARD* I.V VIDEO* BIRTHDAY VIDEO FLYER* PHOTO FRAME* REMOVE BACKGROUND* PROFESSIONAL I.V CARD* SAVE THE DATE* EXPLAINER VIDEO* LYRICS VIDEO AND MORE...
*PLEASE CONTACT* 👉 08148318396 *SAFNA GRAPHICS*.

🌀🌀🌀🌀🌀🌀🌀🌀🌀🌀

Misalin ƙarfe 1 na dare wayar Junaid ne yake bada sautin ƙira, sau biyu ana ƙira yana katsewa ana uku ne sautin ƙiran ya bugi dodon kunnensa wanda tinin bacci ya yi gaba dashi, a hankali yake wutsil-wutsil da idonsa yakai hannunsa kan drower yana lalumen phone ɗinsa, cikin sa'a ya hannunsa ya sauƙa a kan wayar ya ɗaga ƙiran ba tareda ya duba sunan dake rubuce akan screen ɗin wayar ba,
cikin muryar jin bacci ya ce "Hello.." yana lumshe da ido..

"Hy my king kanata shan baccin ka ni kuma ka barni a airport sai faman ƙiran ka nake.."
tayi maganar ne da yaren french.

a hankali ya buɗe eyes ɗinsa ya duba screen ɗin wayar domin ya tabbatar da wa yake wayar, gani ya yi sunan daya saved ya bayyano wato "Girl" Rumana kenam sunan da yake ƙiranta da shi.
murmushi yayi sannan ya mayar da wayar saitin kunnensa cool voice yace "sorry my girl, yanzun kina airport ne?.."
amsa masa tayi! ba tareda ya ƙara cewa komai ba ya katse ƙiran sannan ya miƙe yana hamma domin ba ƙaramin bacci yake ji ba, idanuwansa duk sun ƙanƙance, kai tsaye toilet ya nufa yayi brush sannan ya watsa ruwa a jikinsa shaf-shaf saboda shi a rayuwarsa inba dole ba baya son fita ba tareda yayi wanka ba komin dare..
can bayan wasu mintina ya fito yana ɗaure da towel a kunkuminsa, ya tsane ruwan jikinsa sannan ya shafa mayukansa masu bala'in ƙamshi, ya nufi werdrobe ɗinsa ya zaro ƙananun ƙaya three-quater da rigarsa marar hannu sai da ya ƙara feshe jikinsa da turare kafin ya ɗauki key ɗin motarsa ya zura phone ɗinsa cikin aljihun wandon ya yi ficewarsa,
yana fita harabar gidan kuwa haske ta ko ina kamar ba dare ba, haka ya shige motarsa, horn ya dinga yi wa maigadi amma shuru baccinsa yayi nisa ganin maigadi bashida niyar tashi yasa Junaid fitowa ya buɗe get ɗin da kansa sannan ya yi ficewarsa da gudun gaske..
(wata ƙil baiyi addu'ar fita daga gida ba ma🤔🤔).
Chapter 52 · 0% Book details