← Book details Matar Damusa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 41 OF 58

Sashe 41

Matar Damusa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Junaid ne a zaune fuskarsa ta ƙara haske sai sheƙin da yake, ya kalli Damusar sa da kyakykyawar murmushi a fuskarsa yana shafar gashin Damusar tare da faɗin "my Sujjur sauran mana daƙiƙa 5 mu bar doron duniya gaba ɗaya, akwai wacce ruhin mu yake jikinta kuma ta kasa ceton rayuwar mu, Daƙiƙai 5 suna cika indai bata ceci rayuwar mu ba shikenam munyi bankwana da duniya..
wannan maganganun da yake yi a Damusar yake yinsu, shima Damusa sujjur kamar mutum har da hawayensa, Junaid ne ya rungumi Damusan yana ƙirga mintunan da ya rage musu a duniya....

******
a ɓangaren sarki Raamud shima zama yayi a gaban Damusa ya kifar da kansa akan gwiwowinsa ganin Damusar ya daina shurawa ko motsi baya yi, hakan yasa Sarki Ramud ya fidda rai akan Damusar kuma yana takaicin rashin Junaid da akayi domin ya tabbatar shima Junaid ya mutu tinda har Damusar ya mutu,
Bara'at itama kuka take sosai na rashin Junaid da kuma Damusar, tin tinin ta farfaɗo daga doguwar sumar da tayi, tashinta ta tarar da mummunar labari! duk a cikin su ba wanda ya motsa,
Bara'at ce kawai tayi ƙarfin halin cewa "toh yanzun ya zamuyi da Sujjur?"
Sarki Raamud katse ta yayi da cewa "idan dare yayi zanje na bisine shi.."

******
Shigowar malam cikin ɗaki kenam ya tarar da su Mommy a wannan halin,
shima ya dawo ne domin ya duba jikin Junaid, ƙiran sunan Mommy yayi yace "Hajia Fatima, meya farune na ganku a wannan yanayin?.."
shuru tayi ta kasa cewa komai sai idonta da yake kan Junaid,
Shima Malam ganin Junaid yasa gabansa faɗuwa Rassss!
ya nufo gurin da Junaid yake a kwance yana jijjigarsa amma ko motsi babu, hannu Malam yasa ya rufe masa idonsa sannan yaja masa mayafi ya rufe shi gaba ɗayansa yana faɗin "innalillahi wa inna'ilaihi raju'un,
Kullu nafsin zaa'ikatul maut, kuyi hakuri wanda ya fimu sonsa ya karɓe abunsa, Allah ubangiji yasa can tafi masa nam🙏🙏,
Mommy tana zaune hawaye ne kawai yake go slow akan fuskar ta, daƙer take haɗiyar yawu, zuciyar ta kamar ya fito haka take jinsa...

Ayush ce ta ɗago kanta tana bin Malam da kallo, ga idanuwan ta sunyi lufu-lufu sun kumbura ga sunyi wani irin jaa tsabar kuka,
Miƙe wa tayi ta cakumi gaban gariyar Malam murya a disashe take faɗin
"waya gaya maka Junaid ɗina ya mutu, duk wanda yace Junaid ɗina ya mutu bazan yafe masa ba, ni ce fa zan rigashi mutuwa, ka tasar mun da shi bazai mutu ya barni ba, bacci fa yake yi,....."

Riƙe hannunta Malam yayi yana faɗin "ki kwantar da hankalin ki, kowa ma zai mutu, kema wata rana zaki iso shi idan kwananki ya ƙare.."

daga tsaye ta doku akan gwiwowinta tare da fashe wa da wani irin matsanancin kuka mai raunana zuciya,
a tunanin ta mahaifinta ne ya kashe Junaid, wani irin ƙololuwar baƙin ciki ne ya ziyarci zuciyarta, lokaci guda taji tsanar mahaifinta bata ƙaunar sa, bata haɗa hanya da mungu!
tashi tayi ta fice a ɗakin da gudun gaske tana kuka,

Mommy baki na kakkarwa tace "Malam a ƙira ƴan uwa da abokan arziƙi a sanar musu mutuwar Junaid, ka ƙira sauran malaman su zo a suturta shi, bana so ayi jinkiri, gidansa na gaskiya yafi nan gidan"
murya a sanyaye take magana tana zaune a yanda take ta kasa motsawa,

Malam yayi ajiyar zuciya sannan yace "haka ne, kiyi hakuri daman Allah ya rigada ya rubuta Junaid yana daga cikin matasan cann.."

hawaye yana zubo wa Mommy tace "Malam idan banyi hakuri ba ya zanyi, ban isa na dawo masa da ransa ba, saboda haka hakuri ya zama dole......"
Mommy bata ƙarasa maganar ba suka jiyo ihun Ayush na lokaci guda,
da sauri Mommy ta miƙe ta fice daga ɗakin,
Malam shima bin bayanta yayi yana faɗin "subhanallah me kuma du ya faru.."

Ɗakin Ayush suka shige suna duba ta ganin babu kowa a bedroom Mommy tace "Ina take kuma, ina tsoron kar a kuma rasa rai a cikin gidan nan, mutuwar Junaid ma kaɗai ya isheni.." tana ƙarisa maganar tana kuka sosai,
Malam yace "to ko tana cikin toilet ne ki dubo ta,
Shi dai malam tsoronsa kar Ayush ta cire wannan zoben tinda Junaid ya riga da ya mutu, kar itama ta rasa tata rayuwar..

Bayan Mommy ta shige cikin toilet abunda ta gani ne ya tayar mata da hankali, ta dafa ƙirji tace "nashiga uku, innalillahi wa inna'ilaihi raju'un, Malammm!!!..."

shima da sauri ya shige cikin toilet ganin Ayush kwance a ƙasan tiles ko motsi babu ga kuma jini ta ko ina,
jini ne yake ɓulɓulowa daga cikin cibiyar ta duk ya wanke cikin toilet gaba ɗaya, itama tana kwance cikin jinin tayi jarab da jinin,
hannun Mommy ne yake kakkarwa kamar wacce aka jona wa shocking,
Malam ne ya ɗago ta yana faɗin "mu hanzarta hospital jinin jikinta zai ƙare fa, ɗaukar luɗa yayi mata sannan yayi waje da ita, itama Mommy bin bayansa tayi duk tabi ta ruɗe da haka suka isa harabar gidan suka shige motor gaba ɗayansu, miƙar hanyar da zai sadasu da gate yayi da gudun gaske,
har zasu fita Malam ya sanar da mai gadi cewar kar ya bar kowa ya shugo gidan nan, Baba mai gadi ya amsa masa da toh.."

---------------------> Isar su cikin hospital kenam, likitoci da nurses suka nufi yanda Malam yake ɗauke da Ayush, kwantar da ita akayi akan gadon nan na turawa kai tsaye emergency room aka kaita,
Mommy Office ɗinta ta nufa ta zauna akan kujera ta kifar da kanta saman table tana rera kuka mai cin rai...

*******

Daƙiƙa 5 tana cika Ayush ta finci zoben Dish da ƙarfin gaske cikin zafin nama,
Junaid yana zaune acan sahara shi da Damusar sa suna jiran cikar wahadi, yana lissafin lokaci har sai da yazo kan na biyar kuma na ƙarshe yaga wani haske mai ƙulƙule ya taho kamar walƙiya ya shige jikinsa hasken yabi ta hannunsa ya ratsa jikin Damusar dake hannunsa yana kan Damusa Sujjur,
wani irin baƙin hayaƙi ne yake fita daga jikinsu, har saida wannan hayaƙin ya gama fice wa sannan aka ɓatar dasu, ruhinan ko wannen su ya koma kan gangan jikinsa...

******

Sarki Raamud ne ya tashi yana shirin barin wajen da gawar Damusa yake, har ya bar falon fadar,
Kamar wanda aka zaburi Damusa da ƙarfin gaske ya miƙe tsaye yana karkaɗa gashin jikinsa,
a tsorace Bara'at dake gurin ta ƙwalla ƙiran sarki "Shugabaaa...."

Jin wannan ƙiran yasa ya taho da gudu a tunaninsa MUNAFURR ne ya dawo, ganin Damusa a miƙe ya tashi yasa sarki ya nufi gurinsa da gudu yana faɗin "Sujjurr! Sujjur ka tashi nagode Allah, zunzurutun farin ciki ne kwance saman fuskarsa, yana shafar bayan Damusar,

Ji yayi ya shiga cikin wani irin yanayi da sauri yaja da baya yana faɗin "zoben dish, Ɓingel ta cire.." ya kalli Bara'at yana murmushi, ya kuma cewa "ita ta taimake su, ita ta ceci rayuwarsu, amma kuma ita tana cikin mawuyanci hali..."
kafin ya rufe baki wani baƙin hayaƙi ne shima yake fita daga jikinsa, raɗaɗin da yake ji kamar ƙunar wuta,
ya ƙanƙame jikinsa da hannayensa biyu yana fitar da numfashi sama-sama, ga jijiyoyin jikinsa sunyi burtsi-burtsi shi kaɗai ne yasan irin ƙunar da yake ji a jikinsa,
wannan hayaƙin duk tsafin da yake jikinsa ne yake ta fita..
har shima Damusan yanzu babu wani tsafi a jikinsa,
Sarki Raamud yana cikin wannan halin har hayaƙin nan ya fita gaba ɗaya, yana maida numfashi ya ɗago yana kallon Bara'at wacce ta zuba masa ido tana kallon abun mamaki, ya soma girgiza kai yace "yanzu babu wani abun tsafi da ya ragu a jikina, normal nake yanzu...""
Damusa ne yayi wani irin girgiza sai da wannan macijin da aka wurga masa ya faɗo ƙasi a mace, ...

******

Junaid yana ƙwance saman gado yasa hannu ya yaye mayafin da aka rufeshi da shi, ya tashi cikin hanzari hannun sa yana kan fuskarta sakamakon hasken da yayi masa yawa, daƙer ya buɗe kyawawan eyes ɗinsa fari sol, haske fatarsa ya ƙara fitowa, a hankali yake lumshe ido kamar mai jin bacci ya sauƙar da ƙafafuwansa ƙasan gado, yana miƙa tare da Hamdala ya tashi yana duban kansa,
abunda ya faru dashi ne yake dawo masa kwakwalwa abun yayi matuƙar bashi mamaki, ganin lokaci guda waraka tazo masa,
a hankali yake motsa sweet lips ɗinsa yana faɗin "Deams, mafarki nayi, taya hakan zata faru?..."

yanzu baya jin komai a jikinsa ga wani irin kyau daya ƙara, komai nashi ya canza, hatta sumar kansa yayi tsayi yazo masa kafaɗarsa ga yanda yayi baƙi sai sheƙi yake yi gwanin burgewa,
sajen nan ya kwanta asaman fuskar sa har zuwa gemunsa ya ƙara tsayi ga laushin bala'i baƙi ƙirin sai sheƙi shima yake,
ga ƙaramin baki kamar wanda aka ɗosana! maroon lips ɗinsa ya ƙara fito wa kamar wanda aka shafa maroon stick,
yayi fari sol ya fito asalin kalar iyayensa Bahindiyawa,
he look like his father and d same like sarki Raamud.....
Junaid an dawo masa da cikakkiyar lafiyarsa da kuma ƙirar ƙarfi, ya zama zankaɗeɗe dashi kamar wanda aka ƙara masa tsayi da kuma ƙirar ƙarfi....

*MASHA ALLAH*

*A SAMU A FARA PAYMENT FAH SABODA AN KUSAN GAMA BOOK 1 FREE*

*🤝 SDEENDTM DATA SERVICES🤝*
*MTN* . *Airtel*
1GB = ₦300. 1GB = ₦300
2GB = ₦600. 2GB = ₦600
3GB = ₦900. 3GB = ₦900
4GB = ₦1200. 4GB = ₦1200
5GB = ₦1500. 5GB = ₦1500

*GLO* . *9MOBILE*
1GB = ₦350. 500Mb ₦500
2GB = ₦700. 1.5GB ₦1100
3GB = ₦1050. 2GB ₦1600
4GB = ₦1400. 3GB ₦2000
5GB = ₦1750. 4GB ₦2500

*VALIDITY: 30DAYS/1MONTH*
For cable subscription or sell recharge card
Call this number or whatsapp
👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽
*🪀08066268951*
*ASMEETAH NOVEL✍️✍️*

typing📲

🐅 *MATAR* *DAMUSAA*🐅
(the wife of a tiger)

*written* *and* *story* *by*
*Asma'u Muhammad Auwal*

( *ASMEETAH NOVEL* ✍️)

*WhatsApp me 09065443871*

*Laifin Daɗi qarewa*

*FREE BOOK ZAI ƘARE NE A ƘARSHEN BOOK ONE*

*BOOK TWO DAZAN SHIGA SOON PAID NE,*
*YANA TAFE DA SABON SALO, DA KUMA CAKWALKWALIN CAKWAKIYA, KADA KU BARI A BAKU LABARI DOMIN GANI DA IDO 👀 YAFI JII👉👂*

*MATAR DAMUSAA BOOK 2 PAY ONLY 150👌👇👇👇*

*ASMA'U MUHAMMAD AUWAL,*
*9065443871, OPAY BANK.*
Chapter 41 · 0% Book details