← Book details Matar Damusa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 58

Sashe 4

Matar Damusa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Salati Ayush ta shiga yi tana fad'in "Uma meye haka? Dan Allah ki daina" kuka ne yaci raanta sosai, tazo zata rungumi mahaifiyar tatan. A haukace Uma ta cillata gefe guda tana fad'in "Damusa ce ke! Kar ki ta6ani, Damusa ce ke!! Ta tashi da gudun gaske ta nufi bakin hanya.
Itama Ayush binta tayi tana kuka tana fad'in "Umma Ina zaki je ki dawo dan Allah!.. Kafin Ayush ta sake magana wata karamar motor ce 'kirar Jeep brown colour ta taho da gudun gaske bata Ankara ba tayi sama da Umma, kanta ne yayi mungun buguwa a saman kwalta , kafin kace mai jini kamar anbaliya,
Innalillahi wa inna'ilaihi raju'un daman Umma mutuwa take jira Gashi kuwa rai yayi halinsa, sai ido a bud'e.
Wani irin 'Kara Ayush tayi mai rikitarwa, da gudun gaske ta nufi Uman wacce take kwance ...

Tsugunawa Ayush tayi gaban Uma tana girgiza ta " Dan Allah Uma ki tashi karki mutu ki barni, Idan kika mutu ban San ina zansa kaina baaa" wani irin kuka take na fitar hankali "wayyo Umanaa, ki tashi mana"

Duk kukan da take mai motar yana kallonta ta cikin madubin motarsa ko fitowa bai samu damar yiba,
Motarsa ya fara ja a hankali zai bar wajen!
Cikin 6acin rai Ayush ta mi'ke ta d'auki wani qaton dutsi ta wurga bayan motor da shi, nan take glass d'in motor ta fashe, kansa ne ya bugu da sitiarin motar tsabar burkin daya Danna,

Ransa ne yayi matukar 6aci, DA karfin gaske ya cankar da marfin motar da kafarsa ya fito yana huci.
Itama Ayush gabansa tazo tana fad'in "Kai wani irin Dabban mutum ne Wanda baka San darajan Dan Adam ba, mungu, Azzalumi Mahaifiyata ka buge amma kamar Wanda ka kashe kiyashi,"
Ya kasa juran kalamanta haka yasa hannu ya shaqo wuyanta da karfin gaske, ya d'agata sama da hannu daya, idanuwansa ne suka fara chanza colour,
Ta tsorita sosai da ganin shi haka, ido ta zaro waje tana kakakin mutuwa,
Wani irin shocking yaji yabi jikinsa kamar Wanda ya rungumi electric gass, jiyayi kamar wuta ne yake ci a jikinsa,
Da 'kyarr ya iya wurgar da ita gefe, sauran kad'an ya fad'i 'kasi badon ya ri'ke motarsa da karfi ba, a gigice ya shige cikin motarsa ya figeta da gudun gaske! Shi kad'ai yasan irin rad'ad'in da yake ji a jikinsa, ga hankalinsa ya fara barin jikinsa.

Ayush tashi tayi tangal tangal kamar zata wad'i kasi tayi gurin da mahaifiyar take kwance ta fad'a saman ta, numfashin ta ne ya tsaya cakk, lokaci guda ta sume a gurin.

Motar ce tasau hanya sakamakon ba'a cikin hayyacinsa yake ba, cikin jeji motar ta gangara wata 'katuwar bishiya motar ta daka, kansa ne yayi wani irin buguwa a take shima ya suma.........

Comments and share please 🙏🙏

*Littafi* *na* *daga* *farko* *har* *zuwa* *karshe* *kyauta* *ne*
Fatana Ku kasance cikin farin ciki 😘😘😘

*ASMEETAH* ✍️✍️

Littafi na kyauta ne 👌👌👌

🐅 *MATAR* *DAMUSA* 🐅
(the wife of tiger)

*MALLAKIN*
Asmeetah✍️✍️

*NASARA WRITERS ASSOCIATION*
___________________________________
{{ *_Nasara abin so ga kowa, domin marubuta da cigaban rubutu, alƙalaminmu ƴancinmu._* }}
___________________________________

https://www.facebook.com/103637491942644/

💫💫 *{{N W A}}* 💫💫

بِسْــــــــــــــــــــــمِ اللّهِ الرَّحْمَنِ الرَّحِيْم

Book One
PAGES 11

Kwance take a saman gadon asibiti tana ta sumbatu "Uma! Uma!! Uma dan Allah karki mutu ki barni, Dan Allah Uma ki dawo gareni" tana cikin wannan yanayin hankalinta ya fara dawowa jikinta, ido ta fara bud'ewa a hankali tana ganin Dishi-dishi har idon ya washe
Wata farar Mata ta gani gefen ta tana zaune ta zuba mata ido sai kyakykyawar murmushi dake kwance a saman fuskarta
Tashi ta fara 'ka'karin yi, sai ji tayi matar tace "Sannu ko, ya jikin nakin?"
Tana shirin gyara mata zaman.
Juyowa Ayush tayi tana kallon matar daga bisani tace "Ina Mamana?"
Shafa sumar kanta matar tayi sannan tace "Am sorry my dear, ke kad'ai aka kawo asibitin nan, but mutanen da suka kawo ki sunce already sun sallace Mahaifiyarki bayan sun tabbatar da ta rasu, we're losses your mom"
Fashewa tayi da wani matsanancin kuka tana fad'in "shikenam kin tafi kin barni Uma, Ina Zansa rayuwata, bazan iya rayuwa ba tare dake ba Uma, bani da kowa innalillahi wa inna'ilaihi raju'un" kuka ne yaci raanta sosai.
Rarrashinta Matar take tana bata baki, da haka har Ayush ta samu da dawo hayyacinta, ajiyar zuciya ta shiga ja.
Murya a sanyaye Matar take fad'in "Allah yana tare da ke, insha Allahu bazaki tozarta ba"
Ayush murya Ciki-ciki tace "banida kowa sai Uma na, yanzu Ina zansa kaina"
Ajiyar zuciya Matar tayi ta jawo Ayush jikinta tana shafa bayanta alamar rarrashi sannan tace "meye sunanki?"
"Sunana Ayushmat" atakaice ta bada amsa!
"Shin zaki iya zama a tare da ni?" A cewar matar.
'Dagowa Ayush tayi ta 'kurawa matar ido daga bisani ta mayar da kanta saman jikin matar, batace komai ba.
Matar ce ta sake yin magana tace " no karki damu insha Allah Zan ri'keki tamkar mahaifiyarki, ni sunana *DOCTOR* *FATEEMAH* wannan asibitin da kike gani 's my own, inaso ki kwantar da hankalinki, zaki cigaba da zama dani a gidana". Kafin ta rufe baki taji wayarta tana ringing, d'aukar wayar tayi tare da karawa a kunnenta, ji tayi ance *HAJIYA* *KI* *DAWO* *GIDA* *YANZU* *AKWAI* *MATSALA* daga nan aka katse wayar!

"Ikon Allah meke faruwa ne, kinga Ayush ki jirani Ina zuwa yanzu" ta shafa sumar kan Ayush tare da d'aukar hand-bag d'in ta tana tafiya cikin tsari duk da tana had'awa da Sauri-sauri sai takun takalminta da kake ji qwas qwas qwasss, dan'kararren less ne a jikinta tasha d'inkin Riga da zani sai gyalen data yafa, ko Ina sai 'kamshin turaren jikin ta yake, asalin er washh ce,
Ayush kallon ta take ba 'karamin burgeta Doctor Fatima tayi ba, har sai data 'kule mata kafin da dawo da kallon ta kan ledar ruwan da aka d'aura mata.

Da gudun gaske Doctor Fatima ta shige harabar gidanta da dan'kararren motor ta black colour mai taya ta bayan motar.
En Sanda ta gani su uku sunyi cirko-cirko suna jiran isowarta already mai gadi ya barsu sun shigo cikin gidan, cikin tashin hankali ta nufi gurinsa tana fad'in "lafiya kuwa na ganku a cikin wannan yanayin?" Ta 'karasa maganar tana kallon Ogan nasu.
Ogan ne ya bada umarni cewa "a fito da shi"
Doctor Fatima ce ta maida kallon ta kan Wanda za'a fito dashi daga cikin motor,
Lokaci guda ta furta "innalillahi wa inna'ilaihi raju'un *JUNAID* , maiya faru da shi? ya naga jini a saman kansa? mai kuka mishi? Wayyo Allah na Junaid, Allah yasa dai ba ciwon naka bane ya tashi" tana zubda hawaye tana sumbatu.
Wani daga cikin en sanda ne yace "Hajiya wad'annan tambayoyin nakin bazasu amsu ba anam sai mun shiga daga ciki tukun"
A gigice Doctor tace "to to toh mu je mana jini yanata zuba masa"

Ayush kuwa dake kwance saman gadon asibiti ta 'kudurta a raanta a cewa duk Wanda yayi sanadiyar mutuwar mahaifiyarta sai ta d'auki fansa,
Jinin mahaifiyata bazai zuba a banza ba.....

*ASMEETAH* ✍️✍️

*LITTAFI* *NAH* *KYAUTA* *NEH* 👌👌👌

🐅 *MATAR* *DAMUSA* 🐅
(the wife of tiger)

*MALLAKIN*
*ASMEETAH* ✍️✍️

*NASARA WRITERS ASSOCIATION*
___________________________________
{{ *_Nasara abin so ga kowa, domin marubuta da cigaban rubutu, alƙalaminmu ƴancinmu._* }}
___________________________________

https://www.facebook.com/103637491942644/

💫💫 *{{N W A}}* 💫💫

بِسْــــــــــــــــــــــمِ اللّهِ الرَّحْمَنِ الرَّحِيْم

*BOOK* *ONE*
*PAGE* 12 to 13

Wani katafaren gado na alfurma aka kwantar da Junaid yayi Jina-jina goshin nan a fashe sai tsiyayar da jini yake, da gudun gaske Doctor Fateemah ta nufi d'akin medicine cikin gaggawa ta dawo hannun ta ri'ke da akwatin boxes, nan take ta fara treat dinsa, duk kayinsa sai data zagaye shi da bandeji tare da yi masa allurai,
Sai da ta kammala yimasa magani sannan ta maida hankalinta kan en sandan da suka kawo shi,

"Nagode muku da taimakon gaggawar da kukayi masa, ba karamin wahala yasha ba" ta 'karasa maganar tana goge kwallar da ya zubo Mata.

Ogan cikinsu ne yace "ki godewa Allah Hajiya, Allah ne ya kaimu gurin da yake har muka tsinto shi,
Munje yawon patrol ne cikin wani daji, munga bayan glass din motor a fashe sannan ya daki wata 'katuwar bishiya, a gaskiya bamuyi tunanin zamu ga Junaid ba a wannan yanayin" anan Dan Sandan ya tsayar da maganar sa saboda bayan haka basu San maiya faru da shi ba.

"Ni daman nasan za'ayi haka, Junaid baya jin magana, duk abunda ya 'kudurta a ransa cewa zaiyi to ba wanda ya Isa ya hanashi, hakan zaiyi sanadiyar tashin hankalin kowa,
Yace mun zaije gidan Barrister Ahmad abokin Mahaifinsa! Na dakatar da shi akan kar yaje amma yayi kunnen 'kashi, gashi yanzu abunda ya faru dashi,
A tunani na duk kwana biyun nan a gidan Barrister yake ashe yana jeji rai a hannun Allah..."
Lokaci guda ta fashe da matsanancin kuka "yaaa Allah ka magance mun ciwon dake jikin yarona, shi ba DAMUSA ba, shi ba MUTUM ba".
Magana take a cikin kuka, ta kafa gwiwowinta 'kasi Kai a sunkuye take kuka mai 'kona zuciya.
(Ko ba'a gaya muku ba Doctor Fatima tana cikin mawuyancin hali na rashin lafiyar Junaid).

Duk en Sandan dake waren ba wanda baiji tausayin Doctor Fatima ba
Cikin Rarrashi Ogan yake fad'in "kiyi hakuri Hajiya duk tsananin ciwo yana da magani, insha Allahu Oga Junaid zai samu sau'ki,
Shawaran da zamu baki shine, ki ringa kula da shi sosai , duk yanda za'ayi kar kina barinsa yana fita, tinda a kowani lokaci ciwonsa zai iya tashi.....

Sufa d'aya *JUNAID* yayi daga kwance ya cakko wuyan Dan Sandan bai 'karasa maganar ba.
A wani irin yanayi Junaid yake kallon cikin idanun Dan Sandan da ya zaro ido waje tsabar sha'kar da yayi masa,
Chapter 4 · 0% Book details