← Book details Matar Damusa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 58

Sashe 3

Matar Damusa Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read

yasha, atake Damusan ya samu lafiya ya mi'ke, jinin Junaid yana gudana ne a jikin Damusan, Shiyasa da zaran ran Damusan ya 6aci shikenam za'a nemi hankalin Junaid a rasa", Tashin Hankali ya Junaid zai kasance??? Labari Umma take badawa! "Tin lokacin da Damusa yasha jinin Junaid daga lokacin Junaid ya zamo 'Karfafan Namiji, yanzu shekarunsa 30 cif Amma bai San sha'awa ba, ko kallon mace bayayi balle yaji sonta a ransa, sun gusar masa da duk wani tunaninsa, Idan ran Junaid ya 6aci to kowa ya shiga uku, domin zai iyayin kisan Kai ba tareda saninsa ba, Zai zamana duk wani ire-ire na Damusa zai rinka yinsa hatta kalar kukan Damusa zai rinka yinsa tareda gurnani kalar na namun daji, Idanunsa zasu koma irin na Damusa, kukansa irin na Damusa, sannan ko wani lokaci zai rinka jin kamshin mutum, ga 'karfi ba'a magana duk da saninsa danayi yana yaro 'karfin bala'i gare shi, ya 'Karfinsa zai kasance yanzu kuma? Hakan yasa bashida Aboki ko d'aya, daga shi sai mahaifiyarsa ita ke kula dashi, duk da kudin da suke dashi nasan bata cikin kwanciyar hankali, malumai da dama sun kasa ceton Junaid a halinda yake ciki, Junaid yana zama cikin hankalisa amma duk sanda Damusan ya motsa masa tofa ba zaman lafiya, kowa tsere mishi yake sai dai idan anyi gaggawar d'aureshi da igiya mai karfin gaske," Umma tana zubda hawaye tana fad'in "ni dai nasan Damusan bazai bar jikin Junaid ba, duk sanda Damusan nan ya mutu shikenam shima Junaid mutuwa zaiyi" Ayush kam tayi sumar zaune idon ta ya 'kame 'kam ko 'kifta su batayi, Umma ce ta bubbuge kafad'arta sannan tayi firgitt ta dawo daga sumar zaunen, Tsananin tsorone ya bayyana a fuskar Ayush jin yanayin da Junaid ke ciki duk da bata sanshi ba amma tana jin fargabar haduwa da shi "hatta idanunsa komawa yake irin na Damusa?". Tayi tambayar a ranta tareda jinjina kai , Ayush ce ta maido hankalinta kan mahaifiyarta sannan tace "Umma kenam bashida magani shi ciwon Junaid din?" Wani irin murmushi Umma tayi mai 'kona rai sannan tace "akwai mana, warakar ciwon Junaid yana a jikin ki" Wani irin had'iyar yawu Ayush tayi ido waje tace "Umma meyasa duk wani tsafinsu yake jikina, shin meye abun dake jikina?" Tace "ba nace miki raunin mahaifinki yana jikinki ba, to haka shima Damusan tsafinsa yana jikin mahaifinki, da zarar kin cire wannan abun dake jikinki shikenam kin lalata komai, kin tarwatsa mahaifinki sannan kuma Damusan shima tsafinsa zai lalace da zaran tsafin Damusan ya lalace kuma shikenam Junaid zai samu lafiya, Damusan zai fita daga jikinsa, Sai dai hakan zaiyi matukar wahala saboda dole saikin zubda jininki sosai kafin abun ya fita daga jikinki hakan kuma zai iya jawowa ki rasa rayuwarki" Fashewa Ayush tayi da kukan gaske tana fad'in "Umma ki gaya mun abunda ke jikina, wallahi nayi Alkawari ko zan rasa rayuwata saina tarwatsa tsafin mahaifina sannan na ceto rayuwar Junaid" kuka takeyi sosai. Cikin lallami Umma take fad'in "Zan gaya miki Ayush, badon zaki raunana ba dana dad'e da cire miki saidai mahaifinki bazai bari hakan ta faru ba, saboda hatsabibin boka ne, Amma Zan gaya miki kodan saboda rayuwar Junaid", Tana zubda hawaye tace " *AYUSHMAT* wannan abun tsafin ba komai bane face abunda ke jikin!! Bata 'karasa maganar ba taji an sha'ko mata ma'kogaro, numfashi Sama-sama Umma take ta zaro ido waje, Ji tayi daga sama ana magana cikin tsawa " *KEE* *BARA'ATU* *NI* *ZAKI* *CIWA* *AMANA* *A* *GABAN* *'DIYATA* *ZAKI* *TONA* *MUN* *ASIRI*, *ZAKI* *MUTU!* *ZAKI* *MUTU!!* *ZAKI* *MUTU!!!* *HAHAHA*, *HAHAHAHA*, Dariya ne mai rikitarwa, nan take ta rasa hankalin ta, Itama dariyar ta farayi, tana tafa hannayen ta biyu tare da fad'in " *Junaid* *Damusa* *wayyo* *Damusa* *kamoshi* *naan*" haka ta rinka Maimaitawa tana kwashewa da dariya, alamu sun nuna cewa Uma ta haukace.
Chapter 3 · 0% Book details