← Book details Matar Damusa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 58

Sashe 5

Matar Damusa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Idon Junaid ne ya koma kalar ta Damusa, ba alamar d'igon ba'ki a cikin idon, gurnani yake irinta zakunan da suka samu nama, jijiyoyin jikinsa ne suka tashi tin daga saman kansa har 'kasin sawayensa sunyi tsirbo-tsirbo, sumar kansa dake kwance duk sun tsaya Cirko-cirko, da iya 'karfinsa ya d'aga Dan Sandan nan sama da hannu d'aya, still hannunsa yana sha'ke da wuyansa,
sai 'Kafar Dan sandan da yaketa lilo yana 'ko'karin ceton kansa amma ya kasa hakan, numfashinsa ya tsaya cakk 'karfinsa ya sake babu wani 'karfi a tattare da shi.

Tin farkon al'amarin sauran en sandan da sukaga hakan suna ja da baya har suka fece kowa 'ko'karin ceton ransa yake,

Ita kuwa Doctor Fatima ba abunda take sai ihu, tana 'kwalla 'kiran security na gidan amma basu jiyota ba,
Su dai sunga en sanda sun fita da gudu ko motarsu basu tsaya d'auka ba,
Amma kwata-kwata basuyi tunanin dubowa mai ke faruwa ba,
Domin sune masu aiki akan Junaid da zarar ciwon nan ya tashi,
B-guard ne Doctor Fatima ta samosu saboda Junaid tana biyansu salary duk wata,
Wasu Mazaje ne Manya-manya masu 'kirar 'karfi, irin American man din nan ba'ka'ke ne wuluk ga tsayi ga 'karfi, idan suna tafiya jikinsu har rawa yake,
Kana ganinsu kasan ba 'karamin motsa jiki suke ba.
Irin yasu su hudu ne a cikin gidan, amma duk 'karfin su da 'kyar suke danne Junaid 'kasi idan zasu d'aure shi muddin in ciwonsa ya tashi.

Junaid fa ya kusan yin kisan kai,
Daga gurnani har ya koma ihu irin na Damusosi,
Wani Dabara ne yazo wa Doctor Fatima jiki na rawa ta d'auki Allura ta zu'ki magani mai sa bacci cikin en mintina,
Hakan kuwa tayi cikin 'karfin hali ta caka masa wannan alluran ta bayansa,

Lokaci guda yasau wuyan Dan sandan yarafff ya fad'i 'kasi,
Juyowa yayi a gigice ya kai hannu ya sha'ko wuyan Mahaifiyar tashin yana 'Kara zaro dodonnin idanuwan na shin ya fara gurnani ciki-ciki har jikinsa ya sake shima fad'uwa yayi Allurar ya ratsa jikinsa,

Shafa wuyanta ta shiga yi tana maida numfashi,
Da 'kyar ta nufi gurin Dan sandan dake kwance ya suma, da gudu ta shige cikin toilet d'in Junaid ta d'aibo ruwa a bottle tana yayyafa masa, a gigice ya tashi zaune yana maida numfashi sama-sama, ya samu kansa a cikin wani irin firgici da tashin hankali ya waiga gefen dama da hagun ya tabbatar a free yake, wani irin mi'kewa yayi da gudun gaske ya bar d'akin kafin kace bismillah har ya wuce security ya bud'e get a d'ari ya bar gidan, motarsu kuwa still tana nan bai saurareta ba.

Security suna ganin hakan suka nufi 'katon falon gidan daga nan suka haura up stair yanda zai Kai ka d'akin Junaid,
Samun Doc. Fatima sukayi tsugune a gaban Junaid tana ta rera kukanta, shi kuwa yana kwance 'kasi bacci mai nauyi ya d'auke shi.

"Lafiya kuwa Hajiya? Kodai Tiger ne ya samu matsala"

Dake sunansa Tiger a wurinsu, Direct sun tabbatar da Tiger ne shi domin basu ta6a ganin ikon Allah nan ba, in ba a film ba.

Cikin sheshshekar kuka Doc. Tace "na mishi Allura babu wata matsala yanzu, you can go"

Suka amsa mata da "OK" sannan suka koma gurin tsayuwarsu.

Bayan ta gama kukanta ta rarumi wayanta tayi dialing call wata number
Lokaci guda ta Kara a kunnenta murya 'kasa-'kasa tace "please I wanna that girl to come my house right now"
Daga 6angaren d'ayan shima yayi magana,
Sai ji nayi ta kuma cewa "yeah! Her Name is Ayushmat, room 4."
Lokaci guda aka bata amsa ta katse 'kiran.

Mi'kewa tayi tabar room d'in
'Dakinta ta mi'ka jikinta duk sun mutu ga wani matsanancin ciwon Kai dake damunta, toilet ta shiga ta watsa ruwa a kanta, ta fito jikinta d'aure da towel ko shafa mai bata tsaya tayiba ta zura doguwar riga marar nauyi mai hannun breziya, fad'awa tayi saman 'katoton gadon ta bacci ne yayi awun gaba da ita.

A can asibiti kuwa murna Ayush ta shigayi za'a kawota gidan Doctor Fatima,
"Daman kuwa har na gaji da zaman asibitin" tana fad'in hakan tare da shigewa cikin motar da za'a d'auketa.

Cikin 'kan'kanin lokaci suka iso gidan, horn sukayi mai gadi ya bud'ai musu daman already sunsan da zuwansu,
Mi'kewa motar tayi har sai data je gurin parking tukun,
Doctor Hasheem yayi mamakin ganin motar police a gidan amma sai dai ya kafse kawai baice komai ba.

Har cikin falo suka shiga amma basu tarar da kowa ba, sallama Doctor Hashim yayiwa Ayush sannan yayi tafiyarsa,
Ba komai ne yasa Doctor Hashim tafiya ba illa tsoron Junaid.

Guri Ayush ta samu ta zauna cikin d'aya daga cikin jerin kujerun falon,
Tana ta kallace kallace,
Flowers dake manne a jikin bangon d'akin ne yaja hankali ta zuwa gurin
Ba karamin burgeta flowers sukayi ba,
Ita kad'ai take sau murmushi a kan kyakykyawar fuskarta har sai da dimple d'inta ya lotsa.

Bata ankara ba taji wani irin gurnani ta bayanta irin na namun daji,
A tunanita a cikin television ne ake nuno namun daji,
Sai tada juya zata koma gurin mazauninta karaff ta had'a ido da Junaid tiger still yana wannan yanayin nasan
Idanunsa kuwa irin na asalin *TIGER*
ya tsaya cakk yana mata wani irin kallo kamar wanda ya samu nama.

Tsoro ne ya bayyana a fuskar Ayush
Wani irin 'Kara tayi mai toshe kunne a take ta sume a gurin yaraff ta fad'i 'kasi.

Duk mutanen gidan naan ba wanda baiji ihun Ayush ba
Hatta Doc.Fatima da take bacci saida ta razana da wannan ihun......

*ASMEETAH* *CE* ✍️✍️✍️

*FREE* *BOOK*

🐅 *MATAR* *DAMUSA* 🐅
(the wife of tiger)

*MALLAKIN*
*ASMEETAH* ✍️✍️

The writers of...

1️⃣ Ikram ko Kausar.
2️⃣ Rayuwar Siyama.
3️⃣ Baby Ogah.
4️⃣ Yayana Zan Aura.
At now
5️⃣ *MATAR* *DAMUSA*

*🤝 SDEENDTM DATA SERVICES🤝*
*MTN* . *Airtel*
1GB = ₦300. 1GB = ₦350
2GB = ₦600. 2GB = ₦700
3GB = ₦900. 3GB = ₦1000
4GB = ₦1200. 4GB = ₦1300
5GB = ₦1500. 5GB = ₦1600

*GLO* . *9MOBILE*
1GB = ₦350. 500Mb ₦250
2GB = ₦700. 1GB ₦500
3GB = ₦1050. 2GB ₦1000
4GB = ₦1400. 3GB ₦1500
5GB = ₦1750. 4GB ₦2000

*VALIDITY: 30DAYS/1MONTH*
For cable subscription or sell recharge card
Call this number or whatsapp
👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽
*🪀08066268951*

*NASARA WRITERS ASSOCIATION*
___________________________________
{{ *_Nasara abin so ga kowa, domin marubuta da cigaban rubutu, alƙalaminmu ƴancinmu._* }}
___________________________________

https://www.facebook.com/103637491942644/

💫💫 *{{N W A}}* 💫💫

بِسْــــــــــــــــــــــمِ اللّهِ الرَّحْمَنِ الرَّحِيْم

*BOOK* *ONE*
*PAGE* 14 to 15.

Ayush tana kwance saman gadon Doctor Fatima tin sumar nan datayi bata farfad'o ba,
Abin duniya yabi ya ishi Doc. Fatima itama tana zaune a bakin gadon da Ayush take, tana dafe da goshinta Kai a sunkuye, "Allah yasa dai ba wani abu yaron nan yayiwa yarinyar ba" tana maganar zuci.

"Dodo, wayyo Dodo zai kamani, gashi nan idonsa wani iri, wayyo Allah na, Ku fitar dashi daga cikin gidan nan banason ganinsa". Ayush ce ta farfad'o tana wannan sambatun

"Lafiya kuwa Ayush meyake damunki ne haka kodai kina tunowa da mahaifiyar ki ne?". Ta rirri'keta domin taga niyyar ta so take ta gudu tsabar tsoro.

Ayush tana maida numfashi sama-sama kamar wacce tayi gudu
"Wayyo Alhamdulillah, mafarki nayi ashe" ta juyo tana kallon Doc. Fatima gumi duk ya ji'ke mata KO Ina kamar wacce ta fito daga wanka, duk A.C dake d'akin amma ko kad'an bata jin wannan sanyin AC.

Doc. Fatima itama amsa ta bata cewa "e fa mafarki kikayi, ki kwantar da hankalinki ba abunda zai sameki,
Yanzu dai tashi ki shiga toilet kiyi wanka sannan ki ci abinci saina kaiki d'akin da zaki zauna"

Mi'kewa Doc. Fatima tayi tare da nufan gurin da jerin kayanta suke tana fad'in "Bari na za6a miki kayan da zaki saka kafin gobe muje shopping"

Mi'kewa Ayush tayi ta tsaya cak, tana sa'ke- sa'ke a ranta!
Ji tayi ance go and enter mana.

"To inane Band'akin?". Tayi maganar a shagwa6e.

Murmusawa Doc. Fatima tayi sannan tace "muje na nuna miki abubuwanda zakiyi using dasu"
Tare suka shiga toilet.
Ta bata Brush wanda zata wanke bakinta, ta nuna Mata yanda zatayi using da shower idan tana bu'katar tayi wanka da shi, idan kuma seat-B zatayi duk ta nuna mata, kafin nan ta fito, already ta fitar da kayanda Ayush zata sanya.

Falo ta nufa daga nan ta wuce side din Junaid Wanda tin lokacin da Ayush ta sume masa daga nan ya dafe goshin sa, kan sa ne yad'au zafi sai masifar ciwon da yake yi,
Daman duk lokacin da zai dawo hayyacinsa sai kayinsa da goshinsa sunyi ciwo kafin.
Alluran da Mom d'insa tayi masa da'ace ya juma da yin baccin zai iya tashi cikin hankalisa ba tare da ciwon Kai ba, domin kwakwkwalwarsa ce ta samu Hutu a wannan lokacin,
Ba haka kawai ya tashi daga baccin nan ba
Kwata-kwata bai dad'e da Fara baccin ba ya soma jin qamshin jini mai dad'in gaske da kuma ratsa zuciya,
A cikin baccin yake bud'a hanci yana shan-shane shan-shane, lokaci guda kuwa ya mi'ke daga baccin yana tafe a hankali yana bin wannan qamshin jinin nan kamar Karen da yake bin mushe.

Yana sau'ka a up stairs jikinsa ba 'kwari ga dafin alluran da Doc. Fatima tayi mishi ga kuma qamshin jinin da ya 'Kara kashe masa jiki,
Ido kuwa like tiger still bai washe ba.
A haka har ya iso daf da Ayush yana bibiyar jinin jikinta, ita kuwa flowers sun d'auke Mata hankali..............

Tana sumewa a gurin kuwa nan take ya dawo hayyacinsa, ya dawo asalin JUNAID d'insa,
Yana dafe da goshinsa yake bin ko Ina da kallo, kamar komai na gidan ya dawo masa sabo, bai Lura da Ayush dake kwance a 'kasi ba sai daya juya zai bar gurin sannan kyawawan idanunsa suka sau'ka akanta dai dain lokacin Sucuirity sun shigo falon jin ihun da sukaji itama sai ga Doctor Fatima ta nufo waran da gudu tana fad'in "lafiya kuwa mai yake faruwa a gidan"
Junaid binsu yake da kallo d'aya bayan d'aya still ya maida kallonsa kan Ayush tare da fad'in "Mom! Who's dis girl?? Yayi tambaya tare da Kai idonsa kan Mom d'insa.

Security kuwa komawa sukayi tinda komai normal Tiger ya dawo Mutum.
Chapter 5 · 0% Book details