← Book details Matar Damusa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 39 OF 58

Sashe 39

Matar Damusa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Laila ce ta ɗebi madarar a spoon ta kai saitin bakin Junaid da sauri ya kawar da kansa gefe ganin ba Ayush ba ce, tayi akan ta bashi madaran nan amma Junaid yaƙi buɗe bakin,
ƙololuwar baƙin ciki ne ya ishi Laila kamar zata rausa ihu haka ta ajiye cup madarar a saman gado ta tashi, sai data taka ƙafar Ayush kafin ta wuce ta zauna akan kujerar ɗakin,
girgiza kai kawai Ayush tayi ta koma ta zauna ɗaukar cup tayi ta cigaba da bawa Junaid madarar yana buɗe bakin a hankali yake motsi da bakin, da zarar madarar ya ɓata masa bakin sai ta sa handkerchief ta goge masa,
Laila da Doctor takaici kamar ya hallaka su da kuma kishi, duk babu wanda yayi magana a wani har sai da mommy ta shugo tana faɗin "ha'a Laila Autar mu yau kece a gidan namun..? shuru Laila bata kulata ba tanata turo baki, sai da Dr yayi ƙarfin hali yace "wallahi kuwa mommy munzo duba jikin ogah Junaid ne"
mommy tace "ayyah ai kuwa kun kyauta ga Junaid jiki da sauƙi"
ta kalli Ayush tace "Ayushert kije ki ɗebi abinci kici kina zaune da yunwa a jikinki, kawo madarar zanyi feeding ɗinsa"
miƙe wa Ayush tayi ta fice daga ɗakin, itama Laila tsabar neman masifa tashi tayi tana cewa "nima yunwa nake ji bari naje naci..."
tazo fita kenam Dr ya riƙe hannunta yana girgiza mata kai, cikin zafin rai ta finciki hannunta tana gunaguni ta fice a ɗakin...

samun Ayush tayi a kitchen tana faɗin "ƴar matsiyata an samu guri, Yayana ya sanar mun cewa Mommy ce ta temake ki bakida kowa baki da komai, daman daga gani ke ƴer matalauta ne.."

Juyo wa Ayush tayi da murmushi saman face ɗinta tana fuskantar Laila tace "ok kinyi ƙoƙari fah, na gaishe ki.." tana kaiwa haka ta juya ta cigaba da yin haɗin kayan abincin da take son ci..
ran Laila ne yayi matuƙar ɓaci tace "ke matsiyaciya banda ƙaddara mai Yayana zaiyi dake ma har yake wani nace miki, idan kinga budurwarsa haɗaɗɗiyar balarabiya sai kin kama baki saboda ta fiki komai, kuma nazo naga kinata shishshigi wa Oga Junaid, toh wai ke banda ƙwacen samarin mata ba abunda kika iya ne? kin ƙwace wa Maimoon Doctor Hasheem sannan nima kina shirin ƙwace mun Junaid to ina zaki kai su...."

Ayush juyo wa tayi tana dariya,
dariya sosai take yi har da kama ciki,
kuma darinyan yayi matuƙar mata kyau tinda take bata taɓa yin dariya irin ta yau ba duk da damuwar da take ƙunshe dashi haka ta cigaba da yin dariyan tana nuna Laila da yatsa, da ƙer ta iya dakatar da dariyan ta kama kugu tana juyawa cikin salo kamar wacce take gaban namiji tace "toh ya kika ganni! shin akwai mata macen data fini komai? gaskiya bana tunanin haka domin inda ace yarinyar can ta fini komai da Doctor Hasheem bai gujeta ya koma kaina ba, kodai farin jini nane yayi yawa haka, wow gashi inata rikirkita mazan mutane wasu suna barin ƴan matan su suna dawowa kaina wooo ni Gimbiya Mayushert Ɓingel Abbanta ta ƙarasa maganar tana ƙwashe wa da dariya.."

Baƙin ciki duk yabi ya ishi Laila ji take kamar ta shaƙeta , ta ja dogon tsuka tana faɗin "da ba'a san asalin ƙarago ba sai ya ce shi ɗan kamfani ne, meye haɗinki da masarauta har kina ƙiran kanki da wani Gimbiya matsiyaciyar banza, to inaso ki sani Oga Junaid yafi ƙarfin ki, gwara ma ki kama Doctor shima manage zaiyi da ke wannan kuma ki kiyayi haɗuwar ki da Maimoon domin kararayaki zata yi, munafukar banza son maso wani ƙoshin wahala..."

Ayush murmushi tayi sannan tace "eh naga alama Yaya Junaid yana matuƙar ƙaunar ki tinda har kika bashi abinci a baki yaƙi ci ya kawar da kansa gefe idonsa kuwa akaina.."

Kawar da kai Laila tayi gefe cikin takaici ta nufi gurin electric gas ta tsaya sannan ta kunna! idonta yayi jawur ga hawayen dake tsiyaya daga cikin eyes ɗinta tace "idan kina son ranki da lafiyarki ki rabu da Oga Junaid domin shiɗin nawa ne...."
ita ma Ayush matsowa daf da Laila tayi ta zazzaro manya-manyan eyes ɗinta sannan tace "idan kuma naƙi fah?..."
Laila ce ta hura iskar bakin ta sannan ta juyo a wahalce ta cafki hannun Ayush ta ɗora akan electric gas wanda ya yi jaaa kunnawan da tayi,
wani irin ƙara Ayush tayi sai da Mommy da Doctor suka razana da gudu suka sauƙo downstairs kai tsaye kitchen suka nufa,
banda Junaid wanda aka barshi a zaune saman gado, shima saida ƙirjinsa ya buga jin ihun Ayush gashi ba halin tashi balle yaje yaga abunda yake faruwa ba kuma magana sai hawayen da ke zuba daga cikin ƙwayar idanuwansa,

shigar su kitchen suka tarar da Laila ta danna hannun Ayush kan electric taƙi ɗaga hannun,
ita kuwa Ayush har ta fara shiɗe wa da ƙer Doctor ya finciki Laila ya zabga mata mari har sau uku ya jefar da ita ƙasi, bakin ta kuwa ya gagara mutuwa sai cewa take "sai dai ka kashe ni wallahi indai akan Oga Junaid ne, sai na hallaka ta! akan wannan matsiyaciyar zaka dake ni....." ta fashe da kuka.

Mommy kuma rungumar Ayush tayi sosai tana riƙe da hannunta duk fatar hannun ya ƙoƙƙone, sai naman hannun kake gani ta gagara yin kukan ma sai shiɗewar da take yi, ta kwantar da kanta saman kafaɗar mommy....

miƙewa Laila tayi tana faɗin "wannan raɗaɗin da kike ji a hannunki haka nima nake ji a cikin zuciyata da zarar an kusanci Oga Junaid, tana kaiwa haka tayi ficewar ta daga cikin kitchen....

*🤝 SDEENDTM DATA SERVICES🤝*
*MTN* . *Airtel*
1GB = ₦300. 1GB = ₦300
2GB = ₦600. 2GB = ₦600
3GB = ₦900. 3GB = ₦900
4GB = ₦1200. 4GB = ₦1200
5GB = ₦1500. 5GB = ₦1500

*GLO* . *9MOBILE*
1GB = ₦350. 500Mb ₦500
2GB = ₦700. 1.5GB ₦1100
3GB = ₦1050. 2GB ₦1600
4GB = ₦1400. 3GB ₦2000
5GB = ₦1750. 4GB ₦2500

*VALIDITY: 30DAYS/1MONTH*
For cable subscription or sell recharge card
Call this number or whatsapp
👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽
*🪀08066268951*

*ASMEETAH NOVEL✍️✍️*

typing📲

🐅 *MATAR* *DAMUSAA*🐅
(the wife of a tiger)

*written* *and* *story* *by*
*Asma'u Muhammad Auwal*

( *ASMEETAH NOVEL* ✍️)

https://chat.whatsapp.com/CYC0vxQRZ269ISx36l1Dmt

*WhatsApp me 09065443871*

*NASARA WRITERS ASSOCIATION*
___________________________________
{{ *_Nasara abin so ga kowa, domin marubuta da cigaban rubutu, alƙalaminmu ƴancinmu._* }}
___________________________________

https://www.facebook.com/103637491942644/

💫💫 *{{N W A}}* 💫💫

بِسْــــــــــــــــــــــمِ اللّهِ الرَّحْمَنِ الرَّحِيْم

*BOOK ONE*
🅿️ -------> 79 & 80 <-------

💫✨.
"A gaskiya Laila baki kyauta ba, saboda rashin Imani da kuma rashin tausayi ki ɗauki hannun mutum mai rai ki ɗora akan wuta? ina ganinki mai hankali..."
A wannan lokacin ran mommy yayi matuƙar ɓaci, ta rinƙa surutai tana balbalawa Laila masifa,
cikin ɓacin rai Laila ta tashi tana gunaguni ta yi hanyar waje zata tafi,
ita kuwa Ayush tana can medicine room ita da Doctor yana duba mata hannun...

yana riƙe da hannunta ya gama ɗaure mata shi da bandeji bayan ya yi treat ɗinta,
"kiyi hakuri Ayushert bansan haka zata faru ba wallahi da bazan barta ta biyo ki ba, yarinta ne yake damun Laila! please forgive her.."

murmushi Ayush tayi sannan tace "babu komai ya wuce, nasan duk akan Yaya Junaid tayi mun haka, but shawarar da zan bata shine taso mai sonta, ta daina son maso wani ka sanar mata saƙo daga Ayushert, na barka lafiya..."
ta fizge hannunta da ya riƙe tayi ficewar ta daga cikin room, zuciyarta cike da ɓacin rai,
kuma abunda ya ƙara ƙona mata rai shine abunda Doctor ya gaya mata wai Laila yarinta ne ke damunta,
tana tafe hawaye na zubo mata ta rasa mai ke mata ciwo a jiki,
shigar ta cikin falo kenam ta tarar da mommy zaune tayi tagumi, ganin Ayush yasa tayi firgitt ta tashi tana faɗin "Ayush yadai hannun nakin, anyi gyaran ko mugani.." mommy ta kamo hannun Ayush ta kuma cewa "Allah sarki ki duba kiga fa duk da an manne hannun da bandeji amma wanda ya gani yasan ba ƙaramin ciwo bane...

Ayush tana kwance saman sofa a falo kanta kuwa yana kan cinyar mommy tana mata wasa da sumar gashin ta, Doctor ne ya shugo idon sa kuwa akan Ayush, yana faɗin "toh mommy ni zan wuce, dan Allah ayi hakuri akan abunda Laila ta aikata..."

Mommy tace "ba komai tsautsayi ne, kuma kowa baya tsallake ƙaddararsa,
kayi mata allura ne..?"

"Eh nayi mata allurai guda biyu sai maganin da tasha insha Allahu zuwa gobe zata samu sauƙi.."
Mommy tace "toh shikenam Doctor, Laila ta yi zuciya ta tafi gida, amma ka rinƙa mata nasiha akan sha'anin rayuwa kar ta rinƙa biye wa zuciya domin zata kaita ta baro ta ne..."
Doctor ya amsa mata da "to ba damuwa Mommy insha Allah zanyi iya ƙoƙarina akanta, nagode" cikin girmamawa ya yi mata sallama idonsa kuwa akan Ayush wacce ta kifar da kanta saman cinyar mom ko kallonsa batayi ba...

*****

Sarki Raamud yana zaune a saman gadon su ya naɗe ƙafafuwa kamar mai zaman cin tuwo, ya riƙe hannunsa na hagun, shi kaɗai ne yake jin wannan raɗaɗin da yake ji bayan Ayush!
tafin hannunsa ya yi jawur, ƙonuwar da Ayush tayi ne shima ya shafe shi sai dai shi bai nuna ƙonuwa ba amma gurin yayi jawur dashi,
Bara'at tana zaune daf dashi sai dumama masa hannun take da ruwan zafi, tana faɗin "kayi hakuri shugaba, wannan ciwon nakan lokaci guda ni na rasa gane maka..."

yana ajiyar numfashi yace "meya faru da Ɓingel ɗina? na tabbata akwai wani mummunan abu daya faru da ita.." ya ƙarasa maganar yana duban hannunsa wanda ya nuna alamun ƙonuwa.
Da mamaki a fuskar Bara'atu idonta akan sarki tace "daman Ayush bata mutu ba??"

kallonta sarki yayi da ɓacin rai yace "Ɓingel bata mutu ba, kuma bata cire zoben dish a cibiyar ta ba, idan kuma kinason ganin bayanta bismillah.." ya ƙarasa maganar yana nuna mata hanya.
Chapter 39 · 0% Book details