← Book details Matar Damusa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 28 OF 58

Sashe 28

Matar Damusa Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Ogah Junaid kuwa zama ya yi a bakin bed yayi tagumi wani irin ƙunci ne ya ziyarci zuciyar sa, idonsa ne sukayi jawur shi a rayuwarsa ya tsani ayi masa maganar Aure ji yake kamar ya sheƙe kansa, shi har cikin zuciyar sa yana son Ayush amma maganar Aure ne baya so.
ji yake zuciyarsa tana haurowa, kwakwalwar sa tana tafasa, idanuwan sa ne suka fara canzawa like tiger eyes! hankalinsa ne ya fara fita daga jikinsa yana huci cikin ƙanƙanin lokaci ya faɗi ƙasi yana juye-juye ya riƙe kansa sosai yana wani irin gurnani da ƙarfin gaske,
ji yake kamar ana hura masa wuta a jikinsa, jijiyoyin jikinsa sun fito sunyi burtsi-burtsi launin fatarsa ta koma yellow, sumar kansa sun mimmiƙe daga kwance da suke!
miƙewa ya yi da ƙarfin gaske ga rikitattun eyes ɗinsa na tsoro, tarwatsa ɗakin ya fara yi ya fiffige labulayen ɗakin, duka ɗaya yayi wa mirrow ya dagargaje, wadrobe ɗinsa ya faɗo dashi ƙasi, ya ɗago da makeken katifarsa da hannu ɗaya yayi wurgi dashi,
ya zamar da ɗakin kamar kasuwa,
jawo ƙofar ɗakinsa yayi ya ɓalla door sannan ya fice yana taku irin na ƙarfafan zakuna, ya sauƙo falo da ƙarfin gaske ya finciki ƙatoton plasman dake manne a jikin bango yayi wurgi da shi (wayyo my plasman🥺)
ya harhargutsa kujerun ɗakin, duk ya finfincike flawowin ɗakin, labulayen falon masu tsadar gaske na UK duk ya yayyaga su! gurnani yake na gasken gaske haɗe da ihu-ihu sai ta'adi yake ta yi musu...

Mommy kuwa tana sallah jin yanda Junaid yake ta gurnani yasa hankalin ta yabar jikinta,
Jikin ta ne yake kakkarwa sallar bazai yuba a halin yanzu hakan yasa ta sallame, da gudu ta nufi falo tana faɗin "Innalillahi wa inna'ilaihi raju'un Junaid na shiga uku ciwonka ya tashi kuma babu maza a gidan...."

Itama Ayush tsabar tsoro jikin ta ne yahau ɓari yana kakkarwa ta kasa sauƙa daga kan gadon, lokaci guda kamar wanda aka zaƙuleta ta tashi ta gudu itama ta nufi falon,
Mommy murya na kakkarwa tace wa Ayush "ki koma ciki kar yaji miki rauni Ayush, ki shiga cikin ɗakin ki rufe, ki barni zanji da shi.."

Junaid kuma tsayawa yayi yana fuskantar Ayush ya zuba mata raunannun idanuwansa sai gurnanin daya ƙaru, itama Ayush tsayawa tayi tana kallon sa ta kasa motsawa.
Mommy ce tayo kansa da igiya a hannun ta zata ɗaure shi, ta lallaɓo ta bayansa ta wurga masa igiyar ai kuwa ita da igiyar haka ya yi wurgi da su wani irin ƙara mommy tasau Allah yaso ta akan doguwar sofa ta faɗo abun yazo mata da sauƙi,
a razane Ayush tace "Mommyyy" tayo kanta da gudu ta ɗagota, cikin ƙirar ƙarfi Junaid ya yo kansu gadan-gadan zai kai musu hannu da gudu Ayush ta shige tsakiyar sa ta rungume shi sosai jikinta na kakkarwa, ta ƙanƙame idonta rub tana jiran ta yanda za'ayi wurgi da ita sai kuma abun mamaki wani irin nannauyar ajiyar zuciya ya sau yana numfashi sama-sama ya rufe idanuwan sa rubb, wani irin hajijiya ne ya ɗebe shi zai faɗi ƙasi Ayush ta rirriƙe shi sosai a hankali ta kaishi ƙasi ta kwantar da shi,
kanta ta kwantar saman ƙirjin sa, tana jin yanda zuciyar sa take harbawa da ƙarfi-ƙarfi da haka har zuciyar sa ta dawo normal, sai dai jikin sa ba ƙwari ya kasa motsa ɗan yatsar sa ma still idonsa a rufe...

Mommy sake baki tayi tana kallon ikon Allah, a ranta tana furta "wacece wannan yarinyar? daga ina take? anya kuwa mutum ce, a karo na uku kenam ina ganin yanda take ceton Junaid, Alhamdulillah Allah na gode maka daka kawo mana ɗauki ka kawo mana wacce zata magance mana matsala..."
Murmushi ne akan fuskarta ga haƙorin makkan ta kuwa ya yi matuƙar yi mata kyau,
a hankali take tafe tayo kan Ayush tace "Ayushert ki taso..."
"a'ah Mommy jikinsa da sauran zafi idan na raba jikin mu ciwon zai iya dawowa"

a hankali yake motsi da hannayen sa da ƙer ya iya ɗago hannun ya ɗora su akan gadon bayan Ayush, idonsa ya fara buɗewa a hankali yana kallon dishi-dishi har idon ya washe,
Idonsa ya washe sosai ya koma fari sol kamar ba shi bane idonsa ya koma green colour ba,
Lips ɗinsa yake motsawa a hankali ya furta "Yushert..."
itama ɗagowa tayi suna fuskantar juna ido cikin ido,
"are you okay?" ya furta hakan yana kallon ta! kaɗa masa kai kawai tayi tana ƙoƙarin miƙe wa, Mommy tayo kan Junaid tana tana cewa "my son kana lafiya, tashi maza sannu ko" ta kai hannun ta kansa ta tallafa masa ya tashi idonsa kuwa na kan Ayush wacce ta kawar da kanta gefe ga ido ya yi jawur daga ƙarshe kuwa ta juya da gudu ta koma cikin bedroom ɗin su,
soyayyar Junaid zai mata illah sai dai yaƙi amince wa da soyayyar ta, zuwa tayi ta kwanta a saman gado wani sabon kuka ne ya sake zuwa mata, a cikin ranta kuwa tana faɗin "dole na koya wa zuciya ta hakurin rashin Yaya Junaid, meye amfanin soyayyar da ba Aure? meye mafita? wani shawara zan ba wa zuciya ta?"
tana kwance tana raya abubuwa da dama a cikin ranta, can kamar wanda aka zabureta ta tashi tana faɗin "na samo mafita, yes! yes!! yes!!!, zan ƙaurace masa na wasu kwanaki shi da kansa zai nemeni, ni kuwa nace masa indai bai aure ni ba bazai ƙara gani na ba tinda naga yanzu inbai ganni ba baya jin daɗi"
tana cikin wannan tunanin saiga Mommy ta shugo idon ta akan Ayush tazo ta zauna kusa da ita, tace "Ayush nagode sosai da ceton Junaid daga halin da yake ciki, haƙiƙa ke ƴer baiwa ce, kuma ke kece maganin Junaid! zan so ki Aure shi Ayush kuma naga kin shaƙu da shi sosai, soyayyar ku ya yi zurfi" tayi ajiyar zuciya sannan ta dafa kafaɗar ta tace "kun dace da juna"
juyowa Ayush tayi tana kallon Mommy tana motsi da leɓen ta a hankali tace "Mommy Yayana Junaid baya sona, yace kada na sake masa maganar Aure.." ta ƙarasa maganar tana zubda ƙwalla, Mommy ta jin jina kanta ta ɗanyi jimm kaɗan kamar mai tunanin wani abu daga baya tace "baza su bar shi yayi Aure ba..."
Ayush ta juyo da sauri tana kallon Mommy baki na kakkarwa tace "su waye?.."
"Azzaluman da suka shiga rayuwarsa" Mommy ta faɗi hakan tana zubda kwalla...
"Amma inaso kimun wata alfarma!"
Ayush ta ɗago tana kallon Mom, tace "ina jinki Mommy"
Mommy ta kamo hannayeta biyu tana fuskantar ta tace "ki rinƙa yawan zama kusa da shi, kina shiga jikinsa kamar dai a yanda na ganku yau, insha Allahu a hankali komai zai dawo normal, ciwonsa kuma zaiyi ƙasa, inhar ya shiga jikin ki sosai zakiga kina masa zancen Aure zai amince.."
wani irin haɗiyar yawu Ayush tayi sannan tace "to Mommy amma kince zuwa gobe na fitar da wanda nake so acikin su biyu.."
"eh na gaya miki haka ne saboda Junaid, nasan yana matuƙar kishi da Dr, idan baki sani bama akan ki Junaid ya yi wa Hasheem duka, kada kisa damuwa a ranki kinji ko Doughter??"
kaɗa kai kawai Ayush tayi idonta akan Mommy.....

"to yanzu dai kije ki gyara masa ɗaki, zuwa dare kema zan kai ki ɗakin ki kibar mun ɗaki nima" ta ƙarisa maganar tana miƙewa tsaye tace "bari ni kuma naje kitchen na girka masa wani abincin baici komai ba.."

cikin sanɗa Ayush take taka upstairs, tana raya cewa shin a wani hali zata ga Junaid,
gabanta ne ya yi wani irin bugawa ganin ƙofar ɗakin a cire, ƙarasa shiga tayi tana bin ko ina da kallo yayi kaca-kaca da ɗakin ga mirrow ya dagargaza shi, katifar gadon anyi wulli dashi, ɗakin dai ya zamo kamar wanda akayi wasan dambe a ciki!
a razane ta kai idon ta kan Junaid yana tsaye ta gaban ta ya goya hannayensa kan chest ɗinsa, ya kafa mata eyes ko ƙibtawa baya yi..

Ayush a cikin ranta tace "na shiga uku taya zan fara gyara ɗakin nan, bazan iya ba gaskiya" tana cikin wannan tunanin taji anyi sallama ta bayanta juyawa tayi tana kallon wanda ya shugo, wani mutumi ne ya shugo yana faɗin "Ogah an kawo kayan furniture zamu fara aiki yanzu" Ok kawai yace ya riƙo hannun Ayush yace "muje za'a canza kayan ɗakin..."
har zasu fita ya waiwayo yana kallon ɗakin sirri ya tuna ya danna key a room ɗin, ba wanda yasan da gurin...
Chapter 28 · 0% Book details