← Book details Matar Damusa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 55 OF 58

Sashe 55

Matar Damusa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

tsabar firgici da tsoro a razane Ayush ta ƙwarara ƙara mai razanarwa ta toshe kunnuwanta kanta asaman ƙirjin Junaid nan danan jikinta ya soma kakkarwa,
Junaid rungumarta yayi sosai saboda yasan ba ƙaramin tsoro taji ba, shi kuwa ko a jikinsa bai tsorita ba saboda yasan ɗaya ne daga cikin ƴanmatansa Rumana ko Adity, a hankali ya juyo bayansa domin yaga ko wacece a cikinsu yana bubbugar bayan Ayush alamar rarrashi...

ganin yanda mommy ta fito da gudun gaske ko ɗan ƙwali babu akanta tana salati a ruɗe saboda taji ƙarar bindiga ga kuma ihun Ayush a tunanita an harbeta ne,
sai kuma ga Rumana itama ta fito da sauri tana son ganin meke faruwa..

duk tsayawa sukayi sun yi cirko-cirko danin mutum tsaye yana sanye da baƙaƙen kaya ajikinsa,
wando baƙi da kuma rigar sanyi baƙi masu jikin leda sai sheƙin baƙi kayan suke, da baƙin hula a kansa na sanyi, ga kuma ya rufe fuskar da facemark sannan ya ɗora baƙin glass a ido,
yana sanye da safar hannu baƙi, takalmin ƙafarsa baƙi irin takalmin nan mai safa amma yanada tudu, yana goye da ƙatuwar baƙar jaka a baya, hannu kuma riƙe da ƙaramin bindiga..

Adity ce itama ta fito tana masifar waye ya tasheta a bacci,
tsayawa tayi itama tana kallon mutumin buɗe baki tayi tace "ɓarawo a gidan nan?..."
tayi maganar ne da turanci yanda kowa zai jita,

Rumana ce ta ari bakinta da cewa "ɓarawo kuma da rana?.." itama ta mayar da amsa ta turanci..

Mommy kam ba bakin magana ta tsaya tana kallonsa jikinta har ya fara rawar sanyi, zuciyarta kuwa haka yake bugun 3+3...

har yanzu Ayush kanta yana kife a saman ƙirjin Junaid ta kasa ɗagowa..

Junaid bayan ya ƙareta da kallo shi dai yasan wannan ba namiji bane tayi zubi da mace,
murmushi yasau mai ƙayatarwa sannan yace "you are crazy my Angel...."

jin ya canki sunanta yasa ta motsa, tasa hannu ta cire hular kanta saiga baƙin sumar gashin ta ya wantsilo har gadon bayanta, sannan ta cire glass ɗin idonta saiga dara-dara idanuwanta sun bayyano sun sha kwalli kuwa, ta cire facemark ɗin fuskarta saiga ƙaramin pink lips ɗinta sun fito da ƙayataccen murmushi a fuskarta, tana dariya har fararen haƙoranta suka fito, a hankali take motsa lips ɗinta tace "my Man soyayya ne haka kodai itace kishiyar tawan?.."

shima murmushin ne a saman fuskarsa baice mata komai ba sai ware mata hannu da ya yi alamar taje ta..

da gudu taje gurin shi ya rungumota da ɗayan ɓangaren hannunsa yana bubbuga bayanta a hankali a saitin kunnenta yace "kin tsoritar mun da mata shin kin kyauta mun?..."

dariya tayi tana bugan ƙirjinsa..
ta ɗayan ɓangaren hannunsa kuma Ayush ce itama yake rungume da ita har yanzu bata ɗago da kanta ba,
haka ya haɗa su ya rungumesu a tare.....

mommy ajiyar zuciya tayi ganin ashe Angel ce har hankalinta ya kwanta...

Rumana kam ɗaukar ɗan ƙaramin glass cup tayi ta doka a ƙasi ya dagargaje tana huci ta koma ɗakinta..

Adity kuma idanuwanta fici-fici haka ta dinga fin-fincina su tana son ganin shin meke faruwa ne....

Junaid kuma haka ya haɗe kayuwan Angel da Ayush guri ɗaya asaman faffaɗar ƙirjinsa, shima ya kifar da kansa a tsakiyar kayuwansu .....

*KUYI HANZARIN TURO KUDIN KU DOMIN CIGABA DA BOOK TWO*

*🤝 SDEENDTM DATA SERVICES🤝*
*MTN* . *Airtel*
1GB = ₦300. 1GB = ₦300
2GB = ₦600. 2GB = ₦600
3GB = ₦900. 3GB = ₦900
4GB = ₦1200. 4GB = ₦1200
5GB = ₦1500. 5GB = ₦1500

*GLO* . *9MOBILE*
1GB = ₦350. 500Mb ₦500
2GB = ₦700. 1.5GB ₦1100
3GB = ₦1050. 2GB ₦1600
4GB = ₦1400. 3GB ₦2000
5GB = ₦1750. 4GB ₦2500

*VALIDITY: 30DAYS/1MONTH*
For cable subscription or sell recharge card
Call this number or whatsapp
👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽
*🪀08066268951*

*ASMEETAH NOVEL*

*typing📲*

🐅 *MATAR* *DAMUSAA*🐅
(the wife of a tiger)

*written* *and* *story* *by*
*Asma'u Muhammad Auwal*

( *ASMEETAH NOVEL* ✍️)

*WhatsApp me 09065443871*

*BOOK ONE*⬇️
*99 to 100*

*👉 END 👉 END 👉 ENDED OF BOOK ONE*

*DOMIN SAMUN LITTAFI NA BIYU KU HANZARTA BIYAN KUƊIN KU A FARASHI MAI SAUƘI...*

*MATAR DAMUSAA BOOK 2 PAY ONLY 200👌👇👇👇*

*ASMA'U MUHAMMAD AUWAL,*
*9065443871, OPAY BANK.*

*OR*

*ASMA'U MUHAMMAD AUWAL,*
*2267236949, ZENITH BANK*

*SHAIDAR BIYA TA WANNAN NUMBER*
👇👇👇
*09065443871*

*NASARA WRITERS ASSOCIATION*
___________________________________
{{ *_Nasara abin so ga kowa, domin marubuta da cigaban rubutu, alƙalaminmu ƴancinmu._* }}
___________________________________

💫💫 *{{N W A}}* 💫💫

بِسْــــــــــــــــــــــمِ اللّهِ الرَّحْمَنِ الرَّحِيْم

𝐔𝐩! 𝐔𝐩!! 𝐔𝐩!!! 𝐇𝐮𝐫𝐫𝐲💃💃💃

𝐒𝐀𝐅𝐍𝐀 𝐆𝐑𝐀𝐏𝐇𝐈𝐂𝐒 𝐃𝐄𝐒𝐈𝐆𝐍.
ᴴᴼᴹᴱ ᴼᶠ ᴳᴿᴬᴾᴴᴵᶜ ᴰᴱˢᴵᴳᴺ
ᵂᴱ ᴰᴱˢᴵᴳᴺ ᴬᴸᴸ ᴷᴵᴺᴰ ᴼᶠ ᴰᴱˢᴵᴳᴺ ˢᵁᶜᴴ ᴬˢ:
𝐿𝑂𝐺𝑂* 𝑃𝑂𝑆𝑇𝐸𝑅* 𝐵𝐴𝑁𝑁𝐸𝑅* 3𝐷 𝑀𝑂𝐶𝐾 𝑈𝑃 𝐿𝑂𝐺𝑂* 𝐹𝐿𝑌𝐸𝑅* 𝑆𝑇𝐼𝐶𝐾𝐸𝑅* 𝑃𝑅𝑂𝐷𝑈𝐶𝑇 𝑆𝑇𝐼𝐶𝐾𝐸𝑅* 𝐼.𝑉 𝐶𝐴𝑅𝐷* 𝐼.𝑉 𝑉𝐼𝐷𝐸𝑂* 𝐵𝐼𝑅𝑇𝐻𝐷𝐴𝑌 𝑉𝐼𝐷𝐸𝑂 𝐹𝐿𝑌𝐸𝑅* 𝑃𝐻𝑂𝑇𝑂 𝐹𝑅𝐴𝑀𝐸* 𝑅𝐸𝑀𝑂𝑉𝐸 𝐵𝐴𝐶𝐾𝐺𝑅𝑂𝑈𝑁𝐷* 𝑃𝑅𝑂𝐹𝐸𝑆𝑆𝐼𝑂𝑁𝐴𝐿 𝐼.𝑉 𝐶𝐴𝑅𝐷* 𝑆𝐴𝑉𝐸 𝑇𝐻𝐸 𝐷𝐴𝑇𝐸* 𝐸𝑋𝑃𝐿𝐴𝐼𝑁𝐸𝑅 𝑉𝐼𝐷𝐸𝑂* 𝐿𝑌𝑅𝐼𝐶𝑆 𝑉𝐼𝐷𝐸𝑂 𝐴𝑁𝐷 𝑀𝑂𝑅𝐸...
𝗣𝗟𝗘𝗔𝗦𝗘 𝗖𝗔𝗡𝗧𝗔𝗖𝗧 👉 08148318396 𝗦𝗔𝗙𝗡𝗔 𝗚𝗥𝗔𝗣𝗛𝗜𝗖𝗦.

🌀🌀🌀🌀🌀🌀🌀🌀🌀🌀

Adity ganin yanda Junaid ya rungumi ƴan mata a jikinsa yasa ta fusata cikin zafin nama ta tashi sama ta dirƙo a gaban Junaid, hannu ta kai musu zata cabki wuyan su Angel da Ayush kenam Junaid yayi saurin riƙe hannayenta biyu ya ɗago da dara-daran idanuwansa yana kallonta cikin fushi, girgiza mata kai yayi sannan ya tureta gefe,
tana huci tace "waɗannan karuwanka ne suma ko? toh ka fito fili ka zaɓi wacce kake so a cikin mu, bazan yadda da irin cin amanar nan ba da kuma yaudara, kayi mun alƙawarin zaka aure ni yanzu kuma sai ganin ƴanmata kala-kala nake kuma duk naka, yau ba wacce zan bari da lafiyarta..."
haka ta gama surutan ta da yaren china,
Mommy kuwa kallonta kawai take ita kallon mahaukaciya take mata, ga maganar ta sauri-sauri..

Duk maganganun da Adity tayi Junaid yana sauraronta,
Angel ce ta ɗago tana kallonsa kafin ta maida idonta kan Adity tana faɗin "my man baka so zaman lafiya ba tinda acikin ƴanmatanka har da china, mezakayi da china kuwa?..."
kafin Angel ta rufe baki Adity ta tafo da gudu ta girbe mata ƙafa sai yaraff ta faɗi ƙasi,
cize leɓɓenta tayi da shirin yin mugunta wani irin murɗewa Angel tayi ta miƙe tsaye tareda cankin Adity a cikinta har sai data faɗi ƙasi,

Junaid tsabar baƙin ciki bai tanka musu ba sai ma ɗaukar Ayush da yayi ya haura upstairs da ita, zaije ya kwantar da ita saboda firgicin da ta shiga yasa tayi bacci a tsaye..

Adity da Angel faɗane ya kaure a tsakaninsu suna naushin juna kamar wasu maza,
har zuwa yanzu ba wacce taci galaba akan ɗaya, haka sukayi kaca-kaca da parlour, da sauri Adity ta ɗauki glass bottle ta wurga wa Angel! cikin salo da ƙwarewa wajen iya faɗa, Angel ganin glass bottle yana tafo wa saitin goshinta da sauri ta durƙusa ƙasi ya wuce ta saman kayinta cikin rashin sa'a kuwa bottle ya daki tsakiyar plasman nan take film ɗin da ake showing ya ɗauke gaba ɗaya..

Mommy ce tazo tana rabasu tareda faɗin "meyasa kuke hakane kamar wasu dabbobi kuna faɗa..."
wani irin juyi Adity tayi ta kaiwa Angel naushi cikin zafin nama nan ma Angel ta sake kaucewa gefe sai hannun Adaty ya sauƙa akan leɓɓen bakin Mommy,
daiden lokacin da Junaid yake sauƙowa down ƙwayar idonsa akan su....

Mommy da sauri ta dafe bakinta da hannu tana faɗin "innalillahi wa inna'ilahi raju'un, sun cire mun haƙwara nashiga uku.."
kafin a ankara kuwa jini har ya ɓata hannun mommy, da sauri Angel ta riƙe mommy tana cewa "mommy dan Allah kiyi haƙuri, mun shiga uku! kinga kin fasa mata baki ko? ke a dole ƴar china tsinanniya kawai.."
Jin zagin da Angel tayi mata ne ya ƙara fusata ta zata yo kan Angel, Junaid ya cabki kunkumin ta da hannu ɗaya ya ɗagata sannan ya nufi ɗakinta da ita,

Angel binsu tayi da kallo cikin ɓacin rai kafin ta zauna kusa da mommy wacce har zuwa yanzu tana kame da bakinta, lips ɗinta ne ya fashe, Angel tace "mom please am really sorry, muje na wanke miki bakin.."
riƙo hannun mom tayi sannan suka nufi ɗakin mommy, ita dai mom tayi tsumu ta kasa cewa komai,

(daman ance ɗan kuka mai jawa uwarsa zagi, to wannan kam mai jawa uwarsa duka ne🤣🤣🤣)..

Bayan Junaid ya shige da Adity ɗaki dirar da ita yayi a saman gado, daman ya fito da dorinarsa mai baki uku,
cikin ɓacin rai kafin Adity ta ankara har ya soma zabga mata dorina a jiki,
tana mutsil-mutsil zata tashi ya hankaɗata ƙasi yana wara mata dorina ta ko ina,
ƙin kuka tayi saboda kar mutanen gidan su jiyo ta saboda kar su raina ta,
ganin Junaid yana shirin faffasa mata jiki yasa ta fara ihu ihu take na gaske tana neman agaji,
a gigice ta tashi ta buɗe ƙofar ɗakin ta nufi parlour tana ihu tana sossosa jikinta, nan ma biyota yayi shima yana faɗin "tinda kin raina ni toh yau zan fitar da wannan raini.."
girbe mata ƙafa yayi ta faɗi yaraf a ƙasi ya cigaba da zabga mata wannan dorinar,

kafin kace mai Rumana ta fito da gudu tsayawa tayi tana kwashewa da dariya,
saiga mommy da Angel suma sun fito har bakin mommy ya kumbura suntum,
daga can saman upstairs kuma Ayush ce itama ta sauƙo a gigice jin ihun da ake a cikin gidan domin ihun ne ya tasheta daga baccin da take,

Mommy ce tayo kan Junaid ta riƙe hannunsa tana faɗin "ya isa haka Junaid kar kaji mata rauni, ai duk abunda ya faru laifin ka ne kai ka jawo wa kanka, meyasa zaka zo kana dukanta.."

Junaid cikin fushi ya kai mata canka da ƙafarsa yana cewa "i will teach you a lesson, useless girl.."
ita kuwa tana daga kwance sai ihu take ta zabgawa duk da yabar dukan natan,

ita kuma Rumana dariya take sosai taƙi dakatar wa, a fusace Junaid ya kalli gurin da take a tsaye ya ciro wayarsa daga aljihu saida ya saita goshinta kafin ya wurga mata wayarsa akan goshi, kamar wacce aka zare mata rai tayi tsitt tareda dafe goshinta kamar zatayi kuka tsabar taji zafin bugun da ya yi mata a goshi, abunka da farar fata wato baturiya har gurin yayi jawurr kamar jini zai fita,
wayarsa kuwa mai ƙirar iphone 15 pro faɗuwa tayi a ƙasi ta dagargaje...
Chapter 55 · 0% Book details