← Book details Masarautar Alhamra Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 37 OF 42

CHAPTER 3️⃣5️⃣

Masarautar Alhamra Part 1 Complete Hausa Novel · about 15 min read

*بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيمِ*


Asuba ta gari, iska mai sanyi tana kaɗawa a wani boyayyen fili dake kewaye da daddadan bishiyoyi. Shiru kake ji, sai sautin tsuntsaye dake rera kukan sanyin asuba.... Inuwa yana tsaye, sanye da rawaninsa da saje da gemunsa na bogi wadanda suka ƙara masa kwarjini...

Master Ibrahim ya matso ta bayanta domin fara koyar da ita dabarun yaƙi da takobi. Ya tsaya daidai bayan Inuwa, ya sa hannunsa ya kama nata dake rike da takobin, domin ya nuna mata yadda ake jujjuya shi cikin kwarewa...

A take, wani irin Shock mai karfin gaske ya ratsa Ayat tun daga kwakwalwarta har zuwa tafin kafafunta. Taɓa jikin Master da ta ji ya sa tsikar jikinta tashi, musamman yadda gemun Master yake gogar wuyanta yayin da yake mata bayani cikin raɗa...

Shi ma Master Ibrahim, hancinsa ya shaki wani daddadan kamshi dake tashi daga wuyan Inuwa...ƙamshi ne mai rikita tunanin namiji, wanda bai kamata soja namiji ya kasance dashi ba. Hankalin Master ya fara barin jikinsa, yana jin wani yanayi dake neman rinjayar dabarunsa na soja..

Inuwa cikin muryar dake rawa ya furta
"Master... na koya, zan yi da kaina yanzu."

Ta samu ta zare jikinta daga gareshi, tana kokarin daidaita numfashinta da ya riga ya jagule.

A can gefen wani kududdufi na alfarma wato Power Pool...King Diamond yana zaune tare da Prince Zarith. Suna shan wani ruwa mai launin shuɗi mai suna Al-Kautharul-Jinn, wani irin ruwa ne da ba a samunsa a duniyar mutane, wanda yake ƙara ƙarfin jini da sanya natsuwa a kwakwalwa..

Lokaci guda, King Diamond ya ji tsikar jikinsa ta tashi. Ya shiga wani irin yanayi na shauƙi da bai san daga inda ya fito ba.

Nan take idanunsa suka juye, sai ga Ayat ta bayyana a gabansa cikin shigar gimbiyancinta na alfarma. Ta sa hannu ta yaye mayafin dake fuskarta, tana sakar masa wani irin kasaitaccen murmushi mai sace zuciya..

King Diamond ya daskare, ya kasa daina kallonta, shima ya fara sakar mata murmushi har fararen hakwaransa suka bayyana..

Prince Zarith ya cika da mamaki, domin tunda yake da King, bai taba ganin dariyarsa da ta kai ga bayyanar hakwara ba.

Prince Zarith yana taɓa kafar King cike da mamaki ya furta.
"Lafiya kuwa King? Me kake kallo haka kake murmushi kai kadai?"

King ya firgita, ya dawo hayyacinsa. Ya waiga, ya ga babu kowa, sai Prince Zarith dake kallonsa cikin rashin fahimta. Anan ya tabbatar da cewa Ayat ta riga ta mamaye ransa, har ta kai tana masa gizo a fili...

A ransa ya furta "Wane irin sihiri ne wannan yarinyar take yi min? Tana can tana training, amma ina jin ɗumin jikinta a nan."..

Prince Zarith ya matso kusa da King, ya shaƙi iskar dake kewaye da shi, idanunsa suka rine da launin mamaki..

"King... ina jin ƙamshin shauƙin soyayya a jikinka? Wannan ba yanayinmu na jinnu ba ne kaɗai. Shin wacece a ranka?"

Ya tsaya ya ƙura wa King ido, muryarsa ta rikkiɗa ta koma ta gargaɗi... "Fatan ba bil'adam ba ce... domin akwai babban matsala idan har ita ce. Ka san dokokinmu, kuma ka san abin da zai biyo baya."

King Diamond bai ce uffan ba, sai dai wata uwar harara da ya wurga wa Zarith, wadda ta sa iskar wajen ta yi sanyi lokaci guda. Shima ya sani, mallakar Ayat ba abu ne mai sauƙi ba. Akwai babban ƙalubale daga manyan shugabannin aljanu waɗanda ba za su taɓa amincewa da wannan sarƙaƙƙiyar soyayyar ba. Dole za a fafata, kuma dole jini ya zuba kafin burinsa ya cika...

A can duniyar mutane kuwa, Master Ibrahim ya canza salon horon. Ya kai Inuwa bakin wani katon tafki mai zurfin gaske domin gudanar da training ɗin numfashi a cikin ruwa.

Master Ibrahim ya tsaya a bakin ruwan, idanunsa sun yi ja saboda tsananin son ganin Inuwa ya zama jarumi.
"Wannan karon, za mu ga juriya da jarumtarka a cikin ruwa. Dole ka nitse, kuma ba za ka ɗago ba har sai mintocin da na ɗiba maka sun cika. Wannan shi ne zai nuna idan kai soja ne na gaske."

Ayat ta ji gabanta ya faɗi, wani irin sanyi ya ratsa ƙasusuwanta. Ba tsoron ruwan ne ya firgita ta ba, sai umarnin da Master ya biyar da shi...

"Inuwa, cire waɗannan kayan naka na soja! Ba za ka iya yin wannan training ɗin da nauyin kakin nan a jikinka ba. Cire su yanzu ka shiga ruwan!"

Inuwa ta daskare a inda take. Ta san muddin ta rage kayan jikinta, asirinta na mace zai iya bayyana. Master Ibrahim kuwa yana tsaye yana jiran ganin ya fara cire kayan, idanunsa kyam akan Inuwa...

Muryar na rawa ta ce, "Master... ina jin zan iya yi da kayan nan. Ba sa min nauyi."

Master cikin tsawa ya ce, "Wannan umarni ne Inuwa! Soja baya musu da shugabansa. Cire kayan nan yanzu!"

Ayat ta fara ƙoƙarin taɓa maɓallan rigarta, hannunta yana karkata, tana kallon Master wanda ya ƙi ba ta sararin ko da ƙifta ido ne. A ranta tana kiran King Diamond, ko zai kawo mata ɗauki a wannan mawuyacin lokacin...

Ta ji zuciyarta tana bugawa kamar ganga. Ta kalli Master Ibrahim, wanda yake tsaye tamau kamar gunki, yana jiran ganin ta cire kakin soja..

A hankali ta sake furta
"Master... don Allah, ina neman alfarmar ka bar ni in shiga bayan wancan shingen, domin in rage kayana. Al'ada ta ce ba na son rage kaya a gaban kowa, ko da kuwa shugabana ne."

Master Ibrahim ya haɗe girare, yana kallon Inuwa da wani irin kallo na mamaki. "Inuwa, kai soja ne! Soja ba shi da kunya a gaban ɗan uwansa, musamman a wajen horo."

Inuwa ya ce, "Ina rokonka Master... wannan karon kawai."

Master ya saki wata nauyayyar ajiyar zuciya, sannan ya nuna mata bayan shingen da hannu..

"To, ka je maza! Amma ka sani, duk daƙiƙar da ka ɓata tana raguwa ne daga lokacin numfashinka a cikin ruwa. Ka fito nan da daƙiƙa talatin!"

Ayat ta ruga bayan shingen da gudu. Da sauri ta rage kayan jikinta, amma ta bar wata siririyar riga ta ciki wato vest, ta ciki akwai bell da ya ɗaure mata ƙirji sosai don kada siffarta ta fito. Ta fito tana sauri, ba tare da ta bari Master ya kalle ta sosai ba, ta afka cikin ruwan tafkin..

Ruwan ya kasance mai sanyi sisai, amma hakan ya ba ta damar ɓoye kanta.

Tana nitsewa cikin ruwan, Master Ibrahim ya matso bakin tafkin, yana kallon agogonsa amma hankalinsa yana kan yadda Inuwa ya yi firgigit wajen boye jikinsa...

A ransa ya furta
_"Wane irin soja ne wannan mai kunyar mata? Akwai wani abu da wannan yaron yake ɓoyewa, kuma zan gano shi ko ba jima ko ba daɗe."_

A can gefen Power Pool, Prince Zarith ya lura cewa King Diamond ya tafi wani tunani na daban, idanunsa sun yi haske kamar taurari...

Ya ce, "King, muna magana ka yi shiru. Shin kana nufin za ka sadaukar da matsayinka na Sarkin Aljanu domin wannan bil'adama? Ka sani, idan manyan majalissar aljanu (The Elder Jinn Council) suka ji wannan labarin, yaƙi zai ɓarke tsakanin masarautunmu."

King Diamond ya miƙe tsaye, dogon farin gashinsa yana shawagi a iska...
"Zarith, ba zan sadaukar da komai ba, amma kuma ba zan bar ta ba. Idan dole sai an yi yaƙi don a tabbatar da soyayya, to ni ne zan jagoranci yaƙin. Babu wani aljani da ya isa ya gaya min wadda zan so!"

Ya kalli sararin samaniya, yana jin yadda Ayat take fama da numfashi a cikin ruwa. Ya tura mata wani irin sanyin ƙarfi ta hanyar iska domin ta jure sanyin ruwan da take ciki...

✨
Inuwa ya ɗago daga cikin ruwan bayan minti biyar, numfashinsa yana fita sama-sama "ha...ha...ha"..

Ruwan yana wuyansa, idanunsa sun yi jawur saboda sanyi da juriya. Rawani yana nan daram a kansa, ya jike jagaf ba tare da ya faɗi ba domin an ɗamara shi sosai...

Cikin mamaki da fushi Master ya ce,
"Wai kai Inuwa, meye a cikin rawanin nan da ya fi karfin a cire shi? Ka taɓa ganin soja yana horon nitsawa a ruwa da rawani? Wannan wane irin iskanci ne?"

Inuwa ya ce, "Master... kayi hakuri. Al'ada ce ta gidanmu, ba ma taɓa barin kanmu a fili..."

Master Ibrahim ya matso har bakin tafkin, ya duƙa ya kalli kwayar idon Inuwa. Ya kasa gane dalilin da yasa wannan yaron yake da kishin kai haka..

"Ban yarda ba! Soja ba shi da al'ada idan umarni ya zo. Oyaa, cire rawanin nan yanzu ka miƙo min shi, sannan ka sake nitsawa ba tare da komai a kanka ba! Maza kai nake jira...!"

Inuwa ya fara zuru-zuru da idanu. Zuciyarsa ta fara dukan uku-uku.... Idan ya cire rawanin nan, sumar gashinta mai tsawo zai zubo, kuma vest ɗin dake jikinta zai iya bayyana siffarta ga kuma wandon jikinta tyt ne, surar hips ɗinta zai bayyana idan ta fito...

Master Ibrahim ya daka wa Inuwa tsawa, muryarsa tana sake ruri a sararin tafkin...

“Maza cire rawanin nan yanzu! Idan har ba ka da abin da kake boyewa, me ya sa kake gudun umarni na?”

​Hannun Ayat ya fara rawa, ta kai shi saman rawaninta, tana jin kamar rayuwarta za ta kare a wannan lokacin. Ruwan sanyi ya ratsa ta, amma gumi ne yake keto mata a goshi. A ranta take furta,

“Ya King Diamond… ka ce za ka kare ni, ga shi asirina yana shirin tonuwa.”

​A daidai lokacin da yatsun Ayat suka fara kwance rawanin, sai aka ji sautin takun takalman soja, taku ne mai nauyi da kwarjini...

Wani jami’i ne sanye da kakin masarauta, ya bayyana a cikin kamannin wani babban jami'i dake kusa da sarki, wanda ya fi master miƙami..

Kwarjininsa ya sa Master Ibrahim dakatawa da abin da yake yi...

​“Master Ibrahim!” Muryar jami’in ta dake wajen, muryar da take cike da izza...

​Master Ibrahim ya firgita, ya juyo da sauri ya ga babban jami’in tsaye. Nan take ya gyara tsaiwarsa ya sara masa...

“Yallabai! Ban yi tsammanin ganinka a nan ba.”

​Jami’in wanda ya kasance King Diamond ne a wannan suffar bai ko kalli inda Ayat take ba, amma iskar da take kewaye da shi ta zama mai ɗumi, tana ba Ayat wani irin kwarin gwiwa...

“Sarki yana bukatar ka a fada yanzu! Akwai baƙi daga Masarautar Arewa da suka iso, kuma kai ne aka zaɓa ka jagoranci tsaron taron sirrin da za a yi.”

​Master Ibrahim ya yamutsa fuska, ransa ya ɓaci domin yana tsaka da koyar da horo ne....

“Amma Yallabai, ina tsaka da horar da wannan yaron ne, akwai wani abu da nake so in tabbatar...”

​Jami’in ya daka masa tsawa, idanunsa suka yi wani irin walƙiya da ta sa Master Ibrahim jin tsoro a karon farko...

“Umarnin Sarki ya fi son ranka mahimmanci, ko kuwa kana son ka sabawa masarautar ne?”

​Master Ibrahim ya sadda kansa ƙasa. “Ayi hakuri Yallabai. Zan tafi yanzu.”

Ya juyo ya kalli Ayat wadda take raɓe a cikin ruwa... “Inuwa, ka tashi ka fito! Ka gode wa Allah da aka ƙira ni, amma horar gaba na nan tafe... Gobe za mu dora daga inda muka tsaya.”

​Master Ibrahim ya ruga da gudu ya bar wajen...
Jami’in ya tsaya na wasu daƙiƙu, ya kalli tafkin. Ko da yake bai ce komai ba, Ayat ta ji wata murya a cikin kanta tana cewa..

“Kiyi maza ki fito ki shirya kanki, masoyiyata. Ba zan bar wani ya taɓa sirrin da yake nawa ba.”

​Kafin ta farga, jami’in ya ɓace kamar hayaƙi a cikin iska. Ayat ta saki wani babban ajiyar zuciya, ta jawo jikinta ta fito daga ruwan, tana hawayen farin ciki da kuma fargabar abin da zai biyo baya gobe...


Ko da Master ya je, Sarki ya sanar masa cewa, akwai wani binciken da zasu gudanar...

Duk da ƙiran da King Diamond yayi masa duk na ƙarya ne...

✨✨✨

Gimbiya Zayana tana zaune a takure a kusurwar dakin kurkukun, wanda babu komai a cikinsa sai zafi. Iskar dakin tana da wani irin wari na danshi... Ga wasu ƙattai da miagun sauraye waɗanda suka addabi jikinta, duk inda ta shafa sai ta ji sun mata tabo...

Yau kwana uku ke nan, amma a wajenta kamar shekara guda ne. Babu waya a hannunta da za ta ƙira kowa, babu wata ƙawarta ko hadima da aka bari ta matso kusa da sashen. Shirun wurin yana mata nauyi a kwakwalwa, har ta fara magana ita kadai...

Muryarta a dashe saboda kuka, "Abul... ashe haka kake? Don kawai na nuna bacin raina akan cin fuskar da kake mun a cikin mutane, shi ne ka yardar da ni a nan? Ko duba ni ba za ka yi ba?"

Sau ɗaya kacal a rana ake turo mata da abinci, wanda ko karnukan masarautar ba su taɓa ci ba. Ruwan sha kuma a gora ake ɗuro mata a ajiye shi sai ya daɗe bai isa gare ta ba...

Zayana ta kalli abincin dake gabanta, ta tura kwanon gefe tana kuka...

"Ba zan ci ba! Gara na mutu a nan kowa ya huta. Yanzu haka Maayah tana can tana cin abinci mai daɗi cikin kwanciyar hankali, ga Ayat da Yumna kuma su ma suna can suna shawagi a fada... ni kuma an mance da ni."

Damuwar ta kai matakin da Zayana ta fara ganin jiri. Ta dora kanta a gwiwoyinta, tana tunanin mahaifiyarta dake can Sydney...

"Mommy... da kin san abin da ke faruwa dani da wannan masarautar ya gama amfani... Yanzu babu wanda zai sanar miki halin da nake ciki?...."


Bayan kwana ɗaya...


​Master Ibrahim ya kasa zaune, ya kasa tsaye. Duk da shi ne ya rufe Zayana, amma zuciyarsa tana gaya masa cewa kwana huɗu a cikin cell ga gimbiya irin Zayana ya isa tarbiyya. Ya san Sarki ya fusata ne saboda rashin kunyar da ta yi masa a gaban kowa, kuma hakan ya taɓa kwarjinin sa na uba kuma sarki...

​Master ya nufi sashen Sarki, ya same shi zaune yana duba wasu taswirorin ƙasa, fuskarsa a murtuke kamar babu sauran rahama a cikinta.

​Master Ibrahim ya duƙa har ƙasa, ya gaishe da Sarki cikin girmamawa.
​
"Ranka ya daɗe, Allah ya ƙara maka tsawon rai da lafiya. Na zo ne domin in gabatar da wata magana akan Gimbiya Zayana."

​Sarki bai ɗago kai ba, ya ci gaba da abin da yake yi. "Idan maganar fito da ita ce, to ka adana baki ka fita daga nan, Ibrahim."

​Master Ibrahim ya ce,

"Ranka ya daɗe, na sani cewa ta yi babban kuskure na rashin kunya gare ka. Na san hakan ya yi maka zafi, kuma horon da take ciki ya dace da abin da ta aikata. Amma na duba yanayin lafiyarta, na ga damuwa da rashin abinci sun fara canza mata kamanni. Ina tsoron kada wani abu ya same ta kafin ta gane kuskurenta."

​Sarki ya ɗago, idanunsa sun yi ƙuri akan Master Ibrahim...
​
"Ibrahim, ka san ni sarai. Bana taɓa jure raini daga kowa, ballantana daga jini na. Rashin kunyar da Zayana ta yi min a gaban mutane, ya nuna cewa ban yi nasarar ba ta tarbiyya ba. Idan na fito da ita yanzu, na nuna mata cewa za ta iya yi min duk abin da ta ga dama ne."

​Ya ja numfashi, sannan ya ci gaba..
"Zan bar ta ta ci gaba da zama a can, har sai ta koyi yadda ake magana da uba, kuma har sai ta roƙi gafarar mutuncin da ta tattaka."

​Master Ibrahim ya ga Sarki bai nuna alamar sassauci ba, sai ya yi dabarar kawo maganar mahaifiyarta dake can..

​"Ranka ya daɗe, idan mahaifiyarta ta ji labarin cewa gimbiyar tana cell, na tabbata za'a samu babban matsala sosai. Amma idan ka ba ni izini, zan riƙa duba ta, kuma zan matsa mata har sai ta amince za ta ba ka haƙuri."

​Sarki cikin fusata ya ce, "inason labarin ya je kunnenta, duk abinda suka ta ka ita da ƴar zan magance shi...bana tsoronta don haka kabar maganar nan kawai tin kafin ranka ya ɓaci kaima..."

Master bai ƙara cewa uffan ba, ya miƙe ya ja jikinsa ya tafi...

Yau ranar da ake ta shirye-shiryen gudanar da walimar sauƙar al'kur'ani...

Masarautar Alhamra ta cika da baƙi daga sassa daban-daban na duniya domin halartar taron sauƙar Alkur'ani na Gimbiya Ayat da Gimbiya Yumna. An tsara taron yadda duniya za ta ba da misali, inda manyan malamai za su shaidi tilawar gimbiyoyin...

Ayat tana zaune a ɗakinta, kanta cike da sarƙaƙƙiya. Zuciyarta tana gaya mata cewa wannan ranar ita ce mafi haɗari a gare ta.
Dole ta bayyana a matsayin Gimbiya Ayat don yin tilawa a gaban malamai..
Amma kuma, matsayinta na Inuwa yana nufin dole tana filin taron tana tsaro, musamman yadda Master Ibrahim ya matsa kaimi akan tsaro...

Tana cikin wannan raɗaɗin tunanin, tana kiran King Diamond a ranta, sai ta ji sanyin kamshinsa ya cika ɗakin..

King Diamond ya bayyana a gabanta, tsaye daram cikin kwarjininsa. Ayat ba ta san lokacin da ta tashi da gudu ta rungume shi ba saboda tsananin kewar da take masa. Ta ɗago kanta da sauri tana shirin bayyana masa matsalarta, amma sai ya ɗora yatsansa akan laɓɓanta...

"Ba sai kin yi magana ba. Na riga na saurari maganar zuciyarki, kuma na san damuwarki."

Ya kalli cikin idanunta, muryarsa mai ratsa jiki ta ci gaba

"Ke za ki kasance Gimbiya Ayat, ki fita taron ki yi tilawar Alkur'ani kamar yadda kika yi buri. Ni kuma, zan rikkiɗa in koma Inuwa, zan tsaya a matsayinki na soja mai tsaro. Babu wanda zai gane bambancin."

Ayat ta sake rungume shi a karo na biyu, tana jin wani irin sanyi a ranta...

Ta ɗago tana kallonsa cikin mamaki...
"Ta yaya kake iya shigo wa cikin fadar nan cikin sauƙi? Masarautar nan tana da shingen tsaro na aljanu masu ƙarfi, amma kake ratsa su?"

Cikin gajeriyar magana da murmushin isa ya ce,
"Ta ƙasan ƙasa nake shigo wa... babu shingen da zai iya dakatar da ni daga isowa gare ki."

Suka fara tattaunawa cikin wani salo mai cike da ƙauna. Ayat tana jin yadda zuciyarta take narkewa a duk lokacin da yake kusa da ita. Ta manta da duk tsanar da take masa a baya, yanzu soyayyarsa ta zama jinin jikinta.
Amma duk da haka, saboda izza ta sarauta da kuma nuna kada ya raina ta, sai ta fara janyewa tana yatsine fuska...

Ta furta "Kada ka zata don na rungume ka shikenan na daina jin haushinka. Na yi hakan ne kawai don ina buƙatar taimakonka a gobe.... Amma idan ka gama, kowa ya san inda yake."

King Diamond ya saki wani ƙasaitaccen murmushi, ya matso kusa da ita har tana jin ɗumin numfashinsa..

"Kin fi kowa sanin cewa zuciyarki ba haka take faɗa ba. Amma zan bi ki a yadda kike so... Gimbiya ta."
Ayat ta kawar da kanta gefe, tana murmushin jin daɗi a ɓoye wanda ba ta son ya gani...
*Likes ɗinku shine albashin marubuci*

👍 Like
🔁 Share
💬 Comment


*👑 MASARAUTAR ALHAMRA 👑*

_🪄 Gidan Mulki, Iko da Sirrin Zuciya 🪄_

✍🏽 By ASMEETAH WRITER
~Hasken Jajirtattu~


💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️

```JARUMAI WRITERS TEAM```

▶️ DON BIYO DAGA FARKO 👇
🔗 WhatsApp Channel:
https://whatsapp.com/channel/0029VbBCNlqJUM2RQwWncg43

📚 ArewaPen:
https://arewapen.com/u/asmeetahwriter

📖 Wattpad:
https://www.wattpad.com/user/asmeetahwriter

📲 Contact:
09065443871

📅 FARA TURA BOOK:
🔥 01 — 01 — 2026 🔥

📘 BOOK ONE
```MATAKIN FARKO```
Chapter 37 · 0% Book details