← Book details Masarautar Alhamra Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 25 OF 42

CHAPTER 2️⃣3️⃣

Masarautar Alhamra Part 1 Complete Hausa Novel · about 18 min read

*بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيمِ*


Fadar Gimbiya Maayah ta zama Majalisar Ƙasaita a wannan ranar Party ɗin...

Kowane lungu da saƙo an yi masa ado da fitilun zinare masu haske, ƙamshin furanni masu tsada da aka shigo da su daga ƙasashen waje ya cika wurin.. Waƙar Classic Jazz mai ratsa zuciya tana tashi a hankali a cikin babban zauren taro...

Gimbiya Maayah ta fito cikin wata Doguwar Rigar Sarauta mai ƙyalli, wadda ta fi kowane abu a wurin tsada. Da kyar ake iya jure kyawun ta da ajiinta. Tana tafiya a hankali, kamar tana taka gilashi, fuskarta a ɗaure, babu murmushi, ba fara'a...

A lokacin da Maayah ta fara tafiya cikin babban falonta da aka ƙawatar, duk waɗanda suke wurin sun tsaya cak. Aƙalla mutane 50 ne suka duƙar da kai, suna girmama Girman Kan Gimbiya... Ta kalle su, ba tare da ta nuna ko ɗan tausayi ba..

Ta hango wani saurayi wanda shi ne kawai bai duƙar da kai ba, wani Ɗan Gidan Babban Minista mai suna Zaidu.... Zaid ya miƙe tsaye, yana murmushi cike da sha'awar ta...

Maayah ta wurga masa wani irin kallo, tana nuna shi ta ce,

“Kai! Tashi ka bar wurin nan! Na gaya wa Mama Liyatu cewa ban buƙatar ganin talakawa a cikin fadata. Kuma kai, ba ka da gata da za ka tsaya ka kalle ni kai tsaye! Ka fita yanzu, kafin in umarci Bodyguards su kore ka da ƙarfin tsiya.”

Zaid ya firgita. Ya duƙar da kai cikin gaggawa, fuskarsa cike da kunya, sannan ya fita daga wurin taron da sauri, ba tare da ya yi magana ba. Kowa ya ga wannan al’amari ya yi shiru, saboda sun san dole ne a bi dokokin Gimbiya tinda har masarautar ta aka zo..

Ta juya, tana gyara rigarta da hannu ɗaya...

“Mama Liyatu! Meye wannan? Ina nufin an tace jerin sunayen mutane ne kawai don ganin waɗanda suka dace su shigo fadata!”

Mama Liyatu ta matso da sauri, tace,

“Kiyi haƙuri, Gimbiya. Wataƙila an shigo da shi a cikin rukuni ne. Zan tabbatar an ƙara tsananta tsaro!”

A daidai lokacin da Gimbiya Maayah ke cikin kololuwar kasaitarta, cike da girman kai da jin ikon sarauta, Mama Liyatu ta sulale zuwa ɗakin kula da tsaro, domin duba faifan bidiyon Security (CCTV) na ƙofar shiga fadar..

Manufarta ɗaya ce ta tabbatar cewa babu wani talaka ko wanda bai cancanta ba da ya samu damar shiga cikin Fadar Sarauta.
Cikin faifan bidiyon, wani abu mai firgitarwa ya bayyana a idonta.
Ta ga wani mai gadi, sanye da uniform na tsaro, ya shiga wani ɗaki na sirri a bayan kitchen. Bayan ƴan daƙiƙu, ya fito da ƙaramin kwalba mai ɗauke da ruwa. Da sauri ya nufi cikin kitchen, inda aka tanadar da kayan sha na musamman na Gimbiya, ya zuba ruwan cikin gilashin lemun tsami da aka shirya domin Maayah.
Idanun Mama Liyatu suka kaɗa da tsoro. Jikinta ya yi sanyi...

"Guba!?..."

Ba shakka, wannan yunƙuri ne na kashe Gimbiya Maayah.

A dai-dai lokacin nan ne aka ɗauki kayan sha aka nufi inda Gimbiya ke zaune.
Mama Liyatu ta tashi da gudu, tana huci, gumi na tsatstsafowa a goshinta. Ta manta da komai, rayuwar Gimbiya ce kawai a ranta...

Ta kutsa cikin zauren taron a guje, tana rawar jiki. Ta tarar da Gimbiya Maayah ta ɗaga gilashin lemun tsami zuwa bakinta...

“GIMBIYA! Don Allah ki tsaya!!”

Mama Liyatu ta ƙwala ƙira, muryarta na rawa saboda tsananin tsoro..

Maayah ta tsaya cak. Ta ɗauka Mama Liyatu ta zo ne don ta bata mata rai. Ta sauke gilashin a hankali, fuska cike da ɓacin rai...

“Mama Liyatu, me wannan hayaniya take nufi? Kin san ɗaga murya na lalata min walwala!”

Mama Liyatu ta durƙusa a gabanta, hawaye na zuba ba tare da shiri ba..

“Gimbiya ta, don Allah ki yi haƙuri. Wannan lemun guba ne! Wani ya saka miki guba a ciki! Rayuwarki tana cikin mummunan haɗari!”

Nan take hayaniya ta tashi a falon...

Maayah ta yi shiru na ƴan daƙiƙu…
Sai kawai ta tintsire da dariya, dariya mai cike da izgilanci da ɓacin rai...

“Security!” ta ɗaga murya da ikon Sarauta,

“Ku gano wanda ya kawo wannan gilashin. Yanzu nan take!”

Babban Bodyguard ya karɓi gilashin cikin gaggawa, aka kai shi ɗakin bincike. Mama Liyatu ta bayyana abin da ta gani a faifan bidiyo, mai gadi ne ya saka guba...

Ba a jima ba, aka kama mutumin yayin da yake ƙoƙarin tserewa ta ƙofar baya. An dawo da shi cikin falon taron, sanye da uniform na jabu, wanda ya nuna ba ɗan tsaron Fadar Sarauta ba ne..

An daure hannayensa ta baya, yana durƙushe a gaban Gimbiya Maayah..

Maayah tana zaune kan kujerarta cikin cikakkiyar kasaita...

“Ku fita mun daga nan!” ta umarci duk baƙin Party ɗin...

“Wannan ba nishaɗi ba ne hukunci ne na Sarauta!”

Kowa ya fita cikin fargaban kashen gimbiya da ake shirin yi...

An bar Gimbiya Maayah, Mama Liyatu, da Bodyguards guda uku kaɗai a zauren..

Maayah ta ɗaga ƙafarta a hankali. Takalmin mai tsini wanda farashinsa ya kai na motoci da dama ta ɗora shi a kan kafaɗar mutumin da ke durƙushe...

“Yanzu ka gane inda ka shigo ko?” muryarta cike da izgilanci...

“Ka zo Fadar Sarkin Alhamra domin ka kashe Gimbiya? Wa ya turo ka? Wa ya ba ka izinin saka uniform ɗin mu?”

Mutumin ya kasa magana, yana haki saboda tsoro.
Maayah ta danna ƙafarta a kafaɗarsa da ƙarfi...

“Kin ga ko, Mama Liyatu? Rashin ladabi har ya kai wannan matsayi.”

Ta ɗaga ƙafarta, ta kalli Bodyguards ɗinta da tsauri...

“Wannan hukunci na! Ba zan zubar da jininsa a nan ba, saboda kada ya ɓata min wannan falon mai tsarki. Amma rayuwarsa ta ƙare tun yanzu!”

Ta juya zuwa Mama Liyatum..

“Ki kira Masu Gadi na Musamman.Ku tafi da wannan ƙazamin mutumin zuwa Fourth Chamber!
Ku rufe shi a can. Ku tabbatar cewa kafin faɗuwar rana babu wani alamar rayuwarsa a duniya!”

Mama Liyatu ta runtse ido. Ta san Ɗakin Huɗu wuri ne da ba wanda ya taɓa fita da rai...

“An gama, Gimbiya. Za a yi kamar yadda kika ce.”

Maayah ta tashi ba tare da ta nuna ko ɗigon tausayi ba. Ta kalli gilashin guba, ta girgiza kanta...

“A kawo min sabon lemun tsami mai sanyi. A tsabtace wannan falon kamar ba'a taɓa taka shi ba. Party ɗin nan zai ci gaba!”

Ta juya zuwa ɗakin gyaranta...

A bayanta Bodyguards suka ɗauki mutumin, suka nufi Ɗakin Huɗu....

Can Gimbiya Maayah ta sake mamaye falon da kasaitarta...
kamar babu abin da ya taɓa faruwa..
Kudi, iko, da gata sun gama lalata zuciyarta…


A tsakiyar falon, inda aka gyara shi da labulen alharini, wasu Masu Rawa daga Indiya da aka ɗauko na musamman sun fito...

Mata guda uku da maza biyu, sanye da kayan rawa na gargajiya..
Sun fara rawa mai ban sha’awa (Indian Dance) cike da tsari da fasaha, inda suke juyawa da yin motsin kai da ido na musamman....Anan Maayah take zaune a kan Kujerar alfarma mai ƙasaita, tana kallo ba tare da ta nuna ko ɗan sha'awa ba...

Waƙar Indiya mai daɗi ta cika wurin, kuma Masu Rawa na ƙoƙarin nishaɗantar da Gimbiya ta kowace hanya. Sauran baƙin Party ɗin sun yi shiru, suna kallon rawar da kuma Gimbiya, wadda ta fi kowa muhimmanci a wurin...

Ana cikin wannan nishaɗi na ƙasaita sai aka ji wata ɗan hayaniya a babban ƙofar fadar... Hayaniyar ta kasance muryar mutum ɗaya wanda ke masifa da ƙarfi..

Nan take, wani Bodyguard ya shigo da girmamawa ya durƙusa a gaban Maayah...

“Gimbiya, Babban Minista Alhaji Bello yana waje. Ya zo da zafi yana masifa. Yana neman ganin ki a kan dalilin da ya sa kika wulaƙanta ɗansa, Zaid... Muna ƙoƙarin hana shi shiga saboda yanayin zafin ransa.”..

Maayah ta yi murmushi wanda ya nuna cewa ta shirya domin faɗa... Ta ɗaga hannu, ta yi nuni ga Masu Rawar Indiya da su tsaya...

“Ku barshi ya shigo. Idan har Babban Ministan ƙasa zai zo ya yi min faɗa a gidana, to zan nuna masa matakin sarauta da ikon Gimbiya Maayah! Ku barshi ya shigo. Kuma ku kawo Zaid tare da shi.”

Bodyguards suka buɗe ƙofar. Minista Bello ya shigo, fuskar sa cike da ɓacin rai... A bayansa kuma Zaid ne wanda yake duƙar da kansa saboda kunya...

“Gimbiya! Me kika yi haka?! Wa ya ba ki izinin kore min ɗa daga Party?! Na san cewa Sarki baya nan ne, amma wannan bai ba ki ikon wulaƙanta Babban Minista ba! Ni ba talaka ba ne! Ina da kuɗi! Ina da gata!”

Ministan ya fara masifa, muryarsa cike da zafi.
Nan da nan, Bodyguards guda biyu suka matso kusa da Ministan...

“Mai Girma Minista, don Allah ka sassauta muryarka. Kana cikin Fadar Sarauta ne!”

Amma Maayah ta ɗaga hannu....
“Ku kyale shi. Ina son in ji duk abinda yake da shi. Bari Minista ya yi speech.”

Minista Bello ya ci gaba da masifa, har ya kai ga zagin rashin ladabin Gimbiya... Ya rufe da cewa...

“A tunani na, za ki yi hankali. Amma a’a! Kuɗi da gata sun lalata ki!”

Bayan ya kammala, Maayah ta gyara zamanta a kan kujera. Ta lumshe idanunta tana kallon Minista da ɗansa, kamar tana kallon kashi. Ta fara magana da murya mai sanyi mai shiga jiki!...

“Minista, ka kammala? Zan fara da kai, Zaid.... Ka san dalilin da ya sa na kore ka, ko ba haka ba? Bari in tuna maka!”....

Maayah ta kalli Ministan...

“Minista Bello, ɗanka bai san matsayinsa ba! Yana da fitsara! Yana abu irin na ƙazaman mutane!”

Ta sake juyawa ga Zaid...

“Ka zo Party na, sannan ka aiko min da letter na soyayya a cikin makaranta! Letter! Wai kai har kasan soyayya? Ni Gimbiya ce! Ni ba ƴar makaranta ba ce da za a aiko mata letter na soyayya! Wannan wulaƙanci ne!”

Ta kalli Minista Bello, idonta cike da ƙasaita...

“Minista, ka ce kana da kuɗi da gata? To, ikon sarautata ya fi kuɗin da gatanka! Kuma a cikin wannan fadar, ni ce Sarauniya! Kana gani? Ka raina ni ne saboda mahaifina baya nan? To, ka sani, babu wanda Gimbiya Maayah take jin tsoro a duniya! Ko Shugaban Ƙasa ne! Idan har ɗanka ya sake min kallo na soyayya, ko kuma ya sake zuwa kusa da ni, to zan kore ka Minista! Zan cire maka mukaminka har abada!”

Ta ɗaga hannu...

“Bodyguards! Ku fitar da waɗannan mutanen marasa aji daga nan! Kuma ku tabbatar ban sake ganinsu ba a cikin Fadar masarautar Alhamra har abada!”...

Minista Bello da ɗansa Zaid sun ji matukar kunya da kuma tsoro! An ja su da ƙarfin tsiya daga cikin taron...

Maayah ta jingina a kujerar ta, fuskar ta cike da nasara...

★★★

Bayan korar Minista Bello, Fadar Maayah ta koma shiru, amma tashin hankali ya mamaye zukatan baƙin da ke wurin, sam babu wanda ya ji daɗin wukaƙancin da Maayah tayi wa minista....

A kan kujerar ta, ta jingina, fuskarta cike da baƙin ciki da gajiya....

​“Mama Liyatu, raina fa ya sosu,”

Maayah ta yi magana da murya mai sanyi...

“Wannan Party ya zama cikin kasala! Ba ni da farin ciki! Komai a gidan nan yana da tsari, amma babu nishaɗi.”

​Mama Liyatu ta durƙusa, hannunta a ƙirji...

“Allah ya taimaki Gimbiya, ya huci zuciyarki mai jiran gado. Komai zai daidaita.”

​Maayah ta juya kai...

“Ba wannan nake so ba! Ina so a nemo mun wasu mutane masu barkwanci! Waɗanda za su iya sanya raina nishaɗi! Ina so in manta da wannan ƙazantar mutanen da suka fita..!”

​Mama Liyatu ta yi saurin miƙewa...

“An gama, Gimbiya! Za a nemo miki ƙwararru! Allah ya taimaki Gimbiya mai jiran gado!”

​“Duk wanda ya sanya ni farin ciki,”

Maayah ta ƙara,

“yana da kyauta mai tsoka! Har da mota da gida! Amma idan ka ƙara ɓata min rai… za ka ga tashin hankali!”

​Nan take, aka sanar a birnin cewa Gimbiya Maayah tana neman masu barkwanci don sanya ta farin ciki, kuma kyauta mai tsoka na jiransu....

Cikin ɗan gajeren lokaci, mutane kusan talatin masu neman kyauta suka cika ƙofar Fadar..

​Maayah ta kalle su ta faifan bidiyo (CCTV)...

“Mama Liyatu, ina buƙatar nishaɗi, ba tattara datti ba! Ba na buƙatar yawan wannan ƙazanta! A zaɓi mutum biyar kawai masu ɗan tsabta a ciki. A korar sauran da bulala don su san cewa Fadata ba gidan wasan kwaikwayo ba ce!”

​Hakan kuwa aka yi. Bayan minti talatin, an kawo masu barkwanci guda biyar a gaban Gimbiya Maayah, dukansu sanye da sabbin tufafi kuma suna cikin tsoro...

​Maayah ta zuba musu ido ɗaya bayan ɗaya...

“Shin zaku iya sanya ni farin ciki? Ni ba kamar sauran bane, ni Gimbiya Maayah ce. Ku san cewa ina da wuya wajen dariya.”

​Ta sake ɓata rai...

“Duk wanda bai sanya ni nishaɗi ba, zai sha bulala 50 a gaban kowa! Kowa zai fito, cikin minti ɗaya ya yi barkwancinsa. Idan kuma duk ku ka sanya ni farin ciki, zan baku kyauta mai tsoka gaba ɗaya!”

​Dukansu mutum biyar ɗin suka hadɗiye yawu cikin tsoro...

​Na Ɗaya:

Wani saurayi mai ɗan lukuti ya fito.... Ya fara rawa ta barkwanci yana lanƙwasa jiki, ya fara wata baƙon sauti kamar kukan akuya...

​Maayah ta sauƙe kai, ta toshe kunnenta da hannu...

“Mama Liyatu! Wane ne wannan? Meye wannan sautin na dabba? Ya ɓata min rai! Ku janye shi! Kuma ku tabbatar ya sha bulala 50 kafin ya fita daga gate ɗin mu!”

​Nan take, Bodyguards suka ja shi da ƙarfi, ya fara neman gafarar su...

​Na Biyu:

Wani dattijo ya shigo, ya fara salon sa na tsohuwar barkwanci ta hanyar ƙoƙarin yin yabon Maayah ta ƙarya...
​Maayah ta zuba masa ido. Hawaye suka fara zuba mata, na baƙin ciki da bacin rai...

“Ku! Meye wannan? Kuna nufin baƙin ciki yake so ya sanya ni? Wannan ya fi mai yunkurin kisa ɗin nan ɓata min rai! Ku koreshi! Bulala 50!”

​Na Uku:

Wani mai tumbi ya shigo, ya sanya wani abu a baya da ya ƙara masa girman ɗuwawu. Ya fara lanƙwasa jiki yana motsa tumbin sa da duwawun sa a salon wasa...

​Maayah ta fara ƙoƙarin amai! Ta rufe bakinta da hannu....

“Wai ku! Meye wannan ƙazantar banza! Wannan datti ne! Wannan cin zarafin Sarauta ne! Ku cire min shi daga nan! Bulala 60 saboda ya sanya ni amai...!”

​Na Huɗu:

Wani saurayi mai ƙarfi ya shigo. Ya fara ƙirari da yabon Sarauta da gata...

“ƴar Sarki jikar Sarki! Taka lafiyarki, ƴar gata! Hasken birnin Alhamra!” Haka ya ci gaba da yi da girmamawa mai yawa...

​Maayah ta kawar da kai cikin gajiya...

“Wannan kirari a kowace rana ana min! Idan ma ba a yi min ba, sai an ga tashin hankali! Don haka, kaima ka ban wuri! Ka tafi! Babu wani abu na musamman a cikin kirari! Bulala 50!”

​Na Biyar:

Shi ne mafi tsoro a cikin su. Ya ga yadda Gimbiya Maayah take ba da hukunci. Ya shigo, duk jikinsa na rawa, ya durƙusa a gaban Gimbiya. Yana kuka cike da tsoro!

​“Dan Allah ki yi haƙuri! Na san ba zan iya sanya ki farin ciki ba! Wallahi inada Basir! Zai iya motsa wa saboda wannan tsoron! Ga tamowar da ke damuna! Wayyo Gimbiya! A gafurce ni...bulala hamsin zan iya rasa rayuwata ga iyalai..."

​Nan take, Gimbiya Maayah ta fara dariya! Dariya ta gaske, ba tare da shautin da yake fita ba kamar na marasa aji, sai dai murmushin nishaɗi..

​“Basir kuma? Subhanallah! Hahahaha!” Ta riƙe fuskarta, tana murmushi da nishaɗi!

“Tamowa! Hahaha!”

​Mutumin ya yi mamaki, shi ma bai san cewa wannan roƙo na tausayi zai zama barkwanci ba...

​Maayah ta tsaya, tana dariya cikin class. Ta nuna shi da yatsa...

“Kai ne! Mama Liyatu, wannan mutumin ya yi nasara! An sanya ni farin ciki da tamowa da Basir! Wannan shine nishaɗi na gaskiya!”

​Ta umarta cikin nishaɗi..
“A ba shi kyauta mai tsoka! Motar alfarma, gida mai kyau, da kuma Kuɗi masu yawa! Sannan a ba shi likitan basir da ya dace! Amma sauran, duk su sha bulala 50 kowa!”

​Gimbiya Maayah ta samu dariyarta a kan mugunta da kuma tausayi..

Mama Liyatu ta matso kusa da ita ta furta..

"Gimbiyata, sauran a musu sassauci mana, bulala hamsin yayi yawa kuma basu san da wannan hukuncin ba..na san ki da tausayi, a musu adalci..."

Gimbiya Maayah ta sassauta murya ta ce,

"Sauran ma, a basu dubu ɗari-ɗari saboda son taimaka mun nayi dariya..."

Mama Liyatu tayi murmushi domin wani sa'in gimbiya Maayah nada sauƙin kai...

Hakan kuwa akayi..

Bayan nan
Gimbiya Maayah ta zauna, amma nishaɗin ya mutu kamar wutar da iska ta hura.... Ba ta wuce minti biyu ba, sai ta miƙe, fuskarta ta koma taurinta na dā...

“Mama Liyatu, na gaji! Wannan Party ya ishe ni. Ina buƙatar hutawa!”

Mama Liyatu ta durƙusa da sauri. “An gama, Gimbiya. Za a yi yadda kika ce.”

Maayah ta kalli falon taron, wanda har yanzu akwai baƙi masu gata da kayan ciye-ciye masu tsada...

“Mama Liyatu! Ina nufin kowa ya watse yanzu! Ba na buƙatar ganin kowa a cikin Fada na! Wannan taro ya ƙare! Ku watsar da komai, ko da kuwa nawa ne kuɗin da aka kashe a kan wannan abincin marasa amfani!”

Mama Liyatu ta yi sauri ta tura Bodyguards da masu aiki don su fitar da kowa...

Cikin lokaci ƙanƙani, an watse taron! An kashe fitilu, an rufe ƙofa, kuma duk abincin Ƙasaita da aka kawo ya zama datti!..

Gimbiya Maayah ta shiga ɗakinta, baƙin ciki da gajiya sun koma mata.....


✨✨✨

Ayat ta shigo ɗakin baccinta cike da fara'a, ɗauke da manyan kulolin abinci na alfarma waɗanda aka girka na musamman..

"Lokacin cin abinci!"
ta faɗa cikin sanyin murya tana kallon Reems...

Yau ta ƙuduri aniyar cin abincin dare tare da abokinta kuliya. Ta ajiye tiren abincin, sannan ta juya zuwa sashen sutura don ta cire manyan kayan gimbiyancinta ta sanya lallausan kayan bacci domin ta saki jikinta...

Yayin da Ayat ta ba da baya, King Diamond a siffar kuliya ya daki hancinsa da wani irin kamshin kifi mai daɗi... Tun da yake a duniyar mutane, bai taba jin yunwa irin ta yau ba. Cikin hanzari, ya yi amfani da kafafunsa ya dinga bubbuɗe kulolin abincin. Ganin irin daɗin kifin da aka sarrafa, ya kasa jurewa...

Ya fara ci, sai da ya cinye kula na ɗaya tass.... Ya koma kan kula ta biyu, nan ma ya cinye tass, bai rage ko loma daya ba!..

Ayat ta nufo wurin abincin tana gyara gashinta, amma tana isa, ta tarar da kulolin wayam! Ta zaro ido, numfashinta ya kusa tsayawa...

"Wayyo! Duk ka cinye abincin? So kake na kwana da yunwa?"

Ta faɗa cikin murya mai cike da shagwaɓa...

"To ni yanzu me zan ci? Idan na sake komawa neman wani abincin, za su fara zargin me nake yi da abinci mai yawa haka, ni da ko rabi kula bana iya cinyewa!"...

Ganin Reems yana kokarin nufar wata karamar kula dake dauke da ferfesun kifi mai yaji, Ayat ta yi sauri ta janye kular...

"Wannan ma ba za a bar min ba?" ta faɗa tana turo baki...

Reems ya lallaɓa ya koma gefe ya kwanta kamar wanda aka zalunta...

Ganin haka, zuciyar Ayat ta karaya...

"Laaa... kar ka yi fushi My Reems... ga madara bari na baka."

Ta zuba masa madara mai ɗumi a kwanon azurfa, nan ma tass ya shanye gaba daya...

"Allah, ka cika ci da yawa! Zamanka sai a lambu!"

ta furta tana dariya da kuma mita...

Ta ɗauki ferfesun kifin ta kai loma ɗaya a baki, amma sai ta ga Reems ya zuba mata idanunsa na zinare, yana kallon lomar da take kaiwa...

"Na shiga uku! Wannan ma ba za ka bar min ba?"

Ta numfasa, sannan ta ce,
"To shikenan, bari na gani ko kana sona, za ka bar min wannan?" Ta ajiye masa kular...

Ai kuwa, King Diamond bai ko yi wata-wata ba, ya lankwame ragowar kifin nan tass!...
Ayat ta saki baki tana kallonsa, sannan ta fara kukan shagwaɓa tana shure-shure...

"Mugun kuliya!"

Ta miƙe ta nufi firij ɗinta, ta ɗauko fruits ta zauna can nesa da shi, ta fara cin apple ɗinta cikin ɓacin rai, tana kau da kai don kada ta kalle shi ta ji tausayinsa har ta ba shi ragowar...

King Diamond ya zauna yana lashe bakinsa, yana kallon yadda take cin apple ɗinta cikin fushi... A ransa ya ce,

"Ayat, da kinsan irin daɗi da nake ji na cewa yau kin zama uwar gida dake ciyar da ni, da tabbas ba zaki yi fushi ba."...


Ayat tana zaune a kan kujera can nesa da gadon, tana cin apple ɗinta cikin fushi, tana tauna shi da ƙarfi kamar tana tauna Reems ne....

Tana jujjuya ƙwayar idanunta, tana kau da kai duk sanda ta ji motsin kuliyar. Ta ƙuduri aniyar ba za ta kula shi ba har sai gari ya waye, domin kuwa ya kwashe mata duk abincin da take takama da shi...

King Diamond, dake cikin siffar kuliya, ya lura cewa wannan karon fushin na gaske ne. Ya san cewa idan bai yi dabara ba, Ayat ba za ta ba shi damar kwanciya kusa da ita ba yau....Ya miƙe a hankali, yana takunsa na kuliya mai sanyi, ya fara lallabawa har zuwa ƙafafunta...

Ya fara goga kansa a jikin lallausar fatar ƙafarta, yana fito da wani siririn sauti na kuliya mai ban tausayi...


Ayat ta ji sanyin gashin Reems a fatarta, ta yi ƙoƙarin janye ƙafarta tana mita...

"Ka tafi can! Mugun mai ci da yawa kawai. Ka cinye min shinkafa, ka cinye min tuwon shinkafa, ka cinye min kifi, ka cinye min ferfesun kifi, sannan ka shanye.. madara, yanzu kuma me kake nema? Apple ɗin ma so kake ka cinye?"

Duk da maganganun da take yi, ta kasa jure yadda Reems ya ɗaga kansa yana kallonta da idanunsa masu sheƙi, kamar yana roƙon gafara. Ya yi tsalle ya dawo kan cinyarta, ya fara goga hancinsa a hannunta dake riƙe da apple.

Ganin yadda ya dage wajen ba ta haƙuri, sai Ayat ta fara murmushi, har dariya ta fara subuce mata....

"Allah ya shirye ka Reems, ba ka da dama! To shi ke nan, tunda ka zama mai neman afuwa, bari na raba maka wannan."

Ta gutsuri ɗan ƙaramin guntun apple ta sanya masa a baki...

King Diamond ya karɓa ya fara taunawa, duk da cewa ba shi ne abin da yake so ba, amma taɓa shi da take yi da kuma murmushinta ya fi masa kowane irin abinci daɗi. Ayat ta rungume shi, tana shafa bayansa..

"Ka ga yadda kake da kyan gani? Idan ka daina wannan kwaɗayin, zan fi kowa daɗin zama da kai."

Ta koma kan gado tare da shi, tana jin wani irin natsuwa. Ta manta da duk wani damuwa. A wannan daren, ita da Reems ne kawai a duniyarsu ta daban. Ta kwanta tare da shi, tana raɗa masa a kunne..

"Wani lokacin ina jin kamar kana fahimtar kowace magana da nake yi, Reems.... Shin kai wanene ne a asali?"

King Diamond ya lumshe ido, yana jin ɗumin jikinta. A ransa ya ce,

"Ina fatan ranar da zan amsa miki wannan tambayar, Ayat, ba za ta zama ranar da za ki guje ni ba."....

*Likes ɗinku shine albashin marubuci*

👍 Like
🔁 Share
💬 Comment


*👑 MASARAUTAR ALHAMRA 👑*

_🪄 Gidan Mulki, Iko da Sirrin Zuciya 🪄_

✍🏽 By ASMEETAH WRITER
~Hasken Jajirtattu~


💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️

```JARUMAI WRITERS TEAM```

▶️ DON BIYO DAGA FARKO 👇
🔗 WhatsApp Channel:
https://whatsapp.com/channel/0029VbBCNlqJUM2RQwWncg43

📚 ArewaPen:
https://arewapen.com/u/asmeetahwriter

📖 Wattpad:
https://www.wattpad.com/user/asmeetahwriter

📲 Contact:
09065443871

📅 FARA TURA BOOK:
🔥 01 — 01 — 2026 🔥

📘 BOOK ONE
```MATAKIN FARKO```
Chapter 25 · 0% Book details