CHAPTER 9️⃣
Masarautar Alhamra Part 1 Complete Hausa Novel · about 13 min read
*بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم*
Ba zato ba tsammani sararin samaniyar Alhamra Kingdom ya sauya launi... Wata irin nutsuwa ta ba-zata ta mamaye garin, nutsuwar da ta fi karfin hankali...Tsuntsayen da suke ta rera waƙa a saman bishiyoyi duk sun yi shiru tamkar an zare musu rai... Iskar dake kaɗawa ta tsaya cak. Mutanen gari ne suke ta rarrabe idanu, kowa ya ji a jikinsa cewa akwai wani abu mai nauyi dake tunkaro su...
Daga can nesa aka fara jin wani irin tafiya na musamman, kwatsam sai ga jerin motocinsa sun bayyana a ƙofar gari.. Motoci ne bakake wuluk waɗanda babu irinsu a faɗin duniya, sheƙinsu kaɗai ya isa ya makantar da idon da ya ƙura musu...
Ba mutum ɗaya ba, ba goma ba motocinsu sun fi hamsin, suna taho wa a jere tamkar kyanwar daji...
A cikin kowace mota, akwai zafafan Bodyguards sanye da baƙaƙen kaya irin na jami'an tsaron Amurka... Fuskokinsu a murtuke, idanunsu sanye da bakaken gilashi, ba sa kallon dama balle hagu...
Wannan runduna ta Pavilion Kingdom ba wasa ta zo yi ba. A hannun kowane soja dake kan motocin, akwai wasu zafafan bindigu waɗanda kallo ɗaya zaka yi musu kasan cewa na zamani ne. Ga wasu dogayen takuba a kugunsu masu sheƙi tamkar madubi, waɗanda ke nuna cewa idan aka zaro su, to jini ne kawai zai mayar da su dauɗarsu...
Duk waɗanda suka kalle su a cikin garin Alhamra, sai da ya daskare a inda yake. Waɗanda suke jin labarin Pavilion kawai a matsayin tatsuniya, yau sun ga zahiri.. Kowa ya tsorata, tsoron da ya sa numfashi ma ya zama wahala.
Kai tsaye rundunar ta shine cikin babban masarautar, sun jeru tin daga bakin fada har zuwa babban gate...
Babban jami'in dake jagorantar aiken ya fito, ya shige cikin fadar sarki ya miƙa wata wasiƙa mai ɗauke da tambarin Pavilion, wani tambari mai kwarjini da firgitarwa...
A cikin fada, Sarki Nourdeen ya miƙe tare da karɓan wasikar da hannu biyu, amma yana buɗewa idanunsa suka firfito, hannunsa ya fara karkarwa. Sakon a gurguje yake amma yana da nauyin dake iya rushe masarauta...
_"Ina nan tafe. Zan shigo ƙasarka ta Alhamra City nan ba da daɗewa ba. Lokacin cika yarjejeniyarmu ya yi."_
Sarki ya sulale ya zauna a kan kujerarsa ta sarauta, gumi ya fara keto masa duk da sanyin dake wurin.. Tsoronsa daya shine yarjejeniyar Sirri dake tsakaninsa da Pavilion. Lokaci ya yi, kuma Sarkin Pavilion ba ya yafe alkawari...
Ya kalli fadawansa waɗanda kowanne ya zama mutum-mutumi saboda tsoro. Idan har waɗannan ma’aikatan aike ne kawai kwarjininsu ya kai haka, ina ga shi kansa Ogan? Mutumin da sunansa kaɗai ke sanya sarakuna su rasa baccinsu..
Masarautar Alhamra ta shiga cikin duhu, kowa ya san cewa babban yaƙi ko babban canji yana nan tafe...
A sashen Gimbiya Aayat, tana zaune a babban falonta cikin shigar alfarma na sarauta, tana cin fruits a nutse tana ƙoƙarin danne damuwar takurar da ma'aikatanta suke mata... Kwatsam, sai ga wani ma'aikacinta ya shigo a guje, ko neman izini babu jikinsa na rawa tamkar wanda aka yi wa bushara da mutuwa..
"Ya ke Gimbiyata, a gafarce ni! Wannan yanayin na yau ya girgiza kowa, hatta sarki kansa!"..
Ayat ta ji gabanta ya faɗi... Idan har mahaifinta, babban zaki na Alhamra ya girgiza, to lallai al'amarin ba karami ba ne. Cikin dake wa ta ce, "Me yake faruwa?"
"M... mu... mutanen Pavilion Kingdom ne suka zo!"
A zabure Ayat ta miƙe, tana zazzaro manyan idanunta...
"Pavilion Kingdom?"
Ta maimaita cikin rawar murya. "Shi da ake jinsa a cikin littafin almara da labaran tsoro, yau ya tabbata a cikin wannan masarautar?"
Zuciyarta ta fara bugawa da sauri, tana tunanin ko wane irin asiri ne ya kusa bayyana haka...
✨✨✨
A can ɓangaren Gimbiya Maayah, tana kan electric treadmill tana gudu sosai. Gumi ya jiƙe mata jiki, gashinta ya bazu a baya.. Ba wai don lafiyar jiki kaɗai take wannan gudun ba, tana gudu ne don ta tsira daga tunanin Inuwa da kuma damuwar dake cunkushe a zuciyarta.
Kowane taku dake bugawa a kan injin, tamkar yana rage mata zafin kishin dake ranta ne. A kan wannan injin, Maayah ba gimbiya bace, mace ce kawai dake neman sauƙi a cikin azabar tunani.
Tana tsaka da wannan gudun, sai ga Mama Liyatu ta shigo wurin a guje, tana ƙwala kira..
"Gimbiya! Gimbiya!! Gimbiya!!!"
Maayah ba ta ko kalle ta ba, ballantana ta amsa, tana jin daɗin yadda gudun yake ɗibar mata kewa. Amma jin furucin Mama Liyatu na gaba ya sa jinin jikinta daskarewa..
"Kin ji labarin mutanen PAVILION KINGDOM sun shigo cikin masarautar nan kuwa?!"
Jin sunan Pavilion, Maayah ta firgita, ta nemi ta tsaya cak cikin tsoro, ta manta cewa tana kan injin dake gudu a kan high speed. Ba ta danna maballin dakatarwa ba, nan take injin ya wurgar da ita sama, tayi gaba ta faɗo ƙasa da ƙarfi!
Wani uban ƙara ya fito daga bakinta yayin da bayanta da ƙunkuminta suka daku a kan tattausan darduma mai tauri.. Faɗuwar ba ƙarama bace, domin numfashinta ne ya kusa ɗaukewa na ɗan lokaci..
Mama Liyatu ta kwala ihu, ta yo kanta da gudu tana kiran sunanta. Maayah tana kwance tana murƙususu, azabar dake jikinta ta haɗu da tsoron jin sunan Pavilion ya sanya ta rasa inda za ta sa kanta..
Duk girman kan Maayah da izzarta, yau gwiwoyinta sun yi sanyi. Zuwan mutanen Pavilion ya canja komai a cikin mintuna kalilan....
✨✨
A sashen Gimbiya Yumna, tana tsaye a cikin kitchen tare da wasu ma'aikatanta, domin Yumna mutum ce mai sauƙin kai da son mu’amala da na ƙasa da ita. Tana tsaka da yanka kayan marmari a kan tray, tana murmushi, sai ga wata baiwa ta shigo falon kitchen ɗin a guje tana haki.
"Gimbiya kallo ya barki! Yau mutanen Pavilion Kingdom ne suka zo cikin masarautar nan!"
Wani irin bugawa zuciyar Yumna ta yi, ta ji wani jiri ya ɗibe ta. Ba ta san lokacin da wuƙar hannunta ta suɓuce ba, ta yanke mata yatsa. Jini ya fara zuba amma Yumna ba zafin yankan take ji ba, zafin sunan da ta ji ne ya ratsa kowane sashi na jikinta. Ta ajiye wuƙar, ta juyo idanunta tab da hawaye. Hawaye ne na farin ciki da tsofaffin tunani dake ƙoƙarin dawowa...
Ganin yadda take kuka, sai baiwar ta ƙara da cewa..
"Amma Gimbiya, mutanensa ne kawai suka zo, shi Sarkin Pavilion bai bayyana kansa ba, saƙo kawai suka kawo."
Nan take farin cikin Yumna ya dashe, murmushin dake ƙoƙarin bayyana ya koma ciki. Ma'aikatan suka zagaye ta cikin damuwa, suka ɗauki auduga da magani suka treat ɗin yatsarta da ta yanku, sannan suka raka ta har bedroom ɗinta don ta huta.
Bayan ma'aikatan sun fita, Yumna ta tabbatar ta kulle ƙofar ɗakin. Ta nufi wani sashe na drawer ɗinta dake ɓoye a gefe guda, ta buɗe ta da rawar hannu. Ta zaro wani ƙaton hoto wanda aka adana shi da matuƙar kulawa..
Hoton wani tsararren sarki ne, kyakkyawa na gaske, fari mai kwarjini, sanye da kayan sarauta waɗanda aka ƙera su da gold.
A gefen damansa akwai wani kyakkyawan yaro, haka a gefen hagunsa akwai wani yaron, twins ne maza waɗanda kyawunsu ya kusan ninka na mahaifinsu...
Amma babban abin da ya sa Yumna fashewa da kuka shi ne hoton wata ƙaramar yarinya, wacce ba za ta wuce shekara biyu ba, tana zaune a kan cinyar sarki a tsakiya. Wannan yarinyar ba kowa bace face ita kanta Yumna...
Yumna ta fashe da wani irin kuka mai cin rai, kukan da ta daɗe tana tura shi a can ƙasan zuciyarta. Ta fara shafa fuskokin twins ɗin da mahaifin dake cikin hoton da yatsunta dake ɗauke da bandage..
"Kun kusa dawowa? Ko kuwa ni ce zan dawo gare ku?"
ta faɗa cikin muryar kuka.
Ta ɗaga hoton ta rungume shi a ƙirjinta tana jin tamkar tana rungumar mutanen dake cikinsa ne. Wannan hoton shi ne kaɗai dangantakarta da asalin inda ta fito..
✨✨✨
Sashen Gimbiya Zayana
Lokacin da aka sanar mata, ta tsorata amma bata nuna hakan ba, ta yanke hukuncin zuwa yanda suke tayi ido huɗu da su....
A koda yaushe zuciyarta tambaya take waye Pavilion king? Meyasa yake ɓoye kansa sai dai labarinsa..
Saboda tsoron da ma'aikatanta suke basu sanar mata cewa shi bai zo ba, iya mutanensa ne...
Yayin da Gimbiya Zayana take takawa cikin fadar, idanun kowa na kanta. Wata baiwa mai suna Ladi ta yi kuskuren ƙura mata ido na wasu daƙiƙoƙi. Zayana ta tsaya cak, ta juyo a hankali, idonta ya sauƙa kan baiwar..
“Ke,”
Zayana ta furta da murya kamar sauƙan aradu...
“Idan kina da abin faɗa, ki faɗa. Idan kuma kallon kike, ki tabbatar kallo ne na ƙarshe.”
Ladi ta durƙusa da sauri, jikinta na rawa. “Af...afuwa nake nema, Gimbiya. Kwarjininki ne ya tafi da ni.”
Zayana ta ja tsaki, ta yi murmushin mugunta..
“Kwarjini ko tsoro? Ki sani, idan na sake ganin idonki a nawa ba tare da izini ba, to ranar za ki daina ganin hasken rana. Ɓace min da gani!”
Ladi da gudu tana karkarwa tabar wurin, Zayana kuma ta ci gaba da tafiya tana gyara yatsun hannunta, zuciyarta tana wasi-wasi kan dakarun Pavilion dake tsaye a waje..
A can cikin fadar, Sarki Nourdeen yana zaune a kan kujerarsa, gumi na keto masa. Ganin yadda rundunar Pavilion ta cika harabar fadar ya fahimci cewa idan ya bari Chief Onyx ya tako ƙafarsa zuwa Alhamra, to mulkinsa da mutuncinsa za su iya girgiza..
Cikin sauri ya ƙira babban sakatarensa, ya umurce shi da ya ɗauki alkalami da takarda..
"Rubuta masa saƙo yanzu," Sarki ya faɗa cikin murya mai nauyi.
" *Ka ce masa*.. Ba sai ka zo ba. Ni da kaina zan zo har inda kake."..
Sarki ya yi hakan ne domin kiyaye kansa. Ya san cewa idan Chief Onyx ya shigo fadar, sirrin dake tsakaninsu zai iya bayyana a idon gimbiyoyi da talakawan gari. Ya fi so ya tafi can yankin Pavilion ya fuskanci kaddararsa shi kaɗai, maimakon ya jawo bala'i cikin gidansa..
Duk da cewa zuciyarta ta ɗan buga ganin zafafan makaman da suke riƙe da su, sai ta dake. Ta ƙura wa babban jami'in dake jagorantarsu ido, wani gardi mai ƙaton jiki, sanye da baƙaƙen kaya da gilashi.
Jami'in Pavilion ya ɗago kai ya kalli Zayana. Ko kifta ido bai yi ba, kuma bai nuna alamun rurrusunawa ga matsayinta na Gimbiya ba. Wannan rashin girmamawa ya kusa sa Zayana ta fusata, amma kwarjinin da dakarun suke da shi ya sa ta haɗiye fushin. Ta lura cewa kowace mota tana ɗauke da tambarin Pavilion Kingdom, tambarin da take gani a matsayin kalubale ga mulkin mahaifinta..
"Ina yake?" Zayana ta furta a fili, muryarta na ratsa sanyin iskar wurin. Tana nufin Sarkin Pavilion.
Babban jami'in bai amsa ba...domin ko kallo bai isheta ba.
Sarki ya fito da kansa har bakin fadar, ya miƙa wasiƙar ga jami'in Pavilion dake jagorantar rundunar.. Jami'in ya karɓi wasiƙar ba tare da ya rurrusuna ba, ya buɗe ta ya karanta.
Zayana tana gefe guda tana kallon wannan dambarwar, tana mamakin me ya sa mahaifinta yake ƙasƙantar da kansa haka. Jami'in Pavilion ya jinjina kai, ya yi wa mutanensa nuni da hannu. Lokaci guda suka buɗe motocin su suka shiga, hayaƙin dake tashi ta rufe sararin samaniya yayin da suka fara ficewa daga fadar...
Zayana ta tsaya tana kallon yadda suka fara fita daga fadar cikin tsari da iko. Zuciyarta ta cigaba da wasi-wasi...
"Waye wannan Sarkin Pavilion ɗin? Me yasa kowa ke tsoronsa? Kuma me yasa kamanin mutanensa suke nuna cewa sun fi mu komai?"
Ta ƙaraso kusa da mahaifinta, tana kallon bayan motocinsu dake ɓacewa..
"Daddy, me ya sa za ka ce za ka je wurinsa? Shi wane ne da har zai sa ka bar masarautarka ka nufi tashi? Shin Alhamra ta zama ƙarƙashin ikon Pavilion ne ba tare da mun sani ba?"
Sarki Nourdeen bai ko kalle ta ba, ya juya cikin fada yana cewa, "Akwai abubuwan da kika fi ƙarfin sani Zayana..."
Bayan motocinsu sun ɓace wa gani, Sarki ya koma cikin ƙuryar ɗakinsa na dake yanzu baya tare da ko wace mata...
Bai so Chief Onyx ya zo nan domin idan ya zo, gidan sarautar zai iya zama tamkar gidan kallo, kowa zai so ya ga kwarjinin sarkin Pavilion, wanda hakan zai jawo tambayoyi marasa iyaka...
"Ba zan bari su ganshi a nan ba," Sarki ya raɗa wa kansa yana goge gumin goshinsa. "Idan ya zo nan, asirina zai ruguje a gaban ƴaƴana."...
An bar Gimbiya Zayana a tsaye, jikinta ya yi sanyi. Ta rasa gane dalilin da ya sa mahaifinta yake nuna wata irin fargaba a fili game da mutanen nan. ta juyo, tana takawa a hankali zuwa sashenta, kanta cike da tambayoyin da babu mai ba ta amsarsu.
Tana tafiya tana nazarin wasiƙar da ta ga an bayar, me ya sa sarki ya rubuta masa cewa ba sai ya zo ba? Shin me sarki yake tsoron zai faru idan kowa ya ga fuskar sarkin Pavilion?...
A can ɓangaren Gimbiya Chingching, labarin dake girgiza masarautar bai ma shigo cikin kunnenta ba. Tana zaune a kan lallausar sofa, idanunta sun ƙafe a kan TV tana kallon katun (ƴan gwaigwai), tana ta dariya tana turo baki idan aka daki ɗaya...
Wata ma'aikaciya dake gyaran falon, tana goge wani tebur kusa da ita, ta kasa jurewa sai da ta yi magana..
"Gimbiya Chingching, shin ba ki da labarin rundunar Pavilion Kingdom sun zo wannan masarautar ne?"
Chingching ba ta ko juyo ba, idonta yana kan TV, ta ce cikin shagwaɓa..
"Su waye kuma pabiliyooo...?"
Ma'aikaciyar ta ja numfashi, ganin cewa wannan yarinyar ba ta ma san me duniya take ciki ba. Ga kowa Pavilion tsoro ne da fargaba, amma ga Chingching, suna ne kawai mai wahalar faɗi. Ma'aikaciyar ta girgiza kai kawai ta ci gaba da aikinta, ta ga gara ma ta yi shiru...
Ganin ma'aikaciyar ta yi shiru, Chingching ta ɗan harare ta tana turo baki..
"Kumaaaa za ki dame ni! Yooo ni ina ruwana da wani wani wani mene sunan? Uhmmm ni ki ƙyale ni. Ni yunwa ma nake ji... Dubi ma yadda kike goge nan, kin tare min TV."
Chingching ta koma ta kwanta tana rungume da toy🧸 ɗinta.. tana jira a gama shirinta na abincin rana, yayin da duk gimbiyoyin gidan suke cikin zulumi, ita nata damuwar ba ta wuce abinci da ƴan gwaigwai ba....
Aayat tana can a nata sashen, tana ta zirga-zirga tamkar wadda aka yi wa bushara da saƙon mutuwa. Yau ta kasance rana ta musamman, domin kwata-kwata ba ta yi shigar Inuwa ba. Tana sanye da doguwar riga ta sarauta, gashinta da fuska a rufe ga farin glass akan dara-daran idanuwanta, tana jiran jin ko sarki zai ƙira duk gimbiyoyin don yi musu bayanin abin da yake faruwa...
Duk sanda ta ji motsin takun tafiya a waje, sai gabanta ya faɗi, tana tsammanin bafade ne aka turo ya ƙira su. Amma shiru, har dare ya raba sarki bai nemi kowa ba. Wannan shirun ya fi kowane hayaniya ban tsoro a wurinta, domin tana jin cewa mahaifinta yana ƙoƙarin rufe wani babban rami ne kafin kowa ya gani...
A ɗayan ɓangaren kuwa, Gimbiya Maayah tana can kwance a kan katafaren gadonta, fuskarta a murtuke ba wai don zafin ciwo kaɗai ba, har da takaicin rashin samun damar fita ta ga abin da idonta yake son gani... Faɗuwar da ta yi a kan treadmill ta bar mata raɗaɗi a ƙunkuminta da bayanta wanda ya sanya koda juyawa ta kasa yi..
Mama Liyatu tana zaune a gefenta, tana dunduma mata baya da tsumman da aka tsoma a ruwan zafi tana lallashi...
"Yi haƙuri gimbiyata,"
Mama Liyatu ta faɗa cikin sanyin murya..
"Gobe idan Allah ya kai mu likita zai zo ya duba ki, zai baki maganin da zai sa ki miƙe nan take."..
Maayah ta cije laɓe, tana kife da kanta akan gadon domin kibda ciki tayi...
Duk wani motsi ya tsaya a masarautar.... Ma'aikata suna tafiya ne a cikin sanɗa gudun kada su tayar da fushin sarki...
Domin a wannan ranar har zuwa gobe komai zai iya faru idan wani ya kuskura ya aiwatar da laifi wa sarki, domin a kansa za'a huce takaici...
Iskar daren tana kaɗawa da wani irin sanyi daban, mai ɗauke da ƙamshin dawakan Pavilion da wani irin ƙamshin hayaƙin motocinsu waɗanda suka riga suka bar birnin, amma kwarjinin motocin yana nan maƙale a zukatan mutane..
Kowa yana jiran gobe....
👍 Like
🔁 Share
💬 Comment
*👑 MASARAUTAR ALHAMRA 👑*
_🪄 Gidan Mulki, Iko da Sirrin Zuciya 🪄_
✍🏽 By ASMEETAH WRITER
~Hasken Jajirtattu~
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
```JARUMAI WRITERS TEAM```
⚠️ SANARWA⚠️
Wannan littafi dukiyata ce a matsayina na marubuciya.
⚖️ Ba a yarda wani ko wata ya:
kwafa
gyara
sauya
ko amfani da wani sashe na wannan labari
ba tare da izini na kai tsaye ba.
Duk wanda ya saɓa, alhaki yana kansa..
▶️ DON BIYO DAGA FARKO 👇
🔗 WhatsApp Channel:
https://whatsapp.com/channel/0029VbBCNlqJUM2RQwWncg43
📚 ArewaPen:
https://arewapen.com/u/asmeetahwriter
📖 Wattpad:
https://www.wattpad.com/user/asmeetahwriter
📲 Contact:
09065443871
📅 FARA TURA BOOK:
🔥 01 — 01 — 2026 🔥
📘 BOOK ONE
```MATAKIN FARKO```