← Book details Masarautar Alhamra Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 23 OF 42

CHAPTER 2️⃣1️⃣

Masarautar Alhamra Part 1 Complete Hausa Novel · about 28 min read

*بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيمِ*


King Diamond yana zaune a tsakiyar gadon Ayat, yana shaƙar ƙamshin turaren oud dake tashi daga jikin filon baccinta..

Fuskarsa dake ɗauke da annuri da kwarjini tana haskaka cikin duhun ɗakin. Ya kalli kansa a madubin da Ayat ta gama amfani da shi, ya ga yadda sumarsa fara sol ta dace da lallausan zanen gadon..

​"Reems..." ya furta a hankali, yana jin daɗin yadda sunan ya dawo masa da rayuwa ta sanadin Ayat. Duk da raunukan dake jikinsa, sumbar da ta yi masa a goshi ta zama tamkar maganin da ya fi kowane maganin tsafi ƙarfi....

​A can ƙasa a babban falon cin abinci, Ayat tana zaune ita kaɗai, an jera mata kalar abinci daban-daban na alfarma... Saratu tana tsaye a gefe tana yi mata hidima, amma hankalin Ayat baya kan abincin...

Tana tunanin Reems dake sama....kuliyar da ta yi amanna da ita...

​"Saratu," Ayat ta ƙira muryarta a dake..

"Na'am ranta ya daɗe," Saratu ta amsa cikin ladabi..

"Ina son ki haɗa min wani abincin a ƙaramin kwanon zinare, ki kawo min shi... Kuma ina son madara mai ɗumi."

Saratu ta ɗan yi mamaki,
"Gimbiya, ko har yanzu yunwar ba ta ƙare ba ne?"

Ayat ta watsa mata kallo ɗaya ta cikin mayafinta, wanda ya sa Saratu ta sunkuyar da kai da sauri...

"Kiyi yadda na ce."

​
Da ta kammala cin abinci, Ayat ta ɗauki farantin da Saratu ta haɗa mata ta nufi ɗakinta cikin natsuwa..

Zuciyarta cike take da tausayi, domin tunaninta gaba ɗaya ya karkata ga halittar da ta bari tana kwance a raunane...

​A sama kuwa, King Diamond ya ji takun tafiyar Ayat tana tahowa. Cikin hanzari ya lumshe idanunsa, jikinsa ya fitar da farin hayaƙi, nan take ya sake komawa siffar farar kuliyar nan mai rauni...

Ya kwanta lamo a inda ta bar shi, yana numfashi sama-sama kamar mai barci..

​Kofar ɗakin ta buɗe, ta shigo tare da rufe ƙofar a hankali kamar mai tsoron ta tayar shi daga barci, ta ƙariso ɗauke da tire na zinare...

Halittar tana nan kwance a tsakiyar gadon, kamar yadda ta bar ta tun farko..
Ayat ta matsa kusa, ta sauƙe farantin a gefen gado, sannan ta ce cikin muryar lallami.


“Reems… ga abinci nan. Ka ɗan ci, zai taimaka mika ka samu sauƙi.”

ta faɗa cikin murya mai taushi. Ta ɗauko kuliyar ta ɗora a cinyarta, ta fara ba shi ƙananan naman kaza dake cikin kwanon...

​King Diamond a siffar kuliya ya fara cin abincin, yana jin daɗin yadda hannunta yake taba fuskarsa. A ransa yana cewa,

"Ayat, idan kika san cewa Sarkin Power Pool kike ba wa abinci a hannu, da tabbas kin tsorata. Amma yau, ni ne bawanki, tunda kin zama mai ceton rayuwata."

​Bayan ya gama, ta ba shi madarar ya sha, sannan ta rungume shi a ƙirjinta. Ta ji zuciyar kuliyar tana bugawa da sauri, ita ma nata zuciyar tana amsawa...

✨✨

A babban ofishin tsaro na masarauta, Master Ibrahim ya kasa zama waje ɗaya. Ya kwashe sa'o'i yana kai da kawowa, idanunsa suna kallon agogo. Tun bayan da ya kwantar da Inuwa a gadonsa ranar da aka fasa masa goshi, ya ji shakuwar su ta ƙara ƙarfi, amma yanzu Inuwa ya ɓace masa...

"Ina Inuwa yake?" ya daka wa wasu jami'ai tsawa..

"Ranka ya daɗe, tun da ya tafi ba mu sake ganinsa ba," ɗaya daga cikin jami'an ya ba da amsa cikin tsoro..

Ibrahim ya ji wani baƙin ciki ya turnuƙe shi. Ya fara tuna maganganun jami'an da ya kora a baya, waɗanda suka ce Inuwa ya fara yawon banza da bin mata a gari...

"Shin da gaske Inuwa ya fara koyon halin banza? Shin har ya isa ya fifita wata mace a kaina?"

Ibrahim ya faɗa a ransa, kishi yana ƙara rura wuta a zuciyarsa. Ya riga ya mayar da Inuwa Mataimakinsa wato PA, don haka rashin ganinsa ya zame masa babban naƙasu...


A can ɓangaren Gimbiya Ayat kuwa, tana zaune a gaban madubinta, tana kallon kyakkyawar fuskarta. Ta ji a ranta cewa tabbas Master Ibrahim yana cikin wani hali na damuwa. Kusan sati guda ba su haɗu ba, kuma yau ta fita amma ta laɓe masa..

Ta kalli Reems dake kwance a kan gadonta, ta saki wani ƙayataccen murmushi...

"Reems, ka yi haƙuri zan je na gudanar da aikina. Ina ji a raina Master Ibrahim yana nema na," ta faɗa cikin murya mai sanyi...

Nan take, Ayat ta fara cire kayan sarautar nan masu ƙayatarwa. Ta ɗauko kayan jami'an nan na maza ta zura su, sannan ta maƙala saje, gemu, da gashin baki waɗanda take amfani da su wajen yaudarar mutane...

Bayan ta gama, ta nufi gadon, ta sunkuya ta sake manna wa kuliyar sumba a goshi...

"Babu mai shigowa ɗakin nan domin na kulle ta ciki. Zan bi ta wannan hanyar sirrin dake ɗakin nan na fita. Kar ka ji mamaki, haka ƙaddara ta so da ni. Zan dawo ba da jimawa ba domin duhu ya fara shiga, so nake kawai Master ya ganni in kwantar masa da hankali," ta faɗa a raɗa, kamar kuliyar za ta iya amsa mata...

Ayat ta matsa jikin bangon ɗakin, ta danna wani sirrin mabuɗi, nan take bangon ya buɗe wata hanyar sirri ce dake fita zuwa bayan masarauta inda babu mai gani. Ta sulale ta fice, bangon ya koma ya rufe kansa...

King Diamond, wanda ke cikin siffar kuliya, ya buɗe idanunsa na zinare ya bi ta da kallo. Duk da sumbar da ta bar masa dake sanyaya masa rai, zuciyarsa ta cika da mamaki da kuma sha'awar yadda wannan yarinya take rayuwa a matsayin namiji..


Bayan ficewar Ayat, King Diamond bai zauna jiran dawowarta ba. Ya sauya siffa daga kuliya zuwa asalin siffarsa ta Aljani, inda ya ɓace daga idon kowa ya bi sawun Inuwa...

Yana son gani da idonsa yadda wannan kyakkyawar yarinya take gudanar da rayuwarta a cikin maza..

Yana tafiya yana kallon yadda take shiga cikin jami'ai, kwarjininta a matsayin namiji yana ba shi mamaki..

Suna isa cikin masarauta, sai ga Master Ibrahim ya fito da guguwar fushi. Da ganin Inuwa, bai tsaya wata-wata ba, ya damƙe hannunsa da ƙarfi. Don kada ya zubar masa da mutunci a gaban sauran jami'ai, ya ja shi da ƙarfi har zuwa sashensa...

King Diamond yana biye da su, idanunsa suna ƙuna yayin da yake kallon yadda Ibrahim ya wurga Inuwa a tsakiyar ɗakin nasa cikin zafi. Diamond ya tsaya a gefe guda, yana sarrafa kansa da ƙyar don kada ya bayyana ya hukunta Ibrahim....


Ibrahim ya tsaya a kan Inuwa, yana huci...

"Tun yaushe ka fara yawon bin mata, Inuwa?" Ya fara zazzaga masa maganganu masu zafi na zargi da lalata, yana ganin cewa hakan ne ya sa ya ɓace tsawon sati ɗaya..

Inuwa tana ƙasa, kanta a sunkuye, ta ƙi ɗagowa ta kalle shi. Ta san idan ta yi magana, za ta iya kuka, kuma idan ta kalle shi, fushinsa zai iya sa ya fahimci wani abu a fuskarta...

Ba zato ba tsammani, fushin Ibrahim ya tafi, sai ya maye gurbinsa da wani irin lallami mai sauti. Ya durƙusa a gaban Inuwa, ya sa hannu ya ɗago haɓar sa. A wannan lokacin, Master Ibrahim ya fara magana cikin muryar raɗa kamar yana yi wa mace magana, yana lallashinsa a kan kada ya sake nisa da shi...

"Zan yafe maka kuskurenka," Ibrahim ya faɗa cikin murya mai sanyi, "amma hukuncinka shi ne, yau kai za ka yi min tausa daga wuyana har zuwa kunkumi..."

Nan take Inuwa ta ji zuciyarta ta buga da ƙarfi, wani irin gumi ya karye mata. Tausar namiji daga wuya har kunkumi? Wannan babban haɗari ne ga sirrinta duk da ba yau ne farko ba..

A daidai wannan lokacin, King Diamond ya dafe ƙirjinsa saitin zuciya. Saboda musayar jiki da suka yi a baya, yanzu duk firgicin da Ayat take ji, shi ma yana jinsa a jikinsa. Ya ji yadda jinin Inuwa ya fara gudu da sauri, hakan ya harzuka shi matuƙa. Yana kallon Master Ibrahim da wani irin kallo na kisa, yana jira ya ga inda wannan lamari zai ƙare...

Inuwa ta haɗiye miyau, ba ta da yadda za ta yi. Domin ta wanke kanta daga zargin da yake mata, dole ta yarda da wannan hukunci na Master Ibrahim, ko da kuwa hakan yana nufin ta taɓa jikin namijin da ba nata ba..

Master Ibrahim ya cire rigarsa, ya nuna faffaɗan bayansa mai cike da kwarjini, sannan ya kwanta rub da ciki a kan katafaren gadonsa na alfarma. Inuwa ta matso jiki na ɓari, ta zauna a bakin gadon, sawayenta suna taɓa ƙasa. Ta fara kai hannunta kan wuyansa tana masa tausa cikin tsananin kulawa da fargaba. Hannunta mai laushi ya sa Ibrahim lumshe ido, yana jin wani irin sanyi dake ratsa shi...

Daga gefe guda, King Diamond yana tsaye, idanunsa sun canza launi zuwa wani ja mai ban tsoro. Kishin aljani ya ninka na mutum sau dubu, ganin Ayat, mace ɗaya tilo da take da ikon shiga zuciyarsa, tana taɓa jikin wani namijin, ya sa ya ji kamar zai fashe tsabar zafi. Ya kasa sarrafa kansa, zuciyarsa ta buga, nan take ya rufe idanunsa ya dunƙule hannuwansa biyu cikin tsananin fushi.

Ba zato ba tsammani, sai aka ji wani sauti...
Wani irin ƙarfin tsafe-tsafe dake fita daga jikin Diamond ya daki gadon. Nan take duk ƙafafun gadon suka kakkarye...

Master Ibrahim ya ji gado ya tafi da shi ƙasa. Da ba don katifa mai kauri ba, da tabbas ya faɗi a kan ƙarfuna da katako...

Inuwa ta miƙe da sauri, zuciyarta na duka da sauri-sauri, tana mamakin abin da ya faru...

"Lafiya, Master?" ta faɗa cikin murya dake rawa.

Master Ibrahim ya sauƙo daga kan rugujajjen gadon yana zaro ido. Ya kalli ƙafafun gadon da suka zama guntu-guntu kamar an sare su da gatari..

"Wanne irin abu ne wannan?" ya faɗa yana waige-waige. Ya kasa gaskata cewa gadonsa mai ƙarfi zai ruguje lokaci guda ba tare da wani dalili na zahiri ba. Ya fara zargin ko akwai wani sihiri dake kewaye da sashen nasa..

King Diamond yana tsaye a gefe, yana kallon Ibrahim da wani irin kallon raini... Duk da cewa fushinsa ya sa ya kusan bayyana kansa, ya san dole ne ya yi haƙuri. Idan har ya fita daga masarautar nan a yanzu, to tabbas ba zai sake samun damar dawowa ba saboda tsananin garkuwar dake kewaye da gidan. Dole ne ya zauna a kusa da Ayat a matsayin Reems har sai ya gama shiga jikinta...

Ibrahim ya juya ya kalli Inuwa, duk sha'awar tausar ta tafi, ya maye gurbinta da fargaba..

"Inuwa, tafi kawai. Zan sa a gyara gadon nan gobe. Amma ka sani, sa ido na yana kanka!"

Inuwa ta ruga da gudu ta koma sashenta, zuciyarta na bugawa da sauri bayan hatsarin da ya faru a ɗakin Master Ibrahim...

Tana shiga, ta kulle kofarta, ta sauke wani nannauyan ajiyar zuciya. Ba ta ɓata lokaci ba, ta shige bandaki ta watsa ruwa don wanke gajiyar ranar da kuma kawar da tunanin Ibrahim...

Ta fito daga wanka, ta nufi wurin tufafinta. Ta zaro wata lallausar rigar bacci mai siririn hannu (spaghetti strap), wadda ta tsaya dai-dai gwiwarta. Rigar ta zauna daram a jikinta, tana nuna kyakkyawar surarta ta mace. Ta saki gashinta ya bazu a bayanta, sannan ta haye gadon ta zauna.

Ta miƙa hannu ta ɗauko Reems. Ta rungume shi sosai a kirjinta, tana jin ɗumin jikinsa. Ta fara lulluma dogwayen yatsunta cikin farin gashin jikinsa, tana shafa shi cikin nutsuwa da kwarewa...

Shi kuwa King Diamond, a siffarsa ta kuliya, ya lumshe idanu. Wani irin daɗi da kuncin rai suka ziyarci zuciyarsa. Yana jin kamshin turaren jikinta da kuma taushin hannunta dake yawo a jikinsa. Duk da cewa yana kishin yadda ta taɓa Ibrahim, wannan tattalin da take yi masa ya sa ya manta da komai..

Kamar yadda kuliya take nuna nishadi idan ana shafa ta, King Diamond ya saki jiki, numfashinsa yana sarkewa tsabar jin dadi.

Yayin da take wasa da kuliyar, hankalinta ya tafi wata duniyar daban. Ta fara tunanin mutumin nan da ta hadu da shi a bakin kogi, mutumin da har yau ba ta san sunansa ba, amma kwayar idonsa ta gaza bacewa a ranta..

"Ina zan sake ganin sa?" ta fada a hankali, muryarta na nuna begen sa. Ta kara matse kuliyar a kirjinta, ba tare da sanin cewa mutumin da take mafarkin shine dai dake hannunta a matsayin dabba ba...

Can kuma sai tunanin Master Ibrahim ya faɗo mata. Ta sauke ajiyar zuciya,

"Allah ne kawai yayi hukuncinsa ya karya gadon nan," ta raya a ranta. Ta tabbata cewa Allah ne ya kare ta daga taɓa jikin namijin da ba nata ba, tunda ita mace ce kuma tana da darajar da take karewa..

King Diamond ya ji daɗi a ransa da ta danganta rugujewar gadon da hukuncin Allah, bai so ta fara zargin cewa akwai wani sihiri a kusa da ita ba...
Ya ƙara shige jikinta, yana fatan dare ba zai waye a wannan yanayin ba...


To pah zamu tsallake mu je pavilion meke faruwa a can ne😅😅😅


A cikin Pavilion City...

Bayan wata guda da fara zaman Ching Ching a katafaren gidan Pavilion, rayuwa ta canja salo. A yau, tana sanye da kayan aiki tana mopping a babban falon Chief Onyx...

Shi kuwa Chief yana zaune a kan kujera, hankalinsa gaba ɗaya yana kan kwamfutarsa yana danna ayyukansa, yayin da kofin coffee yake gefensa yana huce wa...

Muryar Ching Ching ce take tashi a falon yayin da take rera waƙarta cikin nishaɗi, tana goge ƙasa da bucket a hannunta. Tana tafe tana goge-goge har ta zo dab da inda yake zaune...
Cikin rashin sani ko kuma ince da gangan, ƙafarta ta zame a kan wurin da ta riga ta jika da ruwa. Nan take ta yi kamar za ta faɗi, sai kawai ta kai wa bucket ɗin watsa, ta kwarara masa ruwan tun daga kansa har zuwa jikinsa...

Chief Onyx ya daka wata uwar tsawa yayin da ya miƙe tsaye, ruwa yana digowa daga jikinsa. Ya watsa mata wani irin kallo cike da takaici da fushi, yana tunanin wani irin hukunci ya dace da ita...

Ita kuwa Ching Ching, maimakon ta ji tsoro, sai kawai ta tuntsire da dariya, ta rasa yadda za ta tsayar da kanta...

"Wane irin rashin hankali ne wannan?" Onyx ya daka mata tsawa cikin zafin rai...

"Ke ba ki da hankali ne ko kuwa ba ki san darajar mutane ba?!"

Ching Ching ta turo baki gaba, ta fara gunaguni cikin shagwaba
"Nifa ba a min tsawa!"

Yayin da Onyx yake huci kamar zaki yana zazzaga mata faɗa, ita kuma sai ta ƙara haɗe rai tana murguɗa baki...
Onyx ya sake daka mata tsawa, "Wane irin iskanci ne wannan? Kin san ko ni wane ne kuwa?!"

Cikin rashin tsoro, ta sake murguɗa baki ta ce,

"Gaskiya nifa ba a min tsawa. Idan za a yi magana, a yi ta cikin lallashi."

Onyx, wanda kowa yake shakka a gari, sai ya tsaya turus yana kallon yadda take shagwaba kamar ba ita ce ta jika shi sharkaf ba. Fushin da yake yi sai ya nemi ya tafi, ya rasa yadda zai yi da ita saboda kwarjininta da rashin tsoronta. Daga ƙarshe, ya girgiza kai yana murmushin takaici..

"Lallai ke ba ki da dama. Kin jikani, sannan kuma kina min gatsali? To ki ma za ki samo min tawul kafin na sake canja ra'ayi!"...

"Gaskiya ba zan je ba," ta ƙara turo baki tana murguɗa shi gefe. "Sai ka sake lallashina sannan zan je na samo maka. Ai da zafi-zafi ka yi min magana ɗazu."

Onyx ya zuba mata ido, ya kasa yarda da abin da yake ji. Yarinya ƙarama take gaya masa ya lallashe ta bayan ta jikashi? Ya sauke ajiyar zuciya, ya rage muryarsa ƙasa-ƙasa cikin yanayi na rarrashi duk da cewa ransa a ɓace yake..

"To... kiyi haƙuri ranki ya daɗi. Don Allah sarauniyar shagwaba, ko za ki iya taimaka min ki kawo min tawul ɗin kafin sanyi ya kashe ni?"

Ching Ching ta girgiza kai, "Gaskiya wannan lallashin bai yi daɗi ba, sam bai ratsa ni ba. Sai ka sake wani mai daɗi wanda zai gamsar da ni, sannan zan tashi."

Onyx ya dafe kansa, ruwa yana digowa daga gashinsa zuwa fuskarsa...

Ya cika ya yi fam, amma ganin yadda take kallonsa da idanunta masu cike da shagwaba ya sa ya kasa kure ta. Ya matso kusa da ita, ya sassauta muryarsa sosai kamar mai rarrashin jariri...

"To Shugaba Ching Ching, kiyi hakuri don Allah. Ke ce mai gida, ni ne yaronki. Don darajar waccan dariyar da kika yi, ki taimaka wa bawanki da tawul, idan ba haka ba rashin lafiya zan yi, wa zai rika kula da ke?"

Ching Ching ta sake tintsirewa da dariya, tana kallon cikin ƙwayar idonsa ta ce..

"Haba Uncle Onyx! Har yanzu dai lallashin nan akwai saura, bai kai can ba..."

Tana cikin maganar ne, Onyx ya ga ba zai iya jure wannan shagwabar ba. Nan take ya sa hannu ya jawota jikinsa da ƙarfi, ya matseta a jikinsa duk da cewa rigarsa a jike take. Kafin ta ankara, ya kai mata sumba cikin wani yanayi na nuna iko.... Nan take duk waccan shagwabar tata da dariyarta suka ɗauke caf...

Bayan ya sake ta, Ching Ching ta tsaya cak kamar an dasa bishiya. Fuskarta ta yi jawur saboda tsananin kunya, ta kasa haɗa ido da shi. Muryarta tana rawa-rawa ta ce..

"Uhmm... dama... dama cewa zan yi zan je na samo tawul ɗin..."

Ta yi ƙoƙarin zame jikinta, amma Onyx bai sake ta ba. Ya ƙara matseta yana raɗa mata a kunne..

"Ina za ki? Ai yanzu ne lallashin ya fara. Tunda kika ce wanda na yi ɗazu bai yi daɗi ba, yanzu zan nuna miki yadda ake lallashi na gaskiya..."

Ching Ching ta ji jikinta ya yi sanyi, numfashinta ya fara fita sama-sama...

Cikin zafin nama, ta zame jikinta tana dariya mai haɗe da kunya, ta ruga da gudu zuwa wani ɓangare tana yi masa gwalo..

"Na yarda! Lallashin ya yi daɗi sosai! Bari na samo maka tawul ɗin kafin ka narke a wurin!"

Onyx ya tsaya yana kallonta yana murmushi, ransa ya yi fari sol... Bayan ɗan lokaci, sai ga ta ta fito.. Amma maimakon tawul, sai ya ganta ɗauke da mopper...
Ta miƙa masa tana dariya,

"Ga shi nan Uncle! Tunda ka ce kai ne yaro na, to yi maza ka goge jikinka da wannan!"

Onyx ya kalli mopper ɗin, ya kalli yadda take kyalkyala dariya, ya kasa cewa komai sai dai kawai ya dafe kai yana murmushin takaici...

Onyx ya kurawa mopper ɗin da take mika masa ido, sannan ya kalli fuskar Chingching wadda take sheƙi da annurin mugunta...
Ya kasa gaskata cewa bayan duk lallashin nan da ya yi mata, har yanzu ba ta daina wasan kura da shi ba.

"Mopper kuma Chingching?" Onyx ya furta cikin murya mai rauni, yana girgiza kansa.

"Kina nufin bayan duk jikan nan da kika yi min, har da datti zan goge jikina?"

Chingching ta ƙara turo baki, ta kauda kai gefe tana fushi...

"Ai kai ka ce kai ne yaro na, ni kuma shugaba. To, a matsayina na shugaba, na ga mopper ta fi dacewa da kai tunda ruwan ma na mopping ne!"....

Ruwan jikinsa na ɗiɗɗiga. Ganin ya nufo ta gadan-gadan ya sa ta daina dariyar, ta ja da baya da sauri...

"Tsaya nan! Kar ka matso kusa da ni!" Ta faɗa tana neman hanyar gudu..

Amma a wannan karon, Onyx ya fi ta sauri. Kafin ta kai ga gudu, ya damƙo damtsen hannunta, ya juyo da ita ta yadda suka fuskanci juna....Ya sa hannunsa ɗaya ya karɓi mopper ɗin ya jefar da ita gefe, sannan ya matso da fuskarsa saitin tata, yadda hancinsu yake gogayya da juna...

"Kin yi wasa da wutar da ba za ki iya kashewa ba, Shugaba Chingching," ya raɗa mata cikin muryarsa mai ratsa jiki wadda ta nuna cewa wasan ya canja salo...
"Yanzu zan nuna miki cewa ko da yaro ne, akwai ranar da yake yi wa shugabansa tawaye."

Chingching ta ji wani irin sanyi yana bin kashin bayanta. Shagwabar nan tata ta ɓace, sai tsoro da kuma wani irin yanayi na daban suka maye gurbinsa. Ta kasa magana, sai numfashi take yi da sauri-sauri.

Onyx ya sanya hannunsa a kuncinta, yana goge wani ɗigon ruwa da ya fantsama mata a fuska tun ɗazu...
"Ba kya tunanin ya kamata ki mun lallashi na gaske? Wanda ya fi wanda na yi miki ɗazu daɗi?"

Maimakon ta amsa, sai kawai ta tura kanta a kirjinsa da yake jike, tana ƙoƙarin ɓoye fuskarta saboda kunyar da ta mamaye ta...

"Yi haƙuri... na daina wasan," ta faɗa cikin murya ƙasa-ƙasa wadda da kyar ake jin ta.

Onyx ya sauƙe numfashi, ya rungumeta sosai a jikinsa, yana jin yadda zuciyarta take bugawa da sauri....

A ransa ya san cewa duk taurin kansa da kwarjininsa, wannan yarinyar ta riga ta gama da shi. Shagwabarta makamin yaƙi ne da ba shi da kariya a kansa...

"Ba zan taɓa gajiya da lallashinki ba, koda kuwa kullum zaki rinƙa jiƙani da ruwa ne," ya furta cikin sanyin murya...

Ya ɗago fuskarta, ya kalle ta cikin idanu, sannan ya sakar mata wani murmushi mai sanyaya rai...

"Amma yanzu, gaskiya ki taimaka min da tawul ɗin, kafin na zama kifi a cikin wannan falon!"

Chingching ta ɗan murmusa, sannan ta yi sauri ta raba jikinta da nashi, ta ruga ɗaki tana faɗin,

"Wannan karon zan kawo tawul ɗin da gaske! Amma sai ka yi alkawarin ba za ka sake yin abin ɗazu ba!"

Onyx ya tsaya a tsakiyar falo yana kallon inda ta bi, ya shafi leɓensa yana murmushi.

"Alkawari?..." ya faɗa a zuciyarsa, yana jin wani irin farin ciki da bai taɓa ji ba a rayuwarsa ta Pavilion...

Bayan ya shiga babban ɗakinsa, Onyx ya yi wanka ya shirya cikin baƙar riga da wando na alfarma na suit waɗanda suka zauna daram a jikinsa, yana fitar da ƙamshin turare mai sanyi da tsada. Ya ɗauki agogonsa na gwal ya ɗaura, sannan ya fito cikin takunsa na isa da nuna mulki...

A waje, bodyguards ɗinsa guda shida sanye da baƙaƙen kaya da gilashi, suna ganinsa suka sara masa tare da buɗe masa ƙofar motarsa ta alfarma Bulletproof SUV... Fuskar Onyx a haɗe take, ya koma babban shugaba Chief mai ban tsoro, ba kamar yadda yake wasa da Chingching ɗazu ba...

A daidai wannan lokacin, Chingching tana maƙale a jikin labulen ɗakinta, tana leƙen abin da yake faruwa ta taga...

Ta zuba masa ido, tana kallon yadda ya sauya lokaci guda ya koma kakin jarumai. Zuciyarta ta buga ganin yadda yake tafiya cikin kwarjini..
Ta turo baki kaɗan, ta raɗa a hankali..

"Lallai mutumin nan ya iya haɗe rai, duba yadda yake wani hura hanci da bodyguards. Amma gaskiya yana da kyau..."

Tana cikin wannan leƙen ne, sai Onyx ya tsaya kusa da motar, ya ɗaga kansa ya kalli tagar ɗakinta kamar ya san tana kallonsa..

Onyx ya tsaya daidai saitin motarsa, maimakon ya shiga, sai ya ɗan dakata sannan ya ɗaga kansa kai tsaye ya kalli tagar ɗakin Chingching, kamar yana kallon cikin kwayar idonta..

Ganin ta firgita za ta janye labulen, sai kawai ya sakar mata wani ƙasaitaccen murmushin nan na gefen baki, murmushin da yake nuna

"Na kama ki kina leƙena."

Ba tare da ya ce uffan ba, ya juya ya shiga motar, bodyguards ɗinsa suka rufe ƙofar tare da tada ayarin motocin suka bar gidan cikin taƙama..

Chingching ta koma baya ta jingina da bango, zuciyarta tana dukan uku-uku. Ta dafe ƙirjinta tana cewa,

"Wane irin mutum ne wannan? Ko baya ma yana da idanu ne?"
Ta kasa daina murmushi ita ma...

Bayan ficewar ayarin motocin Chief Onyx daga harabar fadar pavilion..

Ta koma falon a yayin da ya yi tsit, amma zuciyar ta ba ta daina bugawa ba. Ta turo baki, ta kalli mopper ɗin da ta rage a ƙasa tana cewa,
"Wai ma me ya sa nake kallonsa? Mutum sai girman kai, gani yake shi ne sarki." Ta buga ƙafa a ƙasa, ta nufi kitchen tana gunaguni...

A Ɓangaren Onyx kuwa...
Yana zaune a bayan mota, idanunsa suna kallon titi amma tunaninsa yana kan yadda Ching Ching ta turo baki tana murguɗa masa shi. Ya yi sauri ya haɗe rai sa'ilin da ya ji wani sanyin murmushi yana neman subuce masa...

"Wace irin yarinya ce wannan?" ya tambayi kansa a zuci. "Ya kamata na kore ta daga gidana tunda ba ta da ladabi, amma..." Ya kasa ƙarasa maganar. Shi a ganinsa ba soyayya yake mata ba, kawai dai yana jin daɗin yadda take bashi nishaɗi da shirmitun ta.

✨

Yamma ta yi liss...
Onyx ya dawo gida a gajiye, ransa a ɓace saboda matsalolin aiki. Da shigarsa falon, ya tarar da Ching Ching a kwance a kan doguwar kujerar da ya saba zama, tana cin gyaɗa tana zubar da bawon a ƙasa, ga TV yanda tasa a gaba...

Tunani ya fara yi aina ta samu gyaɗa kuma a gidan nan..

"Ching Ching!" Onyx ya daka mata tsawa...

Ta zabura ta tashi, amma maimakon ta bashi haƙuri, sai ta haɗe rai, ta watsar da sauran gyaɗan a ƙasi...

"Me ya faru? Me ya sa zaka dawo ka cika min kunne da hayaniya? Ka ga yadda na tsorata kuwa?"

Onyx ya zaro ido, "Kece kika tsorata ko ni ne ya kamata raina ya ɓaci? Dubi yadda kika mayar min da falo kamar gidan mahaukata! Kuma a kan kujerata kike kwance?"

Ching Ching ta fashe da kuka, kukan shagwaɓa wanda babu hawaye..

"Dama na sani! Tunda ka dawo kake nema na da faɗa. Ni ba zan iya zaman wannan gidan ba, tunda ba a lallashi na, kullum tsawa, kullum hantara!" Ta fara tattara takalman ta dake watse a carpet kamar wadda zata bar gidan yanzu-yanzu...

Onyx ya dafe kansa, fushinsa ya fara narkewa ya koma damuwa. Bai san yadda ake rarrashin mace ba, amma ya san ba zai iya jure ganin tana kuka ba...

"Tsaya..." ya faɗa muryarsa a raunane...

"Ba kora ki nake yi ba. Kawai dai ki rinƙa gyara wurin."

"Gaskiya na ƙi!" Ta juyo tana kallonsa da idanunta da suka yi dishi-dishi na hawayen ƙarya...

"In har kana son na zauna, sai ka zo ka kwashe datti nan da hannunka, sannan ka ba ni haƙurin tsawar da ka yi min. Idan ba haka ba, yanzu zan fita na tafi daji na zauna da namun daji, su sun fi ka sauƙin kai!"

Onyx ya ja numfashi, ya kalli bodyguards ɗinsa da suke tsaye a waje waɗanda suke ta satar kallon yadda Zaki yake zama Zomo a gaban yarinya...

Ya matso kusa da ita, ya sunkuya ya fara kwashe bawon gyaɗa...

"To Shugaba Ching Ching, kiyi haƙuri. Na yi kuskure,"
ya faɗa yana kau da fuska don kada ta ga yadda kunya ta kama shi...

Ching Ching ta daina kukan lokaci ɗaya, ta matso ta tsaya a kansa tana kallon yadda yake kwashe dattin...

Ta turo baki ta ce, "Lallashin bai yi daɗi ba tukuna. Ka ce 'Ina son ki zauna Shugaba ta, don Allah kada ki tafi'."

Onyx ya ɗago ya kalleta, zuciyarsa tana tafarfasa tsakanin izarsa ta mulki da kuma wani sabon yanayi da yake ji a kanta....

"Ching Ching, kada ki ƙure ni..."

"To zan tafi kenan!" Ta juya da sauri...

"Tsaya!" Onyx ya dakatar da ita. Ya sauke ajiyar zuciya,
"Kiyi haƙuri... Shugaba ta. Don Allah kada ki tafi, ki zauna... kin ji?"

Ching Ching ta juyo da wani mugun murmushin nasara, ta buga tsalle ta koma kan kujerar ta zauna...

"Yauwa! Yanzu ka fara koyon magana.... To maza je ka kawo min ruwa mai sanyi, raina ya ɓaci ɗazu sosai."...

Bayan kalaman rainin da Ching Ching ta yi masa, Chief Onyx ya ja numfashi, ya tsaya turus yana kallon yadda yarinyar nan take neman mayar da shi yaro a gabanta...

A gefe guda kuwa, Gely tana tsaye daram. Duk da cewa ita Robot ce, amma an ƙera ta ne da fasahar da take iya karantar yanayi AI, kuma a yanzu duk wata na'ura ta jikinta tana nuna mata cewa Boss ɗinta yana fuskantar raini...

Gely, wadda ita ce amintacciyar Onyx kuma hannun damarsa, ta matso cikin takunta na robot, muryarta tana fita a sanyaye...

"Boss, ya isa haka. Ka je ka huta, ni zan kawo mata ruwan."

Ching Ching ta turo baki, ta harari Gely da gefen ido ta ce,

"To uwar iyeyi! Ba da ke nake ba, sarkin shishshigi kawai!"

Onyx ya kalli Ching Ching, ya kalli Gely, sai ya tuna matsayinsa. Ya fahimci cewa idan ya ci gaba da biye wa shagwabar yarinyar nan, mutuncinsa da izarsa na babban Chief za su zube a idon duniya...

Nan take ya sauya fuska, ya daka mata wata uwar tsawa wadda ta sanya falon duka ya girgiza!..

"Ya isa haka!" Onyx ya daka mata tsawa cikin wani irin zafin rai wanda ya sanya Ching Ching tsorata, har ta kusan fece wa....

Cikin fusata da muryar nuna iko, ya ci gaba da cewa..

"Na ɗauko ki ne a gaban mahaifinki ba don komai ba, sai don yarjejeniyar da muka yi cewa zai ba ni ɗaya daga cikin gimbiyoyinsa a matsayin Personal Maid wato ƴar aiki. Saboda haka inaso na sanar miki, anan ke ba GIMBIYA ba ce! Ke 'yar aiki ce, kuma dole ki bi doka. Bana son ciwon kai!"...

Falon ya yi tsit bayan tsawar da Chief Onyx ya daka wa mata....

Gely, wato robot tana tsaye daram, idanunta masu hasken blue suna kallon Ching Ching ba tare da ƙibtawa ba. Muryar Gely ta fito a sanyaye a matsayin robot...

"Boss, yanayin jininka ya haura yadda ya kamata. Ina ba ka shawarar ka huta. Zan kula da buƙatun wannan yarinyar."...

Onyx bai sake kallon inda Ching Ching take ba, ya juya cikin takunsa na isa ya nufi sashensa Master Suite, ransa yana zafi. Ya gane cewa idan ya ci gaba da biye mata, mutuncinsa zai zube a idon ma'aikatansa...

A ɓangaren Ching Ching...
Tsawar da ya yi mata ta ratsa har bargon kashinta...
Kalmar ke ba Gimbiya ba ce a nan, ke 'yar aiki ce" ta fi komai yi mata zafi. Ta kalli Gely wadda take tsaye tana mata wani irin kallo na robot, Ching Ching ta harare ta..

"Ke kuma meye kike kallo na? Na sani, ke inji ce, ba kya jin zafi! Amma ya sani, ko ya ce ni ba gimbiya ba ce, jinina na sarauta ne!"

Ta miƙe da gudu, gashinta yana tashi, ta ruga ɗakinta ta faɗa kan gado. Wannan karon kukan ba na wasa ba ne, hawaye ne masu ɗumi suke fita daga idanunta. Ta ji ciwon yadda ya wulakanta asalin ta a gaban robot....

Cikin Sashen Chief Onyx...
Ya rage kayan jikinsa, ya bathroom domin watsa ruwa, ruwan shower ne yake zuba a tsakiyar kansa.... Amma duk da fushin nan, muryar kukan Ching Ching da ya ji kafin ta shiga ɗaki tana sake masa amo a kunne...

Gely ta shigo ɗakin tunda tana da damar shiga ko'ina, ta tsaya a jikin ƙofar toilet ɗin...

"Boss, na lura akwai damuwa a tare da kai wadda ba ta shafi aiki ba. Shin kana buƙatar na share tunaninka game da Ching Ching?"

Onyx ya fito daga wankan, yana ɗaure da tawul a kwankwasonsa, ruwa yana ɗiga daga jikinsa. Ya kalli Gely ya ce,

"Gely, ke robot ce. Ba za ki taɓa fahimtar abin da yake sa ɗan adam ya ji rauni ba. Yarinyar nan tana da taurin kai, kuma dole na koya mata hankali."...

Gely ta amsa,

"Amma Boss, bayanan da nake da su sun nuna cewa tana kuka a halin yanzu... Bugun zuciyarta ya canza zuwa yanayin baƙin ciki mai tsanani. Shin hakan ba zai shafi ingancin aikinta a matsayin 'yar aiki ba?"

Onyx ya daka wa Gely tsawa, "Ya isa haka! Fita ki ba ni wuri!"...

Bayan Gely ta fita, Onyx ya tsaya a gaban madubi. Ya yi ƙoƙarin sanya kayan barci ya kwanta, amma zuciyarsa ta ƙi bashi haɗin kai....
Ya kasa mantawa da yadda fuskarta ta firgita lokacin da ya daka mata tsawa. Bayan kusan awa ɗaya na juyi a gado, ya kasa jurewa...

Ya miƙe a hankali, ya sanya riga, ya fito daga sashensa zuwa babban falo yanda ɗakinta yake...

Ya tsaya a ƙofar, yana jin sautin kukanta a hankali ta cikin ƙofar. Hannunsa yana rawa ya kai kusa da handle ɗin ƙofar, amma sai ya tuna matsayinsa...

"Idan na shiga na lallashe ta yanzu, na nuna mata rauni na," ya faɗa a fili...

Daidai nan, ya ji Ching Ching tana faɗa cikin kuka..

"Daddy... me ya sa ka bari aka kawo ni nan? Mutumin nan ba shi da zuciya... ko lallashi bai iya ba... ina son na koma gida..."...

Girgiza kai kawai yayi, sannan ya wuce part ɗinsa ba tare da ya shiga ba...


An kwashe kwanaki biyu rigima bata sake shiga tsakanin Chief Onyx da Ching Ching ba. Gidan ya yi wa Onyx shiru, ya saba da hayaniyarta da murguɗa baki, amma yanzu fushi ya sa ta zama kurma... Idan ya zo zama kusa da ita, sai ta miƙe ta bar masa wurin, tana gungunai...

"Ai tunda tsawa ka iya yi, sai ka zauna da bangon ka yi ta masa tsawar." Ta koma tana aikin share-share da goge-goge cikin basarwa...

A yau ne abubuwa suka sauya...
Ching Ching ta ɗauko kalar abinci daban-daban daga kitchen, inda Robots masu girki suke aiki waɗanda ba sa fitowa waje... Ta fara jera abincin a kan dining domin Chief ya karya...
Onyx yana zaune a kan teburin, ya zuba mata ido yana kallon yadda take aikin cikin shan ƙanshi, ko ɗago kai ba ta yi ta kalle shi ba...

Onyx ya yi murmushin mugunta a ransa, yana tunani..

"Dama tana da zuciya haka? Na ɗauka bata san komai ba sai shagwaɓa da rigima."

Gely, wadda take tsaye kusa da Chief kamar inuwa, ta kalli kalar abincin da aka kawo, sannan ta kalli Ching Ching da idanunta masu haske... Ta ce,

"Yau Boss ba wannan abincin zai ci ba..."

Kafin Gely ta ƙarasa maganar, Ching Ching wadda fushin kwanaki biyu yake cin ta, ta ɗago ta zabga wa Gely wani irin mari ta ƙarfi! Tasss!...

Maimakon Gely ta ji zafi, sai ga shi Ching Ching ce ta riƙe hannunta tana ihu domin ta ji kamar ta bugi ƙarfe ne..

"Wash! Hannuna! Kalli yadda kika ji min ciwo muguwa kawai..!"
Ta fara juyi tana ihun shagwaɓa da rigima, daman ta kusa kwanaki biyu ba ta samu damar yin hakan ba...

Kwatsam! Sai aka ga wasu haruffa sun fito a ƙirjin Gely suna walƙiya..

"ACTIVATED"..

Idanun Gely suka sauya launi zuwa Ja wur!, alamar ta fita daga hayyacinta na asali. Nan take ta kai hannu ta shaƙe wuyan Ching Ching, ta ɗaga ta sama har ƙafafun Ching Ching suka daina taɓa ƙasa...

Chief Onyx ya zabura ya tashi tsaye, zuciyarsa na bugawa...

"Gely! Sake ta! Gely, I command you, release her now!"
ya daka mata tsawa...

Amma abin mamaki, yau ne karon farko da Gely ta saɓa wa umarnin Boss ɗinta. Ta ci gaba da shaƙe wuyan Ching Ching, yayin da yarinyar take ta shura ƙafafu tana neman numfashi...

Onyx ya ga cewa idan ya yi wasa, Gely za ta iya kashe ta...

Cikin sauri, ya duba agogon hannunsa, ya danna wani maɓalli (Emergency Shut-off) don kashe Gely gaba ɗaya, tun da ba ta ji maganarsa ta baki ba...

Nan take Gely ta ƙame, duk hasken jikinta ya mutu, hannunta ya saki wuyan Ching Ching...

Ching Ching ta fara sulalo wa za ta faɗi ƙasi, amma Chief Onyx cikin zafin nama ya tare ta, ta faɗo kai tsaye cikin faffaɗan ƙirjinsa. Ya matse ta a jikinsa sosai, yana jin yadda numfashinta yake fita da sauri-sauri saboda firgici...

"Kiyi haƙuri... kiyi haƙuri,"

Onyx ya raɗa a kunnenta cikin muryar rarrashi, ya manta da duk izarsa, damuwarsa ɗaya ce a yanzu... lafiyar tursasasshiyar gimbiyar tasa...


👍 Like
🔁 Share
💬 Comment


*👑 MASARAUTAR ALHAMRA 👑*

_🪄 Gidan Mulki, Iko da Sirrin Zuciya 🪄_

✍🏽 By ASMEETAH WRITER
~Hasken Jajirtattu~


💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️

```JARUMAI WRITERS TEAM```

▶️ DON BIYO DAGA FARKO 👇
🔗 WhatsApp Channel:
https://whatsapp.com/channel/0029VbBCNlqJUM2RQwWncg43

📚 ArewaPen:
https://arewapen.com/u/asmeetahwriter

📖 Wattpad:
https://www.wattpad.com/user/asmeetahwriter

📲 Contact:
09065443871

📅 FARA TURA BOOK:
🔥 01 — 01 — 2026 🔥

📘 BOOK ONE
```MATAKIN FARKO```
Chapter 23 · 0% Book details