← Book details Masarautar Alhamra Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 14 OF 42

CHAPTER 1️⃣2️⃣

Masarautar Alhamra Part 1 Complete Hausa Novel · about 18 min read

*بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيمِ*


Ayat dake cikin siffar King Diamond ta kasa daina duba hannayenta da fararen kayanta. Wani irin kishi da haushi ne yake turnuƙe ta. Ta matso kusa da shi tana huci, muryarta dake fita irin ta namiji yana dukan duwatsun dake wurin...

"Ka maida ni yanzu! Na ce ka maida ni!"...

Ta damƙi wuyan rigar dake jikinsa, rigarta ta gimbiyanci wadda take matuƙar so.

"Wallahi ba zan motsa daga nan ba, kuma ba zan tafi ko'ina ba har sai na dawo siffata ta mace. Ba zan iya rayuwa a cikin wannan siffar taka mai ban tsoro ba!"

King Diamond dake cikin siffar Ayat, ya yi murmushin nan na Gimbiya Ayat mai kyan gani, ya haskaka fuskarsa wadda take sheƙi. Ya sanya hannunsa ya ɗan shafa dogon gashin dake kansa, sannan ya ce da muryarta..

"Aayat, kiyi haƙuri. Wannan ba nufina ba ne, haɗuwar jininmu ne ya janyo hakan. Kuma ki sani, ko ni ma ina son siffata, amma yadda kike a yanzu kinfi kowa kyan gani a idona."

Ayat ta ƙara fusata, ta ji tamkar tana faɗa da kanta ne a madubi ta ce,

"Kayi mun shiru! Kar ka sake magana da muryata! Kuma kar ka sake ƙirana da sunana da wannan muryar!"

Ta juya tana kallon magudanar ruwan, tana tunanin ta yadda za ta koma masarauta...

"Ta yaya zan koma gida a haka? Master Ibrahim ya san ni a matsayin Inuwa, mahaifina ya san ni a matsayin Ayat. Idan na shiga masarautar nan a siffarka, kashe ni za a yi!"

King Diamond ya matso kusa da ita, ya ɗora hannunsa a kafaɗarta.

"Ni kuwa ina son kasancewa da ke a haka. Ina son in ga yadda za ki yi amfani da ikona, kuma ina son in ga yadda zan rayu a cikin takurarki. Ba zan maida ke ba yanzu ba domin ina jin daɗin yadda jininmu ya sarƙe."...

Ayat ta buge hannunsa dake kan kafaɗarta da ƙarfi.

"Ba zan tafi ba! Kuma ba zan bari ka tafi ba! Za mu zauna a nan har sai wannan sihirin naka ya karye. Ba zan zama namiji ba, ba zan zama aljani ba!"...

Haka suka ci gaba da tsayawa a bakin kogin, iska tana kaɗawa. Ayat tana ta kai-komo tana zage-zage da muryar namiji, shi kuwa yana tsaye yana kallonta da fuskarta, yana jin daɗin yadda ya samu damar kasancewa da ita ta wannan hanyar...

✨✨

Dare ya tsala har ƙarfe 10, duhu ya lulluɓe kowane sashi na dajin dake kewayen kogin.
A lokacin King Diamond ya haskaka wurin da wani irin koren haske na sihirinsa, wanda ya sanya wurin ya zama tamkar a cikin almara yake. Duk da kyawun hasken, zuciyar Ayat dake cikin siffar namiji tana tafasa da wani irin zazzafan fushi da firgici...

King Diamond yana tsaye a mutum-mutumi, bai ce uffan ba hakan ne kuma ya ƙara rura wutar fushi dake zuciyarta. Ta ɗaga kai ta kalle shi, idanunta cike da tsananin ƙiyayya da tsoro a haɗe...

“KAI!!” ta daka masa tsawa, muryarsa mai nauyi dake fita daga makogwaronta ya sa ta tsorata da kanta...
Ta miƙe tsaye tana fuskantarsa..

“Me kake son aiwatar mun? Me ka ke so kayi da rayuwata, kai mugu?!”

Ta fara zagaye kanta da hannu cikin hauka, tana janyo dogon farin gashin dake kanta wanda yanzu nata ne, tana kuka kamar yarinya karama..

“Na rantse zan kashe ka! Wallahi zan sare ka idan har ka maido min da jikina!”

Cike da raɗaɗi, ta durkushe a ƙasa da ƙarfi, tana bugun ƙasar da hannuwanta masu faɗin gaske....
“NA TSANE KA! NA TSANE KA!! NA TSANE KA!!!” Ihun nata yana dukan duwatsun dake bakin kogin, yana dawo mata da sautin namijin da ba ta son ji, abin da ya sa ta ƙara razana...

A wannan lokacin ne King Diamond ya ɗaga girarsa ɗaya cikin natsuwa. Ya fara takowa a hankali, takunsa ba shi da sauti tamkar iska, har ya tsaya a gabanta yana kallonta daga tsaye... Da muryarta ta mace mai sanyi, ya ce..

“Ki daina ihu.”..

Ta daka tsalle ta miƙe tsaye tamkar wadda wuta ta taɓa..

“KAR KA ƘARA MAGANA DA MURYATA!!” ta faɗa tana toshe kunnenta...

“Na tsane jin muryata tana fita daga wannan bakin naka!”

Ta juya da gudu kamar tana son tserewa daga wurin, amma sai ta tsaya cak bayan taku kaɗan. Ta kalli hannuwanta, faɗaɗin kafaɗunta, da nauyin jikin da take ɗauke da shi. Ta sake fashewa da kuka mai cin rai...
Ta sake faɗuwa ƙasi tana kuka.

“Me zan yi da wannan kaskantaccen jikin naka? Ta yaya zan koma fada a haka? Ta yaya zan kalli idon mutane?”...

King Diamond ya zo tako yanda take sannan ya sunkuyo kaɗan domin ya daidaita fuskar sa da tata. Yana kallonta da wani irin yanayi na nazari, babu fushi a tare da shi..

“Kin zo ne ki kashe ni,” ya faɗa cikin sanyin muryar mace,
“amma kin ga abin da kaddara ta yi.”

Ayat ta girgiza kanta cikin galaita...
“Wannan ba kaddara ba ce! Wannan mugunta ne! Kayi amfani da tsinanniyar sihirinka!”

Ta ci gaba da jan sumar kanta tana kuka. “Mayar min da jikina... dan Allah... dan Allah ka mayar min da siffata...”

King Diamond ya tsaya yana kallonta na wasu dakikoki. A karon farko wani baƙon abu ya motsa a kwayar idonsa. Wani irin yanayi ne na sha’awa da mamakin yadda kaddara ta hada su...

“Yanzu,” ya raɗa mata a hankali, “zaki ji yadda nake ji tun lokacin da na ɗora idona a kanki.”...

Ta ɗago kai da sauri tana kallonsa, sai kuma ta ga shima itan yake kallo, ta ja tsaki...

“Me kake kallo?!”
ta faɗa cikin fushi, hawaye na zuba daga idanunta...

King Diamond ya tsaya a gabanta, ya haɗa hannayensa a ƙirji. Fuskar Ayat dake kansa ta cika da nutsuwa da iko...

“Idan kina son ki dawo siffarki…”

Ya fara faɗa a hankali...

Ayat ta miƙe tsaye cikin ruɗani, zuciyarta na bugawa da ƙarfi...

“Da gaske?”
ta faɗa da muryarsa, tana matsowa kusa...

“Ka san yadda zan dawo? Ka san yanda zan koma ni?!”..

Idanunta suka cika da bege, duk da fushin dake zuciyarta...

“Faɗa min,”
ta ce da sauri,

“Me zan yi? Mene ne zan biya? Komai zan yi!”..

King Diamond ya ɗan karkatar da kai, ya kalleta kai tsaye. Sai wani murmushi mai ban tsoro ya bayyana a fuskar dake kansa, murmushin da bai kai zuciya ba...

“Abu ɗaya ne kawai,”
ya faɗa cikin sanyi...

Ayat ta runtse idanu na ɗan lokaci, zuciyarta na dukan ƙirji..

“Mene ne?”
ta tambaya cikin sauri..

Ya matsa ƙafa ɗaya gaba, ya rage tazara tsakaninsu..

“Dole ne,”
ya ce a hankali,

“mu sake sumbatar juna.”

Ayat ta tsaya cak.
Numfashinta ya tsaya...

“Me…?”
ta furta a firgice.

Ta ja da baya da sauri, idonta a zazzare.
“Ka haukace ne?!”
ta saki kuka.
“Ka manta wacece ni?!”

Ta nuna shi da yatsa tana rawar jiki...

“Ni makiyarka ce! Ni ce wadda ta zo ta kashe ka! Ta yaya zaka ce min haka?”..

King Diamond bai ja da baya ba. Murmushin nan bai ɓace daga fuskarsa ba ya ce,

“Kamar yadda muka yi a farko,”
ya ƙara faɗa cikin sanyi,
“tare da haɗuwar jini…
tare da haɗuwar rai.”

Ayat ta dinga girgiza kai tana kuka.
“A’a…
A’a…
Wannan ba zai yiwu ba…”
Ta dafe ƙirjinta.
“Wancan kuskure ne! Ba ni da iko a kaina a lokacin!”

Ta ɗaga kai ta kalle shi da tsananin fushi.
“Ba zan sake kusantar ka ba!”
ta faɗa cikin ƙarfin hali..
“Ko da zan mutu a wannan siffar!”..

King Diamond ya ɗan sunkuya kaɗan har fuskokinsu suka kusan haɗewa. Ayat ta ja numfashi, zuciyarta na bugawa...

“Ki yi tunani,”
ya faɗa a hankali, muryarta dake fita a bakinsa na girgiza shi...

“Ko ki zauna a wannan jiki…
ko ki dawo naki.”

Ayat ta lumshe idanu da ƙarfi, hawaye na sauƙa..

“Kai mugu ne…”
ta furta a raunane,
“Ka fi yadda na zata.”..

Ya ɗan miƙe tsaye, yana kallonta daga sama..
“Ba mugunta ba ce,”
ya ce cikin sanyi,
“ƙa’ida ce.”

Ayat ta buɗe idanu, ta kalle shi da wani kallo na tsana da ruɗani a haɗe...

“Idan na yi hakan…”
“ka rantse min cewa zan dawo ni.”

King Diamond ya ɗaga gira kaɗan.
“Idan hakan bai yi aiki ba,”
ya amsa,
“to babu abin da zai yi.”..

Ayat ta yi shiru.
Iskar kogin na busawa, ruwan na ƙara amo.
Zuciyarta ta rarrabu gida biyu...
Ta runtse idanu, hannuwanta na rawa..

“Ka juya,”
ta faɗa cikin sanyi.
“Kar ka kusanto ni yanzu.”

King Diamond ya tsaya, yana kallonta.
“Ki yanke shawara,
lokaci ba ya jiran kowa.”...

✨✨✨

Daren Alhamra ya yi nisa, amma Master Ibrahim bai ko kwanta ba. Yana tsaye a harabar fadar, idanunsa suna kallon sararin samaniya, yana jujjuya takobinsa a hannu. Akwai abin da yake damun sa, ya dace Inuwa ya dawo tun sa’o’i biyar da suka wuce, amma har yanzu babu labarinsa...

"Inuwa ba mutum ne mai taurin kai ko karya doka ba,"

Ibrahim ya raɗa wa kansa.
Ya nufi sashen ma’aikatan tsaro, inda ya tarar da wasu dakarun suna hira ƙasa-ƙasa. Cikin muryarsa mai kwarjini, ya daka musu tsawa..

"Wane ne a cikinku ya ga Inuwa tun bayan sallar azahar? Shin akwai wanda ya ga lokacin da ya fita ko ya dawo?"..

Dakarun suka kalli juna cikin fargaba. Ɗaya daga cikinsu ya matso ya rusuna,

"Master, rabonmu da shi tun safiyar hantsi. Ban sake sanya shi a ido ba."..

Ibrahim ya haɗe rai. Ya san akwai matsala. Ya juya da sauri ya nufi hanyar da take kai shi sashen dawakai. A can ya tarar da babban mai kula da dawakai yana shirin kulle wurin...

"Doki nawa ne babu a nan?" Ibrahim ya tambaya cikin hanzari..

Mai kula da dawakan ya bincika, sannan ya ce,

"Master, akwai doki ɗaya da aka fita da shi, kuma ban ga wanda ya ɗauke shi ba, amma dokin yana cikin dawakan da Inuwa yake kulawa da su."..

Wannan bayanin ya tabbatar wa Ibrahim cewa Inuwa ya fice daga fada. Amma ina ya tafi a cikin daren nan? Kuma me ya sa bai gaya masa ba?

Ibrahim bai tsaya wata-wata ba. Ya ɗauki dokinsa, ya kunna fitilar hannu mai ƙarfi ya fice daga masarautar cikin gudu. Yana da ƙwarewa wajen gane sawayen taku a ƙasa. Ya bi sawun dokin da aka fita da shi tun daga ƙofar gari, sawayen suka riƙa kai shi cikin daji, har zuwa hanyar da take kai mutum ga babban kogin nan da kowa yake tsoron zuwa...

"Me Inuwa zai je yi a wannan kogin har ya kai daren nan?" Ibrahim ya tambayi kansa, zuciyarsa tana bugawa da sauri.

Daidai lokacin da Master Ibrahim yake ƙoƙarin ƙarasowa bakin kogin, King Diamond ya ɗan karkata kansa, idanunsa waɗanda suke a siffar Ayat suka haska da wani irin haske mai nauyi. Ya fahimci cewa akwai bugun zuciyar ɗan Adam dake kusantowa cikin hanzari...

Ba tare da ya ce uffan ba, ya ɗaga hannunsa ɗaya ya kewaye su da shi. Nan take, wani irin shingen sihiri mai launin iska ya mamaye su haɗe da Ayat dake cikin siffarsa da kuma dokin dake can ɗaure. Wannan shingen ya mayar da su Fatalwa a idon ɗan Adam, babu mai iya ganinsu, jin motsinsu, ko ganin hasken sihirin dake wurin, amma su suna iya kallon duk abin da yake faruwa a waje....

Master Ibrahim ya bayyana a bakin kogin, riƙe da fitilar hannunsa dake ta haskawa. Ya zaro takobinsa, idanunsa suna yawo ta kowane sashi..

Ayat dake cikin siffar namiji ta daskare a inda take. Ta zura wa Ibrahim ido, zuciyarta tana bugawa da ƙarfi...

"Master! Me yake yi a nan?" ta faɗa a cikin zuciyarta. Ta so ta kwalla masa ƙira, ta so ta ce "Master, gani nan!", amma tana tunawa da muryar namijin dake fita daga bakinta da kuma siffar dake jikinta, sai ta toshe bakinta da sauri.
Ibrahim ya riƙa haska fitilar sa har daidai inda suke tsaye amma fitilar tana ratsa jikinsu ne kamar iska, bai ga kowa ba sai bishiyoyi da duwatsu. Ya tsaya daidai saitin inda dokin Ayat yake, amma ko dokin bai gani ba...

"Abin mamaki," Ibrahim ya raɗa yana goge gumin goshinsa. "Na tabbata sawayen takun dokin nan sun kawo ni har nan. Amma me ya sa komai ya ɓace? Me ya sa wurin ya yi tsit haka?"

Ya zagaya bakin kogin sau uku, yana duba ko da akwai rami ko wata alama amma sihirin King Diamond ya shafe komai. Ibrahim ya tsaya na wasu daƙiƙoƙi, yana jin kamar ana kallon sa amma ganin ba shi da wata hujja, sai ya girgiza kansa cikin shakku...

"Ƙila tunanina ne ya yaudare ni," ya furta cikin rauni... "Inuwa, kana ina?"

Ya jima a tsaye yana sauraron sautin ruwa, kafin daga bisani ya juya ya nufi inda ya bar dokinsa, ya fara tafiya a hankali yana waigowa har ya ɓace cikin duhun dajin...

Ayat ta sauƙe wani nauyayyen numfashi, jikinta har yanzu yana ɓari. Ta juyo ta kalli King Diamond wanda har yanzu yake tsaye cikin natsuwa...

"Ka ga abin da ka jawo min ko?" ta faɗa da muryarsa, cike da takaici ta ce...

"Master Ibrahim zai kamani da laifi idan bai ganni a fada ba kafin gari ya waye, masarautar nan za ta tashi a hargitse!"

King Diamond ya sauƙe hannunsa, shingen ya ɓace. Ya kalle ta da wani kallo mai zurfi.

"Ba zai gano komai ba... muddin kina kusa da ni."


Anan suka cigaba da zama har alfijr ya fito..

Ayat ta tsaya tana kallonsa. Ta sha kuka har idanuwanta sun kumbura, murya ta dusashe. A karo na farko ta sassauta muryarta...

“Dan Allah…”
ta fara cikin rauni, tana ɗan matsowa kusa,

“ka maida min siffata. Wannan ba ni ba ce. Ina jin kaina kamar baƙuwa a jikina.”...

Ta sauƙe numfashi mai nauyi...

“Ni gimbiya ce… ina da mutunci, ina da iyaka.”

King Diamond ya tsaya tsayin daka sannan ya furta..

“Sumbatar nan ita ce mafita,”

Kalmar sumbata ta buge ta kamar wuta. Ta tashi tsaye da sauri, tana zaro idanuwa..

“Me?!”
ta daka masa tsawa da muryarsa,

“Zan zabga maka mari kai da sumbatar! Kana da faɗin sumbata, sumbata, sumbata! Na bi sumbata da gudu!”...

Tana nuna shi da yatsa, hannuwanta na rawa...

“Na fahimci ka raina ni! Ka raina martabata!”...

King Diamond bai motsa ba. Ya ɗan karkatar da kai, murya ta fito cikin sanyi...

“To kuwa,
haka za mu ci gaba da kasancewa a nan… har tsawon rayuwa.”...

Kalmar rayuwa ta sauƙa a kirjin Ayat kamar theoretical hammer...

Nan ƙirjinta ya buga.
Ta kama ƙirjinta da ƙarfi, numfashinta a rikice. Wani irin sanyi ya ratsa ta. Ta ja da baya..

“Rayuwa…?”
ta maimaita a firgice.
“Ka ce rayuwa?”

Ta kalle shi, idanuwa na cikowa da hawaye, amma wannan karon hawaye na tsoro ne, ba fushi kaɗai ba...

“Ni mace ce,”
ta faɗa a raunane,
“ban san rayuwar ka ba… ban san ƙarfin jikinka ba… ban san yadda zan rayu a siffarka ba…”

Ta yi shiru na ɗan lokaci, ta haɗiye kukan...

“Idan na ji ciwo… kai ma za ka ji?”
ta tambaya cikin rawar murya...

King Diamond ya ɗan kalleta kai tsaye. Ya ɗaga tafin hannunsa, inda aka yanke, a yanzu jinin ya tsaya amma alamar ciwo na nan..

“Eh,”
ya amsa.
“Tun daga wancan haɗuwar jini… abin da kika ji, zan ji. Abin da na ji, za ki ji.”

Ayat ta runtse idanu. Zuciyarta ta buga da ƙarfi fiye da da....

“Ka ɗaure ni,”
ta faɗa cikin kuka....

“Ka ɗaure rayuwata da taka.”

King Diamond ya ɗan matsa kusa. Iskar asuba tana ɗaga sumar gashinsu..

“Ba ni na fara ba....Ke ce.”..

Ayat ta buɗe idanu, ta kalle shi da haɗaɗɗen kallo, ta jinjina kai sannan ta ce..

“zan yarda…amma ba don ina so ba, sai don in tsira..”

Ya ɗan yi murmushi ya ce,

“Na sani.”


Ayat na tsaye a gabansa, idanuwanta sun kumbura da hawaye da ta daɗe tana ɓoye wa...

“Shin kana son ɗauke min zuciyata ne?.”

Ya ce,

“Ba zan taɓa tilasta ki ba.
Ko a mulkina, babu ikon da ya fi na zuciya.”..

Ayat ta yi murmushi mai raɗaɗi, murmushi da hawaye ke yawo a cikinsa..

“Ƙarya ne...Ka riga ka shiga zuciyata… ba tare da izini ba.”..

Ta sauke kai, hawaye suna zubo wa...

“Amma yau…”

ta ɗaga kai tana kallonsa kai tsaye,
“zan buɗe iyakata da kaina.”..

A hankali ya ƙira sunanta..

“Ayat...”

“Ka saurare ni,”
ta katse shi, murya na rawa.
“Zan amince… amma ba haka kawai ba.”..

Ta share hawaye da bayan hannunta, ta ɗaga yatsa ɗaya...

“Na farko.. ba za ka taɓa amfani da iko ko sihiri a kaina ba.”

Ta ɗaga yatsa na biyu...

“Na biyu...Duk abin da zai faru tsakaninmu, sai da yardata.”

Ta ɗaga yatsa na uku, muryarta na rawa.

“Na uku… idan na ce daina,
za ka daina, ko da zaka mutu...”

Shiru ya ratsa tsakaninsu.
King Diamond ya miƙa hannunsa tare da dunƙule wa...

“Idan hakan ne farashin samunki,”
ya ce cikin murya mai nauyi,
“zan biya.”..

Ayat tana hawaye
Ta buɗe hannayenta a hankali. Jikinta na rawa...

“Zo,”

ta faɗa cikin kuka...

“Amma kada ka ɗauka nasara ce.”

King Diamond ya kusanto sannu a hankali, kamar yana kusantar abu mai tsarki. Ya tsaya gaban ta, ya buɗe hannayensa shima, a hankali ta shige faɗaɗɗen ƙirjinsa dake siffar ta...

Bugun zuciyarsu ne yake daidaituwa...
Ayat ta ɗora kanta a ƙirjinsa, tana kuka...

Hannunsa ya tsaya a bayanta, ba tare da ya matse ta ba...

“Ka sani,”
ta faɗa cikin kuka,
“idan ka karya sharaɗina,
zan tsane ka fiye da yadda nake tsoron ka.”..

King Diamond ya sunkuyar da kansa a kanta tare da sumbatar gashin dake kanta..

“Idan na karya sharaɗinki,”
ya amsa,
“to na rasa kaina.”..

A wannan lokacin, aljanu dake nesa suka durƙusa ba tare da umarni ba.
Saboda sarkin su ya karɓi yarjejeniyar zuciya...

Ayat ta buɗe iyakarta, ta ba wa King Diamond damar da ya daɗe yana nema. Duk da tsoro da fargaba dake zukatan su, sai ga shi sun tsinci kansu a cikin wani yanayi da ya zarce tunanin ɗan Adam...

Sannu a hankali, King Diamond ya rage tazara tsakaninsu. Da ya matse ta sosai, A hankali ya kai leɓensa kan nata ko ince, asalin leɓen Ayat dake jikinsa ya haɗu da nasa dake jikinta...

Wani irin zurfaffiyar sumbata ce ta shiga tsakaninsu, sumbatar da ta raba su da duniyar gaskiya...
Sumbata ce da ta ratsa kowane sassa na jikinsu, tun daga tafin ƙafa har zuwa cikin ƙwaƙwalwa...

Sun ji wani irin yanayi da ba su taɓa sanin akwai shi ba a doron ƙasa...
Ga Ayat, ta ji kamar dukkan fushi da ƙuncin dake zuciyarta suna narkewa suna zama ruwan sanyi. Shi kuwa King Diamond, ya ji kamar dukkan ikon da yake da shi ya tattara a wannan gaɓar ta leɓensa...

Wannan sumbatar ta ƙara haɗa ƙaddararsu fiye da haɗuwar jinin da suka yi ɗazu. Ta zama tamkar igiyar da ba za ta taɓa tsinkewa ba, wadda ta ɗaure rayuwarsu guri ɗaya...
Sun ɗauki tsawon lokaci a haka, kowa ya rasa sanin inda yake, kowa ya mance da siffar da yake ciki...
Rungumar da suka yi wa juna ta ƙara tsananta, hannunsa ya zagaye kunkuminta cikin kwarewa da nuna mallaka, yayin da ita kuma ta sa hannuwanta ta riƙe wuyansa, tana ƙoƙarin jawo shi kusa da ita fiye da yadda jiki zai iya haɗuwa...

A daidai lokacin da sumbatar ta kai ƙololuwa, wani irin ƙarfi ya tura su baya, domin a duniyar aljanu wannan kuskure ne kusantar bil adam har haka, sun ga Sarkinsu yana shirin karya ƙa'ida hakan yasa aka raba su da ƙarfi...

✨

Wani irin hayaki mai ƙamshi ya mamaye wurin. Bayan hayakin ya lafa, sai ga shi kowa ya tsinci kansa a asalin jikinsa...

Ayat tana tsaye, numfashinta yana fita da sauri-sauri. Ta duba hannunta ta ga ƙananun yatsunta na mace. Ta taɓa fuskarta, ta ji laushin fatarta. Ta ji nauyin dogon gashinta ya dawo kanta. Ta dawo asalin Gimbiya Ayat!
Shi ma King Diamond, ya dawo cikin siffarsa ta aljani mai farin gashi da kwarjini...

Amma wannan karon idanunsa suna kallon Ayat ne cikin wani irin natsuwa da muryar da ba za ta taɓa mancewa ba...

Dukansu biyun sun tsaya suna kallon juna cikin mamakin abin da ya faru. Har yanzu suna jin zafi da zaƙin sumbatar nan a leɓunansu. Ayat ta so ta yi fushi, amma sai ta ji muryarta ta gaza fitowa...

Zuciyarta tana gaya mata abu ɗaya..
"Yanzu kam, ba za ki taɓa rabuwa da shi ba."..

King Diamond ya tsaya yana kallonta, iskar asuba tana wasa da farin gashinsa dake sheƙi. Duk da cewa kowa ya dawo asalin siffarsa, idanunsa ba su daina kallon leɓun Ayat ba, kamar har yanzu yana jin ɗanɗanon sumbatar da ta canza musu ƙaddara...
Ya matso mataki ɗaya kusa da ita, muryarsa ta fito cikin wani irin amo mai sanyi wanda yake ratsa bargon jikinta..

"Kinyi nasara Ayat. Kin dawo cikin gidan sarautarki, kin dawo cikin siffar da kike alfahari da ita."..

Ya ɗan dakata sannan ya ɗaga hannunsa ya nuna saitin zuciyarta...

"Amma ki sani, sumbatar da muka yi ba wai kawai ta maido mana da siffarmu ba ne, ta zama tamkar Sa hannu a takardar rayuwarki. Daga yau, ba za ki iya ɓoye min komai ba. Idan kina cikin farin ciki, zan ji a jikina. Idan kina zubar da hawaye, zuciyata za ta buga..."

Ayat ta tsaya tana kallonsa, jikinta har yanzu yana ɗan goosebumps saboda kwarjininsa...

Ya cigaba da cewa..

"Ki koma fada, ki ci gaba da wasan ɓoyon da kike yi da mutanenki. Amma karki manta sharaɗinmu, Ni naki ne, ke tawa ce. Duk ranar da kika ji kishirwar gani na, kawai ki kira sunana a cikin zuciyarki, zan bayyana a gare ki ko da kuwa dakarun duniya dubu ne suka kewaye ki."..

Kafin Ayat ta samu damar cewa uffan, King Diamond ya yi wani ɗan gajeren murmushi sannan jikinsa ya fara rikiɗewa ya zama tamkar hasken taurari..

Cikin kiftawar ido, ya ɓace a gaban idonta sai ƙamshinsa kawai ya rage yana tashi a sararin samaniyar kogin...

Ayat ta sauƙe wani nauyayyen ajiyar zuciya, ta dafe ƙirjinta tana jin yadda zuciyarta take bugawa da ƙarfi. Ta duba tafin hannunta, ta ga tabon ciwon nan ya ɓace radau, amma ta sani a ranta cewa alamar dake zuciyarta ba za ta taɓa goge wa ba...

"Ya Allah..." ta raɗa a hankali...

Tana tsaye sai kuma ta ga siffar gimbiyancin ta ya sauya ya koma siffar Inuwa, yanda take kafin wannan lokacin..
Ta shafa fuskarta ta ji akwai gemun da sajen, bata san lokacin da ta sau murmushi ba..

Ta juya da sauri ta nufi inda dokinta yake ɗaure, ta hau shi tare da zaburar da shi da gudu domin ta isa Masarauta kafin idon mutane ya fara lura da bacewarta.....


👍 Like
🔁 Share
💬 Comment


*👑 MASARAUTAR ALHAMRA 👑*

_🪄 Gidan Mulki, Iko da Sirrin Zuciya 🪄_

✍🏽 By ASMEETAH WRITER
~Hasken Jajirtattu~


💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️

```JARUMAI WRITERS TEAM```

⚠️ SANARWA⚠️

Wannan littafi dukiyata ce a matsayina na marubuciya.
⚖️ Ba a yarda wani ko wata ya:
kwafa
gyara
sauya
ko amfani da wani sashe na wannan labari
ba tare da izini na kai tsaye ba.
Duk wanda ya saɓa, alhaki yana kansa..

▶️ DON BIYO DAGA FARKO 👇
🔗 WhatsApp Channel:
https://whatsapp.com/channel/0029VbBCNlqJUM2RQwWncg43

📚 ArewaPen:
https://arewapen.com/u/asmeetahwriter

📖 Wattpad:
https://www.wattpad.com/user/asmeetahwriter

📲 Contact:
09065443871

📅 FARA TURA BOOK:
🔥 01 — 01 — 2026 🔥

📘 BOOK ONE
```MATAKIN FARKO```
Chapter 14 · 0% Book details