← Book details Masarautar Alhamra Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 26 OF 42

CHAPTER 2️⃣4️⃣

Masarautar Alhamra Part 1 Complete Hausa Novel · about 19 min read

*بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيمِ*


Yayin da Ayat ta lula duniyar bacci, King Diamond ya fito daga siffar kuliya ya koma asalin sa. Ya zauna kusa da ita, yana shafa lallausan gashinta cikin wata irin kulawa mai ratsa jiki. Wani irin ƙauna yake ji yana ratsa kowace jijiyar jikinsa, ƙaunar da ba shi da mizanin aunata. Ya kalli kyakkyawar fuskarta, ya kasa jurewa, ya kwanta a gefenta a matsayinsa na mutum, baccin natsuwa ya kwashe shi shima...

Ayat mace ce mai yawan juyi a bacci. Cikin daren, ta fara neman inda take jin ɗumi. Ba tare da ta sani ba, ta haye saman King Diamond...
Can ta ɗora ƙafafunta a kan ƙirjinsa, bayan awanni ta yi pillow da cikin sa.... In the last night ta hau kansa gaba ɗaya ta ƙanƙame shi sosai kamar tana tsoron kar ya gudu, tana jin wani irin ɗumi dake sanya mata natsuwa. Shi ma Diamond, saboda gajiyar kwanakin nan, bai ji daddaɗan nauyin da ta ɗora masa ba, suka ci gaba da sharar baccinsu...

Yau ƙaddara ta so hakan, domin dukkaninsu sun makara har aka idar da sallar asuba a masarautar. Hasken gari ya fara ratsa ɗakin... King Diamond ya fara buɗe idanunsa, ya ji jikinsa ya yi nauyi. Yana kallon ƙasansa, sai ya tarar da Ayat ta mayar shi dokinta, ta rungume shi sosai....

Wani murmushin gefen baki ya yi, yana magana a ransa..

"Ta riƙe ni sosai, ta yaya zan janye ta ba tare da ta farka ba?" Ya san muddin ta buɗe ido ta ganshi a haka, babu abin da zai cece shi daga takobinta...

Cikin dabara da takatsantsan, King Diamond ya sa hannayensa ya ɗaga hannunta da ƙafafunta a hankali, ya juyar da ita zuwa gefe...
Sai Yaraffff! ta faɗa a kan gadon. Sakamakon hakan, Ayat ta fara motsawa, tana shirin buɗe idanunta domin ta tsinci kanta a wani sabon yanayi...

Cikin kifawar ido, ya yi amfani da ikonsa, ya ɓace a matsayin mutum ya koma siffar kuliya a gefenta, daidai lokacin da ta buɗe idanunta tana miƙa...

Ayat ta buɗe idanunta, ta ga gari ya waye sosai. Ta ji jikinta yana mata wani irin ɗumi daban, kuma tana jin tamkar ta yi matashi da wani abu faffaɗa.. Ta kalli Reems dake kwance a gefenta yana kallonta kamar yanzu ya tashi...

"Ya salam! Reems, mun makara!" ta furta tare da miƙe wa. Ta fara tunanin juyin da ta yi a daren, tana mamakin me ya sa take jin tamkar akwai mutum a kusa da ita...

"Wannan juyin nawa kam, ko gado ne ya ruguje ba zan sani ba," ta faɗa tana dariyar ciki..


Ta miƙe tsaye tana murza idanunta, tana jin wani irin ɗumi na musamman dake yawo a jikinta. Ta kalli gadon ta ga yadda ya hargitse, alamar ta yi juyi sosai....
Lokacin da ta kalli madubi tana shirin gyara gashinta, sai idonta ya sarƙe da wani abu dake kwance a kan kafaɗar rigarta ta bacci..

Ta sa hannu ta ɗauko shi. Dogon gashi ne guda ɗaya, fari sol kamar hasken wata, kuma yana sheƙi mai ban mamaki...

Ta zaro ido, ta matso da gashin kusa da idonta..

"Wannan kuma daga ina yake?" ta tambayi kanta..

Ta kalli kanta a madubi, gashin kanta baƙi ne wulk, ba shi da ko saƙar fari. Ta juyo ta kalli kuliyar...

"Reems, wannan gashin naka ne?" Ta matsa kusa da kuliyar ta duba gashin jikinsa. Duk da cewa kuliyar fara ce, amma gashin jikinta ɗan gajere ne kuma mai laushi, ba shi da tsayin da zai kai wannan gashin da take riƙe da shi a hannu..

"Wannan gashin na mutum ne, kuma mutum mai farin gashi!.."

Nan take zuciyarta ta harba. Hoton mutumin nan da ta gani a bakin kogi ya dawo mata...

"Mai Farin Gashi!" ta furta a hankali. Wani irin fargaba da tsoro suka baibaye ta...

"Shin ina nufin mutumin nan yana shigo min ɗaki ne yayin da nake bacci? Amma ta yaya? Masarautar nan fa tana da kariya!"

Ta fara duba ko'ina a ɗakin, tana bincike ƙarƙashin gado da bayan labule, tana jin kamar ana kallonta...

King Diamond, wanda ke cikin siffar kuliya, ya daskare a wurin da yake kwance. Zuciyarsa ta buga ganin ta tsinci wannan gashin nasa. Ya san cewa yau ya tafka babban kuskure. Yana kallon yadda Ayat take bincike cikin fargaba, yana jin tausayinta kuma yana jin tsoron abin da zai faru idan ta gano gaskiyar...

Ta sake dawowa kan gadon, ta zauna kusa da Reems...

"Reems, akwai abin da ka sani wanda ni ban sani ba? Me ya sa nake jin tamkar ba ni kaɗai nake a ɗakin nan ba?"..

Ta matse gashin a hannunta, sannan ta miƙe ta nufi wurin tufafinta...

"Yau dole na je na ga babban malamin tsafi na masarauta... Dole na san ko akwai wata inuwa dake biye da ni, domin wannan gashin ba na duniyar nan ba ne."..

Ta shige banɗaki da gaggawa, yayin da King Diamond ya sauƙe wani nannauyan numfashi. Ya san muddin ta kai wannan gashin wurin malamin tsafi, asirinsa na matsayin kuliya zai iya bayyana..

Ayat ta kammala shiryawa cikin kayan gimbiyanci, jikinta na fitar da daddaɗan ƙamshin mayukan alfarma. Ta nufo gadon da niyyar ɗaukar Reems, amma sai ta tarar da gurbinsa wayam. Ta ɗaga blanket, ta duba ƙarƙashin gado, ta bincika kowane lungu amma kuliya ba ta nan...

Cikin matsananciyar fargaba, ta juya kan madubin don ɗaukar gashin nan dake hannunta, nan ma ta iske ba komai!
Hankalinta ya tashi fiye da kowane lokaci...

"Reems! Reems ina ka shiga ne? Don Allah ka fito!"

Ta fara hawaye lokaci guda, zuciyarta na gaya mata cewa ɓacewar Reems babban rashi ne da ba za ta iya jurewa ba.

Tsabar ruɗani ya sa Ayat ta manta da sanya mayafin da take rufe fuskarta da shi. Ta buɗe ƙofa ta fito, gashinta baƙi wul ya bazu a bayanta, fuskarta tana sheƙi tamkar hasken farin wata...
Tana sauƙa falon ƙasa, ma'aikata da bayin da suka saba ganinta a rufe suka daskare...

Saratu da take ganinta kullum ma ta kasa motsi. Kyawun Ayat ya wuce misali, fara ce sol, idanunta masu kalar zinare suna fitar da hawaye... Kyawunta ya zama tamkar nurul-ayn, wani kwarjini ne dake sanya kowa sunkuyar da kai da daskarewa tsabar kallo. Ba su ma iya tambayarta ina za ta ba, sai kawai suka ba ta hanya tana gudu tana ƙiran sunan kuliyarta...

Tana fita harabar sashenta, jami'an dake tsaron wurin duka sumar tsaye suka yi. Ba su taɓa sanin cewa Gimbiya Ayat tana da wannan irin siffar ba. Suka bi ta da kallo, wasu ma har makaman hannunsu ya faɗi ƙasa ba tare da sun sani ba. Sun ɗauka wata halitta ce daga aljanna ta sauƙo cikin masarautar Alhamra...

Cikin kuka da ƙiran sunan Reems, Ayat ta nufi babban lambun dake cikin sashenta. Wuri ne mai cike da furanni jajaye da farare, masu ƙanshi da kyan gaske... Ta shiga duba bayan kowane fure da ƙarƙashin bishiyoyi, amma babu Reems babu alamunsa...

Wannan lambun dake sashenta ya kasance mafaka a gare ta, domin babu wanda yake da ikon shigowa ya takura mata a ciki. Ta duba ko'ina amma shiru, kukan da take yi ya ƙara tsananta...

Ganin ba ta ga Reems ba, ta durƙusa a tsakiyar lambun, ta haɗa kanta da gwiwa ta fashe da kuka mai ban tausayi...

"In har baka nan, to na sani na rasa ka kenan...me ya sa ka tafi a wannan lokacin?" ta furta cikin murya dake rawa...

Ta jima a haka, tana kuka na tsawon kusan minti talatin, tana jin tamkar rayuwarta ta rage amfani tunda ta rasa abokin hirarta kuma garkuwar zuciyarta...

Can sai ga kuliya ya bayyana a gabanta..

Muryar kuliyar dake fitar da wani siririn sauti ya sa Ayat ɗago kanta da sauri. Tana ganin Reems a gabanta, zuciyarta ta cika da farin ciki...

"Reems!" ta faɗa tare da miƙewa da sauri don ta rungume shi. Amma kafin hannunta ya kai gare shi, sai wani zazzafan haske ya bayyana, tare da wata guguwa mai ƙarfi da ta tada furannin lambun sama. Ayat ta sa hannu ta rufe fuskarta saboda ƙura da ƙarfin hasken da ya kusan makantar da ita.

Bayan hasken ya lufa, ta sauƙe hannunta a hankali, tana addu'ar kada abin da take zargi ya zama gaskiya... Idonta ne ya sauƙa akan abin da ya fi kowane tsoro.. Mutumin nan mai farin gashi!..

King Diamond ne tsaye a gabanta, yana mata wani kallo mai cike da mallaka da isa. Ayat ta zazzaro manyan idanunta, kyakkyawar fuskarta ta bayyana tsantsar firgici....Sai da ta ƙare shi da kallon sama da ƙasa, sannan ba tare da ta tsaya wata-wata ba, ta buɗe ƙaramin bakinta ta saki wani uban ihu ta juya da gudu, tana son barin lambun kafin zuciyarta ta buga...

Gudun Ayat bai kai ko ina ba, domin kafin ta ankara, King Diamond ya ɓace ya sake bayyana a gabanta...

Saboda ƙarfin gudun da take yi, ta kasa tsayawa, sai kawai ta faɗa kan faffaɗan ƙirjinsa dake da ɗumi. Firgicin taɓa shi ya sa ta yi baya da sauri tana shirin faɗuwa ƙasa, amma ya miƙa hannunsa mai ƙarfi ya cafko hannunta, ya tsayar da ita kyam a gabansa...

A wannan lokacin, King Diamond ya sauya siffarsa zuwa asalin siffar Sarkin Power Pool. Yana sanye da fararen kaya na alfarma masu ratsin zinare da gwal. Sumar kansa fara sol an tuƙe ta a tsakiyar kansa da wani ƙarfen gwal, fuskarsa tana fitar da wani haske mai ban mamaki sakamakon tsantsar farin jikinsa..

Duk yadda Ayat take da kyau, a wannan lokacin ta ji kwarjininsa ya kusan danne nata. Ya kura mata ido, yana kallon yadda fuskarta take sheƙi ba tare da mayafi ba, yayin da ita kuma take tsaye jiki na ɓari.

Duk da bugun zuciyarta da ya kusan kayar da ita, Ayat ta dake. Ta tsaya kyam tana kallon cikin idanunsa, hannunta dake cikin nasa yana rawa. Ta kasa magana, amma idanunta suna tambayarsa..

"Shin duk wannan lokacin, kai ne kuliya ta? Kuma kai ne ka ga duk abin da na ɓoye?" King Diamond ya matsa kusa da ita, numfashinsa yana dukan fuskarta, ya raɗa mata cikin muryar sa mai cike da kwarjini..

"Ayat... Shin yanzu kin yarda cewa babu inda za ki iya ɓuya min?"...


Ta fizge hannunta daga nasa, tana kallonsa daga sama har ƙasa, idonta cike da ruɗani da tsoro...

Ya ɗan saki murmushi, ya ce cikin natsuwa,

“Meyasa kika firgita haka? Ni ne Reems.”

Cikin mamaki, muryarta na rawa, ta ce,

“Reeeems…?”

Ya gyara tsayuwarsa, ya ce,
“Ke kika sa min wannan sunan. Amma sunana na gaskiya King Diamond.”

Ta zazzaro ido, zuciyarta na bugawa da ƙarfi...

“Kana nufin… kai ne kuliyar da na ceta?”

Ya girgiza kai a hankali...

“Ni ba kuliya ba ne. Ni Aljani ne. Amma meyasa kika tsorata bayan na nuna miki kaina? Shin ba ni kika zo nema ba?”

Cikin fusata da kunya, ta ɗaga hannu, ta zabga masa mari sosai...

Kan sa ya juya gefe sakamakon marin. Ya dawo ya kalleta kai tsaye, ba tare da ya nuna fushi ba..
Hawaye suka cika idonta. Ta fara lissafa masa duk abin da ke ranta, muryarta na rawar baƙin ciki...

“Na cire kaya a gabanka. Na ci abinci da kai. Na ɗauke ka a cinyata. Abu mafi muni ma, na kwana gado ɗaya da kai! Ka cuce ni! Na yi nadamar sanya maka sunan Reems ɗina... Wallahi kai shaiɗani ne!”

Murmushi kawai ya yi, yana kallonta kamar komai bai dame shi ba...

“Kin ceci rayuwata. Kin ciyar da ni. Ina so in biya ki. Da me kike so na biya ki?”

Cikin tsananin fusata ta ce,

“Ba na son komai naka! Kuma ka fita daga rayuwata!”

Ya girgiza kai.

“A’a. Dole ne in biya ki taimakon da kika yi min.”

Ta yi tsaki.

“Ni ba abin da nake so.”

Ta wuce ta gefensa zata tafi, amma sai ta tsaya cak.
Ta juya ta kalli bayansa, shi kuma yana kallon yadda ta tsaya kafin...

“Akwai wani abu…” ta ce..

“Za ka iya zuwa ka ɗauke min kundirmon nono da na siya maka. Ya ishe ni da wari.”

Ya juyo ya kalleta, ya ce cikin sanyin murya,

“Ai ba ki ba ni shi ba. Shin ba zaɓinki ba ne?”

Ta harare shi...

“Kana so ne, shi ya sa na siya maka!”

Ya ɗan murmusa...
“Tooo… wato kin siya min.”

“Eh! Da kuɗina! Kuma yana da tsada!”

Ya katse ta.
“To meyasa baki tambaye ni ko ina so ba?”

Cikin tsawa ta ce,
“To wa ya yi tunanin kuliya na magana?!”

Sannan ta ƙara da tsauri,
“Kada ka manta ka je ka fitar min da shi.”

Ta juya zata wuce.
Sai ya ce,

“Kin manta kin fito ba tare da abin rufe fuskarki ba.”

Da sauri ta ɗaga hannu tana shafa fuskarta, nan ta tuna ashe da gaske ba ta fito da mayafin fuska ba.
Hankalinta ya tashi...

Sai ya miƙa mata gyalen rigarta da take rufe fuska da shi..

Cike da mamaki ta ce,
“Yaushe ka ɗauko shi? Kuma ta yaya bayan kana tsaye ba tare da mayafin ba?”

Ya ce cikin natsuwa,

“Kar ki manta, ni Aljani ne.”

Ta fizge gyalen daga hannunsa, tana hararansa cikin shakku. Ta yamutsa fuska tana kokkoyan abinda yace.... ta ce,

“Kai ki manta ni aljaji ne”

Ta zazzaro masa ido, ta rufe fuskarta da gyalen, sannan ta juya ta tafi da sauri...

fuuu! kamar ana tura ta da ƙarfi..

Saboda wurin self-secret ne, lambun yana rufe da tsaro sosai, ba a jin komai daga can cikin part. Saboda haka, ihun da ta yi babu wanda ya ji shi…

✨✨✨
Pavilion City

Washegari da asuba, hasken rana ya fara ratsa labulen ɗakin Ching Ching. Tana cikin baccin shagwaɓa, babbar yatsanta a baki tana mafarkin tana masarautarsu ana rarrashinta, Uma Altine tana mata wanka kwatsam sai ta ji wani sanyayyan abu ya taɓa ƙafarta...

"Lokacin tashi ya yi, Shugaba Ching Ching."

Muryar Gely ce ta fito a sanyaye, babu alamar wasa...

Ching Ching ta ƙara jan bargo ta rufe kanta tana gunaguni...

"Ke rabu da ni! Ƙarfe nawa ne ma? Kin san ba a tashi na da wuri haka?"

Gely ba ta bata amsa ba, sai kawai ta danna wani maballi a bango, nan take labulen ɗakin ya buɗe gaba ɗaya, hasken rana ya cika ɗakin... Kafin Ching Ching ta farga, Gely ta yaye bargon ta miƙa mata mopper da bokiti...

"Boss yana jiran karin kumallo... Kuma kamar yadda ya ce, ni zan jagoranci aikinki. Yanzu, ki tashi ki gyara ɗakin nan, sannan ki tafi kitchen ki karɓo abincinsa ki kai masa dining..."

Ching Ching ta tashi zaune gashinta duk ya hargitse, ta kalli Gely da ɓacin rai...

"Daga tashi har kin fara? Ke baki san ana sallah bane? In ke arniya ce to baki san ana wanke fuska ba ne?"...

"Na baki minti biyar kacal," Gely ta faɗa tana kallon agogon jikinta..

Kai tsaye sashen Chief, Gely ta nufa..ta iske shi yana shirin shiga wanka..

"Boss, yanzu Ching Ching zata yi sallah kafin ta fara gudanar da aiki..."

"What? Sallah yanzu?..."

Ya duba agogon hannunsa ya ga ƙarfe takwas har ta wuce, ya girgiza kai ya ce,

"Daga yau, kina tashinta ƙarfe biyar tayi sallah..."

Ta amsa masa cikin girmamawa, daga nan ya shige bathroom yana ɗaure da towel a ƙugunsa....


Bayan minti biyar, Ching Ching ta fito tana ta tura baki, tana sanye da kayan aikinta... Gely ta tsaya a kanta, tana sanya ta goge kowane saƙo na falon. Duk sanda Ching Ching ta yi ƙoƙarin ƙin yin aikin, Gely sai ta matso kusa da ita da idanunta masu hasken ja, nan take Ching Ching take tunawa da shaqar jiya, ta cigaba da aikin tana kuka kasa-kasa...

Zuwa ƙarfe tara da rabi...

A bangaren Dining Area...
Chief Onyx ya fito sanye da rigar bathrobe, gashinsa a jiƙe alamar ya fito daga wanka. Ya zauna a kan dining yana jiran abinci...

Can sai ga Ching Ching ta fito daga kitchen tana turo tiren abincin, Gely tana biye da ita a baya kamar tana korar shanu...

Ching Ching ta zo gaban Chief, ta ajiye masa abincin cikin ɓacin rai, har kofin shayin yana neman zubewa...

"A hankali mana, Shugaba Ching Ching,"
Gely ta faɗa cikin muryar robot...
"Kuma ki durƙusa ki gaida Boss yadda ya kamata."

Ching Ching ta zaro ido, ta kalli Onyx tana neman taimako...

"Uncle Onyx! Dubi yadda take sanya ni aiki kamar baiwa! Har gaidaka sai na durkusa?"

Onyx ya ɗauki jaridarsa ya fara dubawa ba tare da ya kalleta ba...

"Gely ce take da iko da ke yanzu. Duk abinda ta ce, shi za a yi."

Ching Ching ta ji ranta ya ɓaci, ta kalli Gely wadda take kallonta da wani irin mugun murmushi... Ta cije leɓe, ta duƙa kaɗan a gaban Onyx...

"Ina kwana..."

Onyx ya kalle ta daga bayan jaridarsa, ya ga yadda idanunta suka cika da shagwabar nan tata mai sanya zuciya narkewa...
"Lafiya lau. Yanzu ki zuba min shayin."..

Ching Ching ta fara zuba shayin, amma da gangan ta karkatar da hannunta ta zubar da rabin tea a kan rigar Chief Onyx!...

"Ayyah! Yi hakuri Uncle! Hannuna ne ya yi sanyi,"

ta faɗa tana ƙoƙarin goge masa da kwalin kanta, tana sanya kirjinta yana gogayya da kafaɗarsa...

Gely ta matso da sauri, ta ture hannun Ching Ching...

"Ni zan gyara wa Boss. Ke kuma, je ki wanke duk kwanonin da aka yi amfani da su a kitchen, duka da hannunki, ba tare da amfani da na'ura ba!"...

Ching Ching ta fashe da kuka...

"Uncle! Kaga abinda take yi min ko? Wallahi na tsani wannan gwangwanin!"

Ta ruga kitchen tana kuka tana shura ƙafa...

Onyx ya kalli Gely, ya ga yadda idanun Gely suka sauya launi zuwa ja na wucin gadi sa'ilin da Ching Ching ta taɓa shi...
Ya fahimci cewa wannan biyayya ta Ching Ching ta zama filin daga ne na kishin Gely...


Ching Ching tana shiga kitchen, ta tarar da ƙaton falon kitchen ɗin cike da Robots masu girki waɗanda suke ta aiki ba ji ba gani...
Ta kalli tarin kwanukan da Gely ta ce ta wanke, ta murguɗa baki...

"Wai ni Gely za ta sanya aiki? To za ta gani. In har ni Gimbiya ce, to yau sai na ruɗa duk tsarin gidan nan!"

Ta san cewa Gely tana kallon komai ta hanyar kyamarorin jikinta, amma Ching Ching ta san yadda za ta yi. Ta matsa kusa da babban Robot ɗin da yake sarrafa girkin safe...

Ching Ching ta sani cewa Chief Onyx yana son coffee ba tare da sukari da yawa ba...duk da akwai wani a can amma zata ƙara kai masa...

Ta kalli Robot ɗin yana haɗa coffee na biyu na Chief...
Cikin zafin nama da sauri, yayin da Robot ɗin ya juya, Ching Ching ta ɗauki babban cokali na gishiri ta zuba a cikin kofin shayin Chief, sannan ta juya shi da sauri...

"Haka ne," ta raɗa a hankali...
"Idan ya sha wannan, lallai zai yi fushi da Gely tunda ita ce take kula da kitchen ɗin!"


Ching Ching ta lura da wani akwatin lantarki (Control Panel) a jikin bango wanda yake ba wa Robots ɗin kitchen umarni... Ta tuna wata rana ta ga Gely tana danna wasu lambobi. Ta matsa wurin, ta fara danna maɓallan ba tare da sanin me suke nufi ba...

Nan take, Robots ɗin kitchen suka fara hauka! Wani ya fara jefa soyayyen ƙwai a sama, wani kuma ya fara zuba ruwan sanyi a kan biredi... Kitchen ɗin ya hargitse, hayaƙi ya fara tashi!..

Ching Ching ta ɗauki coffee mai gishiri ta ruga da gudu tana kukan ƙarya, ta fito falon dining inda Chief da Gely suke... Ta ajiye kofin akan table tare da faɗa wa jikin Chief Onyx tana kuka mai ƙarfi..

"Uncle! Uncle! Ka tsoratar da ni! Dubi abin da Gely ta sanya Robots ɗinka suke yi! Suna so su kashe ni a kitchen! Gely ta haukata su domin ta huce fushinta a kaina!"...

Onyx ya miƙe tsaye cikin firgici, ya ji ƙaurin hayaƙi yana fitowa daga kitchen...

"Gely! Me yake faruwa a can?"

Gely ta tsaya cak, idanunta suna walƙiya...

"Boss, tsarin kitchen ɗin ya fuskanti System Interference... Ba daga gare ni ba ne..."

"Ƙarya take! Ita ce!" Ching Ching ta ƙara nanname Chief, tana goge hawayenta a jikin rigarsa, tana yi wa Gely gwalo ta ƙarkashin hannunsa...

A daidai nan, Gely ta matso za ta janye Ching Ching daga jikin Chief, sai Chief ya daka mata tsawa..

"Gely! Jeki ki dakatar da haukan da yake kitchen yanzu! Kuma idan na gano ke ce kika haddasa wannan, to akwai matsala!"

Gely ta yi shiru, ta juya ta nufi kitchen ɗin. A data center ɗinta, ta san Ching Ching ce ta yi wannan, amma tana jin zafi yadda Chief ya amince da kukan yarinyar nan fiye da rahoton da ita take bayarwa...

Ching Ching kuwa, tana ganin Gely ta shiga kitchen, ta ɗauki kofin coffee nan da ta zuba mawa gishiri, ta miƙa wa Chief tana murmushin mugunta..

"Sha kofinka Uncle, ka huce fushin nan. Ni na haɗa maka shi na musamman..."

Ching Ching ta tsaya tana kallon Chief Onyx da idanunta masu cike da annurin mugunta, tana jiran ya kurɓi kofin nan mai cike da gishiri domin ya zazzage wa Gely masifa...

Tana kishingiɗe a jikinsa, tana nuna alamun tausayi na ƙarya...

Chief Onyx ya kai kofin bakinsa, amma daidai lokacin da zai sha, sai ya ga yadda kwayar idon Ching Ching take rawa da murna...
Kasancewarsa mutum ne mai matuƙar fiƙira da basira, nan take ya gano cewa akwai wata manufa a tattare da wannan murmushin nata..

Ya sauƙe kofin daga bakinsa, ya kalli kofin, sannan ya kalli fuskar Ching Ching...

"Kin ce ke kika haɗa min wannan musamman don na huce?" ya tambaya cikin muryar da ba ta nuna alamar wasa ba...

"Eh Uncle... saboda na ga ranka ya ɓaci," ta amsa tana ƙara narkewa a jikinsa...

Onyx ya yi wani murmushin gefen baki, ya miƙa mata kofin...

"To tunda ke kika haɗa shi da kanki, kuma naga fuskarki ta nuna kina jin ƙishirwa saboda kukan da kika yi, fara kurbawa kiji daɗin abin da kika haɗa min...."

Ching Ching ta zaro ido, zuciyarta ta buga tum-tum!..
"A’a Uncle... naka ne ai... ni ba na shan kofi da safe..."

"Na ce ki sha!" Onyx ya daka mata tsawa guda wadda ta sanya ta kusan saki fitsari...

Ba yadda ta iya, Ching Ching ta karɓi kofin hannunta yana rawa. Ta kai baki ta kurba babban domin ta nuna masa babu komai. Nan take ta ji wani irin ɗaci da gishiri ya ziyarci makogwaronta!..

Gishirin ya kasance mai yawan gaske har sai da ta ji kamar za ta amayar da hanjinta...

"Puhhh!" Ta fesar da ruwan a firgice, ta sake kofin akan cinyarta, duk ya ɓata mata kaya ga zafi...furzarwar da tayi a fuskar Chief ta watsa wa, duk ya ɓata masa fuska....itama fuskar ta ya ɓaci...

"Meye wannan?" Onyx ya miƙe tsaye, ransa a ɓace...

"Gishiri kika zuba min a kofi? Kina so ki kashe ni ne?"

Daidai nan, Gely ta fito daga kitchen bayan ta kashe duk hayaniyar da Ching Ching ta haddasa...

Ta tsaya tana kallon Ching Ching wadda kofi ya ɓata mata fuska da ta Chief, tana ta tari...

Gely ta buɗe wani allo a jikin hannunta, ta nuna wa Chief Onyx bidiyon sirri na kyamarar kitchen..

"Boss, ga dalilin da ya sa kofin yake da gishiri, da kuma dalilin da ya sa Robots ɗin kitchen suka haukace. Shugaba Ching Ching ce ta hargitsa tsarin."...

Onyx ya kalli bidiyon, ya ga yadda Ching Ching take ta danna maɓallan lantarki tana dariya. Ya juyo ya kalle ta wadda yanzu gishiri ya fara sanya mata ƙaiƙayi a maƙogwaro...

"Kin raina min hankali Ching Ching!"

Onyx ya faɗa cikin zafin rai..

"Kin kusan kashe kanki da kanki.... Gely, ɗauke ta ki kai ta kitchen. Tunda tana son danna maɓallan kitchen, to yau duk kwanukan fadar nan ita za ta wanke su da hannunta, kuma ba za ta ci komai ba har sai ta gama!"...

Gely ta matso kusa da Ching Ching, ta damƙi hannunta cikin ƙarfi na ƙarfe...
"Muje, Shugaba Ching Ching. Lokacin wanke-wanke ya yi."

Ching Ching ta fara ihu tana kiran Daddy, amma Onyx ya juya mata baya ya shige sashensa. Gely ta ja ta zuwa kitchen, tana raɗa mata a kunne...

"Na faɗa miki, ni na'ura ce, amma na fi ki saurin tunani. Makarkashiyar ɗan adam ba za ta taɓa yin nasara a kan lissafin na'ura ba."..
*Likes ɗinku shine albashin marubuci*

👍 Like
🔁 Share
💬 Comment


*👑 MASARAUTAR ALHAMRA 👑*

_🪄 Gidan Mulki, Iko da Sirrin Zuciya 🪄_

✍🏽 By ASMEETAH WRITER
~Hasken Jajirtattu~


💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️

```JARUMAI WRITERS TEAM```

▶️ DON BIYO DAGA FARKO 👇
🔗 WhatsApp Channel:
https://whatsapp.com/channel/0029VbBCNlqJUM2RQwWncg43

📚 ArewaPen:
https://arewapen.com/u/asmeetahwriter

📖 Wattpad:
https://www.wattpad.com/user/asmeetahwriter

📲 Contact:
09065443871

📅 FARA TURA BOOK:
🔥 01 — 01 — 2026 🔥

📘 BOOK ONE
```MATAKIN FARKO```
Chapter 26 · 0% Book details