← Book details Masarautar Alhamra Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 22 OF 42

CHAPTER 2️⃣0️⃣

Masarautar Alhamra Part 1 Complete Hausa Novel · about 22 min read

*بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيمِ*


Bayan Ayat ta ɗauki kyakkyawar farar kuliyar nan mai rauni, ba tare da ɓata lokaci ba ta haye dokinta da sauri. Iskar dake kaɗawa tana busota yayin da take ƙara matse kuliyar a jikinta, tana gudun kada raunukan jikin kuliyar su ƙara tsananta...

Tana isa ƙofar masarautar, ta yi sa hannu a littafin jami'ai cikin hanzari, sannan ta jefa kuliyar cikin wata leda ta musamman domin ɓoye ta daga idanun masu gadi. Ta san idan aka ga kuliya a hannun jami’i irin Inuwa, zai iya tada shakku...

Bayan ta ajiye dokinta a rugar dawakai, tana ƙoƙarin sulalewa zuwa cikin masarauta, sai ta hango Master Ibrahim daga nesa. Cikin sani, ta san cewa muddin idonsa ya faɗa kanta, tambayoyi ne zasu biyo baya. Ta duƙa a hankali, ta laɓe bayan dogayen ginshiƙan masarautar, tana jin wasu jami'ai suna bi ta gefenta suna wasa da dariya..

Tafiya mai nisan gaske tayi a ƙafa kafin ta bi ta wata ɓoyayyen hanya, hanyar da ta kai ta kai tsaye zuwa cikin ɓangarenta na alfarma...

Tana shiga ɗakin baccinta, wanda ke ƙamshi da turaren oud, ta ciro kuliyar da ke lumshe ido cikin galala, ta kwantar da ita a tsakiyar gadonta mai laushin gaske.

A gaban babban madubi, Ayat ta fara cire kayan jami'an nan. Ta cire rawani, ta cire saje da gemun da take amfani da su wajen ɓoye siffarta. Nan take, dogon gashinta baƙi wul, ya bazu har zuwa gadon bayanta. Ta zama asalin kyakkyawar mace, mai kwarjini da izzah...

King Diamond, wanda ke kwance cikin siffar kuliya, yana kallon kowane motsi nata. Duk da ciwon da yake ji, zuciyarsa ta buga ganin wannan canjin. Daga jarumin jami'i zuwa mace mafi kyau da ya taɓa gani a duniyar bil'adama.

Abin da ya ƙara ruɗa Diamond shi ne lokacin da Ayat ta cire kayan jamin'an gaba ɗaya, ta ɗaura farin tawul kawai wanda ya bar fatarta mai santsi a bayyane. Ta nufi gadon, ta ɗauki kuliyar a hankali ta nufi banɗaki da shi...

Yayin da take haɗa ruwan ɗumi a cikin bahon wanka, Diamond yana ta maganar zuci..

"Wannan me take shirin aikatawa ne? Shiga banɗaki tare da ni? Lallai wannan yarinyar ba ta san ko ni wane ne ba!"..

Duk da haka, wani sashe na zuciyarsa yana cike da farin ciki. Masarautar nan tana kewaye da hasken garkuwa wanda ke hana aljanu da kowane irin tsafe-tsafe shiga, amma saboda canjin da ya yi zuwa dabba, kuma ta sanadin Ayat, ya samu damar shigowa har cikin zuciyar gidan...

Ya ƙura mata ido yana mamakin yadda kyakkyawar mace irin wannan take rayuwa a matsayin soja. Wani irin sirri ne yake tattare da ita?

Kuma wane irin ɗumi ne hannuwanta suke bayarwa yayin da take shirin fara yi masa wanka?..

Ayat ta gama gyara wa kuliyar jikinta tsaf, ta naɗe ta cikin tawul mai laushi sannan ta fito bedroom ta ajiye ta a kan gado...

"Minti goma kacal zan yi," ta faɗa cikin murya mai sanyi, "amma kinsan wanka na akwai delay."

Ta shige banɗakin, ta fara haɗa ruwan ɗumi da turaruka masu ƙanshi, tana shirin wanke gajiyar ta...

Tana zaune a cikin bahon wankan, tana goga lallausar fatarta da sabulu, kanta na jingine da gefen bahon. Idanunta a lumshe, amma tunaninta yana can bakin kogi...

"Me yasa nake kewar sa?" ta tambayi kanta. "Duk da abubuwan da ya yi min, musayar jikin nan da ya kusan haukata ni, da kuma kallon tsiraicina da ya yi a kogi, me yasa har yanzu nake jin tamkar akwai wani abu da yake haɗa mu?" Ta ji wani irin ɗumi a ranta, tana fatan da ace maimakon wannan kuliyar, 'Mai Farin Gashin' ne ta gani a yau... A cewar ta..


Tana shiga wankan, Diamond ya ji jikinsa ya fara wani irin zafi...

Kasancewar Ayat tana cikin jin daɗin ruwan ɗumi, shi ma King Diamond ya fara jin wannan ɗumin ta sanadin haɗin jinin da ke tsakaninsu. Ikon tsafinsa ya dawo masa da ƙarfi saboda natsuwar da ya samu a ɗakinta..

Cikin kifawar ido, ƙaramar kuliyar nan ta zama haske, sai ga King Diamond zaune a tsakiyar gadon Gimbiya Ayat. Doguwar farar rigarsa ta masarautar aljanu ta bayyana, sumar kansa fara sol ta bazu har gadon bayansa...

Ya zura wa ƙofar banɗakin ido, yana jin sautin ruwan da yake kwarara. Zuciyarsa tana bugawa. Ya tuna daren nan a bakin kogi lokacin da sukayi musayar jiki, sannan sumbatar da ya haɗa su ya fara dawo masa ƙwaƙwalwa...ya tuna yadda ya kalli kyakkyawar surarta tana wanka ba tare da ta sani ba...
Wannan haɗin jinin da sukayi ya sa yanzu duk abinda take ji, shi ma yana ji. Yana iya jin dumin ruwan da yake taba fatarta, yana iya jin kamshin sabulun da take shafawa...

"Ayat..." ya faɗa a hankali cikin ransa. "Kin zamo wata sirri a rayuwata!.. Kuma me yasa kika zama sanadin da zan ji tausayin bil'adama?"...

Diamond ya miƙe a hankali daga kan gadon, ƙafafunsa tamkar baya taka ƙasi yayin da ya nufi hanyar banɗakin. Ya tsaya a jikin ƙofar, yana sauraron numfashinta....

Ya san cewa idan ta fito ta ganshi a matsayin mutum, babban tashin hankali zai faru, amma wani sashi na ransa yana son ta san cewa yana kusa da ita...

A cikin banɗaki kuwa, Ayat ta fara jin wani irin yanayi na daban. Ta ji tamkar ba ita kaɗai ba ce a ɗakin...

Zuciyarta ta fara bugawa da sauri,
Ta miƙe da sauri daga cikin ruwan, ta ɗauki babban tawul ta ɗaura, tana sauraro da kyau...

"Kamar akwai mutum a ɗakin nan..." ta raya a ranta...

Ta fito daga banɗaki, sanyin ruwan ya sa fatarta yin luwai-luwai..

Tana ganin kuliyar nan a yadda ta bar ta a kan gado, sai ta saki wani irin murmushi mai ban sha'awa irin murmushin da babu wanda ya taɓa gani a masarautar nan sai ita kaɗai...

Ta zauna a gaban madubi, ɗaure da gajeren tawul ɗin da ya tsaya dai-dai cinyoyinta...

Ta fara shafa mayuka masu ƙamshi na alfarma, waɗanda ake yi wa gimbiyoyi oda na musamman daga ƙasashen waje. Kowane shafa mai da take yi, ƙamshinsa yana ratsa hancin King Diamond...

King Diamond, wanda ya riga ya koma siffar kuliya kafin ta fito, ya kwanta lamo yana kallonta ta cikin ƙwayar idonsa. A ransa yana jin wani irin takaici da daɗi lokaci guda...

"Ayat..." ya furta a zuciyarsa...

"Idan kika san cewa ni ne abokin wasanki na ƙuruciya, mutumin da kika yi wa rantsuwar kiyaye fuskarki dominsa, shin zaki kashe ni ne ko kuwa zaki rungume ni?"

Ya kalli yadda take shafa man a wuyanta da kafaɗunta.... Ya tuna lokacin da suke yara, lokacin da komai yake da sauƙi kafin ƙaddara ta mayar da shi sarki a duniyar aljanu..

Ganin yadda ta girma ta zama kyakkyawa haka, kuma jaruma mai faɗa a matsayin Inuwa, ya sa ya ƙara jin kwarjininta a ransa.

Ayat ta juyo ta kalli kuliyar, ta miƙa hannu ta ɗaukota ta ɗora a cinyarta. Ta fara shafa kanta a hankali, tana wasa da farin gashinta..

"Kinsan me? Ke kaɗai ce kika ga fuskata a yau bayan shi," ta faɗa cikin muryar raɗa, tana nufin Mai Farin Gashin da ya ganta a kogi...

"Shi ya ruguza min alƙawarina, amma ke... ke kyakkyawa ce. Zan kula da ke kamar jariri har sai kin warke."...

Diamond ya lumshe ido, yana jin ɗumin jikinta da laushin hannunta. Haɗin jinin da ke tsakaninsu ya sa kowane shafa da take yi masa, yana jin sa har cikin ransa tamkar ita ma tana jin abinda yake ji...

A wannan lokacin, Diamond ya manta da sarautarsa, ya manta da mulkinsa na aljanu, kawai yana son ya dawwama a haka, a jikin Ayat, yana kallon kyawun da kowa yake mafarkin gani amma shi kaɗai ya samu nasarar gani...

Yayin da take cikin wannan yanayin na natsuwa, ba zato ba tsammani sai ta ji takun tafiya a babban falon ɓangarenta...ana haurowa saman bedroom...

Zuciyarta ta buga. Babu wanda yake shigowa ɓangaren Gimbiya Ayat ba tare da izini ba, sai mutum ɗaya...
Wato Saratu, nan ma bata shigowa sai da izini..

"Gimbiya Ayat? Kina ciki ne?" Saratu ce ta daki ƙofar ɗakin...

Ayat ta zaro ido, ta kalli kuliya, sannan ta kalli kayan jami'an nan da ke warwatse a ƙasa waɗanda ba ta gama ɓoyewa ba...

Idan Saratu ta shigo ta ga kayan jami'ai a ɗakin, asirinta zai tonu!...

"Menene Saratu?..."
Ta furta tana shafa jikin kuliya...

Saratu daga bakin ƙofa ta ce,
"Daman an kammala shirya dining ne..."

Ta ce, "ok ki je ina zuwa, na fito a wanka ban kuma sa kaya ba..."

Daga nan Saratu ta juya...


Ayat ta miƙe ta ɗauko akwatin magunguna (First Aid Box) na musamman...

Ta dawo kusa da kuliyar, ta fara goge mata ragowar jinin da ya bushe a wasu sassan jikin, sannan ta shafa mata magani mai sanyi da kuma turaruka masu ƙamshi don rage radadin raunin...

Yayin da take gyara masa gashinsa, Ayat ta kalli cikin idanun kuliyar, wani irin tausayi da shauƙi suka mamaye zuciyarta. Ta ji tamkar kuliyar tana fahimtar kowane sauti da yake fita daga bakinta...

"To ni ban sani ba, mace ko namiji?..."

Tana kallon kuliyar ta kasa gane wa amma ita mace take bata...

Sai kuma ta ce, "idan mace ce ke, ina son ki mun wani alama da zan gane..."

Kuliyar tayi tsumu ko motsin bata yi ba..

Ayat ta kuma cewa "to idan namiji ne yi mun alama.."

Nan kuliyar ta ɗago hannu tana shafa kanta..

Murmushi Ayat tayi tare da ƙara ringumarsa..

Ta ce da shi... "Ka zamo abokina ɗan amana...
Daga yau, ke ba kuliya bace," ta faɗa cikin murya mai cike da shauƙi...

"Zan sanya miki suna Reems... sunan mutumin da ya fi kowa daraja a zuciyata."...

King Diamond, wanda ke cikin siffar kuliya, ya ji wani irin shock ya ziyarci zuciyarsa. Sunansa na asali! Sunan da ya binne shi tun ranar da ya zama sarki a duniyar aljanu. Wani daci da dariya suka taso masa a ransa, ya ce a ransa...

"Ayat... ki rasa a wa zaki sanya sunana sai a dabba? Ni ne Reems dinki, asalin mutumin da kike jira, amma yau gashi kina kira na a matsayin kuliya!"

Duk da haka, ya ji daɗin yadda sunan yake fita daga bakinta, ya tabbatar masa da cewa har yanzu yana raye a zuciyarta.

Ayat ta miƙe ta nufi wurin tufafinta na sarauta. Ta saka riga ta alfarma mai ratsin zinare, sannan ta ɗauko ɗankwalin fuskarta ta rufe kyakkyawar fuskarta kamar yadda ta saba, ta bar idanunta kawai masu Golden Eyes a bayyane.

Ta dawo bakin gadon, ta sunkuya ta manna wa kuliyar sumba a goshi...

Wani irin sanyi Diamond ya ji ya ratsa shi har cikin bargonsa...

"My Reems, zan sauƙa ƙasa domin yunwa nake ji. Zan taho maka da abinci kai ma ka ci, ka huta a lallausar gadona," ta faɗa a hankali sannan ta juya ta fice daga ɗakin cikin takun isa da izza.

Tana fita, kofarta na rufewa, sai ga wani farin hayaƙi ya mamaye tsakiyar gadon. Nan take King Diamond ya dawo asalin siffarsa ta mutum. Ya zauna a tsakiyar lallausan gadon, sumar kansa fara sol ta bazu a kan zanen gadon Ayat...

Ya ɗan gyara zama, ya taɓa goshinsa inda ta sumbace shi, sannan ya saki wani murmushin gefen baki...

"Ayat... idan kika san cewa Reems ɗinki yana zaune a kan gadonki a matsayin sarki, shin zaki iya kawo min abincin kuwa?"

Ya kalli ƙofar da ta fita, idanunsa suna shining da wani irin kwarjini da nuna cewa har yanzu shi ne mai iko, ko da kuwa yana cikin gidan masoyiyarsa ne a asirce....

✨✨

Washe gari a safiyar yau, Gimbiya Maayah tana zaune a kan kujerarta ta musamman a wurin dining area na sarauta, tana cin French Toast mai kwai da zuma wanda aka kawo mata a cikin wani faranti na azurfa mai sheƙi...

Gefenta tsaye masu aiki biyar sanye da fararen uniform, ɗaya na shara, ɗaya na gyaran teburi, ɗaya na kawo abinci, da sauransu...

Acan bakin ƙofa Bodyguards guda biyu ne masu jikin dambe, sanye da baƙaƙen kaya..

Maayah ta ɗaga hannu, ba tare da ta kalle su ba..

“Where is my orange juice?”

Muryarta a sanyaye cike da izgilanci..

Wata mai aiki, wadda kana ganinta kasan sabuwar zuwa ce, ta matso da sauri tana rawar jiki.

“G-Gimbiya, a yau an kawo ruwan Passion Fruit ne, saboda an ce lemun orange ɗin ya ƙare a kitchen.”

Maayah ta ajiye cokalin ta a hankali, sa'an nan ta ɗaga kai ta kalli sabuwar mai aikin. Ta yi mata kallo tun daga kanta har zuwa takalmin ta...

“Kin san cewa a cikin Fadar Alhamra, Maayah ba ta shan ruwan Passion Fruit? Kuma kin san cewa lemun orange bai taɓa ƙarewa ba? Yanzu haka, ki tashi ki kawo min sabon ruwan lemun. Idan kuma ba ki same shi ba, to ki je ki samo wanda zai kawo min a cikin minti biyar, sannan ki cire kayan jikinki ki bar mun site...”

Muryar Gimbiya Maayah ba ta da zafi amma ta fi ƙarfin wuta. Nan take, sabuwar mai aikin ta fashe da kuka, ta durƙusa tana roƙon afuwa...

“Gimbiya, dan Allah, ki yi haƙuri. Na yi kuskure. Zan tafi in samo.”

“Too late,” Maayah ta yi tsaki. Ta kalli ɗayan mai aikin, wadda ta fi ta sanin komai...

“Maimaita wa wannan sabuwar dokokinmu! Ba na son ganin ta a cikin fada ta. Cire mata uniform ɗin ta. Kuma Mama Liyatu ta kawo min ruwan lemu.”

Mama Liyatu ta shigo da sauri, tana sanye da doguwar riga mai kyau...

“Gimbiya ta, dan Allah ki yi haƙuri, abinci yayi daɗi fa. Ki bar ta. Zan kawo miki ruwan.”

Mama Liyatu ta san yadda za ta tausasa ran Gimbiya kafin ta fusata...

Maayah ta yi sigh mai nauyi... “Fine. But babu wanda zai iya damuna a cikin gida na.”

Mama Liyatu ta yi murmushi, amma cikin tsoro take faɗin.

“An gane, Gimbiya. Duk abin da kika ce shi za a yi.”

Ta juya, ta yi nuni ga masu aiki biyu da su raka sabuwar mai aikin...

Bayan ɗan mintuna sai ga wani jami’in tsaro na fadar sarki ya shigo domin isar da saƙo.

Ya gaishe da Maayah dake zaune a kan teburin cin abinci, sannan ya ce,

"Sarki ya aiko ni, yana son ganin gimbiyarsa Maayah..."

Maayah ta ɗaure fuska tare da yamutsa ta cikin isa ta ce,

"Kaje kace masa Maayah makaranta zata je, sai ta dawo."

Kafin Maayah ta sake furta wani abun, har jami'in tsaron ya juya ya fita domin isar da saƙon...

Kamar dama jira yake ta faɗi abin da zai sosa ran sarki, domin tun ba yau ba ake sanar da sarki cewa Maayah ta ɓaci da wulakanci da girman kai tamkar Zayana, amma sarki ya ƙi yarda...

Ganin jami’in tsaron ya tafi ne ya sa Maayah faɗin,

"Daga cewa makaranta zan je shikenan sai ya tafi? Faɗa kawai nayi, amma ba wai naƙi zuwa bane..." Ta ƙarisa maganar kamar mai fargabar abun da zai je ya dawo...

Mama Liyatu ta ce,

"To tinda hakane, kawai ki tashi kije ƙiran sarki. Idan ya ganki da uniform ɗinki, zai fi sallamarki da wuri, ya fi dai baki je gaba ɗaya ba."

Maayah ta kalli Mama Liyatu cikin isa ta ce,

"Mama Liyatu, ni fa ba a bani shawara ballantana umarni. Abin da naga ya dace shi zan yi."

Mama Liyatu ta yi shiru, ba ta sake cewa uffan ba..

Maayah ta ƙara da cewa,

"Ya je ya sanar ɗin tinda shi munafuki ne, bai jira na gama magana ba ya tafi. To makarantar zan je, na ga ko kashe ni za a yi!"

Ta ci gaba da cin abincinta cikin kwanciyar hankali, babu ruwanta da kukan yarinyar da aka kora ba tare da wani dalili na kirki ba....

Cikin minti biyar, direbanta wanda shima yake sanye da uniform ya iso ya tsaya a gabanta...

"Gimbiya, motar tana nan a shirye. Makarantar za a tafi yanzu?"

"Yes. Amma ba zamu bi hanyar da talakawa ke bi ba a yau. Zamu bi ta hanyar Presidential Gate, ina so naga yadda take a yau."...

Direban ya sunkuyar da kai,

"Kamar yadda kika ce, Gimbiya."

Maayah ta tashi, ta zuba ido ga Mama Liyatu ta ce,

"A cikin mako mai zuwa Mama Liyatu, ina so ki shirya min gagarumin party.... Zan gayyaci 'ya'yan ministoci da 'yan kasuwa masu kuɗi... Ba na son ganin talaka a cikin fadar Maayah..
Ki tabbatar an kammala komai kafin na dawo daga makaranta."

Ta fita tana takun alfarma da kasaita, dakarun tsaron ta guda biyu suna biye da ita....
Motar Lexus mai sheƙi ta ɗauke ta ta bar bangaren nata...

Kafin Maayah ta bar bangarenta, har jami'in tsaron ya isa gaban sarki ya sanar da shi yadda suka yi...

Tafida dake zaune a gefe ya cika da mamaki ya ce,

"Maayah ce ta ce haka?"

Jami'in tsaron ya tabbatar masa. Sarki Nourdeen yana zaune a kan karagar sa cikin siffarsa ta Zaki, bai ce komai ba...

Suna zaune
Kwatsam, sai wasu jami'an tsaro suka sanar cewa,

"Ga motocin Gimbiya Maayah nan zasu wuce makaranta."

A lokacin ne Sarki ya miƙe tsaye cikin kwarjini. Shi da kansa ya nufi wajen fada zai fita.

Wasu fadawa cikin girmamawa suka ce,

"Mai Martaba, ka bamu izini mu dakatar da su, ba sai ka fita ba."

Sarki ya ɗaga musu hannu alamar su kyale shi...

Yana fita, daidai lokacin da motocin Maayah suka raba titin gate ɗin fita, sarki ya saki wata irin uban tsawa mai firgitarwa cikin muryar Zaki mai cike da daji...

"MAAAYAAAHH!!!"

Wata irin girgiza motar su ta yi har sai da ta ɗan ɗagu daga ƙasa...

Direban ya danna burki da kansa, motocin suka tsaya cak! Saura kaɗan motar da Maayah take ciki ta kife. A cikin motar, Maayah ta yi sumar zaune saboda tsananin firgici...

Kaf jami'an tsaro, fadawa, bodyguards, da dakarun sojoji babu wanda bai tsorata ba, wasu ma har neman guduwa suke yi..

Fadawan dake kusa da sarki ma kowa ya ruɗe, har sai da wani ya saki fitsari a jikinsa saboda tsananin firgici....

Kukan birkin motocin ya haifar da wata baƙin hayaƙi mai yawa a harabar Gate...

A cikin motar Lexus ɗin, Maayah ta daskare, idanunta sun fito waje, numfashinta ya tsaya na mintuna biyar.. Ba ta taɓa jin muryar mahaifinta cikin wannan yanayin ba. Jikinta ya fara rawa, izzar da take ji yanzu ta narke ta koma tsoro tsagwaronsa...

Sarki Nourdeen ya taka zuwa tsakiyar hanyar, takunsa na girgiza ƙasa... Fuskarsa ta Zaki mai cike da gashi tana wani irin haske na ban tsoro, idanunsa ja wur kamar garwashin wuta...

Ya tsaya gaban motar Maayah, kowa na wajen ya ɗuka, wasu sun kifa fuskarsu a ƙasa don kar su kalli fuskar Zakin...

"FITO!!!" Ya sake daka wata tsawar, wadda ta sa gilashin motar Maayah fara tsagewa...

Ƙofa ta buɗe a hankali. Maayah ta fito, cikin takun tsoro da firgita, ƙafafunta sun kasa ɗaukar nauyinta... Ta zube a ƙasa gaban mahaifinta, uniform ɗinta ya ɓaci da ƙura...

"Barka da safiya... Abul," ta faɗa cikin murya mai rawa, kanta a ƙasa...

Sarki ya matso kusa da ita, inuwar fuskarsa ta Zaki ta mamaye duk jikinta. Ya sunkuyo da kansa daidai kunnenta, tana iya jin zafin numfashinsa da kaurin kishirwar jini da ke tashi daga gare shi...

"Izzah tana da iyaka, Maayah," in ji Sarki, muryarsa tana fitowa daga can ƙasan makogwaro kamar gurnani...

"Kina tunanin don na ba ki damar fita school, hakan yana nufin kin fi ƙarfin umarnina? Jami'in tsaro na ya zo gare ki, amma kika ce sai kin ga dama? Shin kin manta cewa ni ne na gina wannan masarautar da jinina da kuma wannan fuskar tawa?"

Maayah ta fashe da kuka, "Don Allah Abul... kayi haƙuri. Ba nufina ke nan ba."

Sarki ya ɗago kansa, ya kalli dakarun tsaron da ke kewayen motar.

"Daga yau, an soke fitar Maayah makaranta na tsawon wata guda. Za ta zauna a ɓangarenta, kuma kowane malami zai zo har gida ya koyar da ita kamar sauran..."


Ya kalli direban da bodyguards ɗin,

"Ku mayar da ita ɓangarenta. Idan na sake jin ta nuna isa ga wanda na aiko, to zan tabbatar ta san cewa ni Zaki ne, ita kuma 'yar dabba ce a gabana!"

Sarki ya juya ya bar wajen, takunsa yana barin gurbin ƙafa a kan kwalta. Fadawa suka fara rarrafe suna mara masa baya, yayin da Maayah ta rage a durƙushe a tsakiyar titi, tana kuka mai ban tausayi, duk izzarta ta koma kaskanci a gaban kowa...


Bayan kora da aka yi wa Maayah, an mayar da ita bangarenta karkashin tsauraran matakan tsaro...

Tana zaune a ɗakinta, ta kalli kayan makarantar da aka hana ta saka, ta watsar da su gefe guda cikin fushi da takaici...

Washegari da safe...

Malami ya zo har gida domin koya mata, amma Maayah ta ƙi fitowa daga ɗaki. Tana jin kanta ya ragu, musamman yadda yanzu sauran ƴan uwanta za su riƙa yi mata kallon wadda aka hukunta...

"Mama Liyatu!" Ta ƙira da karfi...

Mama Liyatu ta shigo jiki na rawa. "Gimbiya, gani."

"Ki sanar da malamin nan ya tafi. Ba zan fito ba. Kuma ki tabbata babu wanda ya sake ambata sunana a gidan nan yau, idan ba haka ba zan sa a yanke harshen duk wanda ya yi hakan."...

Duk da Sarki ya hukunta ta, Maayah tana kokarin dawo da ragowar izzarta akan talakawa da masu aiki...

Amma a zuciyarta, tana tsoron ranar da za ta sake haɗa ido da mahaifinta mai fuskar Zaki...

Labarin abin da ya faru da Maayah ya isa kunnen Gimbiya Zayana...

Zayana tana zaune a nata sashen, wanda yake can nesa da kowa, cike da kamshin turaren na musamman...

Zayana tana kwance a kan wata gadon alfarma, tana wasa da wani kwarangwal ɗin zinare a hannunta...

Ɗaya daga cikin bayinta ta shigo tana sanar da ita abin da Sarki ya yi wa Maayah...

Zayana ta yi wata irin dariya mai sanyi, wacce take da amo kamar iska..

"Maayah yarinya ce. Tana tunanin izzah ita ce tafiya da bodyguards... Shi kuma sarki, yana tunanin fuskar Zakin nan tasa za ta tsoratar da kowa."..

Ta miƙe tsaye, tana taku cikin nutsuwa...

"Maayah ta yi kuskure da ta nuna rauni ta durƙusa...
Ni Zayana, babu ranar da zan durƙusa wa wannan fuskar ta Zakin. Idan ya yi kuskuren yi min tsawa, zan nuna masa cewa akwai abin da ya fi Zaki girma a daji...."

Ba zato ba tsammani, sai ga Sarki Nourdeen ya ƙariso sashen Zayana... Ya shigo ne da nufin ya gargade ta kamar yadda ya yi wa Maayah, domin ya ji labarin ita ma tana wuce gona da iri...

Sarki ya tsaya a ƙofar sashen nata, ya zuba mata wani irin kallo na kwarjini...

Amma Zayana ba ta ko tashi daga inda take ba, ba ta kuma sunkuyar da kai ba. Ta ƙura masa idanuwa waɗanda suka fara canza launi daga baki zuwa wani kalar ja mai duhu...

"Nourdeen,"
Zayana ta ƙira sunan mahaifinta kai tsaye ba tare da faɗin Sarki ko Abul ba....

"Kada ka kawo wannan gurnanin naka sashena. Ka riga ka sani, Ni na bambanta da sauran yaran gidann nan. Kada ka kuskura ka taɓa ikona."

Wani irin iska mai sanyi ya fara kaɗawa a ɗakin, har fitulun ɗakin suka fara disashewa...

Sarki Nourdeen, Zakin da kowa yake tsoro, ya ji jikinsa ya yi sanyi. Ya san cewa Zayana ba mutum ba ce kawai, tana ɗauke da wani abu da ya fi karfinsa...

Sarki ya ja numfashi, ya kawar da kansa. Ba tare da tsawatarwa ba ya ce,

"Zayana ki kiyaye. Iyakarki daban, tawa daban."
Sannan ya juya ya fita da sauri kafin ikon Zayana ya fito fili...

Zayana ta cigaba da zama, tana wasa da ƴar tsanar ƙwarangwal...

"Izzah ba hauka ba ne, Maayah. Izzah ita ce ka sanya kowa ya tsoraci ko da kallonka ne, har da wanda ya haife ka."..

Ta furta tana sakin murmushin gefen baki...

*SYDNEY*

A can nesa, a cikin wani babban bene mai kallon teku, Ruma tana zaune a kan kujerarta ta mulki...

Sanye take da tufa na alfarma, amma yatsunta suna sanye da wasu tsofaffin zobina. Babban cikinsu, wanda yake da wani baƙin dutse mai sheƙi, yana haskaka wani irin kore-kore...

Ruma ta murza zoben, tana rufe idanunta. Tana iya jin bugun zuciyar Zayana daga Alhamra...

Wannan zoben shi ne "remote control" na tausayin Zayana, muddin yana hannun Ruma, Zayana ba za ta taɓa sanin ma'anar jinƙai ba...

"Nourdeen," Ruma ta yi murmushin mugunta...

"Kana tunanin ka raba ni da ɗiyata? Ka riƙe gangar jikinta, amma ni ina riƙe da ruhinta da tausayinta. Duk sanda kake tunanin kai Zaki ne, ka sani cewa ɗiyarka tana da ikon murƙushe maka kwarangwal ɗin jikinka."

✨✨

A Masarautar Alhamra..

A daidai lokacin da Ruma ta murza zoben a Sydney, sai aka ga idanun Zayana sun ƙara yin ja wur a Alhamra. Wani irin kukan tsuntsu na daji ya tashi daga samfurin kwarangwal ɗin da ke hannunta...

_______________Maayah, wadda ke cikin damuwar hukuncin da aka yi mata, ta kasa daurewa. Ta yanke shawarar zuwa sashen Zayana, ko da yake tana tsoronta, tana tunanin ko za ta samu hanyar fita daga halin da take ciki...

Maayah ta isa ƙofar sashen Zayana, amma tun kafin ta shiga, wani sanyi ya ziyarci ƙashin bayanta..

Ta tura ƙofar a hankali, ta ga Zayana a tsaye, fuskarta babu ko ɗigo na ɗan'adamtaka...

"Me ya kawo ki nan, Maayah?"

Zayana ta tambaya, muryarta tana amo kamar tana magana ne daga cikin kabari.

"Kin zo ne ki yi kuka domin sarki ya nuna miki cewa ke ɗaliba ce kawai?"

Maayah ta haɗiye miyau, ta tsaya cikin izzarta ta ce,

"Ba kuka na zo yi ba. Na zo ne mu haɗa kai. Abul yana neman ya raina mu gaba ɗaya. Idan ya fara da ni, ke ce ta gaba."...

Zayana ta fashe da wata dariyar shakiyanci, ta taka har gaban Maayah...

Ta matsa da fuskarta kusa da ta Maayah har suna jin numfashin juna...

"Ba mu duka ba, Maayah... Ke aka raina. Ni, babu wanda ya isa ya gaya min yaushe zan fita ko yaushe zan zauna..... Ki fita daga sashena kafin na sa ki manta sunanki."..

Maayah ta ji tsoro ya fara ratsa ta, ta juya za ta fita, sai Zayana ta ƙira sunanta..

"Kuma ki gaya wa ma'aikaciyarki Liyatu, kada ta sake barin ƙafarta ta taka wannan sashen nawa. Domin bana buƙatar ko wani ƙazami, ke ma na raina tsabtar ki balle ita...."

Ba ƙaramin ƙuluwa Maayah tayi ba, haka ta share ta koma sashenta cikin fushi, tana huci...

Bayi da hadimai kowa ya rarrabe saboda yadda ta koro kowa da tsawa daga part ɗinta... Ta zauna a kan doguwar kujerarta ta alharir, tana kallon silin ɗakin nata...

"Meye ya kaini?"

Ta faɗa a fili cikin takaici...

"Meye ya kaini wurin Zayana? Don tana da wani sirrin kwarjini da kowa ke tsoro? Ni Maayah ce! Ni ce wadda kowa a International Elite School ke tsoro. Idan Abul ya hukunta ni yau, ba yana nufin na zama raunanniya ba."...

Ta cika da takaicin yadda ta nuna rauninta har ta tafi neman haɗin kai...

A gun Maayah, neman taimako ma kaskanci ne. Ta yanke shawarar cewa daga yau, ko da za ta dawwama a sashenta, ba za ta taɓa nuna wa kowa ba, musamman Zayana, cewa tana cikin ƙunci ba...

Ta ƙira Mama Liyatu...

"Mama Liyatu! Ki shirya min abinci mafi tsada, kuma ki ɗauko min sabon littafin nan na Royal Dynasties... Ina son na nuna wa duniya cewa ko a kulle nake, ni ce sarauniya."

Ita kuwa Zayana, tana nan zaune a daƙin da ko iska ba ta ratsawa sai da izininta. Ta san cewa Maayah ta tafi ne cike da takaici, kuma hakan daɗi yake mata...
A tunaninta, Maayah ba ta kai matsayin da za su haɗa kai ba,
ita Maayah tana izzah ne don tana da kyau da masoya, amma ita Zayana izzarta tana cikin jininta ne...

✨✨✨

Sarki Nourdeen yana zaune a babban falonsa, fuskarsa ta Zaki tana kallon hoton Ruma Mahaifiyar Zayana dake jikin bango. Ya daɗe yana kallon hoton, yana tunanin halayyar Zayana...

"Izzar Ruma ce take yawo a jikin Zayana," ya faɗa a ransa...

"Ba wani abu bane illa gado. Yadda Ruma take kallon kowa kamar kaskantacce, haka Zayana take. Ba zan taɓa mantawa da yadda Ruma ta tafi ta bar min wannan ragamar ba."

Sarki bai kawo a ransa cewa akwai wani tsafin zobe a Sydney da ke juya Zayana ba...

Ga shi, ganin cewa Zayana ba ta yi wa kowa tsawa ko yawo a fili kamar Maayah, sai ya fi jin kwarjininta....

A wurin Sarki, Zayana ita ce True Reflection ta mahaifiyarta, mace mai mulki da taurin kai...


👍 Like
🔁 Share
💬 Comment


*👑 MASARAUTAR ALHAMRA 👑*

_🪄 Gidan Mulki, Iko da Sirrin Zuciya 🪄_

✍🏽 By ASMEETAH WRITER
~Hasken Jajirtattu~


💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️

```JARUMAI WRITERS TEAM```

▶️ DON BIYO DAGA FARKO 👇
🔗 WhatsApp Channel:
https://whatsapp.com/channel/0029VbBCNlqJUM2RQwWncg43

📚 ArewaPen:
https://arewapen.com/u/asmeetahwriter

📖 Wattpad:
https://www.wattpad.com/user/asmeetahwriter

📲 Contact:
09065443871

📅 FARA TURA BOOK:
🔥 01 — 01 — 2026 🔥

📘 BOOK ONE
```MATAKIN FARKO```
Chapter 22 · 0% Book details