← Book details Masarautar Alhamra Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 28 OF 42

CHAPTER 2️⃣6️⃣

Masarautar Alhamra Part 1 Complete Hausa Novel · about 16 min read

*بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيمِ*


Ayat ta tura ƙofar ɗakinta da ƙarfi tana shirin yin kukan haushi, amma tana sa ƙafarta ciki, sai ta tsaya cak. Ta zaro ido tana waige-waige. Ɗakin dake hargitse da barguna a ƙasa da kuma kayan da ta wargaza ɗazu lokacin neman Reems, yanzu ya koma tsaf tamkar ba a taɓa shiga ba.
Kowane abu ya koma muhallinsa; barguna an ninkasu, gadonta an gyara shi da sabon zanen gado mai sheƙi, kura ma babu ita ko kaɗan.
2. Bacewar "Warin" Kundirmo
Ta nufi inda ta ajiye kundirmon nonon nan da yake ishenta da wari, ta duba ko'ina amma ta tsinci gurbinsa wayam. Ba kundirmon kaɗai ba, hatta kwanukan azurfar da ta riƙa ba shi abinci a ciki duk sun ɓace. Ɗakin ya ɗauki wani irin daddaɗan ƙamshi na fure-fure, wanda ya fi ƙamshin kowane turaren da take amfani da shi daɗi.
"Lallai aljanin nan ba shi da dama," ta furta a fili, tana jin wani irin sanyi a ranta duk da fushin da take nuna tana yi.
3. Sakon Kan Madubi
Ta ƙarasa gaban madubinta don ta cire mayafin fuskarta, sai ta ga wani abu dake haske a inda ta ajiye gashin nan ɗazu. Wata ƙaramar sarƙa ce ta zinare mai kyan gaske, wadda take da wani jan dutse a tsakiya dake walƙiya kamar jini.
A ƙarƙashin sarƙar, akwai wani ɗan guntun takarda mai rubutu da aka yi shi da wani kalar tawada mai kyan gaske. Ta ɗauka ta karanta:
"Na kwashe 'kundirmon nonon' kamar yadda kika umarta. Wannan sarƙar kariya ce gare ki. Muddin tana wuyanki, babu wani aljani ko mutum da zai iya cutar da ke ba tare da na sani ba. Ki daina fushi da Reems ɗinki..."
4. Murmushin Sirri
Ayat ta murza takardar a hannunta tana son ta yi fushi, amma sai ta tsinci kanta da yin wani ɗan murmushi na ɓoye. Ta kalli sarƙar, ta taɓa jan dutsen nan, ta ji wani irin ɗumi dake shiga jikinta yana sanyaya mata zuciya.
"Wane irin takura ne wannan? Daga taimako sai ya zama yana bibiyar rayuwata," ta fada, amma duk da haka, ba ta jefar da sarƙar ba, sai ta sanya ta a cikin aljihun rigarta tana shirin ɓoye ta...


Kwanaki bakwai sun shuɗe cur, amma Ayat ta ji su tamkar shekaru bakwai. Tun ranar da ta kore shi a lambu, King Diamond bai sake bayyana ba, kuma Reems (kuliya) bai dawo ba. Ta tsinci kanta cikin wata irin damuwa da fargaba, ko yaushe zuciyarta tana dube-dube, tana kiran sunansa a asirce duk da cewa ta ce ya fita daga rayuwarta.
Yau ta shigo ɗakinta daga can falo ranta a ɓace, ma'aikata sun kai ta bango da wasu maganganu. Cikin fusata, ta fizge mayafin fuskarta ta wurgar da shi akan gado, sannan ta wuce banɗaki tana gunaguni.
2. Sallamar Sarki
King Diamond yana nan a cikin masarautar, domin kariya ta asiri ta hana shi fita sannan ya sake dawowa. Amma yau, ya yanke shawarar komawa fadarsa ta Power Pool. Ya bayyana a tsakiyar ɗakin Ayat domin ya yi mata kallon ƙarshe.
Ya matsa kusa da gadon, ya ga yadda mayafin fuskarta yake a murtuke. Ya ɗauka a hankali, yana jin taushin zaren mayafin a yatsunsa. Wani irin sanyi ya ziyarci ƙirjinsa, ya yi murmushin gefen baki, "Ta kore ni... amma tana nemana," ya raɗa a hankali, domin yana jin yadda zuciyarta take buga sunansa.
3. Gamuwar Ba-Zata
Yana tsaye yana kallon sashen kayayyakinta, ya furta: "Gimbiya... ba ki da ƙarfi kamar yadda kike nuna wa duniya."
A daidai nan Ayat ta fito daga bathroom. Ganin mutum tsaye a tsakiyar sirrin ɗakinta ya sa ta zabura, numfashinta ya kusa tsayawa.
“ME KAKE YI A NAN?!” ta daka masa tsawa, duk da cewa tsoro ya fara ratsa ta.
King Diamond ya juyo cikin natsuwa da kwarjininsa na sarki. Ayat tana tsaye, idanunta cike da wata irin fusata dake gauraye da kunya. Ta tsaya ƙyam kamar kowace sarauniya, amma hannunta dake rawa ya bayyana raunin zuciyarta.
4. Takun Sanya
“Na ce ka fita daga rayuwata,” ta faɗa cikin daka-tsawa. “Amma ka ƙara shigo mini ɗakina?”
King Diamond ya zuba mata idanunsa na zinare, bai kau da kai ba. “Ke ce kika ce na zo,” ya ba ta amsa cikin muryar nan tasa mai ratsa jiki. “Na zo ne domin abin da kika buƙata.”
Ya ɗaga mayafin fuskarta dake hannunsa. Ayat ta zaro ido, "Ka... ka taɓa kayana?"
“Ban taɓa ba,” ya ce cikin nutsuwa, “amma gaskiya na gani.”
Ayat ta ji kamar ƙasa ta haɗiye ta tsabar kunya. Ta ƙaraso kusa da shi tana huci, “Ba ka da kunya! Kai aljani ne mara tarbiyya!”
5. Yarjejeniyar Zuciya
Maimakon ya yi fushi, sai ya saki wani murmushi mai cike da ikon mallaka. Ya matso kusa da ita sosai yadda numfashinsa yake dukan fuskarta.
“Idan da gaske kina son in bar ki,” ya faɗa cikin wata irin murya mai sanyi dake girgiza jijiya, “kar kika sake kiran sunana... koda a cikin zuciyarki ne.”
Kalmar ta daki ƙirjin Ayat tamkar aradu. Ta so ta yi musu, ta so ta ce ba ta kiran sunansa, amma bakinta ya gaza buɗuwa. A wannan lokacin ne ta gano babban sirrin dake firgita ta: Ko tana nuna ƙiyayya a fili, zuciyarta ta riga ta kamu da shi... ta riga ta fara jin bugun zuciyar Sarkin Aljanu a nata jinin.
Haka suka tsaya suna kallon juna, babu mai cewa uffan, yayin da iskar ɗakin ta sauya zuwa wani yanayi na daban...

Dakin ya dauki shiru, sai kawai sautin numfashinsu dake fita cikin sauri-sauri. Ayat ta tsaya tana kallon cikin idanun King Diamond wadanda suke sheƙi tamkar taurari. A fuskarta, akwai sauran burbushin fushi da ƙiyayya, amma a cikin kwayar idonta, wani irin sirri ne na ƙauna dake neman mafaka. Shi kuwa Diamond, kallon da yake mata kallon mallaka ne, kallon da yake ratsa kowace jijiyar jikinta.
2. Kusa Da Juna
Tsananin kwarjinin King Diamond ya sanya Ayat jin jiri, ta fara yin baya-baya tana son nisantar dumin jikinsa dake neman ruda mata tunani. Tana gab da faduwa, sai ta ji wani kakkaran hannu ya zagayo ta kunkuminta. Cikin wani irin zafin nama da kwarewa, Diamond ya jawo ta da karfi, ya mannata da faffaden kirjin sa.
"Yarafff!" Haka kirjin Ayat ya daki nasa, wani irin shock ya ratsa dukkaninsu. A wannan lokacin, babu sauran sarari a tsakaninsu; kunkuminsu ya hade daram, kirjinsu ya manne da juna ta yadda za su iya jin yadda zukata suke bugawa a tare.
3. Tawaratsin Shauki
Ayat ta kasa kwatanta abin da take ji. Ta so ta ture shi, ta so ta kwace kanta, amma hannun Diamond dake kan kunkuminta ya zama tamkar igiyar karfe. Ya daukaka hannunsa daya, ya damko keyarta cikin wata irin kulawa mai dauke da zafi, ya sanya ta dago fuskarta don ta kalle shi.
Idanunsu suka sake sarke wa da juna a wani matsayi na karshe. A nan ne Ayat ta gane cewa dukkan kiyayyar da take nunawa, tana yi ne domin tana tsoron karfin ikon da yake da shi a zuciyarta.
4. Sumbatar Da Ta Tsayar Da Lokaci
Ba tare da wani jinkiri ba, King Diamond ya sunkuya, ya hada bakinsa da nata a cikin wata irin zazzafar sumba (kiss) mai cike da sakonni dubu. Sumba ce ta nuna mallaka, ta nuna kauna, da kuma neman gafarar dukkan yaudarar da aka yi a baya.
Ayat ta ji duniyar tana juya mata. Da farko ta daskare, amma cikin dakika kadan, sai ta tsinci kanta da mayar masa da martanin sumbatar, hannunta ya sarke a wuyansa tana mai kankame shi. A wannan dakin, a wannan lokacin, babu wata gimbiya, babu wani aljani; sai masoya biyu wadanda kaddara ta gama hada su.
5. Numfashin Ruhi
Dukkan wani fushi ya narke ya zama soyayya. Iskar dakin ta canza kalar ta, tana fitar da wani irin ni'ima. King Diamond ya kankame ta, yana jin tamkar ya samu taskar da ya dade yana nema. Sun jima a haka, suna aikawa juna sakonni ta hanyar sumbatar, yayin da zuciyar Ayat take raya mata cewa: Wannan shi ne mutumin da aka halitta domin ya mallaki dukkan abin da nake da shi...


Muddin ka taba Gimbiya Ayat, tabbas ka taba zuma! Da zarar sumbar ta lafa, Ayat ta dawo hayyacinta, fuskarta ta canza kalar zuwa wani ja saboda tsananin kunya da bacin rai. Ta fara dukan kirjin King Diamond da kananan hannayenta, hawaye na wanke mata fuska.
“ALLAH YA ISA! Macuci, ka kuma yi again? Ban yafe ba!” ta fada tana huci. Ta dora hannu a kanta cikin rudani. “Na shiga uku! Na yi gamo da bakin ALJANI!” Ta fara shawagi a cikin dakin kamar wadda aka zare wa lissafi, tana son kawar da dumin bakinsa dake yawo a nata.
2. Dokar Gimbiya
Ta tsaya cak a gabansa, tana nuna shi da yatsa, jikinta na rawa. “Ka san me? Daga yau, ka daina kusantata! Ka daina shigowa dakina, ka daina bin rayuwata!”
King Diamond ya gyara tsayuwa, ya sunkuya kadan don ya daidaita idanunsa da nata, wani kwarjini na musamman na fita daga jikinsa. “Amma ke ce kika kira ni,” ya fada cikin muryar raɗa. “Ke ce kika sa ni zama ‘Reems’. Ke ce kika dauke ni, kika ba ni wuri a zuciyarki—ko baki sani ba.”
Ayat ta hadiye yawu, ta ji maganarsa ta soke ta. “Na yi kuskure,” ta fada cikin tsauri, “kuma ba zan sake shi ba.”
3. Al'ajabin Reems
Ba zato ba tsammani, sai aka ji wani sauti: “Meow.”
Ayat ta juya da sauri, idonta ya sauka akan gadonta. Wata farar kuliya ce sol, zaune tana kallonta da wasu idanu masu taushi. Ayat ta rude, ta kalli Diamond, ta kalli kuliya. “Ku... ku nawa ne a nan?”
King Diamond ya dan murmusa, murmushin dake sanya kowa natsuwa. “Na bar miki bangare na a nan domin kada ki ji kadaici. Shi asalin kuliya ne, ba ni ba. Na san yadda kika shaku da shi, hakan ya sa na baki shi don rage kewa. Idan kika fita daga masarautar nan, zaki iya kirana ta zuciyarki zan bayyana, amma a nan tarkon masarauta zai hana ni shigowa.”
4. Sallamar Guguwa
Duk da cewa Ayat ta ji wani daci a ranta na cewa zai tafi, sai ta saki murmushin keta. “Allah na gode maka da tarko ya kasance! Na gaji da kai, bana son kara ganinka!” Ta dauki kuliyar ta nufi kirjinsa da ita tana tura masa. “Ku duka biyun ku fita daga dakina yanzu! Idan kuka sake kusantata, wallahi sai na sa an binne ku da rayunku!”
King Diamond ya saki wata dariya marar sauti, dariyar dake nuna sha'awar karfin zuciyarta. “Kin fi karfin da nake tsammani, Gimbiya Ayat.” Nan take, ya bace tamkar hayaki, ya bar dakin da kamshinsa kadai.
5. Saƙon Iska
Ayat ta zauna a kan gadon tana sauke numfashi, ta rungume sabon kuliyarta. “Na maida maka sunanka Reems,” ta fada tana shafa kansa. “Kiyaye ni daga irin wannan mai farin gashi, wai shi King ko?...” Kuliyar ta lumshe ido cikin natsuwa.
Amma tana cikin wannan tunanin, sai ta ji muryar King Diamond ta ratsa iskar dakin: “Ko kin so ko ki ki... zan dawo.”
Ayat ta shafa sumar gashinta, ta turo baki tana gunaguni: “Wannan aljani fa, ba ya jin magana!”....


A harabar fadar, limousine baƙaƙe mai tsawo ya tsaya jiran Gimbiya. Motar tana sheƙi kamar madubi. Driver ɗinta ya tsaya cikin tsabta, uniform dinsa yana nuna tsoron aiki fiye da alfahari.
Maayah ta shiga motar ba tare da ta kalli kowa ba. Bodyguards guda biyu suka bi a baya cikin babban jeep.
Driver ya shiga, ya gyara rawaninsa.
“Gimbiya, ina roƙon albarka.”
Ta ɗora ƙafarta kan kujerar gaba—alamar raini da iko.
“Ka saurare ni da kyau,” ta ce cikin murya mai sanyi.
“Idan muka makara ko da minti ɗaya, zan kore ka. Ba wai daga aiki kaɗai ba—daga cikin fadar nan ma. Ina son na shiga aji kafin mai kula da aji.”
Zufa ya keto wa driver. Bai ce uffan ba. Ya taka gas da gudun sarauta.
Mulkin Aji
Makarantar tana daga cikin mafi tsada a birnin. Da zarar motar Maayah ta tsaya, yara masu gata suka taru suna kallon shigowarta—kamar yadda ake kallon wata sarauniya a titi.
Da ta shiga aji, shiru ya mamaye wurin. Wannan aji na ƙarshe (Final Year) ne, amma ikon Maayah ya fi na shekarunsu.
Ta zauna a kujerarta—kujerar da babu wanda ya taɓa kusantar ta.
Malami ya fara darasi, amma Maayah ba ta saurare shi. Ta buɗe littafi, amma tana zane-zane—tana zanen kanta a matsayin sarauniya, wasu kuma a ƙasa suna durƙushewa.
Sai wata yarinya—’yar scholarship—ta yi kuskuren amsa tambaya.
Maayah ta miƙe tsaye.
“Ke!” ta nuna ta da yatsa.
“Wannan amsar taki ta ɓata min kunne. Kina lalata min ajin alfarma. Ki fita yanzu!”
Malamin bai yi magana ba. Ajin ya yi shiru kamar an rufe numfashi.
Bayan haka, Maayah ta ɗauki waya a hankali, tana murmushi mara tausayi. Ta kira wani saurayinta na wasa...

“Yanzu ka fita, ka siyo min Ice Cream mai zafi! Kuma dole ne ya zama mai sanyi!” (Wata sabuwar fitina ce kawai don ta ji daɗin ikon ta!)

Ta katse wayar, ta jingina a kujerarta.
A wannan aji—
Gimbiya Maayah ce doka.
Ikonta ya fi na malami.
Babu wanda ya isa ya taɓa ta.
Babu wanda ya isa ya ce mata a’a....

Bayan Khausar ta kori yarinyar scholarship kuma ta aika boy friend ɗin ta na wasa neman ice cream mai zafi, aji ya koma cikin shiru da tsoro. Kowa yana jiran karin darasi ko kuma wani sabon fitina daga Gimbiya.
A wannan lokaci ne, Babban Malami ya shigo aji tare da wani Saurayi Mai Kyakkyawan Surar Jiki! Wannan saurayin tsaunin mutum ne! Yana da kirar jiki mai cike da alhurma da ƙarfi, sannan Sajen fuskarsa a kwance luf-luf, wanda ya ƙara masa wani irin kwarjini!
Malamin ya gabatar da shi. “Ya ku ɗalibai, ga Sabuwar Malamin ku na Siyasa da Tarihi! Malam ZAIN! Ya dawo daga wata babbar Jami’a a ƙasashen waje! Zai koyar da ku da tsanani! Kuma ina rokon ku ku ba shi cikakkiyar biyayya!”
Malam Zain ya zuba wa ɗalibai ido. Fuskarsa a ɗaure take da tsauri da iko!
Arangama ta Farko: Bi ni ko Mutu
Duk ɗalibai aji sun miƙe tsaye, ciki har da Malamin Darasi na Dā! Suka yi Gaisuwa da Girgiza Kai ga Malam Zain!
Sai dai Gimbiya Khausar!
Khausar ta yi zaman ƙasaita! Ta ɗora hannu ɗaya a teburin ta, bata da niyyar miƙewa ko yi masa gaisuwa! Ikon Sarauta bai yarda da girmama Malam ba!
Malam Zain ya zuba mata ido! Bai nuna mamaki ko tsoro ba! Ya zama tazara mai ban tsoro a cikin ajin!
Kowa ya shiga tsoro! Sun san cewa Khausar ba ta gaisuwa ga kowa! Kuma sun san cewa Malam Zain ba Malami mai tsoro ba ne!
Malam Zain ya ajiye jakarsa a tebur! Ya nufi Gimbiya Khausar a hankali! Ya tsaya a gaban teburin ta! Ya sanya hannun sa a tebur da ƙarfi, ya kalle ta cikin tsantsar idon ta!
“Ke!” Ya furta da murya mai ƙarfi da tsauri! “Miƙe tsaye!”
Khausar ta zaro idonta cike da tsoro! Babu wanda ya taɓa yi mata irin wannan maganar a cikin rayuwar ta! Ba ta gane cewa wannan malam baya tsoron ta ba!
Khausar ta yi murmushin izgili! “Wa kake gayawa haka? Malam, na ga ka shigo aji! Amma ni ba ɗaliba ba ce! Ni Gimbiya Khausar ce! Kowa a aji nan zai gaishe ni! Kuma ba ni da lokacin miƙewa!”
Malam Zain ya kalli ɗaliban aji! Ya ga tsoro a idanun su! Ya gane cewa Khausar ce Sarauniyar Aji!
Ya yi murmushi mai sanyi da tsauri! “Ki yi shiru! Idan har kina son zama Sarauniya a cikin gida! Amma a cikin wannan aji, ni ne Sarkin ki! Kuma a cikin wannan aji, duk wanda ke da rai dole ne ya miƙe tsaye idan Mai Iko ya shigo!”
Ya sake cewa da murya mai ƙarfi da tsauri!
“Miƙe tsaye, Khausar! Yanzu! Idan har ba haka ba, zan fitar da ke daga aji! Kuma zan sanya a rubuta miki laifi a cikin record ɗin ki! Ni ba na jin tsoron kowa! Ko da kuwa Ƴar Wacece ce!”
Khausar ta yi fari tas! Jikinta ya fara rawa! Ta fahimci cewa wannan mutumin baya wasa! Tana iya ganin azabar hukunci a cikin idanun sa!
Dole ne ta zaɓa: Girman Kai na Sarauta ko kuma Biyayya ta Farko!
Khausar ta tashi a hankali, amma cikakkiyar fushi ya rufe fuskarta!
“Wannan shine na ƙarshe!” Ta furta da murya mai rauni!
Malam Zain ya yi murmushin nasara! Ya shiga cikin cikakken iko!
“An gaishe ni! Yanzu ki zauna! Kuma ki mai da hankali! Idan har kika sake yi min raini! Zan hukunta ki yadda ba za ki taɓa manta ba! Gimbiya!” Ya jaddada kalmar Gimbiya da izgili!
Khausar ta zauna! Fushin ta ya haura sama! Cakwakiya ta fara!


Uncle Raees ya koma teburinsa. Ya gyara sajen fuskarsa da kwanciyar hankali!
“Yara, ni Bako ne a aji nan! Kuma ina buƙatar sanin sunanku da halinku! Daga yau, tsari na zai zama Ilimi shi ne Sarki! Ba Mulki ba! Kuma duk wanda ke zaune a aji nan Jahili ne da ya zo neman ilimi! Don haka, babu wanda ya fi wani! ”
Ya ɗauki litattafan Computer Science! Ya zuba wa ɗalibai ido. “Za mu koyi Computer Science yanzu! Kuma zan fara da jerin sunayen ku! Duk wanda zai faɗi sunansa dole ne ya miƙe tsaye!”
Tilastawa da Juriya
Ɗalibai suka fara miƙewa ɗaya bayan ɗaya, suna faɗin sunayensu cikin girmamawa. Lokacin da aka zo ga jerin sunayen (register), Uncle Raees ya kalli jerin sunayen har ya zo kan Khausar.
Khausar ta yi zaman ƙasaita! Ta ƙi miƙewa! Ta harara wa Uncle Raees! A cikin zuciyarta: “Wane ne wannan mutumin? Ashe bai san wacece ni ba? Wannan rashin kunya ne!”
Uncle Raees ya taka zuwa wurin Khausar! Ya tsaya a gaban teburin ta! Ya kalli kowane ɗalibi a aji!
“Wannan Gimbiya fa? Ko sunan ta za ta faɗa da girman kai?”
Khausar ta dube shi da girman kai! “Class! Me kuke jira? Ku sanar masa mana! Wannan ina ga bai san aikinsa ba! Ko kuma yayi gangancin wulaƙanta ni!”
Wasu daga cikin ɗalibai sun shiga shirin faɗa masa sunan ta (saboda tsoro), amma Uncle Raees ya katse su da tsawa!
“Ku yi shiru! Ita nake so ta miƙe ta faɗa sunan ta! Domin duk ɗaya kuke a aji nan! Ba mulki ba! Ba siyasa ba! Ba iko ba! Ba kuɗi ba! Sai Naman Ilimi wato Yaƙi da Jahilci! Domin duk wanda yake zaune a ajin nan Jahili ne, yazo neman ilimi!”
Khausar ta yi murmushi mai izgili! Ta girgiza kai! Taƙi miƙewa! Tana tunani: “Wannan malamin ya fi rashin kunya fiye da Fatsu!”
Hukunci Mai Zafi
A fusace, Uncle Raees ya buga teburinta da ƙarfi! Wani babban sauti ya cika ajin! Har sai da Khausar ta zabura! Ba ta son tsawa!
Uncle Raees ya sanya hannun sa a tebur, ya kalle ta da tsantsar tsawa ta Turanci:
“You are very stupid! Stand up! You have absolutely no respect for the rule of law! Who do you think you are? You are a student, and in this class, you are nobody but a learner! Miƙe! Sanar da sunanki yanzu!”
Khausar ta yi fari tas! Cikin baƙin rai da tsanani, ta miƙe! Sai da ta ɗauki mintuna kafin ta buɗe baki.
“Name: SHAHZADI NOOR MUHAMMAD ALHAMRA! Better known as Khausar!” Ta furta da girman kai!
Tana furtawa, ta zari jakarta! Tana shirin fitowa daga aji! Alamar cewa ta gaji da wannan wulaƙancin!
Uncle Raees ya yi saurin riƙo hannunta! Ya zaro ido da fushi mai zafi! Ya yi magana a fusace cikin Turanci mai tsanani!
“I am not done with you! You will sit down right now and write an apology letter to this entire class for your display of poor character and arrogance! You will not leave this class until I dismiss you! Sit down!”
Uncle Raees ya zaunar da ita da ƙarfi! Khausar ta zauna! Jikinta ya yi sanyi! Fuskarta cike da hawaye na fushi! Wannan mutumin ya karya ikon ta!
Malam Zain (Uncle Raees) ya koma teburin sa! Ya fara darasi a kan Harshen Computer (Computer Language) kamar babu abinda ya faru! Amma Khausar ta zama cikakkiyar Jahiliya a aji! Ba za ta taɓa gafarta wa Uncle Raees ba!....

*Likes ɗinku shine albashin marubuci*

👍 Like
🔁 Share
💬 Comment


*👑 MASARAUTAR ALHAMRA 👑*

_🪄 Gidan Mulki, Iko da Sirrin Zuciya 🪄_

✍🏽 By ASMEETAH WRITER
~Hasken Jajirtattu~


💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️

```JARUMAI WRITERS TEAM```

▶️ DON BIYO DAGA FARKO 👇
🔗 WhatsApp Channel:
https://whatsapp.com/channel/0029VbBCNlqJUM2RQwWncg43

📚 ArewaPen:
https://arewapen.com/u/asmeetahwriter

📖 Wattpad:
https://www.wattpad.com/user/asmeetahwriter

📲 Contact:
09065443871

📅 FARA TURA BOOK:
🔥 01 — 01 — 2026 🔥

📘 BOOK ONE
```MATAKIN FARKO```
Chapter 28 · 0% Book details