← Book details Masarautar Alhamra Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 29 OF 42

CHAPTER 2️⃣7️⃣

Masarautar Alhamra Part 1 Complete Hausa Novel · about 19 min read

*بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيمِ*


Saboda tsantsar fushin da Chief Onyx ya nuna, hakan yasa yanzu kowa ya koma matsayinsa..

Gely ta koma yadda take a da na’ura mai bin umarni ba tare da nuna wani shauki ba... Tana yin dukkan ayyukanta cikin kwarewa, shirya ofis da tura sakonni, tana nan tsaye a bayan Chief koda yaushe in har ba wani aiki ya sanya ta ba...
Ta daina nuna kishi amma idanunta na na’ura koyaushe suna bin kowane motsi na cikin gidan...

Ching Ching kuwa, duk da cewa fushin Chief ya tsoratar da ita, amma tana nan da dabi’arta. Ta fara yin ayyukan wanke-wanke da goge-goge cikin ɓacin rai, amma duk sanda ta ga Gely ta zo wucewa, sai ta nemi abin da za ta faɗa don ta ɓata mata rai...

Wata rana, Ching Ching tana share falon Chief inda Gely take tsaye tana duba wasu takardu...

Ching Ching ta matso da tsintsiyar ta har karkashin kafar Gely, ta fara sharewa da karfi, tsintsiyar na dukan sawayenta...

"Ke! Matsa min a wurin!"

Ching Ching ta faɗa tana hararar Gely...
"Kin zama bango a nan, ko kin manta Chief ya ce ke na'ura ce kawai? Matsa na goge wurin, 'yar gwangwani kawai...."

Gely ta matsa gefe ɗaya a hankali ba tare da ta nuna ɓacin rai ba...

"Shugaba Ching Ching, tsaftace falon nan aikinki ne. Amma ki sani, duk tsintsiyar da kike bugana dashi, na'urar jikina tana daukar hoton yadda kike bata aiki."..

Ching Ching ta yi dariyar raini...
"Hoto? Oho miki! Ke dai kin ji haushi don kin ga Chief ya daina bari kina zama a cinyarsa. Ni ko da ya kore ni, ai ya taɓa sumbata ta... Ke fa? Ko taɓa ki baya son yi yanzu."

Ta matso kusa da kunnen Gely ta raɗa mata..

"Ko kin gyara ofis ɗari, ni ce mutum a nan, ke kuma inji ce. Kuma ko ba daɗe ko ba jima, sai na sake sanya shi ya kalle ni..."

Gely ta ci gaba da kallon takardun hannunta...
"Lissafi na ya nuna cewa mutum yana da saurin mantawa da haɗari... Ina baki shawara ki nutsu, kafin Boss ya cire ki daga matsayin 'yar aiki ya mayar da ke 'yar gudun hijira."

Ching Ching ta murguɗa baki ta wuce tana rera waƙa..

_"Gwangwani... gwangwani... ko an gyara ta, gwangwani ce!"_

Duk da cewa Gely ba ta nuna komai ba, amma a cikin kwakwalwarta ta na’ura, tana ta lissafa dukkan cin mutuncin da Ching Ching take mata. Ta san cewa Chief ya hana ta nuna soyayya ko kishi, amma bai hana ta kiyaye doka ba. Don haka, ta fara neman duk wani ƙaramin kuskure na Ching Ching don ta kai kararta wurin Chief, amma ta yadda Chief zai ga ita Gely mai gaskiya ce....

✨✨

Bayan kwanaki da Chief Onyx ya ja musu kunne, gidan ya yi tsit, kowa yana ƙoƙarin kiyaye iyakarsa..

Chief ya rage yawan magana, ya nutsu cikin ayyukansa na ofis, yayin da Gely da Ching Ching suke gudanar da nasu ayyukan kamar yadda aka tsara..

Ching Ching tana yin shara da goge-goge, amma zuciyarta ba ta daina bugun neman dabarar yadda za ta sake kusantar Chief ba..
Tana share falon ofis, tana kallon Chief ta ƙarkashin ido, tana son ta sake jin wannan ɗumin jikinsa, amma kwarjininsa ya hana ta magana...

Gely kuwa tana tsaye a gefen Chief, tana miƙa masa takardu cikin tsari... Ko kallon inda Ching Ching take ba ta yi ba, amma tana lura da duk yadda Ching Ching take ta murguɗa baki tana share ƙarƙashin teburin Chief..

Kwatsam, sai Ching Ching ta ga wata dama.. Ta ga kofin coffee Chief ya kusa ƙarewa. Ta ajiye tsintsiyar, ta matsa kusa da teburin, ta sa hannu za ta ɗauki kofin tare da faɗin

"Uncle, bari na wanke maka kofin nan na kawo maka wani shayin mai daɗi..."

Daidai lokacin da ta sa hannu, sai Gely ita ma ta sa hannu a kan kofin. Hannun Gely na ƙarfe ya taɓa na Ching Ching...

"Shugaba Ching Ching, wanke kofuna a kitchen aikinki ne,"
Gely ta faɗa cikin muryar robot mai sanyi...

"Amma ɗaukar kofin daga hannun Chief da kawo masa shayi, aikina ne na PA. Koma ki ƙarasa share wurin da kika bari."

Ching Ching ta harari Gely, ta ƙara matse kofin...

"Ni na ce zan yi! Uncle, kalle ta ko? Ko kofin ma ba za ta bari na ɗauka ba?"

Onyx ba tare da ya ɗago kai daga takardar da yake dubawa ba ya furta..

"Gely tana da gaskiya... Ching Ching, koma ki ƙarasa share-sharenki. Idan kin gama, ki tafi ki gyara babban falon baƙi..."

Ching Ching ta saki kofin cikin fushi, ta koma tana buga ƙafa a ƙasa. Ta san cewa Gely tana amfani da aiki ne don ta nisanta ta da Chief...

Yayin da Gely ta fita da kofin, ta gifta ta gaban Ching Ching. Ta ɗan tsaya kaɗan, ta kalle ta da idanunta masu sanyi, sannan ta raɗa mata a hankali yadda Chief ba zai ji ba..

"Nasarar da kika samu ranar, kuskure ne na lokaci ɗaya. Amma a yau, ni ce nake riƙe da kowane mataki na tafiyar sa. Ki ci gaba da shara, Shugaba Ching Ching."

Ching Ching ta kusa fashewa da kuka saboda haushi. Ta gane cewa yanzu Gely ba ta kishi ta hanyar ihu, tana kishi ne ta hanyar nuna cewa ita ce take da iko da komai na Chief.

Bayan Gely ta fita, Ching Ching ta matso kusa da teburin Chief, ta durƙusa a ƙasa kusa da ƙafafunsa kamar tana goge wurin...

"Uncle... gaskiya Gely tana takura min... Kuma... kuma ni har yanzu ina tuna abin da ya faru a ɗakina. Shin kaima kana tunawa?"

Onyx ya dakata da rubutun da yake yi. Ya kalle ta, ya ji wani irin tausayi da kuma shauƙin da yake ƙoƙarin dannewa...

"Ching Ching, na faɗa miki mu bar wannan maganar. Ki yi aikinki, ni ma na yi nawa."

Amma Ching Ching ta sanya hannunta a kan gwiwarsa a hankali, tana kallonsa cike da shagwaba...

"Amma ni bazan iya dainawa ba Uncle. Kullum idan na rufe idona..."

Kafin ta ƙarasa maganar, sai suka ji sautin takun ƙafar Gely tana dawowa...

Ching Ching ta janye hannunta da sauri ta fara goge ƙasa tana rera waƙa, kamar ba ita ce take magana ba...

Gely ta shigo ofishin riƙe da kofin shayin Chief, amma nan take na'urorin kyamarar idonta suka gano cewa akwai wani canji a yanayin zafin jikin Chief Onyx da kuma matsayin da Ching Ching take. Ko da yake Ching Ching ta janye hannunta da sauri tana goge ƙasa, Gely ta riga ta gano cewa an taɓa Chief a wurin da bai kamata ba...

Gely ta ajiye shayin cikin natsuwa, sannan ta juyo ta kalli Ching Ching...

"Shugaba Ching Ching, na'urorin dake ƙasan teburin nan suna da matukar muhimmanci.. Kada ki kuskura ki sake taɓa ƙafar Boss da sunan goge ƙasa, domin hakan zai iya goge wasu muhimman bayanai."

Ching Ching ta turo baki, ta miƙe tsaye tana kakkaɓe jikinta...

"Ke dai idonki ne ya nuna miki hakan! Ni goge wurin nake yi."

Chief Onyx ya yi gyaran murya don ya kawo karshen wannan takaddamar...

Ya kalli takardar dake gabansa, sannan ya kalli Gely da Ching Ching...

"Ya isa haka. Akwai wani babban aiki da nake son a kammala yau. Za a sauya duk labulen babban falon gidan nan zuwa labule masu sarrafa kansu wato Smart Curtains...."

Ya kalli Gely,

"Gely, ke ce za ki tsara yadda za a jera su..."
Sannan ya kalli Ching Ching,
"Ke kuma, tunda ke kika san yadda kuke son launin ɗakin ya kasance, ke za ki taya ta wajen jera labulen daki-daki. Ina son ku yi aiki tare don komai ya kammala kafin yamma..."

Ching Ching ta kalli Gely, Gely ma ta kalle ta...
Wannan shi ne karon farko da za su yi aiki kafada-da-kafada ba tare da Chief yana kusa ba...

✨

A Babban Falo...
Gely tana tsaye a kan wani dogon matakala tana ƙoƙarin haɗa wasu wayoyi a saman silin, yayin da Ching Ching take kasa tana ƙoƙarin miƙa mata labulen ɗaya bayan ɗaya...

"Miƙo min labule na gaba," Gely ta bada umarni ba tare da ta kalle ta ba...

Ching Ching ta ɗauki labulen, amma maimakon ta miƙa mata cikin natsuwa, sai ta tura shi da karfi yadda Gely za ta rasa daidaiton ta...

"Gashi nan! Ke komai sai kin nuna isa, kamar ke ce kika yi kanki."

Gely ta riƙe matakalar da kyau, ta kalli Ching Ching daga sama...

"Kina ƙoƙarin sanya ni faɗuwa ne? Kin sani cewa idan na faɗo a kanki, nauyin karfen jikina zai iya kakkarya ki."

Ching Ching ta bushe da dariya...
"To ai gara na karye da na zauna ina ganin kina nuna wa Uncle ke ce komai. Kin san me ya faɗa min dazu? Ya ce har yanzu yana tausayi na..."

Gely ta sauƙo daga kan matakalar a hankali har ta iso saitin fuskar Ching Ching...

"Boss yana tausayinki ne saboda ke marainiya ce mai bukatar kulawa, ba don yana sonki a matsayin mace ba. Kuma idan har kika sake taɓa shi a ofis kamar yadda kika yi ɗazu, zan sanya na'urorin tsaro su daka miki wutar lantarki wato electric shock da sunan kuskure..."

Ching Ching ta zaro ido...

"Kin ga! Kishi kike yi! Uncle ya hana ki kishi amma har yanzu kina nan kina yi."

Daidai nan, Chief Onyx ya leƙo falon don ganin yadda aikin yake tafiya...
Ching Ching tana ganinsa, sai ta saki labulen hannunta ta ruga wurinsa, ta faɗa jikinsa tana kuka..

"Uncle! Uncle! Kaga Gely ko? Wai cewa ta yi idan na sake taɓa ka zata sanya wutar lantarki ta kashe ni! Ka ji irin muguntar da take kulla min a ƙarƙashin ƙasa ko?"

Onyx ya kalli Gely, sannan ya kalli Ching Ching. Ya rasa wanda zai yarda da shi a cikinsu, domin kowacce tana da tata makarkashiyar...

Ching Ching ta daskare a wurin lokacin da Chief Onyx ya ture ta daga jikinsa. Kalaman sa na sake jaddada mata cewa ita 'Yar Aiki ce ke sun sanya ta jin wani irin ɗaci a makogwaronta...

Ta kalli Gely, ta tarar Gely tana kallonta da wani irin sanyayyen kallo na nasara, kodayake Gely ba ta yi magana ba...

Bayan Chief ya wuce, Ching Ching ta juya tana turo baki, tana gatsine da harara kamar za ta cinye Gely...
Ta koma ta ɗauki labulen ta jefa shi a ƙasa kusa da ƙafar Gely...

"Gashi nan! Kowa ma a gidan nan bashi da mutunci,". ta faɗa cikin rarraba murya...

Gely ta sunkuya a hankali ta ɗauki labulen ta goge shi...

"Ɓacin ranki ba zai sauya gaskiya ba, Shugaba Ching Ching. Boss baya son damuwa, kuma ke kin zama damuwa a gare shi. Ki bari mu kammala wannan aikin idan ba kya son ya ƙara fushi da ke."

Ching Ching ta tsaya tana kallon yadda Gely take motsa jikinta cikin tsari...

"Ke Gely, wai tunda kike kishin nan, me ya sa kike ikirarin ke inji ce? Kin sani sarai kina son Chief, kuma kina jin haushin yadda yake magana da ni."

Gely ta koma kan matakalar, ta fara saka labulen a jikin na'urar saman ɗakin...

"Lissafi na ya gaya min cewa Boss mutum ne mai daraja. Kishi ko soyayya duk wasu sakonni ne na biochemical da ke cikin dan adam. Ni kuwa, tsarin nawa electronic ne. Amma hakan baya nufin zan bari wata yarinya ta lalata tsarin zaman lafiyarsa..."

Ching Ching ta kalli ƙafar matakalar, wani mugun tunani ya faɗo mata..
Ta matsa kusa da matakalar, ta fara jijjiga ta a hankali tana nuna kamar tana gyara labule ne a ƙasa...

"Haba Gely, kema ai kina son ki zama mutum ko? Na gani a fina-finai, duk robot irinki yana son ya zama mutum don ya mallaki zuciyar masoyinsa..."

Gely ta ji matakalar tana rawa, ta duba ƙasa ta ga Ching Ching tana ta jinjiga ƙafar matakalar...

"Ching Ching, ki dakata da wanna shashanci... Wannan aikin yana da haɗari."

"Ba zan dakata ba!" Ching Ching ta faɗa tana ƙara jijjiga matakalar...

"Sai kin faɗa min yadda kike ji idan Chief ya sumbace ni...!"

Daidai nan, hannun Gely ya sarƙe a cikin wayoyin wutar lantarki na labulen, wani ɗan tartsatsin wuta ya fito. Matakalar ta ƙara girgiza, Gely ta rasa daidaitonta, ta fara zamowa ƙasa...

Ching Ching ta firgita ta ja baya tare da faɗin,

"Ayyah! Gely za ta faɗo!"

Amma maimakon Gely ta faɗo a ƙasa, sai ta yi amfani da saurin na'ura ta damƙo jikin bangon, sannan ta diro ƙasa daidai gaban Ching Ching. Sautin ƙarfen jikinta ya yi ƙara Gwam! a kan tiles ɗin falon...

Gely ta matso da fuskarta dab da ta Ching Ching, idanunta sun yi wani irin haske mai ban tsoro...

"Kin yi kuskure mai girma. Yin wasa da rayuwar na'ura a lokacin aiki, babban keta doka ne. Kuma yanzu, zan tabbatar Boss ya ga wannan danyen aikin naki."

Ching Ching ta fara ja baya, tana girgiza kai

"Ƙarya kike... ni... ni gyara miki matakalar nake yi..."

Gely ba ta tsaya sauraron duk maganganun kare kai na Ching Ching ba...
Ta juya da sauri, takun ƙafafunta na ƙarfe suna bada sauti mai ƙarfi a kan tiles ɗin falon, ta nufi ofishin Chief Onyx...

Ching Ching ta biyo bayanta da gudu, tana kuka tana murza idanu...

"Gely! Gely! Wallahi wasa nake yi! Kada ki gaya masa, Ke gwangwani!"

Amma Gely ta riga ta isa ƙofar ofishin, ta danna maɓallin buɗewa sa’ilin da Chief Onyx yake ƙoƙarin duba wasu taswirori. Ya ɗago kai yana kallonsu cikin mamaki da gajiya...

"Wai meye hakan kuma?"

Gely ta tsaya daram a gaban teburinsa...

"Bods, ina son na gabatar maka da rahoton Safety Violation wanda ya faru a lokacin aikinmu na falon baƙi."

Onyx ya ja numfashi, ya kalli Ching Ching wadda ta tsaya a jikin ƙofa tana kuka tana girgiza kai...

"Ina saurarenki Gely."

Gely ba ta yi magana da baki ba, sai kawai ta ɗaga hannunta na hagu, wani haske ya fito daga cikin hannun nata Hologram Projector, nan take wani babban allo na bidiyo ya bayyana a iska a gaban Chief...

A cikin bidiyon, an ga komai fili, yadda Gely take kan matakala, da kuma yadda Ching Ching ta matsa ta fara jijjiga kafar matakalar da duk ƙarfinta, har sai da Gely ta kusa faɗowa sa'ilin da wutar lantarki ta fara tartsatsi...

Chief ya kalli bidiyon har ya ƙare. Fuskar sa ta sauya daga gajiya zuwa wani irin fushi mai sanyi wanda ya fi kowane zafi...
Ya kalli Ching Ching, wadda yanzu jikinta ya fara rawa domin ta san kyamarorin jikin Gely ba sa ƙarya...

"Ching Ching," Onyx ya kira sunanta cikin muryar dake nuna tsananin takaici...

"Kin san cewa idan Gely ta faɗo daga wannan matsayin, ba ita kaɗai za ta ji rauni ba? Wayoyin wutar da suke wurin za su iya tada gobara a gidan nan, ko kuma su kashe ki ke kanki idan wutar ta taɓa ki..."

Ching Ching tana turo baki ta ce,

"Uncle... wallahi wasa nake son yi da ita ne... tana nuna min isa ne shi ya sa..."

"Wasa da rayuwa ba wasa ba ne!" Onyx ya daka mata tsawa. Ya kalli Gely, ya ga yadda wasu wayoyin hannunta suka ɗan ƙone saboda tartsatsin wutar...

Ya juya ya kalli Ching Ching ya ce..

"Tunda wasa kike so, to yau babu barci a gadon da kike kwanta wa. Za ki kwana a cikin ɗakin ajiye tarkace, kuma ba za ki ci abinci ba har sai kin goge dukkan fentin dake jikin bango... Kuma idan kika sake kuskure ɗaya, zan ƙira mahaifinki na sanar masa cewa, yayi haƙuri dake domin yanka ki zanyi..!"

"Aiyyooo Ni rago ce... Da za'a yanka ni..."
ta furta tana turo baki...

Ya ce, "ai da ke, gwara a kawo mun ragon, idan na ɗaure shi zan zauna cikin ƙoshin lafiya..."

Ching Ching ta fashe da kuka ta nufi ɗakin ajiye tarkace, tana jin haushin kanta da kuma tsananin ƙiyayyar Gely...

Gely kuwa ta tsaya tana kallon hanyar da ta bi, sannan ta juyo ta kalli Chief...

"Boss, zan je na gyara na'urorin jikina da suka lalace,"

Onyx ya jinjina kai, ya dafe kansa yana tunanin cewa zamansa da Ching Ching ya fara zarce yadda yake tsammani....

✨✨✨

_Alhamra City_

Bayan kwanaki na fargaba da tunani, Ayat ta tsinci kanta da rashin natsuwa...

Ta kasa jure rashin jin motsin King Diamond, kodayake tana da Reems na gaske a kusa da ita...

Ta sanya kayanta na jami’i, ta fice zuwa bakin kogi wurin da ta saba hutawa...
Tana isa, ta dafe sarƙar dake wuyanta, ta lumshe ido tare da ambatar sunan

"King..." a ranta..

Kafin ta buɗe idonta, ƙamshin jikinsa ya gauraye iskar kogin. King Diamond ya bayyana, tsaye cikin kwarjini...

Ayat ta yi maza ta miƙe, ta nuna ɓacin rai...

"Me ya sa ka zo? Na gaya maka ka fita daga rayuwata!" ta faɗa tana huci...

Diamond bai tanka ba, sai murmushin gefen baki da ya yi, ya zauna a kan wani babban dutse tare da yi mata nuni da ta zauna a kusa da shi. Cikin turo baki, ta zauna tana harararsa..

Bayan sun kwashe mintuna cikin shiru, Diamond ya kalli ruwan kogin, sannan ya dubi Ayat...

"A zaman da na yi a cikin masarautarku, na ga abubuwa da dama... Masarautar Alhamra ba ta cancanci sunanta ba. Masarauta ce dake numfashi akan jinin talakawa."

Ayat ta zabura ta miƙe, tana nuna shi da yatsa, muryarta na ainahi yana fito...

"Kana so ka raina mana masarauta ne? Ka kiyaye kalaman ka!"..

"Na riga na raina ta, Ayat," Diamond ya dakatar da ita da wani irin kallo...

"Domin masarautar ku ba ta da tsarin adalci. Na zagaya can kurkukun ku na ɓoye, na ga tsofaffi waɗanda suka isa haifan mahaifinki, na ga mata da ƙananan yara a kulle cikin duhu. Ba abinci, ba ruwa, sai duka da azaba...
Abin da ban sani ba shi ne…
me suka aikata?”

Ya yi shiru na ɗan lokaci, sannan ya ce a hankali...

Yawancinsu laifinsu ɗaya ne, shine talauci...
Sun kasa biyan harajin da gimbiyoyi suke amfani da shi wajen siyan mayukan ƙamshi daga ƙasashen waje."...

Kalaman Diamond ne suka fara ratsa zuciyarta kamar kibiyoyi...

Ya ci gaba da bayyana mata yadda jami'an fada suke wulakanta mutane a kasuwa, da yadda yara suke mutuwa saboda rashin magani yayin da gimbiyoyi suke gasar girman kai..

Kalmar ta tsaga zuciyar Ayat da take mazannin Inuwa a yanzu...
Hawayenta suka fara gangarowa.
Fuskarta ta jiƙe sharkaf, har gashin gemunta ya fara tujewa...

Diamond bai tsaya nan ba...

“Masarautar ku tana rayuwa ne da sunan sarki,
amma babu adalcinsa...
Gimbiyoyi na cikin fada
amma talakawa na cikin ƙabari suna raye.”...

Ayat ta rufe fuska da tafin hannunta..

“Ka yi shiru…” ta faɗa cikin raunannen murya...

Ya miƙe tsaye, ya matso kusa da ita, ya ce cikin tsanani..

“A’a.
Yau ba zan yi shiru ba.”

Ya matso kusa da ita, ya kalli cikin idanunta da suka yi jawur...

"Ayat ko in ce Inuwa...Shin me ya sa kike sanya wannan shigar maza kina fita? Shin don ki kare talakawa ne ko don ki taimaka musu? Ko kuma don ki gamsar da son zuciyarki na son yawo ne kawai?"

Ayat ta kasa ba shi amsa, sai kuka dake ƙara ƙarfi...

Sai ya ƙara faɗi da kalma mai ɗaci..

“Gaskiya ɗaya zan faɗa miki, Ayat…
kaf gimbiyoyin wannan masarauta, babu wanda ke da amfani...Hatta ke, domin burinki shine ki yi ɓadda kama ki fita yawo da wasa.... Idan har ba za ki iya amfani da wannan damar wajen ceton waɗanda suke ƙasa da ke ba, to wannan shigar taki ta jami'i babban kuskure ne."...

Kalmar ta sauƙa kamar hukunci..
Ayat ta buɗe baki…
amma ta kasa furta komai...

Idanunta sun yi jawur, hawaye na zuba ba tare da izini ba...
Jikinta na rawa kamar ganyen da iska ke kaɗa wa...

“Ya isa!” ta fashe da kuka, muryarta na karyewa..

“Ya isa haka, ka daina zarginmu kamar bamu san me muke ba...!”

Ta ƙara matsowa dab da shi kamar zasu haɗe, ta ce,

“Kana tunanin ban sani ba?
Kana tunanin ban gani ba?
Kowace rana ina ganin wahalar su!”...

Ta buga ƙirjinta da tafin hannu..

“Nan! A nan nake ji!”

Hawayenta suna gangaro wa cikin tsananin firgici...

“Amma ka san menene?” ta ce cikin kuka..

“Ni mace ce! Gimbiya ce!
An haife ni cikin sarƙoƙi na zinare..
amma sarƙoƙi ne!”

Ta juya baya kaɗan, ta share hawaye da hannun rigarta..

“Ba a bar ni in fita ba.
Ba a bar ni in yi magana ba.....Duk abin da zan yi, sai ace sunana zai lalace!
Masarauta! Martaba! Izzah!
Waɗannan kalmomi sun kashe ni tun ina yarinya!”

Ta kalle shi cikin razanannun idanuwanta..

“Shi ya sa nake shigar maza!
Ba don nayi wasa ba,
Ba don a raina ni ba, sai don na samu numfashi...
Don na iya gani da ido na sannan na ji da kunnena..**”

Ta durƙusa ƙasa ba tare da shiri ba..
Kukanta ya ƙara tsananta..

“Kana ganin ina gudu ne?
A’a! Ina neman hanya ne..
Ina neman inda zan fara!**”
Diamond ya tsaya shiru, fuskar sa a ɗaure...
Sai ya ce cikin kaifaffen murya..

“Kuka ba ya gyara masarauta, Ayat...”

Ta ɗago kai a firgice.
“Ka daina faɗin haka, kana ƙona mun rai ne!” ta sake fashewa da kuka..

“Ka daina raina min ciwo na!..
Kai ka zo ka gani ka tafi ne!
Ni kuma zan zauna da sakamakon hakan...”

Ta miƙe tsaye ta matso kusa da shi, har suka kusan shafar juna...

“Ka yi min hukunci cikin zafi..
Amma ka san me?
Inda abun na da sauƙi to
da ni ce ta fara gyara komai!”

Diamond ya ɗan yi murmushi cikin tsauri...

“Shi ya sa kike da rauni,” ya ce...

“Kin fi kowa ganin gaskiya,
amma kin fi kowa tsoron ɗaukar nauyi.”

Kalmar ta ƙara doke zuciyarta..

“Tsoro?” ta ce da ƙarfi.
“Ka san meye asalin tsoro na? Uhmm to na fi tsoron zama kamar su!
Na fi tsoron zama gimbiya marar amfani!..”

Cikin ɗaga murya ya furta.

“To ki daina kuka!
Ki daina ɓoye kanki!
Ki tsaya a gaban masarautarki da sunanki na gaskiya!
Idan kina son kare talakawa
ki fara da gaskiya!”

Ta kalle shi cike da fushi da kuka...

“Kai ba ka da ikon gaya min yadda zan ceci masarauta ta...
Ba ka san abinda zan rasa ba idan na tsaya tsaye!”

Ya matso kusa da fusakarta har sai da ta lumshe rinannun idanuwanta sannan ya furta mata a hankali..

“Na sani.
Kuma shi ya sa na zo.
Domin zaki rasa komai
kafin ki ceci komai.”

Bayan shiru ya ratsa, iskar kogin na kaɗawa, Ayat ta buɗe idonta waɗanda suka ɗan natsu kaɗan duk da hawayen dake cikinsu...

Ta kalli Diamond, ta ga wani abu a cikin idonsa wanda ba ta taɓa gani ba..

Ya nuna mata cewa ba wai ya zo ne domin ya dasa mata ciwo a ranta ba ne, ya zo ne ya nuna mata cewa ita kaɗai ce maganin ciwon masarautar...

​"Diamond," ta furta cikin siririyar murya...

"Zan rasa komai... amma zan tabbatar na ceci waɗanda suke bukatar ceto."

​Diamond ya jinjina kai, sannan ya fara ɓace wa a hankali cikin hazo...

"Zan kasance inuwar dake biye da Inuwa... har sai ranar da Ayat za ta tsaya da kafafunta."....

Muryar ta bi iska lokaci guda ya ɓace..
Ya barta da ciwon zuci mai tsanani domin ta tsani ta ji ko ta ga wasu suna cikin wani mummunan hali, hakan yasa duk sanda ta fita sai ta tallafa wa marasa shi kuɗin aljihunta saboda su rage raɗaɗi....


*Likes ɗinku shine albashin marubuci*

👍 Like
🔁 Share
💬 Comment


*👑 MASARAUTAR ALHAMRA 👑*

_🪄 Gidan Mulki, Iko da Sirrin Zuciya 🪄_

✍🏽 By ASMEETAH WRITER
~Hasken Jajirtattu~


💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️

```JARUMAI WRITERS TEAM```

▶️ DON BIYO DAGA FARKO 👇
🔗 WhatsApp Channel:
https://whatsapp.com/channel/0029VbBCNlqJUM2RQwWncg43

📚 ArewaPen:
https://arewapen.com/u/asmeetahwriter

📖 Wattpad:
https://www.wattpad.com/user/asmeetahwriter

📲 Contact:
09065443871

📅 FARA TURA BOOK:
🔥 01 — 01 — 2026 🔥

📘 BOOK ONE
```MATAKIN FARKO```
Chapter 29 · 0% Book details