← Book details Masarautar Alhamra Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 10 OF 42

CHAPTER 8️⃣

Masarautar Alhamra Part 1 Complete Hausa Novel · about 17 min read

*بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيمِ*


Bayan Inuwa ya sauƙe Chingching a part ɗinta, ya fara takawa cikin sanyin jiki yana shirin komawa tasa muhallin. Zuciyarsa tana cike da farincikin hirar da suka yi da kanwarsa..

​Kwatsam yana shirin shiga wata kusurwa sai ya ji an rufe masa fuska da wani baƙin mayafi mai kauri. Kafin ya yi yunkurin kwata, wasu jami’an tsaro guda biyu masu ƙarfi suka cafko shi, suka fara jansa da karfi. Ba su ba shi damar yin magana ba, suka jefa shi cikin wata mota dake fake a gefe, suka tada motar da gudu suka nufi part ɗin Gimbiya Maayah....

​Motar ta tsaya a harabar katafaren sashen Maayah. Jami’an suka fito da Inuwa, yana ta faman kokawa yana son ya ɓalle ya gudu, amma riƙon da suka yi masa na maza ne. Saboda yadda suka ji ba shi da nauyi sosai, ɗaya daga cikinsu sai kawai ya yi masa ɗaukan kafaɗa, ya saɓo shi tamkar buhun shinkafa, suka nufi cikin falon gimbiyar.
​Suna shiga suka dire shi a tsakiyar katafaren falon dake shimfide da kafet mai tsada...

​Maayah tana zaune a kan wata Plate Sofa kamar katifa a ƙasi tana sanye da riga ta alfarma wadda ta bayyana kyan fatarta. A gabanta akwai wani katafaren tray cike da yankakken kayan fruits masu sanyi, tana ci a nutse tamkar ba ta san abin da ke gefen ta ba..

​Ba tare da ta kalli inda suke ba, ta daga dogayen yatsunta ta yi musu nuni da su fita. Nan take jami’an da sauran ma’aikatan mata dake falon suka fice cikin hanzari, suka bar Inuwa tsaye a tsakiyar falon cikin ruɗani.

​Daga nan ne aka cire wa Inuwa baƙin mayafi dake fuskarsa. Da farko ya rintse ido saboda hasken fitilun dake walwali a falon, yana buɗe su sai ya yi ido hudu da Maayah. Mamaki da fargaba suka mamaye shi.
​Maayah ta ajiye ƙaramin wuƙar dake hannunta, ta ƙura wa Inuwa idanu. Wani irin kallo take yi masa, kallo mai cike da nuna isa da kuma wani ɓoyayyen saƙo dake nuna sha'awa da burgewa.... Idanun Maayah sun yi wani irin sheƙi, gata kyakkyawa ajin farko..

​Inuwa ya ji jikinsa ya fara sanyi. A matsayinsa na mace, ta san ma'anar wannan kallon. Ta san cewa inda asalin namiji ne babu abin da zai hana sha'awarsa ta tashi a wannan lokacin saboda yadda Maayah ta baje kyan surarta a gabansa cikin kissa da kisisina...

​"Inuwa..." Maayah ta kira sunansa cikin wata irin murya mai sanyi da take ratsa jijiya. "Ka ga yadda ka yi nasarar sa ni tunani tun daga ranar da idona ya fara ganinka? Meye sirrinka? Me kake boyewa a karkashin wannan rawanin naka?"

​Inuwa ya sunkuyar da kai kasa, yana tunanin yadda zai fita daga wannan tarkon na Gimbiya Maayah ba tare da asirinsa ya tonu ba.

Maayah ta tashi daga kan katifar ta a hankali, tana taku ɗaya-ɗaya tamkar kyanwar da ta ga ɓera...
Rigar jikinta tana jan ƙasa, ƙamshin turarenta na Oud mai tsada ya mamaye hancin Inuwa. Ta zo daidai gabansa, ta tsaya tana kallon kwayar idonsa, kafin ta fara zagaye shi kamar yadda zaki yake zagaye abincinsa...

Ta sanya hannunta ɗaya ta fara shafa kafaɗarsa tana gangarawa zuwa hannunsa. Muryarta na fita ƙasa-ƙasa, tana raɗa masa a kunne..

"Inuwa... na yi bincike a kan duk sojojin masarautar nan, amma ban ga kamaninka ba. Ba ka da ƙasusuwa irin na maza sojoji. Ka yi fita daga daban, kuma hakan ne ya sa zuciyata ta kasa nutsuwa."

Ita kuwa duk wannan shashshafa da kalaman Maayah ba su motsa mata komai ba face takaici da haushin yadda ƴar uwarta take nuna rashin kamun kai. Ta ɗaure fuskarta cikin yanayi na gatsine, tana jujjuyar da manyan idanunta tana kallon silin ɗin ɗakin. A ranta tana cewa,
"Wannan mahaukaciyar me take nufi ne? Shin ba ta da sauran abin yi ne sai bibiyar sojoji?"

Maayah ta kai hannunta tana son ta shafi gefen fuskarsa, Inuwa ya kauce da sauri yana harararta..

Maayah ba ta fasa ba, ta sake zagayawa ta bayansa, ta tura kanta a tsakanin kafaɗunsa, ta rungumo shi ta baya tana ƙoƙarin jin bugun zuciyarsa...

"Me kake gudu Inuwa? Izza kake nuna min ko kuwa tsoron matsayina kake ji? Idan ka karɓi soyayyata, zan mayar da kai babban kwamandan da kowa zai rurrusuna masa a ƙasar nan," tana goga fuskarta a bayan rigarsa.

Inuwa ya ja wani uban tsaki a cikin ransa, wanda ya kusa fitowa fili. Ya fara jin ƙyamar yadda Maayah take ƙanƙame shi. Ya yi amfani da dabarar maza sojoji, ya juyo da ƙarfi ya raba jikinsa da nata, ya matsa baya taku biyu yana huci..
Cikin muryarsa ta maza wadda ya riga ya koyi kwaikwayonta, ya ce..

"Gimbiya Maayah! Na zo nan ne don hidimar tsaro, ba don wasan kwaikwayo na soyayya ba. Ni talaka ne, ke kuma gimbiya ce. Bai kamata ki ɓata mutuncinki a kaina ba. Kuma idan har kika sake sanya a kamo ni ta wannan hanyar, zan kai ƙararki gaban mai Martaba Sarki, duk abin da zai faru ya faru!"

Maayah ta daskare a wurin, ta zaro ido tana kallon Inuwa. Ba ta taɓa tunanin akwai wani namiji a duniya da zai ƙi wannan tayin nata ba. Maimakon ta ji tsoron barazanar sarki, sai kawai ta ji Inuwa ya ƙara mata kyau da kwarjini a idonta. Ta ciza laɓe, tana murmushin mugunta...

"To ka je ka faɗa wa Sarkin! Amma ka sani, duk inda ka shiga a masarautar nan, idona yana kanka. Ba za ka taɓa tsira daga tarkona ba har sai na mallaki abin da nake so a tare da kai."

Inuwa bai sake tankawa ba, ya juya cikin fushi ya nufi ƙofa, ya buɗe ta da ƙarfi ya fice, ya bar Maayah a tsaye tana kallon inuwarsa tana shafa wurin da ya taɓa, tana jin wani irin shauƙi daban.

Ya fara takawa cikin sauri yana ficewa daga sashenta, yana muzurai shi kaɗai ƙasa-ƙasa...

"Banza! Mahaukaciya! Jaka kawai!"
ya furta tare da jan wani dogon tsaki. "Wato ita a tunaninta kowa ma namiji ne ko? Ta rasa wanda za ta bi sai ni? Yarinya ba ta da sauran aiki sai lalata da ma'aikata? Allah ya kyauta!"

Haka ya riƙa surutai yana gunguni har ya ɓace a cikin duhun dake tsakanin gine-ginen masarautar, ya nufi tasa part don ya cire wannan kayan sojan da yake ji sun yi masa nauyi saboda haushi.

A can cikin falo kuwa, Mama Liyatu tana laɓe a bayan labule tun ɗazu tana kallon duk abin da yake faruwa. Bayan Inuwa ya fice ta fito a hankali tana takawa zuwa inda Maayah take a tsaye, tana kallon ƙofa tamkar gunki...
Mama Liyatu ta ga yadda Maayah ta zama wata iri, fuskarta na sheƙi, kuma tana shafa hannunta da Inuwa ya taɓa..

"Gimbiyata," Mama Liyatu ta kira sunanta cikin muryar tsoro. "Wannan yaron da kike bi... shin kin tabbata namiji ne na ƙwarai? Na ga kyan fuskarsa ya wuce na namiji, sannan yadda kika rungume shi ɗazu bai nuna wani yanayi na namiji ba. Meye sirrin dake tattare da shi?"

Maayah ta juyo ta kalli Mama Liyatu, wani murmushin mugunta na nan a kwance a fuskarta. Ta koma ta zauna a kan kujera, ta ɗauki koren apple ta gutsura..

"Mama Liyatu, shi ya sa nake son sa. Domin ya banbanta da kowa. Sannan ya nuna mjn ba ya buƙatar soyayyata. Wannan shi ne babban kalubalen da nake so. Amma ki sani, koda mace ne shi a siffar namiji, sai na mallaki zuciyarsa, balle kuma ina da yakinin cewa jarumi ne mai jinin sarauta a jikinsa."..

Mama Liyatu ta girgiza kai, "Amma Gimbiya, idan Sarki ya ji labarin nan fa? Kin san yadda yake kishinku."

Maayah ta yi wata 'yar dariya mai sauti. "Sarki yana can yana fafutukar yadda zai kare masarautarsa daga barazanar Pavilion, ba shi da lokacin binciken wanda nake so. Ke dai kawai ki sa ido a kansa, duk inda ya sanya ƙafa ki sanar da ni."

✨✨✨

A ɗayan ɓangaren kuwa, Ayat ta isa sashenta. Ta banka ƙofa ta shiga, ta cire rawanin kanta ta wurgar a kan gado. Ta kalli kanta a madubi, gashin kanta ya bazu a kafaɗarta, idanunta sun cika da ƙwallar takaici...

"Wace irin rayuwa nake ciki?" ta tambayi kanta...

"Ina tsaka-tsakiyar yaƙi da kaina.."

Ta shige banɗaki don yin wanka..

Bayan ta kammala wanka ta cire duk wata siffa ta Inuwa, ta saka lallausan leshi mai kyan gaske wanda ya dace da jikinta. Ta sauko ƙasa zuwa babban falonta tana takawa a hankali, fuskarta a rufe..

Tana isa falon, sai ta tadda ma’aikatanta, karkashin jagorancin Saratu, suna tsaye jere tamkar wadanda suke jiran sako daga sama. Fuskar kowacce dauke da tambaya da kuma damuwa.

Saratu tana kallonta, sannan ta yi gyaran murya ta ce.

"Gimbiya, me ya sa yanzu kika koyi wannan halin ne? Tun safe ba kya fitowa sai dare, anya lafiya kuwa? Abun ya yi yawa ai..."

Ayat ta ji wani irin haushi ya taso mata, domin ranta ya riga ya ɓaci da rigimar Maayah. Ta tsaya cak, ta kalli Saratu da idanuwanta wadanda suka nuna bacin rai a fili...

"Kuna so ne na fito na taya ku aiki?"
ta tambaya cikin kakkausan harshe.

Saratu maimakon ta yi shiru, sai ta kara matsowa,

"A'a, amma dai ki fito kowa ya ganki, a ga lafiyarki. Idan kina kulle kanki kullum, me kike so mutane su ce?"

Ayat ta ji tamkar ana huda mata zuciya da mashi. Ta girgiza kai cikin takaici ta ce..

"Hakan ya zamo wajibi ne? Ba na so ku riƙa shishshige wa rayuwata! Kowa ya yi aikin dake gabansa, ku yi rayuwarku na yi tawa. Ban hana ku yin farin ciki ba, ban rage ku da komai ba, to me ya sa kuke son takura ni?"

Saratu ta ɗaure fuska, "Ai dole mu shiga lamuranki Gimbiya, domin amanarki aka ba mu, kuma ya zama wajibi mu kula da ke yadda ya kamata."..

Kallonsu ta shiga yi, sai kuma ta tuna yadda ma'aikatan Maayah suke rawar jiki idan suka ganta, ba su isa su hada ido da ita ba balle su yi mata magana barkatai. Amma nata ma’aikatan, saboda sun san ta da saukin kai da tausayi, sun mayar da ita tamkar tsararsu...
Ta ji wani raɗaɗi a ranta, kowa a masarautar nan yana son ya tsara mata yadda za ta yi rayuwa..

Ta ɗaga musu hannu ɗaya alamar ta gaji da maganar su fita su ba ta wuri.
Duk suka fita suka bar ta a tsakiyar falon, tana jin tamkar ta fasa ihu don ta huta...

*Washegari*

A sashen Gimbiya Yumna, kowace safiya tana farawa ne da nishaɗi. Yumna tana zaune a gaban babban madubin ta na alfarma, yayin da bayinta suke ta faman gyara mata gashi da sanya mata lalle. Suna cikin wasa da dariya..

Ummi ɗaya daga cikin baiwa ta ce,

"Gimbiya, gaskiya yau fuskarki ta yi wani irin haske na daban. Anya ba mafarkin alheri kika yi ba kuwa?"

Yumna tana murmushi ta ce,
"Ke dai Ummi kullum maganarki kenan. Kawai hutu ne ya karɓe ni."

Zainab ta ce "Hutu dai ko kuwa tunanin Malam? Ai muna sane yau ne ranar karatunki...!"

Duk bayin suka sa dariya, Yumna kuwa ta ɗan ji kunya, ta duƙar da kanta tana murmushin dake bayyana fararen haƙoranta.

Suna tsaka da wannan wasan ne, sai wata amintacciyar baiwarta, Safina, ta shigo ɗakin da sauri. Ta zagaya bayan Yumna, ta rungume ta ta baya sannan ta raɗa mata a kunne cikin muryar raɗa..

"Yau kin manta ne? Dream Lover ya zo... Yana can lambu yana jiran ki."

Yumna ta zaro ido, zuciyarta ta fara bugawa da ƙarfi. Wani irin farinciki ya rufe ta, ta kalli Safina ta ce

"Malam ya zo? Da gaske kike yi Safina?"

Safina ta ce
"Da gaske nake mana Gimbiya. Tun ɗazu yake can ya shimfiɗa dadduma yana duba littafansa."

Yumna ta miƙe da sauri, ta umarci bayin su gama shiryata cikin gaggawa. Allah ya jarrabe ta da tsananin son wannan Malamin nata, wanda yake koyar da ita karatun boko da na Larabci a wani tsararren lambu dake gefen sashenta...

Malamin, wanda kyakkyawan Balarabe ne mai farar fata da dogon hanci, yana da sanyi da sauƙin kai. Sai dai babban abin tashin hankalin shi ne, shi kansa Malamin bai sani ba cewa Gimbiyar dake koyon karatu a hannunsa tana ƙaunar sa fiye da komai. A wurinsa ita Gimbiyarsa ce mai girma, a wurinta kuwa shi ne rayuwarta...

Yumna ta isa lambun, ta tadda Malam zaune a kan dadduma, ya sa fararen kaya ya naɗa rawanin Larabawa. Ta ƙaraso tana tafiya a hankali don kada ya fahimci yadda take jin nauyinsa..

"Assalamu Alaikum, Malam. Ina fatan ban daɗe ba?"

Ya ɗago ya kalle ta da idanunsa masu kwarjini, sannan ya yi murmushi mai sanyi
"Wa'alaikumussalam Gimbiya Yumna. A'a, yanzu ma na ƙaraso. Ki zauna mu fara da karatun Larabcin tukunna kafin mu koma na Turanci."

Yumna ta zauna a kusa da shi, ƙamshin turaren sa ya fara buge ta. Ta buɗe littafi amma idonta yana kan yatsunsa dake nuna mata haruffan...

"Gimbiya, wannan kalmar ana ƙiranta 'Al-Hubb'. Kin san ma'anarta kuwa?"

Yumna ta kalli Malam, fuskarta ta yi jawur, ta ce a ranta

"Kamar ka san abin dake cikin zuciyata..." Amma a fili sai ta ce "A'a Malam, meye ma'anarta?"

Cikin muryar natsuwa ya ce,
"Ma'anarta ita ce Soyayya. Ita ce jigon rayuwa."

Yumna ta sauƙe ajiyar zuciya, tana kallon kyakkyawar fuskar Malamin da take matuƙar so, yayin da asalin soyayyar take a ɓoye a tsakaninsu.

A cikin masarautar Alhamra, kowace Gimbiya tana da nata malamin da yake zuwa har sashenta don koyar da ita, domin kiyaye mutuncinsu da kwarjininsu...

Malam ya lura da yadda Yumna take ta murmushi tun farkon zaman, ya gyara zama sannan ya kalle ta cikin natsuwa ya ce..

"Sarkin murmushi, idan kin gama murmushin, sai ki sanar da ni a wace ayar kika tsaya a karatunmu na Kur'ani. Kin san mun yi nisa sosai."

Yumna ta ɗan sunkuyar da kanta, tana jin wata irin kunya mai daɗi. Ta buɗe babban littafin dake gabanta sannan ta ce..

"Malam, mun kusan kammala suratul Baƙara gaba ɗaya. Na kusa na yi sauƙar Alkur'ani mai girma."

Malam ya jinjina kai cikin gamsuwa da farinciki, ya ce..

"Haka ne Gimbiya. Kin mayar da hankali sosai a kan karatu, kuma hakan babban abin alfahari ne. Yanzu sauran mana shafi uku kacal mu kammala wannan surar. Yanzu za ki iya karanta min daga inda muka tsaya, sai na ƙara miki wani karatun ko?"

Yumna ta gyara zama, ta nutsu, sannan ta fara karatun cikin muryarta mai sanyi da zaƙi wadda take sa natsuwa a zuciyar duk wanda ya ji ta. Karatun nata ya fito ne daki-daki, ba tare da kuskuren tajwidi ko na haruffa ba...
Yayin da take karantawa, Malam ya zuba mata ido, yana sauraron yadda haruffan suke fita. Duk da cewa malami ne shi, a wannan lokacin ya ji wani irin kwarjini da natsuwa sun mamaye shi. Ya fara jin cewa wannan ɗalibar tasa tana da wani sirri na musamman dake sa karatun nata ratsa ko'ina.
Ita kuwa Yumna, tana cikin karanta kalmomin Allah, amma a gefen zuciyarta tana jin daɗin yadda Malam yake sauraronta cikin kulawa. Lambun ya yi shiru, sai sautin muryarta da kukan tsuntsaye dake rera waƙa a saman bishiyoyi....

✨✨✨

A sashen Chingching, baccin daɗi take sha, domin ita a rayuwarta ba abin da take so irin bacci...
Altine ta shigo ɗakin, ta daɗe tana jijjiga ta..

"Gimbiya, tashi Malam ya zo yana jiran ki!"

Chingching ta turo baki, ta koma ta nade a cikin bargo. Sai da aka sha fama da ita, kafin Altine ta samu ta sanya mata dan madaidaicin hijab dinta. Ganin yadda Chingching ta ki takawa da kafarta, dole Altine ta goyo ta a bayanta har zuwa lambun da Malam ke jira...


Malam dake ustaz ne mai kamala da uban gemu mai tsawo da sheki, ya gyara zama bayan an dire Chingching a dadduma. Ya kalle ta ya ce..

"Gimbiya, a ina muka tsaya da karatunmu?"

Chingching ta kalli fuskar Malam, ta yi fari da ido ta ce.
"Malam ai mun tsaya a wurin da Malam ya aske gemunsa!"

Malam ya ji tamkar ya nitse, ya kalle ta cikin mamakin shiriritar dake kanta..

"Kur’ani nake tambayarki Gimbiya, ba zancen gemuna ba. A ina muka tsaya?"

Ta yamutsa fuska, "Yoo Malam ni na manta, gaya min farkon sa."

Malam ya girgiza kai, "Ba kina Suratul Anbiya'i ba?"

Ta jujjuya idanu tamkar mai tunani, daga bisani ta ce,

"Ehh, haka ne ashe!"

"To karanta min daga inda kika tsaya," in ji Malam..

Chingching ta sake cewa,
"Me ma farkon ayar?"

Bayan Malam ya karanto mata farkon ayar, sai Chingching ta tashi ta daka wani tsalle na farinciki tana ihu, sannan ta dawo ta zauna. Abun mamaki tana farawa sai ta karanta karatun tsaf, babu gyara ko guda ɗaya duk da shiriritar dake kanta...

Malam ya yi murmushin jindadi, ya bude shafin littafin don ya kara mata karatu....
Yana fara karantawa, ita kuma Chingching ta ƙura wa gemunsa ido. Gemun yana ta motsi sama da ƙasa yayin da Malamin yake karatu, gashi yana ta sheki...

Chingching ta fara dariya ƙasa-ƙasa. Duk sanda Malam ya sunkuyar da kansa yana karatu, sai ta kai hannu tana shirin taɓa gemun. Da zarar Malam ya ɗago kai, sai ta janye hannunta da sauri tamkar ba ita ba. Haka ta yi ta yi, tana wasan ɓuya da gemunsa.
Ana karshe ne, tana ganin Malam ya nutsu a cikin karatun, sai ta kai hannu ta damƙe gemun gaba daya ta jawo shi da karfi!..

Malam ya saki wata irin kururuwa, jikinsa ya ɗauki rawa..

"Ke meye haka! Sake min gemu! Nace ki sakar min gemu kar ki cire min! Baki da hankali ne? Zaki cire min gemu! Innalillahi wa inna ilaihir raji'un... Kin kashe ni!"

Ta saki gemun, ta faɗa ƙasa tana kwashewa da dariya. Ta riƙe cikinta tana birgima a kan dadduma, har hawaye ya fara zubo mata tsabar dariya...

Malam ya zauna cikin kalar tausayi, yana shafa gemunsa dake masa zafi, yana kallon yadda wannan yarinyar take tamkar ba ta san zafin da ya ji ba. Ya sauke ajiyar zuciya mai nauyi, har zuciyarsa ya ji ya gaji da koyar da ita, domin kowace rana da nata sabon iskancin take zuwa...

Bayan Chingching ta gama dariyar ta gyara zama tana kallon Malamin cikin yanayin natsuwa na karya, ta ce,

"To Malam, mu ci gaba mana..."

Malam ya sauƙe ajiyar zuciya, amma saboda tsaro sai da ya sanya hannunsa na hagu ya danne gemunsa sosai, gudun kada ta sake damƙe shi. Ya fara karanta mata ayoyin Kur'ani cikin muryar raɗa, yana sa ido a kanta.

Chingching tana sauraron karatun kamar wata shiryayya, har Malam ya fara tunanin yau ta nutsu. Kwatsam! Sai idonta ya sauƙa a ƙasan hantsar wandonsa. Sakamakon yadda Malamin ya naɗe ƙafafunsa a kan dadduma, rigarsa ta ɗan janye, sai ga hantsar wandonsa ya yage ta ciki, inda wani abu ya ɗan fito ya yi ƙulƙule...

Chingching ta zaro ido, ta dafe baki tana faɗin,

"Ah ah ahh ahhh! Me zan gani haka?!"

Malam ya tsagaita da karatun, ya ɗago yana kallonta cikin shakku..

"Meye ya faru kuma Gimbiya?"

Ta duƙar da kanta tana maƙale dariya, "Ba... ba komai Malam, ci gaba kawai."

Malam ya ci gaba da karatu, amma ina! Chingching hankalinta ba ya kan karatun, tana ta leƙe-leƙen wannan wurin da ya yage. Dariyarta ta fara cin ƙarfinta, tana ƙoƙarin danne ta amma abin ya faskara. Lokaci guda ta fashe da wata mahaukaciyar dariya tana karkarwa..
Ta miƙe tsaye tana zagaye daddumar, tana ihu tana dariya har tana neman faɗuwa. Malam kam ya kusa fashewa da kuka tsabar takaici. Ya ce.

"Wai me yake faruwa ne? Idan ba kya son karatun, sai na tashi na tafi na bar miki fadar!"

Cikin dariya da gurguwar magana, Chingching ta dawo ta zauna, tana faɗin

"Yooo Malam, ina karatu zai yiwu ina hango ɗan tulu a tsakiyar wandonka... Kuma wandon ya yage!"

Malam ya firgita, ya yi maza ya gyara zamansa yana rufe wurin. Chingching ta ƙara kwashewa da dariya..

"Malam! Maganin meye ne sa tumatur a tsakiyar wandonka ta ciki? Na ga ya yi ƙulƙule kamar tumatur, kamar kuma dankali... Kai, dankali ne ma! Wallahi dankali ne!"

Malam ya ga cewa idan ya ƙara minti ɗaya a wurin, to mutuncinsa zai zube ƙasa warwas. Ba tare da ya ce uffan ba, ya kwashe littafinsa da sauri-sauri, ya miƙe ya fara sauri yana ficewa daga sashen...

Chingching tana biye da shi da dariya tana kwala masa kira

"Malam mai ɓerarren wando! Ga kuma ƙaton dankali a ciki! Malam ya ɓoye dankali a wando!"..

Ta zube a ƙasa tana dariya sosai, yayin da Altine dake gefe ta rasa ko za ta yi dariya ko za ta yi kuka saboda kunyar abin da Auta ta yi wa ustaz....


👍 Like
🔁 Share
💬 Comment


*👑 MASARAUTAR ALHAMRA 👑*

_🪄 Gidan Mulki, Iko da Sirrin Zuciya 🪄_

✍🏽 By ASMEETAH WRITER
~Hasken Jajirtattu~


💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️

```JARUMAI WRITERS TEAM```

⚠️ SANARWA⚠️

Wannan littafi dukiyata ce a matsayina na marubuciya.
⚖️ Ba a yarda wani ko wata ya:
kwafa
gyara
sauya
ko amfani da wani sashe na wannan labari
ba tare da izini na kai tsaye ba.
Duk wanda ya saɓa, alhaki yana kansa..

▶️ DON BIYO DAGA FARKO 👇
🔗 WhatsApp Channel:
https://whatsapp.com/channel/0029VbBCNlqJUM2RQwWncg43

📚 ArewaPen:
https://arewapen.com/u/asmeetahwriter

📖 Wattpad:
https://www.wattpad.com/user/asmeetahwriter

📲 Contact:
09065443871

📅 FARA TURA BOOK:
🔥 01 — 01 — 2026 🔥

📘 BOOK ONE
```MATAKIN FARKO```
Chapter 10 · 0% Book details