← Book details Masarautar Alhamra Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 30 OF 42

CHAPTER 2️⃣8️⃣

Masarautar Alhamra Part 1 Complete Hausa Novel · about 31 min read

*بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيمِ*


Bayan dawowarta daga bakin kogi, Ayat ba ta jira gari ya waye ba. Cikin shigar Inuwa, ta nufi ofishin Master Ibrahim dake cikin babban sashen tsaro na masarauta.. A lokacin, Master Ibrahim yana duba wasu taswirorin tsaro a ƙarƙashin hasken fitila, fuskarsa cike da gajiya..

​Jin motsin mutun, ya ɗago kai, hannunsa ya kai kan takobinsa.. "Wane ne?"

​"Ni ne Master, Inuwa ne," ta fada cikin natsuwa yayin da ta shigo cikin hasken fitilar...

​Master Ibrahim ya sassauta ransa, ya ajiye takobin..

"Inuwa? Me ya faru a wannan lokacin? Na zaci kana sashenka kana huts wa."

​Inuwa ya ƙarasa gaban teburin, ya tsaya dakyau, ƙafafunsa a buɗe, hannayensa a baya kamar soja na gaske..

"Master, na zo ne in roƙi alfarma guda ɗaya. Ina so a rantsar da ni a matsayin PA (Personal Assistant) ɗinka a hukumance. Ina so in yi rantsuwar aminci ga masarautar Alhamra a daren nan."

​Master Ibrahim ya nuna mamaki a fuskarsa..

"Rantsuwa? Amma ai na riga na ba ka muƙamin. Me ya sa kake sauri haka, kuma a cikin daren nan?"

​Inuwa ya gyara tsayuwa, idanunsa a dishe.
"Master, na fahimci cewa yin aiki ba tare da cikakken ikon rantsuwa ba, tamkar tafiya ce ba tare da makami ba. Ina so in hidimta wa wannan masarautar fiye da yadda nake yi a baya. Ina so in zama idonka, kunnenka, da kuma hannunka a duk inda zalunci yake."

​ Master Ibrahim ya ga wani abu a idon Inuwa, wani irin kishin ƙasa da gaskiya da bai taɓa gani a idon sauran jami'an fada ba..

​ Ya miƙe tsaye, ya gyara kakin sa. Ya jawo wani kofon azurfa dake ɗauke da ruwan da aka karanta wa dokokin masarauta, sannan ya zaro takobinsa mai kaifi, ya saita shi a gaban Inuwa..

​"Daga yau, Inuwa, ka zama fiye da jami'i a gare ni. Ka zama amintaccena."

​Inuwa ya ɗora hannunsa a kan takobin, muryarsa na fita ba tare da rawa ba, ya furta kalaman rantsuwa..

"Na rantse da dukkan martabar Alhamra, zan kare marar ƙarfi, zan yaƙi azzalumai, kuma zan zama mai gaskiya ga masarautar nan koda hakan zai yi sanadin raina."

​Bayan rantsuwar, Master Ibrahim ya ɗauki kati mai nauyi ya rubuta babban umarni (Official Decree). Ya sanya hatimin sa, sannan ya ce,

"Wannan katin zata ba ka ikon shiga kowane lungu, kowane kurkuku, da kowane ofis a cikin Alhamra. Duk wanda ya raina ka, ya raina ni. Kuma gobe, zan tura saƙo ga Sarki domin ya sa hannu akan wannan muƙamin naka a hukumance."

​Inuwa ya karɓi takardar, ya yi gaisuwa ta soja... A ransa yana cewa,

"Diamond, yanzu ne aka fara wasan. Zan nuna maka cewa mace tana iya zama takobi!"

Master ne ya katse shi da faɗin "ina buƙatar gobe da sassafe ka fito domin rantsar dakai a karo na biyu a gaban mutane...

Daga nan ta fice, kai tsaye sashenta ta wuce a sirrance dake duhu ya shiga amma haske ta ko ina...

_Washegari ✨_

Tun kafin rana ta fito sosai, aka buga gangar taro a babban dandalin jami'an tsaro na masarauta.. Daruruwan jami'ai, tun daga kan kwamandoji, sojojin fada, har zuwa kan masu tsaron kofanni, duka suka taru cikin shigar su ta alfarma. Kowa yana tambayar dan uwansa,
"Me ke faruwa? Shin akwai yaƙi ne ko kuma Sarki ne ya dawo?"

A tsakiyar dandalin, Inuwa yana tsaye kusa da Master Ibrahim. yana sanye da sabon kakin sa na PA wanda aka yi wa ado da wasu igiyoyin zinare a kafada, yana sanye da baƙin gilashi waɗanda suka boye kumburin idonsa na kukan daren jiya, fuskarsa a murtuke tamkar bashi ne a kansa..

Master Ibrahim ya taka zuwa gaba, ya zare takobinsa ya ɗaga shi sama don kowa ya yi shiru. Shiru ya gauraye filin..

"Jami'an Alhamra! Na tara ku ne a nan don wata muhimmiyar sanarwa,"

Master ya faɗa cikin muryarsa mai kwarjini..

"Kamar yadda kuka sani, tsaro da adalci sune ginshikin wannan masarauta. Don haka, na zaɓi jami'i Inuwa a matsayin PA (Personal Assistant) na na musamman."

Wani gunaguni ya tashi a cikin jami'an. Wasu jami'an da suka daɗe a aiki suka fara kallon-kallo cikin bacin rai da hassada..

Master Ibrahim ya ɗaga hannu ya tsayar da su..

"Wannan ba zaɓi ne na kashin kaina kadai ba. Sarki ya aiko da yardarsa ta hanyar hatimin sa na musamman. Daga yau, Inuwa shine idona. Duk inda kuka gan shi, tamkar ni ne. Yana da ikon shiga kowane ofis, kowane kurkuku, da kuma kowane sashe na wannan fada ba tare da izini ba. Duk wanda ya raina shi, ko ya ki bin umarninsa, zai fuskanci hukuncin cin amanar masarauta!"

Master ya miƙa wa Inuwa wani babban takobi na azurfa da aka rubuta sunan sa a jiki. Inuwa ya karba, ya yi gaisuwa ta alfarma, ya juya ya kalli dakarun. A lokacin, fuskarsa ba ta nuna tsoro ba, sai wani irin kwarjini da ya sanya manyan kwamandojin ma sunkuyar da kai...

Bayan taron ya watse, Inuwa bai jira komai ba. Ya gyara tsayuwar sa ya kalli wasu dakarun guda huɗu da ya zaɓa..

"Ku biyo ni yanzu. Akwai wasu bayanan sirri da zan bincika a sashin kurkuku na karkashin kasa."

Dakarun suka bi shi ba tare da gardama ba. Inuwa yana tafiya zuciyarsa tana tuno kalmomin King Diamond..

"Zaki rasa komai... kafin ki ceci komai." Ya san cewa daga yau, yakin ya fara...

Inuwa ya sauƙa zuwa kurkukun ƙasa, wanda dake cike da duhu da wari...
Ba a taɓa ganin Master ya zo wannan wurin ba sai yau da PA sa yazo... Inuwa yana tafiya, yana lura da fuskokin mutanen dake cikin sarƙoƙi. Ya ga tsofaffin da King Diamond ya faɗa masa, ya ga yara da mata..

"Wane ne wannan tsohon?"

Inuwa ya tambayi mai tsaron kurkukun..

"Ranka ya daɗe, wannan shi ne tsohon da ya gaza biyan harajin gonarsa na shekara biyu," mai tsaron ya ba shi amsa..

Inuwa bai ce uffan ba, ya biyo dukkan ɗakunan, yana rubuta sunayensu a cikin wani ƙaramin littafi. Bai ba da umarnin a sake su ba tukuna, domin ya san idan ya yi hakan yanzu, sauran manyan jami'ai za su iya tawaye. Amma kallon da ya yi wa mutanen, kallo ne na..
"Zan dawo gare ku."

✨✨

Bayan kwanaki biyu, sunan Inuwa ya zama kamar wutar daji a cikin masarautar Alhamra da ma bayan gari. Ana maganar wani matashin PA mai hazaƙa, mai kwarjini, wanda har wasu suke ganin idan ya ci gaba da haka, zai iya fin Master Ibrahim tasiri a fadar...

Wannan shahara ta kai kunnen kowace gimbiya, musamman Zayana dake jin cewa kowa ya zama bawan ta..

Inuwa yana ofishinsa, sai ga wani bawan Gimbiya Zayana ya shigo cikin girmamawa. Ya ajiye wani ƙayataccen katin gayya na zinare dake ƙamshin turaren Oud...

"Ranka ya daɗe, Gimbiya Zayana tana gayyatar ka zuwa sashenta a daren yau. Tana son tattaunawa akan wasu al'amura na tsaro," bawan ya faɗa ya fice..

Inuwa ya ɗauki katin, yayi murmushi. Ya sani cewa gimbiyoyin Alhamra ba a barin su fita, sashensu shi ne masarautar su. Idan aka ƙira jami'i sashen gimbiya, ko dai ana son a ba shi cin hanci ne, ko kuma ana son a ƙulla masa makirci ne..

Da daddare bayan Inuwa ya kammala komai, ya nufi sashen Gimbiya Zayana.. Sashen ya kasance daban da sauran, komai na cikinsa ya nuna almubazzaranci da dukiyar talakawa. Zayana tana zaune a kan wata doguwar kujera, sanye da riga ta alfarma wadda aka yi wa ado da lu'u-lu'u..

"Ka zo, Inuwa," ta faɗa cikin murya mai daɗi wadda take amfani da ita idan tana son cinma wata manufa...

"Na ji labarin yadda kake shirin zama zakaran masarauta. Har ana cewa kusan ka kusa fin Master Ibrahim iko."

Inuwa ya tsaya ba tare da ya sunkuyar da kai ba..

"Gimbiya, aiki na kawai nake yi. Kuma babu jami'in da ya kai Master Ibrahim."

Zayana ta miƙe tana zagaye shi, ƙamshin turaren ta ya mamaye wajen...

"Inuwa, ni mace ce mai son jarumai. Ina so ka zama nawa. Ka bar aiki ƙarƙashin Master Ibrahim, ka dawo sashena ka zama PA na kaina. Zan ba ka ninkin kuɗin da kake karɓa, sannan kowa a fada zai rinƙa jin tsoronka..."

Ta ɗora hannunta a kafaɗarsa, tana ƙoƙarin amfani da kyan fuskarta don rudar da shi. Inuwa ya ji zuciyarsa tana tashi. A ransa ya ce,

"Gimbiya Zayana, ashe har yanzu ba ki san ko ni waye ba."
Inuwa ya matsar da hannun nata cikin sanyi ba tare da nuna ƙarfi ba ..

"Gimbiya, ni ba na siyarwa ba ne. Kuma matsayina na PA na Master Ibrahim, har da kula da yadda gimbiyoyi suke mu’amala da kuɗaɗen masarauta yake. Don haka, kada ki ɓata katin gayyarki a kaina."

Zayana ta fusata, cat eyes ɗinta suka yi wuta...

"Ka nuna cewa ka raina ni? To ka sani, duk wanda ya ƙi zama abokina a fadan nan, to makiyina ne. Kuma makiyina ba ya daɗewa a raye."

Inuwa ya yi murmushin raini, ya gyara baƙin gilashin idonsa...

"Na ji tsoro, Gimbiya... Amma ki sani, makiyin naki yana da asirai da yawa a aljihunsa." Ya juya ya fice, ya bar ta tana huci...

Bayan ta bar sashen Zayana cikin fushi, Ayat ta lallaɓa ta koma sashenta na gimbiyoyi... Tana shiga, ta garkame kofarta dake saje da jikin bangon ɗakin, wanda ba wanda zai yi tunanin akwai ƙofa a wurin... Cikin sauri ta cire kakin PA na musamman dake jikinta, kayan da suke da nauyi amma yanzu ta saba da su har tana jin su tamkar fatar jikinta...

Bayan ta fito daga wanka, ta sanya riga ta gimbiyoyi mai laushi. Ta tsaya a gaban madubi, tana kallon kanta. Tana murmushi ganin yadda ta yi nasarar yaudarar duk masarautar..

"Inuwa..." ta ƙira sunan a hankali, "Yanzu ka zama babban jami'i, amma Ayat ce take juya akalar komai."

Babban fargabarta yanzu ita ce Saratu da sauran bayinta masu kawo mata abinci da gyara ɗaki... Tunda yanzu a matsayin Inuwa dole ta fita tun asubahi kuma ba za ta dawo ba sai dare, ta yanke shawarar yin wata dabara..

Zata sanar da manyan bayinta cewa tana fama da wani irin ciwon kai da baya son hayaniya ko haske... Don haka, zata bayar da umarnin cewa babu wanda zai zo wurin bedroom ɗinta sai idan ta kira...

Ta ce a riƙa ajiye mata abinci a babban falon sashenta, sannan su fita su rufe kofa. Wannan zai ba ta damar shigowa ta kofar sirri a matsayin Inuwa, ta ci abincin, ta sake fita...

Kuma zata sanar cewa daga yau ita zata na gyara bedroom ɗinta, da wankin bathroom da komai duk abinda ya shafi bedroom...

Kuma kamar yadda kowace masarauta take ware wa manyan jami'anta wurin zama na musamman (Officer’s Quarters), Master Ibrahim ya ware wa Inuwa wani sashe mai kyau da kima kusa da ofishin tsaro..

Sashen yana da faɗi, akwai ɗakin karɓar baƙi, ɗakin kwana mai ɗauke da gado na alfarma, da kuma wani ɗaki na sirri da Inuwa zai rika ajiye makamansa da takardun rahoton sa...

Wannan ma babban kalubale ne a rayuwarta..amma ta yanke cewa..

Wannan sashen zai zama Gidan ma ɓoya wato Safe House... Idan ta fita daga sashenta gimbiya da asubanci, sai ta nufi can ta ƙarisa wayewarta a matsayin Inuwa kafin ta fito filin aiki.. Wannan zai sa mutane su ga cewa Inuwa yana da nasa ɗakin, kuma baya bukatar zama a wani wuri daban...

Duk da tana jin daɗin nasararta, zuciyarta ba ta daina bugawa ba. Idan ma'aikatan gyaran sashen PA suka shiga dakin Inuwa suka iske turaren mata ko kuma wani abin da zai nuna mace ce take zama a wurin, to asiri zai tonu...

Dole ta zama mai tsafta da taka-tsantsan...

"Dole ne in riƙa raba rayuwata kashi biyu," Ayat ta faɗa wa kanta yayin da take shirin kwanciya..

"Idan na zama Inuwa, dole in daina kamshi irin na Ayat. Idan na zama Ayat, dole in daina tafiya irin ta Inuwa."...

Haka ta kusan kwana tana wannan tunanin...

✨✨✨

Maayah tin daga lokacin da wancan malamin ya bayyana ya kuma nuna ikonsa ya fi nata daga lokacin take cikin damuwa, ta ƙi cin abinci, ta daina yawan shiga Swimming Pool! Ta zauna a ɗakinta cike da shiri na faɗa!..

Mama Liyatu ta shigo cikin tsoro ganin yanayin Maayah ya sauya kwana biyun nan...

“Gimbiya, me ya same ki haka? Kullum a cikin fushi duk da daman ba'a gane farin cikin ki da baƙin cikin ki amma kin rage fitowa falo! Wane ne ya yi miki laifi a Makaranta? Ko dai a cikin masarautar nan ne?..”

Maayah ta kalli Mama Liyatu cikin harzuƙa..

“Wani sabon malami ne da suka kawo! Wai shi Uncle Jalal! Ya yi min wulaƙanci! Ya ƙira ni da jahila! Ya yi min tsawa! Ya keta min Ikon Sarauta!”
Ta ƙarisa tare da zubda hawaye..

Mama Liyatu ta tsorata sosai domin rabon da ta ga hawayen Maayah ta manta sai lokacin da tayi jinya..

Mama Liyatu ta rufe fuskarta da hannu!..

“Yaa ALLAH! Wannan kuskure ne! Maayah, ki bar shi! Malami ne! Ki yi haƙuri!”

Maayah ta miƙe..

“A’a! Mama Liyatu! Ba zan gafarta masa ba! Idan har ba a hukunta shi ba, to Sarauta ta ta zama na ƙarya! Na riga na kori Minista! Wane ne Malami da zai zo ya zaunar da Gimbiya! Ni ce Sarauniya!”...

Ta ƙarisa maganar tare da shirin shiga bathroom domin yin wanka,

"Bani da niyyar zuwa school amma sai na je, domin bazan shiga damuwa har na haka kaina zuwa saboda wani jakin malami..."

Mama Liyatu ta ce, "Amma Gimbiya, ai kin makara yanzu fa ƙarfe 9 ne..."

Maayah ta juyo tana kallonta ta ce, "Zan iya zuwa duk lokacin da naso, saboda haka ki je ki haɗa mun breakfast kafin na fito a wanka..."

Hakan kuwa akayi..

Tana zaune a gado, ta gama shiri!..

“Zan nuna masa! Zai san cewa Girman Kaina ya fi girman Iliminsa! Zan yi amfani da Ikon Kuɗi da kuma Siyasa don in rushe shi! Ko kuma in sa shi ya zama bawana!”

Ta kuma shiga wani tunani da bam game da shi...

“Amma kuma sai dai Jalal yana da kyau! Surar jikinsa tana da kyau! Da ace bai yi min raini ba, da na yi amfani da shi a matsayin Saurayin Wasa! Amma yanzu, zan wulaƙanta shi! Zan sa shi ya roƙe ni a gaban kowa! Sai ya gane cewa Gimbiya Maayah ba ta da iyaka!”

✨✨

Ranar ta fara ne da wani irin zafi, amma zafin ran Uncle Jalal ya ninka na ranar yawa. Yana tsaye a cikin ajin lissafi computer, idanunsa radau tamkar na zakanya. Ya riga ya shimfiɗa doka..

"Duk wanda ya makara, zai ɗanɗani zafin rana a waje..."

A waje, ɗalibai kusan goma ne suke tsaye duk da sun fi awa da zuwa, jikinsu har rawa yake yi saboda sanin waye Uncle Jalal, mutumin da ya kusan kashe ɗaliba a Maiduguri saboda raini...

Can sai ga jerin tsararrun motoci. Motar Maayah ta tsaya cif, sannan bodyguards suka buɗe mata ƙofa.. Ta fito cikin takun kasaita, sanye da rigar makaranta wadda aka yi wa ado da gwal...
Ta kalli ɗaliban dake waje cikin kallon banza, ta wuce su kamar ba mutane ba...

Ta zo shiga aji, sai wata murya mai nauyi da kwarjini ta dakatar da ita..
Ba tare da ya kalle ta ba

"Tsaya a nan. Dokar gidan ku ba ta aiki a cikin ajina."

Maayah ta tsaya cak. Ta cire gilashin idonta, ta kalle shi tun daga ƙasa har sama..

"Kai kake magana da ni haka? Ko baka san wacece ni ba? Ni ce Maayah, wadda kake cin abinci a ƙarƙashin inuwar masarautar mahaifinta."

Uncle Jalal ya juyo, ya tako zuwa bakin ajin idonsa cikin nata..

"Ni kuma suna na Jalaludden... Kuma a nan, ni ne sarki. Mahaifinki ne ya gina makarantar, amma ni ne nake gina tunanin ku...
Ki koma waje ki tsaya a rana kamar sauran, ko kuma ki koma gida."

Bodyguards ɗin Maayah su biyu suka matso, fuskarsu a murtuke..

Wani daga ciki ya furta
"Malam, kana wasa da rayuwarka ne? Wannan Gimbiya ce!"

Uncle Jalal ya yi murmushin raini..

"Ko aljani ne kuka turo, idan ya shigo ajina a makare ko ba da izini ba, sai na koya masa hankali... Idan kuma ku ka matso kusa da ni, zan nuna muku cewa ni ɗan Nigeria ne, ba a ban tsoro da uniform..."

Malamai ne suka taru suna ba Uncle Jalal haƙuri...

"Dan Allah Uncle Jalal, baka san wacece ita ba? Za a iya rufe mana makaranta!"..

Idonsa akanta ya furta..

"In dai tana so ta shiga aji na yau, to hukunci biyu ne, Ko ta tsaya a rana na awa guda, ko kuma ta sha bulala 10 a tafin hannunta!"

Maayah ta girgiza saboda ɓacin rai. Wannan ne karon farko da wani ya kalle ta ya faɗi wannan maganar..

Cikin rawar murya ta fushi ta furta
"Bulala? Ni za ka buga? Talaka kawai! Kai da baka da komai sai wannan tsohuwar rigar dake jikinka? In har ka kuskura ka taɓa tsokar jikina, to a yau zaka samu labarin na sheƙe kaina, kuma jini na zai zama silar rugujewar zuri'arka!"

Kowa a cikin malaman mamaki yayi jin ta ƙira shi da talaka, alhalin shima ɗan manya ne..

Uncle Jalal ya zuba mata ido, ya ga tana rawar murya kamar za ta fashe da kuka saboda tsoro da girman kai... Ya lura cewa tana shirin yin kuskure mafi girma. Daga ƙarshe, saboda roƙon sauran malamai, ya ƙyale ta ta shiga, amma da wani sharaɗi a ransa...

Uncle Jalal ya ci gaba da koyarwa. Maayah tana zaune a baya can, ta ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya, tana danna wayarta iPhone ta alfarma, tana hirar tsegumi da ƙawayenta, tana tura musu hotonsa tana yi masa ba'a...

Ba zato ba tsammani, taji an gizge wayar daga hannunta da ƙarfin tsiya..

Ta miƙe tsaye tana harararsa,
"Ba ni waya ta yanzu! Ka san nawa aka saye ta?"

Ta ce,
"Ban sani ba, kuma ba na buƙatar sani... Amma na sani cewa a cikin aji, hankali yana kan allo, ba kan waya ba. Wannan wayar tana hannuna har sai an tashi. Idan kika sake magana, zan fasa ta a nan ƙasa."

Maayah ta koma ta zauna, hawayen takaici suka cika idonta. Duk ajin ya yi shiru, kowa yana mamakin jarumtar Uncle Jalal...

Bayan an tashi, kowa ya fita. Maayah ta tsaya tana jiran wayarta. Uncle Jalal ya miƙa mata ita a hankali..

"Gimbiya, kiyi kuka idan kina so. Amma ki sani, daraja ba a sayen ta da kuɗi ko sarauta, ana samun ta ne ta hanyar ladabi. Gaba ki kiyaye ni."

Maayah ta fizge wayar, ta watsa masa wani kallo mai tafiya da mashi, sannan ta juya ta fice...


Ƙarfe biyu na rana, kowa ya watse a makarantar...
Uncle Jalal ya fito daga cikin ginin makarantar, riƙe da jakar laptop ɗinsa. Ya nufi inda ya faka babban mashinsa (Superbike) kalar baƙi da jan wuta, wanda kowa ya san darajarsa ta haura miliyoyin da nairori...
Ya ɗauko Helmet ɗinsa mai ƙyalli, ya saka, sannan ya tada injin mashin ɗin..
Sautin mashin ɗin kadai ya isa ya tsorata duk wani mai ƙananan motoci a wurin..

Bayan ya fita daga makarantar ya hau kan tsararren kwalta sai ga motocin Maayah guda uku sunyi parking a gefen kwalta suna jiran fitowarsa, ganin ya fito yasa suka bi bayansa.. Suna isa wani lungu da babu mutane sosai, sai motar farko ta yanke masa gaba, ta biyun kuma ta tare shi ta baya. Dake ba wani gudu yake akan mashin ba, kuma bai san ana biye da shi ba...
🔥
Jalal ya kashe injin mashin ɗinsa a hankali. Bai ko cire Helmet ɗin ba, ya sauka daga kai ya tsaya tamkar wani soja na musamman..

Maayah ta fito daga motarta, tana sanye da gilashinta akan dara-daran idanuwanta, fuskarta cike da izgilanci...

"Jalal, na gaya maka sarauta ta fi ƙarfin koyarwar ka. Yau za ka gane cewa ko daga ina ka fito, a nan Alhamra ni ce mai iko. Ku sauƙe mun kan ɗan banza...!"

Bodyguards guda huɗu suka tunkaro shi. Na farkon ya kai masa naushi, Jalal ya ɗaga hannu ɗaya ya tare naushin, sannan ya yi amfani da karfin Helmet dake rufe da fuskarda ya bugi hancin mutumin..
Kwas! Jini ya ɓalle..

Sauran biyun suka tunkaro shi da sandunan tasers..

Jalal ya yi tsallen kurege, ya buga wa ɗaya ƙafa a ƙirji, ya kuma damƙi hannun ɗayan ya murɗe shi har sai da ya ji ƙarar ƙashi. Cikin ƙasa da minti biyar, ƙataguban mazajen da ake ji da su a fadar Alhamra suna birgima a ƙasa cikin azaba..

Maayah ta ja da baya da gudu, tana rawar jiki. Ta nufi motarta da nufin ta arce, amma Jalal ya riga ta. Ya damƙi damtsenta, ya juyo da ita da ƙarfi...

Cikin muryar dake tashi daga cikin Helmet...

"Kin yi tunanin kowa tsoron ki yake yi? Kin saba da malaman da kike saya da kuɗi, to ni kuɗin mahaifina ma ba su gaban idona balle ke..."

Yana magana, ya finciko jakar hannunta mai tsada da nufin ya jefar da ita gefe don ya koya mata hankali...
Amma yayin da ya finciki jakar, sai ta buɗe, kayayyakin ciki suka watse a kan kwalta...

Dalolin kuɗaɗe ne da turaruka suka zubo, amma a tsakiyarsu, wasu kwalabe guda biyu da ledoji masu ɗauke da kwayoyi (Tramadol da sauran kwayoyin sa maye) suka zazzage...

Jalal ya saki hannunta, ya cire Helmet ɗinsa. Gumi na yanko masa, idanunsa suna kallon kwayoyin. Ya durƙusa ya ɗauki kwalbar, ya girgiza ta...

"Wannan ne sirrin Izzah taki? Kwayoyi kike sha don ki manta da rashin tarbiyyarki? Ashe Gimbiya Maayah ƴar maye ce?"

Maayah cikin tsoro da fargaba tayi saurin durƙusa wa ƙasa, duk wani taƙama da girman kai ya tafi. Ta sani sarai cewa idan labarin nan ya fita, ba ma makaranta ba, duk darajar gidansu ta zube...

Tana kuka cikin tsoro
"Uncle Jalal... don Allah. Ba yadda kake tunani ba ne. Ka ba ni kayana... zan biya ka duk abinda kake so!"

Jalal ya kalle ta cikin rainin wayo
"Kina tunanin ina buƙatar kuɗinki? Ki duba mashin ɗin da nake kai, ya ninka albashin dukkan malaman makarantar nan sau goma. Ban zo nan koyarwa don kuɗi ba, na zo ne don in gyara ɓatattun yara irinki."

Ya ɗauki kwayoyin ya zuba a aljihunsa, sannan ya kalli Maayah wadda take durƙushe a gabansa...

"Wannan kwayoyin za su zauna a wurina. Idan kika ƙara min rashin kunya a aji, ko kika sake turo waɗannan karnukan naki, to asirinki zai zama labarin gari. Kuma daga gobe, ke za ki riƙa share min aji na kafin in fara koyarwa sannan ki goge mun allo... Kin ji abinda na faɗa?"

Maayah ta gyaɗa kai cikin kuka da kunya. Ta gane cewa a yau, ta haɗu da asalin Uban gida....

✨✨✨

Ching Ching tana zaune a cikin ɗakin ajiye tarkace, wanda yake cike da ƙura, tsofaffin akwatuna, da duhu... Tana ta faman goge fentin jikin bango da yayi ƙura da yana-yana da wani tsohon kyalle, hawaye yana ta zuba a fuskarta.

Tana jin yunwa, da tsoron duhun dake cikin dakin, kuma tana jin haushin kanta da ya kaita ga wannan halin...

Kwatsam, sai ta ji ƙarar buɗe ƙofa. Ta ɗago kai tana tunanin Chief ne ya zo ya ce ta tafi ta kwanta a gadonta, amma sai ta ga Gely ce ta shigo, riƙe da wani haske da kuma kular abinci...

Ching Ching ta harare ta, ta ci gaba da goge-gogen ta cikin fushi...

"Kin zo ne ki yi min dariya? Ko kin zo ne ki ga yadda nake shan wahala?"

Gely ba ta tanka ba. Ta ajiye abincin a kan wani akwati kusa da ita, sannan ta ɗauko wani magani mai ƙarfi na goge fenti da kuma wani kyalle mai kyau...
Ta durƙusa a gefen matakalar, ta fara goge fentin da sauri-sauri fiye da yadda Ching Ching za ta iya...

"Boss yace ba za ki ci abinci ba," Gely ta faɗa cikin muryar robot dake cike da natsuwa...

"Amma tsarin lissafina ya gaya min cewa idan ba ki ci abinci ba, ba za ki iya gama aikin nan ba, kuma za ki ƙara ciwo wa kanki, wanda hakan zai jawo wa Boss ɗan uwan damuwa... Don haka, ki ci abincin nan kafin na gama goge miki matakalar."

Ching Ching ta saki kyallen hannunta, ta kalli Gely cikin mamaki..

"Ke Gely... me ya sa kike taya ni? Bayan ni ce na yi ƙoƙarin janyo miki rauni ɗazu?"

Gely ta ci gaba da aikin, hannuwanta na ƙarfe suna ta gogayya da matakalar cikin sauri..

"Ni na'ura ce, ba na jin rauni kamar ɗan adam. Amma na ga yadda kika firgita lokacin da kika ga zan faɗo. Hakan yana nufin ba mugunta ba ce a zuciyarki, shagwaba ce kawai da rashin tunani."

Ching Ching ta ji jikinta ya yi sanyi. Ta ja kular abincin ta fara ci cikin sauri, tana kallon yadda Gely take taya ta aikin cikin sauƙi..

"Na gode Gely," ta faɗa ƙasa-ƙasa, wanda hakan shi ne karon farko da ta taɓa faɗar kalmar godiya ga Gely...

Gely ta kammala goge matakalar cikin ƙanƙanin lokaci, sannan ta tashi tsaye.. .

"Kada ki bari Boss ya san cewa na taya ki, kuma kada ki bari ya ga abincin nan. Idan kin gama, ki kwanta a kan waɗannan bargunan, zan rage miki sanyin ɗakin ta hanyar sarrafa na'urar sanyaya ɗaki ta gidan (Central Cooling)..."

Ta juya za ta fice, sai Ching Ching ta ƙira sunanta..

"Gely! Shin... shin muna iya zama ƙawaye?"

Gely ta tsaya a bakin ƙofa, idanunta suka yi wani haske na musamman..

"Ƙawance tsakanin mutum da na'ura abu ne mai wahala, Shugaba Ching Ching. Amma idan kika daina wasa da rayuwata, ni ma zan ci gaba da kiyaye naki mutuncin a gaban Boss..."

Ta fice ta bar Ching Ching a cikin ɗakin, amma yanzu ɗakin bai yi wa Ching Ching duhu da tsoro kamar ɗazu ba. Ta gane cewa Gely tana da wani ɓangare na kyautatawa duk da cewa ita ƙarfe ce...

Washegari da sassafe, Chief Onyx ya nufi ɗakin ajiye tarkacen... Zuciyarsa tana buga masa tsantsar tausayi, domin ko ba komai ya san ɗakin akwai duhu da ƙura, kuma Ching Ching ba ta saba da irin wannan wahalar ba. Ya ɗauka zai tarar da matakalar tana nan yadda ya bar ta, ita kuma Ching Ching tana kuka ko kuma ta yi barci ba tare da ta gama aikin ba...

Amma yana buɗe ƙofar, sai ya ja ya tsaya cikin tsananin mamaki.

Matakalar ta yi fes, fentin jikinta duk ya fita har tana sheƙi kamar sabuwa... Ching Ching kuwa tana barci a kan wasu tsofaffin barguna, fuskarta tana ɗauke da alamun gajiya amma akwai wata natsuwa a tattare da ita.

"Ta yaya yarinyar nan ta gama wannan aikin duka a dare ɗaya?" Onyx ya raɗa a hankali. Ya san ƙoƙarin Ching Ching, ya san kuma wahalar goge fenti, lallai akwai wani abu a ƙasa.

Yana shirin juyawa, sai ya hango kwanon abincin da aka tura a ƙarƙashin wani tsohon akwati. Ya ƙarasa ya ɗauko kwanon, ya ga ragowar abincin da aka ci. Sannan ya kalli tsarin sanyaya ɗakin (AC), ya ga cewa iskar dake fitowa a wannan sashen tana da ɗumi na musamman wanda aka tsara don mutum ya iya barci cikin jin daɗi...

Ya miƙe tsaye ya fito daga ɗakin, ya nufi falon dining inda ya tarar da Gely tana ƙoƙarin haɗa masa coffee na safe.

"Gely," Onyx ya ƙira sunanta cikin muryar dake nuna ya gano komai.

Gely ta juyo cikin natsuwa..

"Ina kwana, Boss. An riga an kammala dukkan ayyukan da ka bayar a ɗakin tarkace. Shugaba Ching Ching ta yi aiki tuƙuru."

Onyx ya ajiye kular abincin a gaban Gely. "Wannan abincin fa? Kuma waye ya ba da izinin sauya tsarin AC na dakin tarkace don ya yi mata ɗumi?"

Gely ta yi shiru na daƙiƙa biyu, idanunta suka yi walƙiya alamar tana sarrafa bayani wato tana processing...

"Boss, bincikena ya nuna cewa idan Ching Ching ta kwana cikin sanyi da yunwa, jikinta zai iya yin rauni, wanda hakan zai jawo maka asarar lokaci wajen kula da ita. Don haka, na ɗauki matakin taimaka mata don amfanin wannan fadar...."

Onyx ya matso kusa da Gely, ya zuba mata ido.. "Kin taimaka mata wajen goge fentin ma, ko?"

Gely ta sunkuyar da kanta kaɗan. "An yi hakan ne don tabbatar da an kammala aikin a kan lokaci kamar yadda ka bayar da umarni."

Onyx ya yi wani ɗan gajeren murmushi, wanda yake cike da mamaki. Ya gane cewa Gely ta fara yin abubuwa ba kawai don ita Inji ba ce, sai don tana da wata irin kulawa ta daban.

"Kin kyauta Gely," Onyx ya faɗa cikin murya mai sanyi...
"Amma kada ki sake keta umarni na a asirce. Yanzu je ki tashe ta, ki gaya mata ta je ta yi wanka ta shirya, sannan ta zo nan ta ci abinci a gabana."

Gely ta nufi ɗakin tarkacen, tana zuwa ta taɓa kafaɗar Ching Ching...

Ching Ching ta farka a firgice, tana gani Gely sai ta yi murmushi...
"Gely... ashe gaskiya ne banyi mafarki ba? Kin taimaka min?"

Gely ta jinjina kai. "Boss ya gano komai. Amma maimakon ya yi fushi, ya ce ki tashi ki shirya ki zo ki ci abinci a gabansa. Wannan dama ce ta gyara tsakaninku."

Ching Ching ta tashi cikin murna, ta rungume Gely
. "Na gode Gely! Ke ce babbar ƙawata!"

Daga nan suka fito tare, Chief Onyx yana kallon yadda Gimbiya da Robot ɗinsa suke tafiya tare, yana jin cewa fadar ta fara samun wani sabon yanayi na zaman lafiya wanda bai taɓa tunani ba...

✨✨

Bayan kwanaki biyu da faruwar hakan, zaman lafiya ya wanzu a fadar...

Ching Ching ta rage shishshigi, yayin da Gely kuma ta rage takura mata. Amma Chief Onyx ya sani cewa dorewar wannan zaman lafiyar tana buƙatar jarrabawa...

Wata rana, Chief Onyx yana duba wasu tsofaffin na’urori a wani sashe na gidan da ba a cika amfani da shi ba. Kwatsam, sai aka samu matsalar wutar lantarki (electrical surge) a gidan wadda ta sanya duk kofofin zamani na gidan suka kulle kansu wato sunyi Lockdown Mode...

Wutar ta tashi ne daga babban ɗakin sarrafa injina, inda hayaƙi ya fara turnuƙewa. Chief Onyx ya tsinci kansa a kulle a cikin wani daki mai ƙofa ta ta zamani mai sarrafa kanta, kuma na’urar sadarwarsa ta daina aiki saboda matsalar wutar.

A Babban Falo...
Ching Ching da Gely ne kawai a falon. Nan take Gely ta dakata, idanunta suka yi ja wur alamar Alert Mode...

"Akwai matsala, Shugaba Ching Ching. An samu gobara a bangaren sarrafa wuta, kuma Boss yana kulle a can."

Ching Ching ta zabura, fuskarta ta yi fiyau saboda tsoro. "Me kike jira? Je ki cece shi!"

Gely ta girgiza kai. "Wutar lantarkin ta hargitsa tsarin jikina, ba zan iya buɗe kofofin lantarkin ba daga nan. Ina buƙatar wani ya shiga ta cikin ramin iska Air Duct wanda yake da matuƙar ƙunci da barazana, ya je ya danna maɓallin kashe wutar daga ciki. Ni kuma jikina na ƙarfe ba zai iya wucewa ta ramin ba..."

Ching Ching ta ce, "mu je ki nuna mun wurin..."

Haka suka nufi sashen dake da ɗan nisa zuwa wurin..
Suna isa Ching Ching ta kalli ƙaramin ramin iskar dake jikin bango, sannan ta kalli Gely. Ta sani cewa ita ce kaɗai za ta iya wucewa ta wurin saboda ƙanƙantarta...

"Zan yi!" ta faɗa cikin ƙarfin hali. "Nuna min inda zan bi."

Gely ta buɗe ramin, ta ba wa Ching Ching wani ƙaramin kyalle mai ruwa don ta rufe hancinta saboda hayaki...

"Ki yi hankali, Shugaba Ching Ching. Idan kika isa can, ki danna jan maɓallin dake hannun dama. Idan ba ki yi nasara ba, dukkanmu muna cikin haɗari...domin gobara zai iya tashi, kuma zai fara ne daga inda kike..."

Ba ta wani tsaya ta jin abinda Gely zata faɗa ba... Kawai ta hau wani matakala ta shige cikin ƙaramin rami dake sama,
ta fara tafiya a kwance tana jan ciki a cikin ƙanƙantar ramin, tana shaƙar hayaƙi, tana jin tsoron duhun wurin, amma tunanin Chief Onyx yana cikin haɗari ya ba ta ƙarfi zuciya...
Gely kuwa tana tsaye a waje, tana gaya mata hanyar da za ta bi ta hanyar amfani da sauti Ultrasonic Sound wanda Ching Ching kaɗai take ji, yadda ta maƙala a kunnenta....

Iskar cikin ramin ta yi zafi, tana ɗauke da wari mai ƙona hanci. Jikinta a manne da bangon ƙarfe, ƙirjinta na bugawa da ƙarfi saboda ƙuncin wurin...

Ta ja numfashi a hankali, tana jan jikinta gaba da ƙyar...
Tayi nisa sosai karon farko ta miƙa hannunta na dama don ta tura kanta gaba
⚡⚡⚡
“AAAHHHH!!”

Wata wutar lantarki ta ratsa tafin hannunta, ta gangaro har ƙashin bayanta. Jikinta ya kankame cak! Ta buge kanta da bangon ramin, hawaye suka cika idanunta nan take...

Ta janye hannunta da sauri, numfashinta ya rikice..

A waje, Gely ta ji ihun ta ta hanyar ultrasonic sound..

“Fatan kina lafiya, Shugaba Ching Ching?” muryarta ta fito da sauri, cike da tashin hankali..

Ching Ching ta haɗiye kuka..
“Na… na ji shocking… amma zan iya,”
ta furta cikin muryar da ke rawa.
Ta sake gwadawa, wannan karon da hannu na hagu..

⚡⚡⚡⚡
“AHHHH!! Wayyyyoooo!!”

Wannan karon wutar ta fi ƙarfi. Ta ji kamar an tsaga jijiyoyin hannunta. Jikinta ya fara rawa ba tare da iko ba. Ta cije leɓenta da ƙarfi don kada ta yi ihu amma ciwon ya fi ƙarfin juriyarta..

Hawaye suka gangaro suka gauraye da zufar dake gangaro mata..

“Ki dakata! Ki dakata idan ba za ki iya ba!” Gely ta yi magana da gaggawa..

Amma Ching Ching ta riga ta yi nisa. Ta san babu juyawa baya..
Ta duba gaba ta hango wayoyin lantarki waɗanda suka yanyanke, suna walƙiya suna fitar da ƙaramin haske mai ban tsoro...

Wurin ya yi hatsari sosai. Ƙasa da ƙafa guda kaɗan ne kawai ke tsakaninta da maɓallin ja..

Ta ja jikinta gaba tana tura ciki, tana ƙoƙarin kauce wa wayoyin, amma ramin ya yi matsi sosai..

⚡⚡⚡⚡⚡
Wutar ta kama ƙirjinta da kafaɗarta lokaci guda..

“AAAAHHHHH!!!”

Wani zazzafan ciwo ya bugi cikinta. Ta ji numfashinta ya tsaya cak. Jikinta ya sake kankamewa, bakinta ya buɗe ba tare da saninta ba,
Sai ga jini ya fara zuba daga gefen bakinta..

Idanunta suka yi duhu, gani ya fara dishi..

“Ching Ching!! Ki amsa! Ki amsa!” Gely ta yi magana ta hanyar sauti...

Ching Ching ta buɗe bakinta da ƙyar..

“Ka… kada ki damu…” ta furta cikin rauni. “Uncle… yana can…”

Ta tuna fuskar Chief Onyx. Shirunsa da girman kansa...

“Ba zan bari ya mutu ba…” ta faɗa a ranta.

Da ragowar ƙarfin da ya rage mata, ta tura jikinta gaba. Wutar ta sake ratsa jikinta sau ɗaya, amma wannan karon ta ƙi yin ihu. Ta yi shiru tana kuka a ranta...
Hannunta na rawa ya kai KAN MAƁALLIN JA...

Ta rufe idanunta.
Ta danna..
⛔⚡

Nan take, duk walƙiya ta mutu. Hasken haɗari ya kashe kansa. Iskar zafi ta ragu. Ramin ya yi shiru tamkar kabari...

Ching Ching ta kife kanta, jikinta duk ya mutu ba ƙarfi.. Numfashinta yana fita da shigowa da ƙyar.. Jini yana kan zubowa ta leɓenta, hannayenta suna rawar sanyi…
Amma ta yi nasara...

A waje, Gely ta karɓi siginar tsarin dawowa..

“Wuta ta muta… Shugaba Ching Ching… kin yi nasara.”

Idanun Ching Ching suka rufe a hankali.
A ƙarshe kafin ta suma, murmushi kaɗan ya tsallake leɓenta...

“Uncle… ya tsira…”


Nan take, ƙarar ƙararrawa (Alarm) ta katse gaba ɗaya. Wutar walƙiya ta mutu. Hayaki ya fara raguwa a hankali, kamar yadda numfashi ke dawowa bayan tsananin firgici...
Daga bisani, dukkan kofofin zamani na gidan suka buɗe kansu lokaci guda..

Chief Onyx ya fito daga ɗakin da aka kulle shi, yana tari mai ƙarfi, ƙirjinsa na motsi sama da ƙasa. Idanunsa sunyi ja sakamakon hayaki, amma hankalinsa yana nan daram. Bai tsaya ko’ina ba ya juya da gudu kai tsaye zuwa ɗakin sarrafa wutar lantarki...

A zuciyarsa, tambaya ɗaya ce kawai ke juyawa..

“Waye ya iya kashe wannan bala’in?”

Da ya isa wajen, sai ya ci karo da Gely tsaye a ƙasan matakala, kanta a ɗage sama, idanunta a manne da ramin iska. Ta tsaya cak, tamkar ana jiran rai ya fito daga kabari...

Ba wani motsi sai numfashin Chief Onyx kaɗai ke cika wurin..

Cikin murya mai tsauri yana ɗaga mata murya ya ce,

“Me kike yi tsaye a nan? Kuma ta yaya aka kashe wutar alhali na san ke ba za ki iya shiga wannan ramin ba?!”

Gely ta sauƙe kanta a hankali. Murya na fita cikin rauni..

“Shugaba Ching Ching ce…” ta furta..

Chief ya ɗan tsaya..
“Me kika ce?”

“Shugaba Ching Ching ta shiga ta sama… ita ce ta kashe wutar.”

Kalmar ta faɗa kamar fashewar bam a zuciyarsa..

“WHAT?!” ya ƙara da tsawa, ya matso kusa da ita. “Shin kin ba ta kayan kare jiki? Hannu? Ko wani kariya?”

Gely ta girgiza kai a hankali...
“A’a, Boss…”

Ya kalleta kai tsaye, idanunsa cike da fushi da tsoro a lokaci guda..

“You are very stupid, Gely.”

Ya juya, ya kalli ƙaramin ramin iska dake sama. Hankalinsa ya rikice. Ya san babban mutum ɗaya ba zai iya shiga ba, balle mutum biyu. Kuma ramin ya yi matsi, ba za a iya haura wa don ceto kai tsaye ba..

A wannan lokaci, Gely ta sake magana, amma wannan karon muryarta ta yi sanyi sosai..

“Boss… tunda tsarin yana iya sarrafa kansa… akwai hanya. Za mu iya buɗe ramin daga ƙasa, ta yadda bangon da take kai zai buɗe, ita kuma za ta faɗo a yadda take kwance.”

Chief ya juya da sauri.
“Amma ban san ta ina take ba!” ya ce cikin muryar tsawa...
“Kuma da alamun ta suma! Idan ta faɗo ba tare da tsari ba.....”
Bai ƙarasa ba...

Gely ta ɗaga hannunta. Idonta ya canja launi, wani jan haske (scanner) ya fito daga idonta ya harba sama cikin ramin iska.. Hasken yana tafiya a hankali, yana duba kowane sashe..

A zuciyarta, tana bin alamomin bugun zuciya…
Raunin jiki…
Matsayin mutum…
Can sai hasken ya tsaya...
“Na gan ta, Boss.” Gely ta ce cikin tsanani...

“Tana kusa da maɓallin ja. A yadda take kwance, tana fuskantar gefe… bayan ta danna, nan take ta suma.”

Chief Onyx bai ƙara magana ba. Ya juya kai tsaye.
“Je ki buɗe tsarin daga computer.
Ni zan tsaya a daidai inda take.”

Ya matsa ya tsaya a yanda take ya buɗe hannayensa, zuciyarsa na bugawa da ƙarfi fiye da kowane lokaci a rayuwarsa...

“Da zarar kin buɗe… zan cafke ta.”

Gely ta yi saurin juyawa zuwa computer ɗin sarrafawa..

A sama kuwa…
Ching Ching tana kwance a cikin ramin, jikinta babu ƙarfi. Jini yana ta zuba daga bakinta, yana bin gefen leɓenta zuwa wuyanta. Numfashinta yana fita da shigewa cikin wahala, tamkar wuta na ƙoƙarin mutuwa..

Idanunta a rufe.
Ba ta san abin da ke faruwa a ƙasa ba...

A ƙasa, Chief Onyx ya tsaya kamar dutse. Idanunsa ba su bar kallon saman ba...

Sai
CLICK!
Bangon ramin ya buɗe.
A cikin daƙiƙa guda, jikin Ching Ching ya zame ya faɗo ƙasa..
Cikin zafin nama Chief ya cafke ta a hannunsa...

Ƙarfin jikinta ya buge ƙirjinsa. Zafin jikinta ya ratsa shi....haka yake riƙe da ita kamar jaririya..

“Ching Ching…” ya furta a karon farko cikin raunanniyar murya..

Yana kallonta ga yadda jini yake fita a bakinta...
Fuskarta yayi fari sol...
Numfashinta a raunane.
A wannan lokacin ne Chief Onyx ya gane abu ɗaya..
Ta kusan rasa rayuwarta saboda shi....
*Likes ɗinku shine albashin marubuci*

👍 Like
🔁 Share
💬 Comment


*👑 MASARAUTAR ALHAMRA 👑*

_🪄 Gidan Mulki, Iko da Sirrin Zuciya 🪄_

✍🏽 By ASMEETAH WRITER
~Hasken Jajirtattu~


💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️

```JARUMAI WRITERS TEAM```

▶️ DON BIYO DAGA FARKO 👇
🔗 WhatsApp Channel:
https://whatsapp.com/channel/0029VbBCNlqJUM2RQwWncg43

📚 ArewaPen:
https://arewapen.com/u/asmeetahwriter

📖 Wattpad:
https://www.wattpad.com/user/asmeetahwriter

📲 Contact:
09065443871

📅 FARA TURA BOOK:
🔥 01 — 01 — 2026 🔥

📘 BOOK ONE
```MATAKIN FARKO```
Chapter 30 · 0% Book details