Sashe 8
Marubuciya Book One Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kamar bai ji dadin maganar ba ya ce .
"To ai shi ke nan Salma, ina yin wannan ne kawai a matsayinki na amana a guri na , tunda haka kika ce Allah ya dawo dake lafiya."
Ta amsa masa da"Amin babana."
Sannan sukai sallama ta kashe wayar
Yayan baban nata yana kashe wayar ya kalli matarshi dake gefe ya ce .
"Allah sa mu dace , Allah raba mu da sharrin hajjiya Aisha."
Matar tashi ta amsa da
"Amin dai wallahi, ai ni tunda ta d'aga hannu zata mareka na tsani matar nan , banda ma ta'be wa irin tata , mene na zama a gidan babu d'a babu jika."
Ya ce .
"Allah dai ya kyauta."
Fitowarta daga bandaki ke nan Hadiza, ta ajiye buta kana tayi mika
Karima ta kallah dake gefen mahaifiyarta tana cewa.
"Aunty Karima naga fa yau duk sai a hankali ke , kodai kodai an samu karuwa ne ."
Cikin yanayin mutuwar jiki Karima ta ta'be baki tana cewa.
"Hmmm."
Umman ta ta ce .
"Kyaji dai da rashin kunyarki."
Hadiza ta ta'be baki tana cewa.
"Kai Mama kwana nawa ne na bar miki gidan , kinga dai Sultan ya turo, yana dawowa zaku sha biki ."
Da gudu Hadiza ta fad'a daki jin wayarta na ruri.
Karima kam ta tashi ta shige lungunta domin sam yau bata jin dadi , ta dauki wayarta da nufin zuwa tirkot tai kalloh .
Bayan Hadiza ta dauki wayar cikin raha ta fara cewa.
" 'Kawata Ruma kwana biyu ya garin ko online bana ganinki."
Daga can bangaren Ruma ta amsa mata da cewa .
"Ai baki da mutunci wallahi, sati biyu ke nan da sace min waya."
Hadiza ta ce .
"Ohh Allah sarki Allah maida alheri, ke yarinya an sa mini rana fa ."
Dariya Ruma tai tana cewa.
"Kai haba dan Allah ki ce lokacin zuwana sokkoto ya yi , da Sultan din aka sa ."?
Hadiza ta ce .
"Kwarai kuwa yaron hutu ba , ai yana dawowa daga Jemani zaku sha biki."
Ruma ta ce .
"Tom Allah ya kaimu kawata gaskiya ina missing dinki da novels dinki ."
"Yawwa kin ga wata marubuciya Autar marubuta, Littafin ta na Fatima da zarah, kin tuna Littafin da Salma ta taba yi, shegiya ashe satar ilmi take ."
Dariya Hadiza ta kwashe da ita tana cewa.
"Aiko na gani , na rasa inda nasan Littafin to Allah ya kyauta ko ta dawo garin ne ."
Ruma ta ce .
"A'a wallahi , an yi nisan kiyo ai waya sani ma ko karuwanci ta tafi kuma dazu babansu ya rasu ."
Hadiza ta ce .
"Tab to Allah ya kyauta."
Tunda Karima ta bude data ta ci karo da rasuwar kanin babanta wato Malam Aminu, nan ta shiga cikin firgici da tashin hankali, Allah sarki Malam Aminu Allah jikan wanda muka rasa , Allah yasa mu yi kyakykyawan karshe isar annabi Muhammad.
Anan kuwa umman Salma an sha kuka an more , gashi har dare ya rufa , yau dai Malam Aminu Allah ya yi , yabar mana duniya, shima Umar ya shiga yanayi mai matukar girma domin lamarin babu wanda bai girgiza ba .
Haka Alaji Yusuf abin dai ba a cewa komai. Allah ka jikan wanda suka rigamu gidan gaskiya.
Karfe 10:02 Salma na zaune kan gado tasa laptop a gabanta , typing din ma yaki yiyuwa, samm ta rasa inda yake mata ciwo, komai bata jin dadinsa , domin hatta abincin dare bata iya ci ba
"A gaskiya ya kamata na koma gida, nasan na yi rashin hankali ku gafarce ni Umma."
Ta fashe da kuka yayin da take maganar a cikin zuciyarta
"Allah ne yasan halin da suke ciki, tabbas ni Mahaukaciya ce."
Ta sake fashewa da sabon kuka, tunanin gida Salma ta ringayi a daren yau, ta kasa aikata komai domin tana tunanin ya kamata ta koma gida, ko dan tafiyar da Aunty Hauwa zatai ta barta, haka har bacci ya dauketa a wannan wajen.
Yau da asubar fari Karima da mijinta suka tafi Kano, Umman Hadiza ta ce idan sun isa sai a kira ta tai musu gaisuwa.
Gida ya cika da maza da mata masu shigowa suna yin gaisuwa, idan Umma ta tuna babu Malam Aminu babu Salma sai ta sake shiga cikin tashin hankali da matukar rauni.
Allah ya horewa Salma saurin typing da hikima cikin rubutu, hakan yasa marubuta da yawa suke zuwa domin su yi Littafi tare .Tana daukar wayarta Facebook ta shiga kai tsaye , bayan ta ga yadda akai mata comments sosai yasa ta fito domin gamawa da na WhatsApp.
Wata number ce mai 56 karshe ta fara bude sakonta.
"Ke Mahaukaciya karuwa kawai, kina tunanin ban gane ki ba ne , wawiya mara hankali."
Abin da Salma ta gani a rubuce ke nan, mamaki ne ya rufe ta tare da tunanin tabbas wrong number ake nema akai mata magana.
Autar marubuta ce .
https://whatsapp.com/channel/0029VasuzYr6rsR0bxO94J1I
*SADAUKARWA GA Marubuta masu tsaftataccen alkalami*🥰✍️
Kaggagen labari ne ✍️
A yi hakuri masoya wanna lokacin ma babu editing❌
~Ba labari ba ne mai tsayi~
Autar marubuta ce
MARUBUCIYAR .....
Gubar rayuwata
Kawar karuwai
Dajin mutuwa
Fatima da zarah
Mahaukacin so
Dangin dalas...🥂👇
MARUBUCIYA ✍️
Na
Autar marubuta
________________________________________
Page 19&20
Salma jimm ta yi tana tunanin wannan sako, ba tare data fice daga ciki ba , hakan yasa ta sake ganin shigowar wani sakon .
"Kina magana da Hadiza RM, kin gudu daga gidanku to asirinki ya tonu."
Salma ta sake karantawa
Hadiza kuwa Shahada kawai tai ta tura wannan sako ga Autar marubuta, domin bata da tabbacin Salma ce , sai dai wannan Littafin na Fatima da zarah yake bata yakinin wannan Salma ce , idan kuma ba ita bace hakuri Hadiza zata bata kawai.
Murmushi Salma tai kafin tai mata reply ta ce .
"Lallai yarinyar nan ta ya ta gano ni , tabbas Hadiza bata kaunata, ai ba komai bane danta gano ni , daman gida zan koma ."
Typing Salma ta fara mata tana rubuta .
"Hmmm."
Abin data tura mata ke nan
Ran Hadiza ya baci da ganin wannan reply, hakan yasa ta sake tura mata da cewa.
"Karki damu, ni bazan tona miki asiri ba, amma ki sani nayi miki nisa nayi miki rata, alkalamin ki bazai ta'ba taddo nawa ba ."
Ta tura mata, sannan ta shiga channel din Salma wanda ta ga an yi sharing dinsa a group dinta,abin da ya fara d'aga wa Hadiza hankali ganin tarin followers dake wannan channels sun ninka nata sun kuma ninkawa , tsaki tai ta fito daga ciki ,kana ta goge Link din a cikin group dinta sannan tai remove din wacce ta turo .
Salma kam kawai sakon ta bude tai shiru ba tare da amsa ba , hakan yasa Hadiza ta gamsu Salma ce .
Wata wutar kiyayyar Salma ta sake ji tana ruruwa a zuciyarta, ganin yadda Salma take matukar samun masoya da yadda ake son Littafin ta .
"Na tsaneki Salma, bana kaunarki wallahi, ni ce ajalinki duk inda kike anan zaki mutu, dani kike zancen."
Sannan ta rafka wani uban tagumi tana tunani
Umman ta ce ta shigo dakin tana cewa.
"Lafiya Hadiza."
Hadiza ta d'ago kai cikin rashin jin dadi tana cewa.
"Dazu Inna ta kira waya , ta ce ba yanzu zata dawo ba tana gidan Baba Musa , Yayan baban yayaUmar ."
Umman Hadiza tai dariya da cewa.
"Allah sarki Inna masu yaya da yawa."
Hadiza ta sake zabga tagumi, ganin halin da take ciki yasa Umman ta cewa.
"Wai lafiya Hadiza na ."
Hadiza tai nannauyar ajiyar zuciya sannan ta ce ."Umma burina zai lalace, kinga kudin da nake samu zan dena samu , sannan shaharar da zan yi ita ma lalata min ita za tai."
Ta'be baki Ummanta ta yi , kana ta ce .
"Wa ce ce kuma ,me yasa zata miki haka."
Hadiza ta ce .
"Hmm Mama akwai matsala dai kawai , shi ke nan tawa ta kare , kudin da muke dan samu ma yanzu ba zasu zami ba ."
Umman nata ta rike kugu tare da fad'in.
"Tab aiko ta yi kadan, batasan dawa take yi ba , shirya yanzu muje wajen Malam Zarto, kafin ta hanaki ke kin hanata."
Hadiza tai jimm kana ta kara da cewa.
"Allah ko Umma, amma zaki gane gun Malam din."?
"Ayyuririri."
Umma tai bud'a sannan ta kuma cewa.
"Ke Hadiza nifa haifaffiyar sokkoto ce , kina gani nan nayi aure, har na haifi Adam , abin da ya kaini zaman Kano auren babanki ne , kuma bayan babu shi ,gani na dawo sokkoto, mu muka san koina shirya kawai."
Tana gama magana ta fad'a daki
Kafin Hadiza ta motsa daga inda take sai ga sallamar Karima
Murmushi Hadiza tai tana cewa.
"Ahh mutanen Kano an yi 7 an dawo sannu da zuwa Aunty."
Karima cikin gajiya ta aje jakar dake hannunta tana cewa.
"Yawwa sannu Karima ina Umman."?
Hadiza ta kalli kofar dakin Umma kana ta ce .
"Yanzu ta shiga daki, shima Yaya Adam bai dade da fita ba , yau ba shi da aiki ."
Tana gama magana Umma ta fito da fad'in.
"Sannu da hanya Karima ya aka ji da karin hakuri."?
Karima ta ce .
"Mun gode Allah Umma wani gun zaki ne ."?
Ta tambaya ganin ta sako takalmi da hijabi
Hakan yasa Hadiza ita ma ta dauko nata hijabin...
Gombawa d'ibar fari , ba a kwana daku ba an tashi daku 💪