Sashe 3
Marubuciya Book One Complete Hausa Novel · about 7 min read
Anan kuwa tunda garin Allah ya waye Umman Salma bata fito ba , sakamakon yadda kanta yake mata ciwo tun daren jiya.
Sai dai har yanzu bata ji motsin Salma ba, saboda Salma ta saba kullum tana fitowa tayi shara, koda kuwa zata koma bacci. Wannan tunanin yasa Umman nata dauriya tana fitowa waje , ta tura dakin Salma yana budewa ta ga babu alamun motsinta , ban daki ta leka nan ma babu labarinta.
"To ina Salma ta shiga ne ."? Take tambayar kanta
A lokacin Umma taji gabanta ya fadi tare da tunanin tabbas sam bata ji motsin Salma ba , hakan yasa ta nufi dakin malam Aminu, karo taci da Umar
Ya durkusa har kasa yana gashsheta. "Ko ka aiki Salma ne ."
Jin Umma ta ce dashi haka ya sa shi fad'in.
"A'a yanzu ma na bude gidan , don yau da asuba duk bamu je masallaci ba." Ya karasa maganar yana nuna mata mukullin da kwad'o
Ajiyar zuciya tai tana cewa."To ina ta shiga haka ."
Jin wannan kananun maganganu ne ya sa Malam Aminu fitowa,
"Wai me ake yi ne ? Me ke faruwa."?
Umma ta maida masa da cewa. "Salma ce ba a gani bafa Malam."
"Kamar ya ba a ga Salma ba , ku sake dubawa dai ."
Ya fad'a cikin mamaki
Umma ta sake sauke ajiyar zuciya tana cewa."To babu dai inda ban duba ba ."
Malam Aminu yasa kai cikin gidan ya nufi dakin Salma, suma suka bi bayanshi .
Ido suka tsurawa dakin kamar suna duban wani abu
Wani akwati dake kasa malam yasa hannu yana bude cikinsa, ganin hijabai a ninke guda uku yasa shi cewa.
"Ina sauran kayan nata ? Ko daman su ke nan."?
Umma da Umar suka leko suna duban kayan .
"Haba dai kayan Salma ai duk basa nan." Cewar Umma
Malam Aminu ya ce .
"To tabbas kuwa Salma ba a gida ta kwana ba ."
"Kira babanka muji ko taje can ."
Umar dajin haka ya zaro wayar a aljihunansa yana danna kira ga Alaji Yusuf, kira guda ya yi, mamansu Karima ta miko masa wayar .
"Salamu alaikum Umar." Bayan Alaji ya d'aga wayar
"Baba ina kwana, an tashi lafiya."?
Alaji ya ce ."Lafiya alhamdulillah har kun taho ne ."?
Jin wannan maganar yasa Umar ya fara yin jimm kafin ya ce .
"Baba bata zo bane ."?
Alaji ya ce ."kamar ya ta taho ne ."
Umar ya mikawa malam Aminu wayar yana cewa."Baba kai masa bayani."
"Wanne irin bayani mene ke faruwa ne." Alaji Yusuf ya fad'a yayin da baban Salma ya kara wayar a kunne .
"Dama Salma ce ba a gani ba , kuma ga dukkan alamu bama ta kwana a gida ba ." Ya fad'a masa haka kai tsaye
"Wannan wacce irin magana ce, to ina taje ku sake dubawa dai." Alaji yana gama magana ya kashe wayar
"Alaji meke faruwa kuma." Cewar matarshi
"Wai Salma ce , ba a gani ba tun jiya." Ya karasa maganar yana mikewa tsaye
Cikin mamaki mamansu Karima ta ce ."Innalillahi garin ya kuma."
Alaji ya ce .
"Ai yanzu zanje taraunin wannan wanne irin magana ne."
Jingum-jingum su Umma sukai, domin duk inda suke tunanin samun Salma babu labari.
Lokacin da dabara ta zo wa Umar ya kira number zainab
A spiker yasa wayar tana ta shiga amma ba a dauka ba , tana katsewa ya sake kira .
A bacci Zainab kiran ya tasheta , ta jawo wayar tana dauka .
"Su Salma an sami wayar Yaya Umar ke nan."
Jin haka yasa Umar murmushi yana kallon su Baba.
"A'a Zainab ni ne ba Salma ba ce ."
"Ahu Yaya Ina kwana." Ya amsa da fad'in."lafiya lau Zainab ko Salma tazo nan ."
Taji gabanta ya ce rasss
Sai da tai shiru kana ta ce ."Salma kuma bata zo ba , lafiya kuwa."?
Umar ya ce ."Lafiya lau, dama tun jiya ne ba a ganta ba ."
Cikin tashin hankali Zainab ta ce ."Innalillahi amma jiya da dare ta zo gidanmu ta kawon Littafin Hadisina , harda jaka a hannunta na ce ina zata ta ce gidan Aunty Murja."
Malam Aminu da Umma suka kalli juna.
Sannan Umar ya ce .
"Tom shi ke nan bari na kira Aunty Murjan." Ya gintse wayar .
Duk Zainab taji ta nemi wannan baccin ta rasa , cikin matukar mamaki ta mike ta zauna, kallon Littafin da Salma ta kawo mata a daren jiya tai, cikin mamaki tasa hannu tana dauko Littafin
Sun sake shiga matukar tashin hankali sosai yayin da suka kira Aunty Murjan wato kanwar umman Salma, domin ta tabbatar musu rabonta da Salma za ai wata biyu zuwa uku, hankalin su ya sake matukar tashi tsaye a wannan yanayi
Da sauri Husna ta shigo daki tana tashin Karima "Aunty Karima ki tashi , ga baba can ya fita , Salma ce ta bata tun jiya ."
Zumbur Karima ta mike tana cewa."Mee wacce Salma."
Husna ta ce ."Nima yanzu mommy take sanar mini." Sukai jugum- jugum.
Sokkoto birnin shehu 😍
Su Hadiza sun sauka lafiya lau, yanzu da Adam ya shirya fita aiki yake cewa."Mama yaushe zaku tafi ne , kinsan an kusa kawo kaya, ya kamata ace kuna Kano."
Umman Hadiza ta kalli dan nata tana fad'in."Adam ka jini da kunnen Basira, baka ganin mun debo duk kayanmu ne , tom mun dawo nan , mun dawo nan , idan kuma baza ka iya rike mu bane sai naji ."
Adam ya ce ."A'a Umma shi ke nan, ni zan tafi wajen aiki." Ya musu sallama ya tafi ransa babu dadi .
Haka Umman Hadiza ta samu daki ta zuba kayanta, sakamakon gidan 'dan ta ne Adam da suke zaune da mahaifiyar baban Adam, lokacin da Allah yayiwa baban Adam rasuwa ta koma Kano tai aure, bayan mahaifin Hadiza shima ya rasu shi ne ta dawo sokkoto, ta ce bazata kuma aure ba , tunda dai duk wanda ta aura sai Allah yayi masa rasuwa.
Salma kuwa anan ba a cewa komai, domin ta matukar jigata da gajiya da tafiya saidai har yanzu bata iya hangen komai a inda take . Komai nata ta zubar kafafunta kuwa sun kunbura tsabar gudu da irin abubuwan da take takawa a hanya
Wani rami ta hango cike da ruwa, sai dai gurin ya cika da ciyayi da kananun ramuka da kayoyi, yadda taji tana bukatar amfanuwa da wannan ruwan yasa ta fara takawa a hankali tana shiga cikin ramin .
Kafin ta karasa ciki, ta fara jin wani kuka mai karfi yana ziyara a kumnenta , amma ta duba koina da ina babu abin data iya gani , dawo da kanta da zatai zuwa cikin wannna ramin ta ga wani bakin abu a cikin ruwan idanu jajaye yana dilalo yawu yana kallon ta .
Firgita tai da ganin wannan halitta da bata ta'ba gani ba , hakan yasa ta fito da gudu tana canza hanya , shima binta yayi a guje yana kuka tana neman cizanta .
"Innalillahi wa innailaihir rajiun, la ila ha illallahu , innalillahi, Allah ya Allah." Abin da Salma ke nan ta ringa fad'a tana gudu kamar zata fadi
Tsalle ya yi. Ya kamo mata riga , ta fincike ta sake sa giya tana ihu .
Ya dade yana binta suna cin wannan uban gudun , duk abin ya yazo bakinta fada take tana addu'a,
Kamar irin yadda mutum yake yin gudu yana duban bayanshi haka Salma take, sai wannan halittaar ganinta yake kara bata tsoro.
Shiru Salma taji babu kukun wannan dabba , tana juyawa kuwa babu ita babu alamun ta, nan take jikinta ya fara rawa yana 'bari , domin tabbas a tunanin ta wannan ba komai bane bace àljani koda kuwa wacce irin dabba ce , cikin wannna yanayi ta cigaba da tafiya, tafiyar na harde mata kamar zata fadi, tari ne ya biyota tana kokarin amai , ta kai kasa tana zubar da wani irin koren ruwa daga bakinta , lokaci guda kuma tsoron wannan abin yana ranta , ta mike tana d'ingishi domin barin gurin kafin wannan abin ya dawo .
Sai da ta jigata sosai ba kadan ba, ta fara tafiya tana jan kafa .
Autar marubuta
*MARUBUCIYA* ✍️
Na
Autar marubuta
____________________________________________
Page 7&8
Lokacin da Alaji Yusuf ya karaso, babu wani labari dai na Salma, nan suka zauna suna tunanin mafita da yadda za a bullowa lamarin.
"Da dai an sanar da 'yan sanda ko."? Inji Umma
Alaji Yusuf ya ce ."Yanzu yarinyar nan bana tunanin 'bata tayi ko sace ta akai , to mu sanar da yan sanda mu ce musu me ."
Malam Aminu ya ce ."Haka ne ."
Umma ta sake fad'in."Sanin gaibu ai sai Allah duk bamu da tabbacin meke faruwa da Salma ko ."
A lokacin Zainab ta rado sallama tana turo kai , ganinsu jigum wasu a tsaye yasa taji duk ta sake shiga yanayi, haka ta gashshesu, suka amsa