← Book details Marubuciya Book One Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 19

Sashe 5

Marubuciya Book One Complete Hausa Novel · about 8 min read

Salma ce kwance kan kujera , bayan ta yi wanka da ruwan zafi , aka bata wani riga mara nauyi ta Sanya
Sannan likitan da aka kira ya sanya mata ruwa , tare da rubuta mata magunguna , kana ya tafi .

"Har yanzu bansan sunanki ba ."
Salma tai maganar tare da kallon ta
Murmushi tai tare da rike hannun Salma tana cewa.
"Suna na Hauwa'u, kuma ni yar jarida ce , sannan 'yar gata ce ni kafin iyayena da mijina su rasu , yau watanni 4 da kwanaki da rasuwarsu , sakamakon hadarin mota ."
Hawaye suka gangaro mata
Salma ta share mata hawayen tare da fad'in.
"Ki yi hakuri Aunty, Allah ya musu rahma."

Aunty Hauwa tai murmushi tare da cewa.
"To salmana ki kwantar da hankali nan gidanku ne , na samu kawa, sannan waccen matar da kika ganta .
Sunan ta hajjiya Aisha matar mahaifina ."

Kafin ta karasa maganar wani saurayi ya bankado labulai kana yasa ido yana kallonta .
"A'a Aunty Hauwa wannan babyn fa ."
Ya nufo da nufin ta'ba Salma

Tsawa Aunty Hauwa tasa masa tare da cewa.
"Baka da hankali ne Anas, mene haka ."?
Jin haka yasa shi cewa .
"Ai shi ke nan."
Ya wuce sama yana tafiyar yan shaye-shaye.

Hankalin Salma ya matukar tashi ganin wannan yanayi , hakan ya sa ta kalli aunty Hauwa tana cewa.
"Aunty wa ye wannan kuma ."?

"Ki kwantar da hankalinki , wannan yaron hajjiya Aisha ne , amma ba babanmu daya ba , kusan anan gidan ya girma."

Salma tai ajiyar zuciya

Lokacin Aunty Hauwa ta mike da cewa .
"Ina Suwaiba ne , ko har ta tafi."

Salma ta bata amsa da cewa.
"Ai tunda ta gama girki ta tafi."
Ta ce .
"Okay."....

Umar ne cikin daki har ya kwanta, rike yake da wayarshi yana kallon hoton Salma, baisan lokacin da hawaye suka zubo masa ba
Ya share su tare da sake sa ido cikin hoton yana cewa.
"Haba Salma, yaushe zaki dawo?
Kin barni cikin kunar zuciya da kewar ki, rayuwa bata mini dadi Salma."
Ya aje maganar yana rumgume wayar yana kuka .

Wayyyo masu karatu a jona da wannan page 😫
Sai mun had'u a wani.

07040805269
WhatsApp only

Ku yi mini subscribe 🥰🥂🙏 Something big is coming....😌
https://youtube.com/@fatimaismailabdullahi?si=l3dnPNRKygK5lG4g

*SADAUKARWA GA Marubuta masu tsaftataccen alkalami*🥰✍️

Masu YouTube na baku damar karanta wannan Littafin 👌🙏kar a yi kuskuren canza mini duk abin da aka gani a wannan labarin ✍️

A yi hakuri masoya wanna lokacin ma babu editing❌
~Ba labari ba ne mai tsayi~

MARUBUCIYAR .....
Gubar rayuwata
Kawar karuwai
Dajin mutuwa
Fatima da zarah
Mahaukacin so
Dangin dalas...🥂👇

*AUTAR MARUBUTA CE*✍🏻👼🏻
🌹__________🌹_________🌹__________🌹_________🌹
_Faduwar wani tashin wani_
_Yau ake yi, gobe sai labarin_
_Burina Rayuwata, rubutuna dan masoyana_
_Cikawa da imani fatana_🤲🏼
<><><🌹><><><>🌹<><><>🌹<><><><>🌹<><><><><>🌹<>

Ku yi mini subscribe 🥰🥂🙏 Something big is coming....😌
https://youtube.com/@fatimaismailabdullahi?si=l3dnPNRKygK5lG4g

MARUBUCIYA ✍️
Na
Autar marubuta
________________________________________
Page 11&12

Misalin karfe 11 na safe , Adam har ya iso Kano, domin a halin da ake ciki yanzu yana zaune a falo, sun gaisa da Alaji da kowa da kowa .
Sai dai abincin da Karima ta aji ye masa , bai fara ci ba , kawai ruwa ya iya sha .
"Assalamualaikum."
Karima ta shigo da sallama, harara ta jefa masa tana cewa.
"Wai dan Allah ka ci abinci."
Murmushi Adam ya yi yana cewa.
"To ta ya zanci abinci, kin kawo mini kuma kin fita , tare zaki zo mu ci ."

Murmushi ita ma Karima tai masa tana cewa.
"Haba , sai ka ce a novel."

"Hhhhh ."
Adam ya yi dariya , sannan ya ce .
"Novels ko, ki ce kina karantawa ke ma ko kina rubutawa."
"A'a, wane ni , rubuta novels ai sai 'yan baiwa , fasihai marubuta."

Adam ya ce .
"Tom kema ai 'yar baiwa ce Sosai, kuma a gurare da dama ."

"Kin ga kanwata Hadiza ma marubuciya ce ."

Zunburo baki Karima ta yi kana ta ce .
"Ammma baka ta'ba fad'a min ba ."
"Tom ni dai gaskiya ka bani number ta."

Adam ya bude baki cikin mamaki yana cewa.
"To mene na sauri , naga dai kin kusa komawa kusa da ita , kuma bake za a ba number ta ba , ita za a ba taki ."

Ya gyara zama yana cigaba da cewa.
"Wato naji haushin dawowarsu Umma, naso sun yi zamansu a nan ."

Karima ta sake murmushi tare da fad'in.
"Nifa ka fara cin abinci sai sanyi yake yi."..

Ya ce .
"To masoyiya."
Tai murmushi a karo na ba adadi

Aunty Hauwa ce tai saurin fitowa harabar gida
Kana ta doshi kusa da wani mutum dogo yasha malum-malum
"Haba Baba ai daka iso ciki , amma ka tsaya anan."

Babban mutum din ya yi murmushi yana cewa.
"Haba Hauwa'u, ai ba saina shigo ba , sauri nake yi ma , saboda mun zo daurin aure garin naku ne , na ce bari na shigo naga 'yata."

Aunty Hauwa tai murmushi tare da fad'in.
"Allah sarki Baba ,yasu momy dasu Khalid."?
Ya maida mata da cewa.
"Suna nan alhamdulillah Hauwa'u, ya kuma hakuri da zama da hajjiya Aisha."?

Murmushi Aunty Hauwa ta fara yi , sannan ta ce .
"Baba ke nan."

Hakan yasa ya sake cewa.
"Tomm Hauwa'u , hajjiya Aisha ta gama takaba, kuma kema kin fita harkin cigaba da aiki ."

"To maganar gaskiya a matsayina na mahaifinki , bazan sa ido wannan muguwar matar ku cigaba da zama ba , duk abin da Alaji ya bari naki ne ,kuma zaman ta ya kare anan , tunda ba mutunci ta sani ba ."

Aunty Hauwa ta durkusar da kai kasa ta ce .
"Haka ne Baba ,sai dai akwai kadarorin Daddyna da yawa a gunta , ammma bana son a tayar da wannan maganar , sai na dawo daidai, domin har yanzu wannan mutuwar tana dawo mini sabuwa."

Ganin yadda kulla ke kokarin zubo mata ya sa shi cewa .
"Shi ke nan Hauwa'u, babu komai a cigaba da hakuri."
"Ni zan koma yanzu, domin an kusa daura auren .Ina abokiyar taki Salma."?

Aunty Hauwa ta ce .
"Tana ciki , ai har gida zamu zo ne ."
Ya ce .
"Tom shi ke nan, Allah ya kawo ku Hauwa."
Sannan ya fita , Aunty Hauwa tai ajiyar zuciya sannan ta koma ciki

Allah sarki Umma duk tabi ta rame, rashin Salma yana matukar dukanta
Tana zaune tsakar gida malam Aminu ya fito daga daki.

"Malam sannu da fitowa."
Ya ce ."yawwa sannu da gida , sai dai ya kamata ki cire damuwa a ranki , domin da ikon Allah Salma zata dawo ."
Umma ta ce.
"Tom malam idan zata dawo sai yaushe, wa ne yasan a wanne hali take yanzu, ai dole abin ya dame ni ."

Ta sake kallon mlm Aminu tana cewa.
"Tom malam ko zamu koma wajen malam Sharif mai almajirai ne ."

Malam Aminu ya yi ajiyar zuciya tare da fad'in.
"Karki manta , malamai suna ta addu'a, in Sha Allah Salma zata bayyana kawai ki cigaba da addu'a ke ma ."

"Sannan ya kamata kije gidansu Umar, an kawo kayan Karima."

Yana rufe baki Murja kanwar umman Salma ta rado sallama

Aunty Hauwa ce zaune cikin dakinta tana yin waya .
Salma ce ta shigo da sallama, kana ta zauna a kasa
Aunty Hauwa ta cigaba da wayarta tana cewa.
"To director in sha Allah ma London zasu tura mu , domin zamu fi jin dadi."
"Tom shi ke nan sai na jika ."

Sannan ta aje wayar tana murmushi da kallon Salma.
"Ina kwana Aunty."?
"Lafiya lau Salma ya jikin naki."?
Salma ta ce .
"Alhamdulillah naji sauki Aunty."

Sannan Aunty Hauwa ta ce
"Kina bacci dazu yayan babana ya zo yana tambayar ki ya zo daga Akko local government daurin aure."

Salma ta ce .
"Allah sarki har ya sanni ."?
Aunty Hauwa tai dariya ta ce .
"Eh mana , mahaifiyarsu daya da babana ."

Salma tai murmushi

Hakan yasa cewa da Aunty Hauwa.
"Salma kin bani labarin ki, a gaskiya yayan babanki bai kyauta ba , ta ya zai kore ki a gidansa kawai dan kin zama marainiya."

Wani dassss Salma taji a ranta , domin batason Aunty Hauwa tana tuno labarin data bata na karya da gaskiya.

Cikin yanayin tsoro Salma ta ce .
"Aunty wallahi ma irin yadda 'yan fashi suka tare mu , suka ringa kashe mutane shi ne yake cina ."

Ta fashe da kuka tana cewa.
"Allah sarki Salma, cann nabar gawarta aunty babu yadda na iya ."

Aunty Hauwa tasa hannunta kan kafadar Salma tana cewa.
"Ki yi hakuri Salma, in sha Allah komai ya wuce , sai dai yayan babanki duk sanda na samu lokaci zamu je gurin shi a Kano."

Salma tai murmushi mai yake kana ta sunkuyar da kai.
"Ammm Salma mene ne burinki , kin gama makaranta ne ."?
Salma taji tambayar a kunnuwanta

"Aunty na gama makaranta."
"Sai dai bani da burin da ya wuce na zama marubuciya."

Murmushi Aunty Hauwa tai tare da cewa .
"Masha Allah, buri mai kyau ke nan Salma, kina da baiwar rubutun ko zaki shiga makaranta ne ."?

Cikin jin dadin maganar Salma ta ce .
"Aunty basai nayi makaranta ba , domin lokuta da yawa nakan kirkiro labari."
."Ina son zama MARUBUCIYAR online, mai ilmantarwa Sosai."

Aunty Hauwa ta ce .
"Allah sarki Salmana karki damu."

Hadiza tana zaune rike da wayarta, kashe datar ta ke nan ta fito daga Facebook
Kana ta shiga app din da take rubutu, ba tare da bata lokaci ba ta fara rubutu kamar haka .

"Aure dadi
By
Hadiza RM

Paid book."

Ba tare da tasa kudin littafin ba ta cigaba da rubutu kamar haka.

"Page 67."

Mahaifiyarta ce ta katse ta da cewa .
"Hadiza ina bayi kina ta kirana lafiya."?
Chapter 5 · 0% Book details