← Book details Marubuciya Book One Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 19

Sashe 6

Marubuciya Book One Complete Hausa Novel · about 8 min read

Hadiza ta ce .
"Muna waya ne da amaryar Yaya Adam, na ce ki zo mu gaisa baki zo ba ."
Umman nata ta ce .
"Tom ni dai bari naje gidan wannan kawar tawa Saude, domin biki kwana kadan ya rage ."
Hadiza ta maida mata da cewa.
"Tom a dawo lafiya."
Ta maida kanta kasa ta cigaba da rubutun .
Autar marubuta

*SADAUKARWA GA Marubuta masu tsaftataccen alkalami*🥰✍️

Masu YouTube na baku damar karanta wannan Littafin 👌🙏kar a yi kuskuren canza mini duk abin da aka gani a wannan labarin ✍️

A yi hakuri masoya wanna lokacin ma babu editing❌
~Ba labari ba ne mai tsayi~

MARUBUCIYAR .....
Gubar rayuwata
Kawar karuwai
Dajin mutuwa
Fatima da zarah
Mahaukacin so
Dangin dalas...🥂👇

*AUTAR MARUBUTA CE*✍🏻👼🏻
🌹__________🌹_________🌹__________🌹_________🌹
_Faduwar wani tashin wani_
_Yau ake yi, gobe sai labarin_
_Burina Rayuwata, rubutuna dan masoyana_
_Cikawa da imani fatana_🤲🏼
<><><🌹><><><>🌹<><><>🌹<><><><>🌹<><><><><>🌹<>

Ku yi mini subscribe 🥰🥂🙏 Something big is coming....😌
https://youtube.com/@fatimaismailabdullahi?si=l3dnPNRKygK5lG4g

MARUBUCIYA ✍️
Na
Autar marubuta
________________________________________

Page 13 & 14

Ga kayan lefe nan kota ina birjik Dactor Adam ya yi kokari sosai .

Amarya Karima abin da ya bata mata rai kuwa , irin littattafan da ta ga Hadiza take rubutawa.
Sakamakon tana yawan ganin littafinta ana sharing din shi , sai dai sai yau tasan kanwar Adam ce .
Wato Hadiza RM , ta tara masoya sosai da tarin mabiya , an santa sosai tayi kaurin suna a rubuta littattafan batsa

Washe gari

Bayan Aunty Hawwa ta shirya tsaf domin tafiya gurin aiki , sai sukai sallama da Salma sanna ta wuce , Salma harda rakota falo
Anas dake zaune tare da mahaifiyarshi yake cewa.
"Aunty Hauwa a dawo lafiya, Allah ya tsare."
Ta maida masa da cewa.
"Ameen Anas."
Tana murmushi sannan ta wuce, tana farin cikin yadda ta ga Anas kwana biyu yana girmamata .

Haka Salma ta koma dakinta Anas yana binta da kallo

Hannu hajjiya Aisha ta sa ta makeshi tana cewa.
"Kai wanne sabon hauka ne ke damunka kwana biyu, sai shishshigewa Hauwa kake , karka ce mini waccen tsintacciyar yarinyar kake so."
Ta aje maganar tana nuna hanyar da Salma tabi

Dariya Anas ya yi yana cewa.
"Haba mommy, me zan yi da waccen yarinyar ."
"Kawai abin da nake so ki gane , Aunty Hauwa da kuma ke , ku zauna lafiya, saboda naji Aunty Hauwa tana cewa.
Zasu je Dubai su yi wata biyu ."
Sannan ya sake fuskaantar hajjiya Aisha yana cigaba da fad'in.
"Kin san wannan yayan baban nata , yana gaf da cewa mu tashi, to wallahi mommy mu yi biyayya mu ci abin da zamu ci , in ba haka ba mun zama sorry, mu zauna lafiya har lokacin da zata tafi Dubai ."

Hajjiya Aisha tai shiru tare da tunanin gagarumin shawarar da Anas ya kawo mata .

Salma kam tana kwance kan gado , domin kuwa babu aikin fari bare na baki , sai zama da kwanciya.
"Allah sarki Umma, dan Allah ki yafe mini ."
Salma tai maganar tare da tunanin gida .

Mikewa tai sakamakon yunwar da taji tana ji , ta fita zuwa kichin domin samo wani abu.
Sai dai gashi har yanzu Suwaiba yar aiki baza zo ba , ga rana tana yi sosai.
Hakan yasa Salma tai tunanin yin taliya jollop

Tukunya ta dauko tare maimakon ta dora sai ta tsaya cak
Tana kallon electric din.
Tunanin da take , ta ya ne zata kunnata , tana ganin irinta ne kawai a cikin films.

Ba zato taji an rike mata hannu tare da damke rigarta ta baya .
"Innalillahi."
Ta fad'a cikin tashin hankali da juyawa baya
"Kaii ne ."?
Ta cewa Anas
Wata shegiyar dariya ya yi yana cewa.
"Tom wa kike tunani ni ne ."

"Sake ni ."
Yaki sakinta

"Wallahi zan maka ihu ."
Ta sake fad'a
Wata dariya ya sheke da ita tare da cewa.
"Tom ai nan gidanmu ne , daga ni sai ke sai mommy."
"Kawai malama ki cire wannan rigar." Ya fad'a yana dora hannunsa a bayanta.
Bige hannunsa tai da nata tana jin tsoro jikinta na rawa
"Dan Allah ka yi hakuri."
Jin hakan yasa ya fincike hannun rigar Salma sai ji take
Feshhh
Rigar ta yage
Daidai karfinta ta wurgar dashi tasa gudu , ya mike da gudu ya bi bayanta .
Da sauri Salma Allah ya bata sa a ta shige dakinta ta kulle ,
Ta dafe kirjinta dake bugun dubu dubu , jikinta na rawa da durkusa kasa .
"Innalillahi wa innailaihir rajiun.
Wannan wacce irin masifa ce."?
Ta tambaya kanta cikin tashin hankali.

"Ki bude kofar nan , ki bude kofar nan ."
Taji muryarshi yana magana a kofar dakin , wani tsoron ne ya sake rufeta
Shiru tai masa kawai tana ta kakkarwa
"Shi ke nan, kere na yawo zabo na yawo ai ."
Jin hakan ya tambatar mata da ya tafi , sakamakon taji sautin takunsa .

Kuka Salma ta fashe dashi tana cewa.
"Innalillahi wa innailaihir rajiun."😭

Haka ta zauna a dakin nan ko bacci bata iya yi ba , ga yunwa tana ji har saida Aunty Hauwa ta dawo .
Koda Aunty Hauwa ta dawo bata fita falo ba , kawai dai ta bude kofar dakinta sannan ta cire wannan rigar."
"Assalamualaikum Salma."
Ta shigo rike da jakar aikinta a hannu
Murmushi Salma tai mata mai cike da matukar kewa kafin ta ce .
"Sannu da zuwa Aunty."
Aunty Hauwa ta zauna gefen gado tana cewa.
"Ya baki da lafiya ne Salma,na ga idonki ya yi ja ."

Murmushi na yake Salma ta kuma yi kana ta ce .
"Lafiya lau Aunty babu abin dake damuna."

Aunty Hauwa tai ajiyar zuciya tare da zuge wannan jaka tana cewa.
"Tom ai shi ke nan."

Waya ta zaro Hot 30i sabuwa a cikin gidanta tare da SMS din Glo da MTN
Sannan ta mikawa Salma
Wani dassss Salma taji a zuciyarta tasa hannun ta karba kamar mai jin tsoro.
Kafin ta ce komai Aunty Hauwa ta sake zaro wata bakar laptop karama ta sake mika mata
"Salma wannan naki ne ki yi amfani dasu saboda rubutun ki ."

Wasu hawaye ne suka zubowa Salma lokaci guda
Domin bata taba tsammanin irin wannan ba .
Cikin kuka ta ce .
"Bansan ta ya zan gode miki ba Aunty, Allah ya saka da gidan aljanna, Allah ya jikan iyaye , Allah yasa baki abin da kike nema , wallahi Aunty..."

Aunty Hauwa ta dakatar da ita da cewa.
"Na gode Salma, ki gode Allah, ammma ki yi shiru ki dena wannan kukan ."

Salma ta share hawaye tana sake kallon irin wannan kaya da suke hannunta .
Sannan Aunty Hauwa ta sake fad'in.
"In Sha Allah zuwa dare zan nuna miki yadda zaki rubutu a laptop din , ki yi saving, ki yi share."

"Sannan anjuma zamu je ai miki register na SMS."

Salma ta girgiza kai alamun tom domin ta kasa magana
Tana gama magana ta mike , ta sake kallon Salma tana cewa.
"Salma ki maida hankali kinji, sannan akwai wani marubuci Sir Abubakar Sadiq, shugaban kungiyar Lafazi writer's Association, zan had'a ki dashi , domin shiga kungiyar zai taimaka miki."

"Too Aunty."
Abin da ta iya fad'a ke nan, sai Aunty Hauwa ta fita .

Allah sarki Umman Salma addu'a ta rike gashi ta fara dangana da rashin Salma, domin a yanzu haka tana zaune tana sauraran redio

Hadiza ce kwance a tsakar gida tana danna waya .
Umman ta ce ta fito daga daki cikin masifa tana cewa.
"Wai ke babu inda zaki iya zuwa ne , kullum kina gida yau juma'a ma babu inda zaki."

Hadiza ta ce .
"Haba umma to ina zani , islamiyya dai yau babu ai."

Tana rufe baki wani yaro ya shigo yana cewa.
"Assalamualaikum, wai Hadiza ta zo in ji wani a cikin mota ."
Hadiza suka had'a ido da mahaifiyarta

Bayan korafin rashin ganin page 5 &6 da page 7&8 tom zan sashi a channel kadai.🥴

Autar marubuta
07040805269

*SADAUKARWA GA Marubuta masu tsaftataccen alkalami*🥰✍️

Masu YouTube na baku damar karanta wannan Littafin 👌🙏kar a yi kuskuren canza mini duk abin da aka gani a wannan labarin ✍️

A yi hakuri masoya wanna lokacin ma babu editing❌
~Ba labari ba ne mai tsayi~

MARUBUCIYAR .....
Gubar rayuwata
Kawar karuwai
Dajin mutuwa
Fatima da zarah
Mahaukacin so
Dangin dalas...🥂👇

*AUTAR MARUBUTA CE*✍🏻👼🏻
🌹__________🌹_________🌹__________🌹_________🌹
_Faduwar wani tashin wani_
_Yau ake yi, gobe sai labarin_
_Burina Rayuwata, rubutuna dan masoyana_
_Cikawa da imani fatana_🤲🏼
<><><🌹><><><>🌹<><><>🌹<><><><>🌹<><><><><>🌹<>

Ku yi mini subscribe 🥰🥂🙏 Something big is coming....😌
https://youtube.com/@fatimaismailabdullahi?si=l3dnPNRKygK5lG4g

MARUBUCIYA ✍️
Na
Autar Marubuta
_______________________________________
Page 15&16

"Tom ka ce tana zuwa."
Ummanta ta bawa yaron amsa , sannan ya fice
"Tashi ki je ."
Cewar Ummanta
Hadiza babu musu ta tashi da sauri ta fara shiryawa, wata abayarta tasa ruwan toka , sannan ta baza turare aka fita .

Cikin taku mai kyau ta fita waje ta hangi wani dogon saurayi fari kalar hutu, ya jingina jikin bakar motarshi yana danna waya .
Kamar kamshin turaren Hadiza ne ya dakeshi, ya juyo yana kallonta tare da cire gilashi.

Ganin taki karasowa inda yake , hakan yasa ya taka cikin taku na girma ya tsaya a gabanta .
"Assalamualaiki ma 'a bociyar kyau da kasaita."
Ya fad'a yana murmushi

Murmushi tai kamar baza ta amsa ba, sannan ta amsa .
Kana ya cigaba da cewa.
"Suna na Sultan yaron gidan Alaji Babawo."

Da sauri Hadiza ta sake kallo hadadden saurayin cikin mamaki .....
"Tom sannu da zuwa."
Cikin kunya da durkusar da kai ta fad'a.

"Wato Hadiza ina yawan ganinki zaki tafi islamiyya, da nai tambaya ake sanar mini ai baku dad'e da dawowa nan ba ."
Hadiza ta ce .
"Haka ne , amma dan Allah mene ya kawoka saboda Umma ta sani aiki a ciki."

Murmushi ya yi yana rausaya kai , kana ya ce .
"Tom babu damuwa Hadiza, idan kin amince zan dawo wani lokacin."

Ta ce .
"Babu damuwa."

Da gudu ta shige gida tana tsalle , ita ma Umma dake jiran shigowarta ta fara tambaya.
"Ya akai mene ya faru ."?....
Chapter 6 · 0% Book details