← Book details Marubuciya Book One Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 19

Sashe 16

Marubuciya Book One Complete Hausa Novel · about 8 min read

Karfe 8 suka shirya tsaf domin tafiya, tun a wannan lokacin Salma bata duba wayar taba , tana gama shiryawa ta jefata a cikin jaka , falon suka fito da akwati sun sha abaya ruwan toka iri daya .
Aunty Hauwa ta kalli Salma tana cewa.
"A'a har Yanzu Farida bata fito ba , kota tafi ne ."?
Dariya Salma tai tana cewa.
"Ta tafi fa tun dazu."
Sannan suka fito , Aunty Hauwa ta tsaya rufe kofa , ita kuma Salma take sanya akwati a cikin Booth, suna gamawa suka shiga , sai aka dau hanya , ni ko nace Allah ya tsare .
Karima kamar hawan jini zai kamata , ta yi harta gaji, amma Salma bata dauki waya ba, bata duba maganar ta a WhatsApp ba , ta yi mata text amma Salma shiru, hakan yasa Karima take tunanin to ko dai har an kashe Salma ne, ta yi tunanin sanar da Yaya Umar amma ta ce babu abin da zai iya akai.
Matukar tashin hankali Karima ke ciki, hakan yasa ta cigaba da kiran Salma voice call ko Allah zaisa hankalinta ya yo wajen .
Gidan biki kam ya fara cika, sai hayaniya ake .
Anan kam tafiya ta mika musu sosai, domin Aunty Hauwa sun kusa Kano, iskar da Salma take ji yasa ta take jin bacci , amma batai wannan bacci ba , kamar an tsikareta tasa hannu a jaka ta zaro wayar ta.
Tsaki taja ganin wata number 21 missed call, kawai ta bude data, nan ma karo ta ci da wannan number an yi sako ta WhatsApp sau 13
Kawai Salma taji gabanta ya fadi, tasa hannu ta bude wannan sakon .
"Aslm."
"Salma babu lafiya wallahi."
"Kina magana da yayarki Karima daga kano"
"Karki mamakin ta yadda akai na gano ki."
"Rayuwar ki na cikin hatsari karki shigo Kano, domin an sa a kashe ki ."
"Dan Allah yar uwata karki shigo Kano."
Abin da Salma ta gani ke nan gutsutstsuran sakonni harda voice call
Gabanta taji ya Fadi, ta sake komawa tana kara karanta wa.
"Tsaya tsaya Aunty Hauwa."
Cikin tashin hankali Salma ta fad'a, babu musu suna gaf da shiga Kano Aunty Hauwa taja gefe ta tsaya
"Mene ya faru Salma."?
Ta tambaya yayin da take cire facemask, har Salma ta had'a gumi
"Dubi dubi dubi Karima."
Aunty Hauwa ta aje numfashi tana cewa.
"Kimin yadda zan gane Salma."
Cikin sarawar ciwon kai ta mika mata wayar tana karantawa sannan ta Dora mata da cewa.
"Tun asuba take kirana Karima ce ita ce 'yar yayar babanmu."

"Wannan zancen kuwa Salma gaskiya ne,? amma kirata kiji." Ta mika mata wayar
Karima ganin Shigowar kiran Salma yasa zuciyarta wani irin bugun tsoro da fargaba, ganin koina ya tara mutane yasa ta shige lungunta ta shiga bandaki ta rufe, kafin ta d'aga kiran ya katse, yana sake shigowa tai saurin d'aga wayar tsabar farin ciki yayin da Karima taji muryar yar uwarta sai ga hawaye
"Salma ni ce , ni ce nan Karima." Cewar Karima yayin da Salma tasa wayar a spiker
"Karima ya kike , ina kika samo ni da har kika san wannan zancen."?
Cikin kasa kasa da murya Karima ta ce . "Duk ba lokacin wannan maganar bane yanzu Salma, kina ina ."?
Salma ta ce "Gamu mun kusa shiga Kano ."
Ajiyar zuciya Karima tai kafin ta ce . "Tom ina cikin tashin hankali Salma, kinsan Hadiza ko."?
Salma ta ce. "Wacce Hadiza Karima."?
"Hadiza RM marubuciya."
Dasss Salma taji a ranta , bayan Karima ta bata amsa.
"Eh Karima." Ta bata amsa jiki a sanyaye.
"Tom ita ta shirya yadda za a kasheki Salma da zarar kin shiga Kano daidai titin da ya shiga gidan wannan redion, akwai wani da babbar mota ta shirya kasheki Salma."
Salma ta kalli Aunty Hauwa cikin matukar rauni da tashin hankali, Karima ta cigaba da cewa. "Ba wasa nake miki ba Salma akwai hatsari a Shigowar ki Kano , akwai maganganu sosai."

Jin hakan yasa Salma cewa. "Tom ke Karima duk ina kika san wannan."?
"Ina auren yayanta Adam na yi aure Salma, gidanmu daya dasu , sun dawo sokkoto." Inji Karima
Girgiza kai Salma tai tana cewa. "Gaskiya Karima hankali na ya tashi , me nai mata haka ."?
Da saurin baki Karima ta ce . "Salma ina ce kin yi cuta, kika makance kika kuturce , to wallahi duk ita ce , duk ita ce ta aikata miki wannan bata kaunarki Salma."
Girgiza kai Salma ta sake yi cikin tsananin mamaki tana kallon Aunty Hauwa, duk sun kasa cewa komai tsabar mamaki da rudanin da suka shiga , hakan yasa Karima sake fad'in."hello Salma."
Salma tai ajiyar zuciya tana cewa. "Ina jinki Karima, abin ne ya bani mamaki, nasan cewa Hadiza bata sona , amma ban yi zatan abin yakai haka ba , karki damu Karima, na gode sosai yar uwata, zami waya ."
Karima ta ce ."Tom shi ke nan." Sai a lokacin Karima taji sanyi a zuciyarta da walwala

Salma ta kalli Aunty Hauwa da ta yi jimm tana cewa. "Aunty mene abin yi ."?
Kawai Aunty Hauwa ta ja motar suka cigaba da tafiya

Karima ba karamin farin ciki ta tsinci kanta ciki ba ,duk ta saki jiki sai annushuwa take , su Hadiza an sha kunshi an yi kyau, har wasu kawayen ta marubuta sun zo domin ta ya ta murnar aure, su Ruma ma an zo tun jiya aka yo Shigowar dare .

Gaban Salma matukar faduwa yake sosai ,haka suna cikin tafiya har suka hau kan wannan titin da zai kaisu gidan wannan redionqq,ql1qadi , hakan yasa Aunty Hauwa ta tsaya domin karta take shi, babu wanda ya fita cikinsu har wannan tsohon ya mike da sanda da robarshi ya matso kusa da murfin kofar tasu yana fad'in.
"A taimaka mana da na Allah da annabi, a taimaka mana."

MARUBUCIYA ✍️
Na
Autar marubuta
________________________________________

Page 39&40

Wani iri Salma taji irin yadda wannan tsohon yake kallonta, juyawar da zatai ta ga wata babbar mota ta yo kansu gadan gadan
Ihu Salma tasa tana cewa. "Wayyo Aunty Hauwa gata nan."
Sai ji suke "Tau tau tau 'dau ."
Karar bindiga ana harbata 'yan sanda ne da farin kaya .
Jin hakan yasa wannan mai shigar tsofaffi ya ke ce da gudu yana cillar da sandar, shima mai tuka wannan babbar mota ya diro , Allah ya bawa wani dan sanda damar cafke shi , ya kaishi kasa yana bangare shi tare da sa maka ankwa.
Salma matukar rudewa ta yi jin wannan karar ta bindiga, karo na biyu ke nan data ta'ba jin irin wannan, sai da Aunty Hauwa ta nutsar da ita sannan ta dawo hayyacinta, domin tana ganin kamar za a kuma irin lokacin da zata je Zaria, haka wannan 'yan sanda suka tafi da shi , duk da cewa wasu sunbi dayan amma basu samu damar kamashi ba .

Haka su Aunty Hauwa suka isa gidan wannan redion, sai dai Salma duk ba a daidai take ba , har saida aka zubo musu shayi ,kana ta ga fuskoki kala kala suna kawo mata gaisuwa sannan ta fara nutsuwa

Bayan wannan driver ya ci duka sosai , ya fara basu hakuri.
Sun yi masa jina- jina yaji jiki. "Zaka fad'a mini me ne ne yasa zaka kashe mutane har guda biyu ko kuwa , daman ka saba kashewa ko." Cewar wani kofur din yan sanda dake rike da kulki .
"Wallahi yalla6ai ba haka bane , motar ma ba tawa ba ce dan Allah ku yi mini rai." Jin haka yasa wannan kofur cigaba da lafka masa sanda ta koina.
Dpo ne ya tsaya daidai bakin kantar yana cewa'
"Kai kofur sani , sashi a bakin daki ."
"Okaysir ." Cewar kofur
Ihu wannan matashi ya saka yana cewa."wallahi yalla6ai zan fadi gaskiya, ku yi mini rai karku rufe ni ."
Dpo ya ce .
"Muna sauraran ka ."
Yana haki kamar zai shid'e ya ke cewa.
"Wallahi dubu dari biyu aka bamu, aka bamu hoton yarinyar da zamu kashe, motar ba tawa ba ce yalla6ai, mun dade a gurin muna jiransu, hakan yasa dayan yayi shigar tsofaffi domin samun damar lekawa kowanne mota , idan yaga akwai wacce aka bamu hotonta sai ya mini a lama na taho na danne motar , daga nan sai mu gudu." Cikin jigata ya karasa maganar
"Wa ne ne ya saku aikin ."? Cewar DPO
" Wallahi yalla6ai Daga sokkoto ne , sunanta Hadiza." Inji shi
Dpo ya kalli kofur sani yana cewa. "Ka dauki bayanansa yanzu a kawo mini officer."
Dpo ya wuce ciki, yayin da wannan yake ihu yana fad'in.
"Yalla6ai dan Allah ka ce su dena dukana, wallahi ban taba kashe rai ba ." Kofur sani ya ce ."Yi mini shiru ."
DPO yana shiga office, babu dadewa kofur sani ya Kai masa wannan bayanai , ganin hakan yasa DPO yin waya ga abokan aikinsu zuwa Sokkoto birnin shehu .

Misalin karfe 1 mai tattaunawar mai suna Muhammad Ayuba ya fara hira da Salma, babu boyeboye Salma ta bayyana cikakken sunanta da tarihinta
Tattaunawar ta yi nisa har ta zo gangara, kallon Salma ya yi yana cewa. "To hajjiya Salma, akwai maganar da take yawo cewa. Kina daga cikin sahun marubuta matasa masu shahara da kuma arziki, alhalin baki dade cikin duniyar marubuta ba ."

Murmushi Salma tai sannan ta ce . "To ai ita shahara ko daukaka daga Allah ce, ba boka babu Malam, kuma arziki na kasuwanci ne , duk da cewa ina samun wani abu daga rubutu, to amma bai kai kasuwanci na ba ." Ta aje maganar tana kallon shi, hakan ya tabbatar masa ta gama bashi amsa , ya dubi takardar dake hannunshi , kana ya d'ago yana cewa. "To autar marubuta mun saurari, kalubalenki kafin ki kawo wannan matsayi, mun ji kuma tarin nasarori da jeren littattafan ki ."
"Wacce shawara zaki bawa marubuta masu tasowa da kuma wanda suke cikin rubutu ka'in dana 'in."
Ajiyar zuciya Salma tai tana gyara zaman gyalen abayarta
Sannan ta fara cewa."Tom har ila lau dai shawarar guda daya ce zuwa biyu."
Chapter 16 · 0% Book details