← Book details Marubuciya Book One Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 19

Sashe 17

Marubuciya Book One Complete Hausa Novel · about 4 min read

"Marubuta su ji tsoron Allah, su rubuta abin da zai amfani al'umma, kar si hassada a junansu , su jayo kananun marubuta a jika , tabbas yin hakan zai kawo babban cigaba."
Muhammad Ayuba ya ce .
"Tom ko mu dakata ne , anjuma sai mu cigaba, domin ba kai tsaye bane ."
"A'a haba dai a cigaba ai kadan ya rage ." Cewar Salma
Dariya Muhammad Ayuba ya yi , sannan ya ce ."Okay wa ne ya ce miki sauran kadan , ki gaji ke nan."
Salma tai dariya
Hankalin shi ya mayar ga aikin yana cewa." Tom yanzu zamu amsa sakonni masoyanki."

"Wannan take cewa , gaskiya Autar marubuta Allah ya kara daukaka da nisan kwana muna tare da ke . Daga Basira Hudu
Salma ta ce . "Amin summa Amin ina godiya."
Sannan ya kuma karanto wani sakon yana cewa.
"Aslm, nima marubuciya ce , dan Allah Autar mu, ki bamu shawarar yadda zamu magance marubutan batsa da masu tura mana abin banza a cikin group, saboda sai mun sakankance ake tura mana abin da bai dace ba na gode."

Da sauri Salma ta ce .
"Wannan abu ne da kullum nake bawa marubuta shawara, da farko dole ya zama kanmu yana hade ne , duk marubuciyar batsa ku hana ake sako muku novels dinta cikin group,duk wanda ya sako ku cireshi koda ita ce , sannan zancen masu tura abin batsa cikin group."
"Gaskiya wannan ruwan dare ne cikin group din marubuta, Allah ya shirya masu yi, abin da zaku yi anan shi ne , ba wai iya marubuta ba , duk inda kuka ga an tura irin wannan, sai ku yi saving number wannan wanda ya tura din, Tom da zarar ka ganshi cikin group kai maza kayi reporting admin su cire shi, su ma marubuta idan sun yi saving number irin wannan mutanen, to da zarar ya turo request a group zai shigo,sai ai cancel din shi kar a yi approval nashi ." "Idan ta kama su ringa saving numbar tasu irin daya , kamar kawai si yi saving da A, ko Y koma mene, to duk inda ka gansu zaka ganesu. Domin masu wannan halin kullum yawa suke karawa."
"To Ina tabbatar muku idan kun dauki wannan shawarar wannan matsalar ta kau sai dai wata ."

Sokkoto
Yanzu misalin karfe 1:47, an taru sosai a cikin masallaci, wakilin Hadiza ake jira domin a daura aure,
Nan gidansu Amarya kuwa, sai farin ciki ake ana ta hidima da Kai kawo, su Umman Hadiza an sha kyau sosai uwar Amarya, ana ta yin hotuna da 'yan uwa , motar yan sanda ce ta tsaya a kofar gidan, kana yan sanda uku suka fito, macen cikinsu ce tasa kai, Kai tsaye cikin gidan , hakan yasa 'yan uwa aka fara binta da kallo.

"Ina Hadiza."?
Cewar 'yar sandar da hausa bata wadaci bakinta ba
"Gata can amaryar ." Cewar wata mata , ganin wannan 'yar sandar yasa Karima isowa wajejen gurin da sauri .
Bayan ta ishe Hadiza da ta ci kwalliya ta ce . "Ki wu ce muje zuwa office akwai tambayoyi da zaki amsa ."
'yar sandar ta sake magana
Hankalin kowa ya yo wajen caaaa ana mamakin meke faruwa
"Kamar ya na wuce , bikina fa ake babu inda zani mene nai muku , ." Inji Hadiza
Umman Hadiza ce dake dakinta ta fito da sauri tana cewa. "Ina zata je , ranar auren nata ma sai an yi mata bakin ciki da hassada , to wallahi Allah yafi karfinku ."
Jin hakan yasa wannan 'yar sandar daba bahaushiya ba fad'in.
"Babu ruwanmu da biki, zami aikinmu ne , idan baza ki taho ba zami sa miki karfi , muna da yawa a waje ."
Hankalin Hadiza taji ya tashi sosai

MARUBUCIYA ✍️
Na
Autar marubuta
________________________________________

Page 41&42

Bayan Salma sun gama wannan tattaunawar, har abinci suka samu suka ci, sukai sallah, sannan suka hau mota.
Ganin Aunty Hauwa ta murza kan mota sun jiya yasa Salma cewa.
"Aunty wannan titin ai bazai kai mu Tarauni ba ."
Aunty Hauwa ta kalleta tana cewa.
"Eh zamu je station ne , sun kira mu , domin an taho da Hadiza daga sokkoto." Salma ta aje numfashi mai nauyi , Aunty Hauwa ta cigaba da tafiya.
Chapter 17 · 0% Book details