← Book details Marubuciya Book One Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 19

Sashe 2

Marubuciya Book One Complete Hausa Novel · about 7 min read

A firgice ta aje wayar tare da tula mata kaya tana dariya 😂
"Kaiiiiiiiiiiii Husna wallahi littafin nan abin tausayi, gaskiya marubuta suna kokari, ai wallahi komai nacin baba yau saina gama karanta shi ."
Dariya suka sake fashewa da ita , sannan suka fita tare domin yi wa baban nasu sannu da zuwa.

Salma kamar hankalinta ya fita ta yanke wannan d'anyen hukunci na barin gida , kayanta ta tattara ta zuba a wata karamar bakko , sannan ta fara sanya ido, mahaifiyarta harta kwanta , shima Umar haka sai dai duk basi bacci ba , kuma ba a rufe gida ba sakamakon malam Aminu bai shigo ba .

A hankali ta dauko wannan bakko ta jawo dakin , daidai sanda ta hangi mahaifiyarta na kwance ta ji kuka ya sake rufeta , haka tai sauri ta wuce ta kofar dakin Umar ta fita waje tana kuka , tana kuka zuciyarta na sa'ka mata tana shirin yin babban kuskure, wannan ba shi ne hanyar cikin burinta ba , ammma wata zuciyar na fad'a mata aka sin haka , hakan yasa kawai tai gaba ta nufi tasha tana kuka .
Babu jimawa mlm Aminu ya dawo , aiko babu wata -wata ya rufe gida .

Cikin tasha take tafiya tana kuka tana waige -waige
"Salma Ina zuwa lafiya kuwa."?
Da firgice ta juya don ganin me magana
Kalifa ne saurayinta
"Ina zaki , ke da bakya fitowa da dare."

Salma ta share hawaye tana cewa.
"Kalifa ka rantan dubu biyar in sha Allah zan biyaka ."

Dariya Kalifa ya yi yana cewa.
"Haba sweetheart, ai kinfi karfin rance a guri na , kina da kyau da hankali."

"Zan baki dubu 10 Salma, amma idan kina so ."
"Ina so mana."
Ta fada cikin kuka
"Tom ki dena kuka ki zo muje dakina minti biyar zaki a can zan baki dubu 10."

Wani abu Salma taji ya tokare mata zuciya dajin wannan batu daga bakin Kalifa , ashe tabbas gaskiya ake fada a kanshi ya lalata yan mata da yawa .
Abin da yazo kanta ke nan.

Ba tare da ta ce Komai ba kawai ta juya zata tafi.
Jawo mata hijabi ya yi yana cewa.
"Haba Salma karki wasa da damarki ."

Juyowa tai cikin sabon bakin ciki da takaici ta falla masa mari , bata san lokacin data d'uro wata ashar ba tare da cewa.
"Wallahi zan maka ihu anan gurin banza jahili mahaukaci wawa dabba ."

Kawai ta dauki kayanta tai gaba
Koda taje tasha bata san inda zata ba , kuka ta tsaya kawai tana yi , zuciyar ta na saka mata ta koma gida

"Sister ina zaki ."?
Wata yarinya da bata wuce sa'ar ta ba ta tsaya gaban ta tare da wani saurayi tana tambaya, Salma tai shiru kafin ta ce .
"Unguwa zani ."
Ta fada kamar tanajin tsoro .
"Ki dena kuka komai tsanani yana tare da sauki ki yi hakuri."
"Ki zo ga mota yanzu zata tashi zaria zamu ."

Salma ta bi bayansu ta shige motar , ba tare da tunanin babu Wanda ta sani a zaria ba .
Bayan sun zazzauna mota ta cika ta fara tafiya Salma ta cigaba da kuka tana shashsheka .

Hakan yasa wannan matashiyar ta kalli wannan kyakykyawan saurayi da suke matukar kama da juna , murmushi ya yi mata kawai , hakan yasa ta dora hannu jikin Salma tana cewa
"Sister."
Salma ta d'ago cikin hawaye
"Ki yi hakuri dan Allah."

Murmushi Salma tai tare da share hawaye tana cewa.
"Na gode mene sunanki ."
Ita ma tai murmushi tare da fad'in ."Suna na Salma, ga yanana can Yaya Umar."

Salma bata san lokacin da tai dariya ba tana cewa.
"Abin mamaki, nima suna na Salma kuma ina da Yaya Umar."

Ta karasa maganar tana kallon wancen Umar din .

Murmushi d'ayar Salman tai tana cewa.
"Masha Allah, mu zamu tafi zaria ne , saboda munzo ziyara nan kuma ga shi mun yi dare."

Salma ta ce .
"Uhmm Allah ya sauke mu lafiya ."

Sauran mutanen motar sun yi shiru kowa da abin da yake sakawa a ransa, babu gida gaba babu baya , sawu na motoci da mutane duk ya dauke a wannan hanya .

Lokacin driver yaji mutum ya fado gaban motarsa , wanda kowa Saida ya firgita , yana shirin tsayawa, wani mutum ya ce .
"Karka tsaya wallahi hanyar nan bata da kyau."
Driver ya ce .
"Innalillahi mutum ne fa na kad'e ."
Yayi sauri ya fito , kowa hankalinshi ya tashi , mutumin da ya kade jikinsa duk jini yana cewa.
"Kai sauri kaja motarka ku tafi , yan bindiga dadi ne suka biyo ni , kai sauri kaja motar ku bar nan ."

Cikin rudewa driver ya ce .
"Taso mu tafi bama barka anan ba ."
Yana zuwa kusa dashi sai karar bindiga suka ji ta koina

Sai ihu da salati , mutane suka fito daga motar sai gudu
Sun yi wa driver da wannan mutumin kaca-kaca da harbi
Salma da gudu suka nufi wata hanya su biyar cikin tashin hankali suna gudu .
Sai ji sukai a bude wuta a ta wajen su juyawar da Salma zatai taga duk an zubar da su kasa , sai ita kadai a tsaye
Ta fashe da kuka ganin yadda wannan Salman take rike da gawar yayanta Umar an fasa masa kai .

Yan bindigar ne suka sake biyosu suna harbi , da kyar Salma Aminu ta rarrashi Salma ta taso tabar gawar yayanta Umar agun suka cigaba da gudu suna faduwa suna kuka

Gudu suke sosai basu san inda suke sa kafarsu ba , daji ne ga duhu

Haka har asuba tai musu a wannan gurin ,jikin dayar Salma duk yayi rauni haka ta fadi a wannan wajen .

Babu gida gaba babu gida baya , kurgurmin daji ne sai bishiyu , hakan yasa Salma ta tsaya gurin dayar Salman tana kokarin tashinta zaune .
Bayan ta tasheta ta jingina ta jikin wata bishiya tana wani irin nishi tana cewa.
"Mun yi tafiya Sosai sister, daga nan babu inda zan kara , sai dai nasan mun tserewa wannan yan bindigar mun yi musu nisa."

Tana yi tana wani irin nishi idanunta sun yi jaaa
Salma kawai ta fashe da kuka mai matukar gwanin ban tausayi.
'Dayar Salman ta cigaba da cewa .
"Sister Allah yana tare da ke , ammma ni mutuwa zan yi a wannan gurin , sun kashe Yaya Umar a gabana , sun kashe mutane da yawa, Allah ya hada mu a aljanna."

Cikin tashin hankali da sabon kuka Salma Aminu ta fara cewa.
"A'a Salma, ba mutuwa zaki ba , bazan barki anan gurin ba , mu karasa gaba ko zamu samu wani rafi mai ruwa , zaki dawo daidai."😭

Kawai shiru Salman tai domin irin jigatar da tai da irin abin da take ji yasa bata iya magana sai kokarin magana da hannu tana nuna tabar ta a gurin ta tafi.
"Salma bazan barki anan gurin ba , ki karfafa gwiwarki Allah zai taimaka mana."
Tai maganar tare da kokarin cicci'bata a bayanta .
"Timm."
Salma taji ta fado kasa , da sauri ta juyo ta durkusa gabanta
Tana juyota ta ga ko motsi bata yi
"Salmaaa."😭
Ta fada cikin murya mai kara da kuka
"Salma."😭
"Haba dan Allah, innalillahi wa innailaihir rajiun."
Salma ta fad'a tana jijjigata

Kuka ta kifa tana yi sosai ita ma kamar ranta zai fita a wannan lokacin
Ba karamin tashin hankali Salma ta shiga ba ganinta a wannan yanayi , haka rana ta fara fitowa mai zafi ta fara dukanta .

Yadda taji matukar yunwa da kasala yasa ta mike tsaye domin tafiya gaba ko Allah zai had'a ta da wata halittar
Ta juyo ta kalli Salma dake kwance matsayin gawa ta rushe da kuka tana cewa.
"Innalillahi wa innailaihir rajiun, ki yafe mini Salma, wallahi kafafuna basa daukata nima , da saina dauke gawarki a wannan wajen."
😭
"Ki yafe mini , ki yi hakuri."😭

Ta juya cikin tashin hankali na kuka tana d'ingishi ta fara tafiya tana juyowa tana kallon gawarta .

Autar marubuta
07040805269
WhatsApp only

*MARUBUCIYA* ✍️

Na
Autar marubuta

____________________________________________

Page 5&6

Haka Salma ta cigaba da tafiya cikin matukar wahala da tsoron wannan dajin , tana tafiya tana duban hanya tana juyo bayanta, har tai nisa sosai ta dena ganin gawar Salma, lokacin da taji matukar yunwa ne yasa ta sake fad'a wa cikin wani dajin, sai dai babu wata itaciya da ta gani wacce ake ci , sai wata bishiyar goruba , d'anya shakaf , ganin ta yi mata tsayi yasa ta zauna kasan bishiyar tana tunanin daga nan ina zata je , babu zato taji abu yana bin bayanta, da sauri tasa hannu ta kamoshi cikin tsoro tana yar'bar dashi .
A million ta mike tasa gudu ganin koren mucijin data kamo da hannunta, ta sake danna kanta cikin dajin .
Chapter 2 · 0% Book details