← Book details Marubuciya Book One Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 19

Sashe 19

Marubuciya Book One Complete Hausa Novel · about 5 min read

A social media kuwa babu abin dake yawo kamar irin yadda marubuciya Hadiza RM ta yi yunkurin kashe Autar marubuta, abin da yake yawo ke nan a duk inda ka shiga , sai dai a halin yanzu an tura Hadiza zuwa kotu, Umman Hadiza tana cikin matukar damuwa, domin Karima babu tsoro ta bayyana cewa wannan Autar marubuta da Hadiza tai yunkurin kashe wa , to 'yar uwarta ce , shi kanshi Adam ya yi mamakin irin yadda bata ta'ba bashi labarinta ba.
Umman Hadiza kuwa tsanar Karima ta yi sosai, domin yanzu bata son jinin wannan Autar marubutar ,
Da safe Karima ta shirya tsaf domin tafiya Kano, nan Umma babu abin da ta iya cewa da ita , domin asan samun Umma, Adam ya saki Karima, sai dai bazai iya hakan ba , wai a hakan ma Umma tana yin haka ne ba tare da tasan Karima ce ta yi sanadin tonon asirin Hadiza ba , da abin yafi haka kam.

Da safe suna gama karyawa sai ga Alaji Yusuf nan, nan ya zo gurin Salma suka gaisa harda bata hakuri, domin tun daga rasuwar kanin shi yayi sanyi sosai, har albarka ya sa mata sannan ya koma .
"Salma yau zamu je Bauchi fa , domin babu lokaci." Cewar Aunty Hauwa
Umma ta ce .
"Yau kuma daga zuwa ."
Salma tai murmushi ta ce . "Eh Umma ai Aunty Hauwa bata da lokaci sosai, wannan ma sa'a aka ci ya zo kan ga'ba ."
Salma ta kalli Yaya Umar.
"Tare da kai fa zamu tafi."
Zaro idanu ya yi yana cewa.
"Tare dani kuma , yau ina da aiki fa ."
Harararshi Salma tai tana cewa ."To wallahi sai kaje babu ruwanmu da aikinka."
"To ko dai an samu wani ne acan, sai a fadan na nemi daidai ni." Inji Umar
Dariya Umma da Aunty Hauwa suka yi , nan sukai ta wasa da dariyar su, har lokaci ya ja , sannan suka tashi sukai wanka , Aunty Hauwa da Salma suka hau mota daya , sannan Umar yaja motar da za a kai wa Aliyuu
Sun isa Bauchi cikin farin ciki da walwala, nan suka sauka gidan Aliyuu, aiko Baba Laure ma tana wannan gida, sakamakon Fatima ta haifi na miji kwana biyu yau ke nan, Salma tai matukar farin ciki, haka ita ma Baba Laure sai murna take da ganin Salma, aikawa akai aka kira Aliyuu can gurin shayi da burodi, mamaki ne ya ishe shi da ganin Salma a wannan lokacin, nan Aunty Hauwa tai ta koda Salma gabansu tana tabbatar musu wannan makauniyar tasu ita ce Autar marubuta fa, farin ciki da mamaki ya kama kowanne a cikinsu, haka aka sha wasa da dariya har sukai canjan numbobinsu, haka Fatima ta roki alfarmar Salma ta yafe mata saboda irin abubuwa data aikata mata , Salma ta ce babu komai.
Da suka tashi tafiya Aunty Hauwa ta bawa Fatima dubu 50 asai wa jariri fanfas, sannan ta sake bawa Baba Laure dubu 50 ta ce ta yi hakuri a haka .
Sannan suka rankaya suka fito waje domin rakasu, nan ne Salma ta mikawa Aliyuu mukullin wannan mota , sannan take tabbatar wa da Baba Laure hajjin bana tare da ita za ai, murna kam ba a cewa komai, duk sun kasa zaune sun kasa tsaye ganin wannan arziki a gidansu, bari Baba Laure da taji zata hau jirgi a je ga ....
Haka sukai musu addu'a suka hau mota suka juyo Kano

Anan kuwa umman Hadiza ta samu ta kawowa Hadiza ziyara
Tana zaune tana ta jira domin ganin an fito da ita . Da gudu Hadiza ta nufi Umma tana kuka kafin ka ce komai ita ma Umma ta dau kuka
"Innalillahi wa innailaihir rajiun, Umma kinga yadda duniya take yi dani, sultan ba ya nan , kotu yanke mini hukuncin zama a gidan yari za tai , shi ke nan rayuwa ta ta lalace Umma, innalillahi wa innailaihir rajiun."
Haka Hadiza tai ta sunbatu Umma tana kuka , Allah yasa mu dace , Allah ka raba mu da sharrin zuciya.
Karima harta iso Kano da dare , aiko tana zuwa gidansu, ta taho tarauni gidansu Salma
Nan su Salma suna dawowa suka tarar da Karima, aiko aka sha hira sosai , irin yadda Karima ta gano Salma duk ta sanar da ita , farin ciki dai yau cikinsa aka kwana
Har Salma take cewa da Umar tana son za ai rijiya ko masallaci domin mahaifinta, ya ce mata ai shi ke nan
Da safe suna karyawa Aunty Hauwa tai wanka ta shirya
"Tom Salma ni zan koma ." Cewar Aunty Hauwa
Murmushi Salma tai tana cewa."Babu dadewa zan biyoki kuwa Auntyna , gaskiya zan yi kewarki ."
Aunty Hauwa ita ma tai murmushi tare da fad'in."Tom ina nan Ina jira , amma da Allah ki amsa tambayar da akai miki zuwa BBC."
Salma ta ce . "In sha Allahu Aunty duk zanje har ma da gidan TV da suka gayyace ni ."
Aunty ta ce .
"Tom shi ke nan sai na jiki ."
Nan ta shige mota, suna tai mata addu'a, Salma harda kuka sannan Aunty Hauwa ta wuce Gombe.
Bayan kwana biyu
Salma tana zaune tana rubutu , sai ga Umar ya shigo
Salma ta kalleshi tana murmushi
"Ni fa na zo na hanaki rubutu, domin soyayya nake so mu yi ." Cewar Umar
Ajiyar zuciya Salma tai tana cewa.
"Tom zaka ga soyayya ni Gombe ma zan tafi gobe , domin shagona da Auntyna." Inji Salma
Umar ya jefa mata wani kallo yana cewa."To yaushe ne auren namu."?
Salma ta kifa laptop cikin kunya tana durkusar da kai .

Alhamdulillah masu sauraro, nan na kawo karshen Littafina mai suna MARUBUCIYA ✍️
Wanda ni Autar marubuta na rubuta , Allah ya bamu ikon ganin kuskureen mu , abin da ba daidai ba Allah ya ganar damu, godiya ga d'imbin masoyana a duk inda suke , sai Allah ya sake had'a mu cikin wani sabon labarin ✍️.
Bissalam.
Chapter 19 · 0% Book details