Sashe 12
Marubuciya Book One Complete Hausa Novel · about 8 min read
Rassss Salma taji a zuciyarta
"To mu kaita mana Baba."
Da sauri Baba ta kalleshi.
"Kai baka da hankali ina muka ga kudi , yana karbar kudade sosai."
Salma ta sauke ajiyar zuciya yayin da shima Aliyuu ya zube tashi
"To haka zamu barta yanzu ke nan Baba."?
Ya tambaya cikin damuwa
Kafin Baba Laure ta ce komai Fatima ta ce .
"To ai naga cewa tai Auntinta wata biyu zatai ta dawo, yanzu gashi har wata uku sai ta koma garinsu ."
Aliyuu ya jefawa matarshi wani kallo
Baba ce tai magana da fad'in.
"Tom babu inda zata , mu zamu nemi kudin gurin yan uwa da abokan arziki ai mata magani, yaushe kika zama mara tausayi Fatima, ke yanzu ace ke ce cikin wannna halin a dauke ki akaiwa yan uwanki dadi zasu ji , bari wannan yarinyar da bata da gata sai Allah."
Salma tai kasa da kai tare da hawaye
Aliyuu ya yi murmushi ya ce .
"Allah yaja da ranki uwata , Allah sa aljanna makoma ."
Baba Laure ta ce .
"Amin dan albarka ta shi ka tafi wajen nemanka , nima zan fara samo wani abin."
Aliyuu ya ce ."To Baba nima akwai wasu sittiru na masu kyau, zan kaiwa Salisu mai dinki ya siyar dasu , a yi a had'a kudin nan ."
Baba tai murmushi tare da fad'in.
"Yaron kirki ka gado mahaifinka, Allah ya jikanshi da rahma, Allah ya yi wa nemanka albarka."
Ya amsa da."Amin babata saina dawo."
Sannan ya wuce ya tafi
Sokkoto ❤️
Karima ce zaune cikin falonta, yau kimanin wata uku da kwanaki bata ganin posting Littafin wannan marubuciya, har number ta ta dauka ta ce ."Aslm."
Ammma har yau babu alamun hawanta, sau da yawa tana gwada kiran number ta, amma bata samu, tana tunanin ko a wanne irin hali take ciki Allah masani .
"Salamu alaikum Aunty."
Hadiza ta shigo ta zauna a kujerar kusa da ita , da sauri da firgita Karima ta tashi , sannan tai ajiyar zuciya
"Wai Aunty tsoro na baki ne haba ."
Murmushi Karima tai tana cewa.
"Eh mana bansan kin shigo ba ."
Dariya Hadiza tai , sannan Karima ta zame ta zauna a kasa tana dafa kirjinta, domin ita Karima yanzu tana matukar jin tsoron Umma da Hadiza, hatta hira bata sakewa su yi kamar daah.
Wayarta Hadiza ta cigaba da dannawa
Sai dariya take ganin irin yadda ake tambayar cigaban Littafin HIJIRA na Autar marubuta, mutane ba adadi
"Aunty Karima sauran wata 4 fa biki, dazu sultan yake cewa na gashsheki, kin ga yadda ya kara kyauu kuwa, gaskiya Germany ta yi, ya ce sai mun yi aure zamu koma tare ."
Murmushin yake Karima tai tana cewa.
"Tom Allah ya kaimu musha biki."
Kano State
Tarauni
Anan kuwa umman Salma ana zaune ana hutawa, an gyara gida , gida yayi matukar kyau sosai , an sha kyau an gyara koina an yi fenti an sa tayil, har babbar waya Umar ya saiwa Umma, suturu kuwa kala kala alhamdulillah.
Umma ganin karfe 4 ta yi yasa ta mike ta dauko redionta , kana ta kamo daya daga cikin tashar da take yawon sauran.
"Assalamualaikum masu saurare yau zamu fara kawo muku sabon Littafi, duk da cewa ba sabon Littafi bane a gurin mutanen da sukai following YouTube channel din mu , aje ayi subscribe a danna mata kararrawa mun gode." Kana aka saki wani sauti mai taushi
Umma tana zaune tana kasa kunne domin jin an fara wannan labarin, tsabar kewar Salma yasa Umma ta koyi sauraran novel, saboda Salma kullum sai tasa wannan redio ta saurara, daga lokacin tafiyar Salma zuwa yanzu taji su da dama , kuma taji tabbas akwai Basira da tarin nasihohi da tarbiya harda zaman ta kewa da ake dauka , ba kamar yadda Alaji Yusuf yayan baban Salma ya fahimci marubuta ba .
"Fatima da zarah.
Mallakar Autar marubuta."
"Kashi na daya ."
Kan Umma ne ya sara mata, har saida tasa hannu ta rike , cikin wannna yanayin
Umma ta cigaba da saurarar labarin da aka fara shi da kasar saudiya.
"SAUDIYA."
"Dawowarsu ke nan daga asubiti , Najib da Ahmad tare da mahaifiyar su da bata da lafiya, eh tabbas wannan iyalin kana iya ganin tsantsar soyyayar mahaifiyarsu..."
Umma ta kasa kasa kunne don jin yadda wannan labarin zai kasance....
Autar marubuta 🥰
MARUBUCIYA ✍️
Na
Autar marubuta
________________________________________
Page 29&30
Baba Laure ce zaune tsakar gida tana yi wa Salma kitso, zanen hausa take rangada mata a kanta mai matukar kyau, gefe guda kuma ga Fatima can tana iza wuta
Aliyuu ne ya shigo yana yin sallama, murmushi ya jefawa mahaifiyarshi da cewa.
"Babata ta kaina." Kana idanunsa suka kai kan Salma idanunta sama kamar shi take kallo, sai dai bata iya ganin komai.
Shagala ya yi da kallon Salma irin yadda wannan kitso yayi matukar fito da kyawunta "Allah ya yi halitta, kodai kyan wannan yarinyar ne yasa akai mata wannan sihiri."
Abin da Aliyuu yake fad'a ke nan a zuciyarshi, ganin yadda ya shagala da kallon Salma yasa Fatima ta taso ta bangaje shi ta wuce tana harararshi.
A wannan lokacin ya dawo hayyacinsa yana murmushin ya'ke
"Tom mene ne ya dawo da kai ne ."?
Cewar Baba Laure, saida ya sosa 'keya sannan ya iya cewa.
"Baba daman kawu Tanimu ne ya kirani , ya ce ya turo dubu 20 a had'a ai wa Salma magani ."
Baba Laure ta ce .
"To Masha Allah, Allah ya saka muna godiya, amma banda abinka basai ka bari saika dawo ba , sai kawai ka kamo kafa ka taho ."
Ya murmusa yana sunkuyar da kai
"Da Allah kama hanya ka tafi mana, kasan muna neman kudi gashi yanzu har an sake wata guda wannan kudin basu hadu ba ."
Wayar Aliyuu ce ta fara ringin , yasa hannu ya cirota a aljihunansa
Dariya ya yi yana cewa.
"Baba mutuminki ne Sa'adu yake kira." Ya d'aga wayar yana sata a spiker Baba tana dariya
"Salamu alaikum."
Sa'adu ya yi sallama, Baba ce ta amsa masa tana cewa.
"Sa'adu ya gidan ya katsina."
"Sa'adu ya ce lafiya lau babarmu ya mutanen gidan."
Ta ce .
"Alhamdulillahi Sa'adu ya manyan naku."
Ya mayar mata da fad'in.
"Lafiya lau, daman na kira na fad'a miki ne gobe Malam Shafi'u zai tafi Niger, to naji kuma kina cewa zaku kawo yarinya ai mata magani, nace bari na sanar dake."
Da sauri Baba Laure ta saki kan Salma ta mike tsaye tare da cewa.
"Niger zai tafi gobe kuma ."?
Ya ce .
"Eh wallahi Baba Laure."
Ta ce ."To shi ke nan Allah ya kaimu goben." sannan sukai sallama ya kashe , cikin tashin jin dadi Aliyuu ya ce .
"Tom Baba mene abin yi ."?
Ta kalleshi da cewa.
"Mene abin yi kuwa Ali , yanzu yanzu sai Allah zamu tafi katsinan , kaje tasha ka samo mana mota ."
Zaro ido ya yi yana cewa."Yanzu kuma baba kudin fa basu hadu ba ."
"Babu wannan zancen Ali , tashi Salma."
Ta d'ago Salma tsaye
"Kaje ka samo mota , kudin ko a can zasu hado."
Aliyuu ya juya da sauri yana cewa.
"Tom bari na samo mai motar."
Masha Allah Hadiza an yi kiba bulbul, sai shirin aure ake , irin yadda take son Sultan ba a cewa komai , mu dai sai dai mu ce Allah sa a yi damu wannan gagarumin biki .
Washe gari
Katsinawan dikko, kunya gareku badai tsoro ba 😌
A daren jiya su Baba Laure suka isa garin Katsina, aiko gari yana wayewa tun asubar farko suka nufi gurin Malam Shafi'u, sun tarar da layi sosai kafin a zo kansu .
Bayan Malam Shafi'u ya ga Salma ya tabbatar musu sihiri ne gami da aiken àljanu akai wa Salma.
Sai dai Salma abin yana matukar bata mamaki, wane zai mata sihiri a wannan duniya me take dashi
Malam Shafi'u ya debo ruwa cikin wani 'ko'ko , kana ya zuba ganyen magarya ciki, ya kaishi gaban Salma tare da fad'in.
"Karanta ayatur kursiyu ki tofa a ciki ."
Kamar yadda ya bukata haka Salma tai kana bayan ta gama ya ce tasa hannayenta a ciki, bayan ta zasu ya dauki carbi yana ta ja , ko mene yake cewa Allah masani
"Rufe idanunki."
Ya fad'a
Ta rufe , cigaba ya yi da jan wannan carbin wajen minti talatin, daga bisani ya fara karanto wasu ayoyi da surori cikin Littafin Allah mai girma.
Kuka Salma ta fara yi , sakamakon irin zafin da take ji a duk jikinta, jinta take kamar ba ita fa , wajen awa daya da rabi sukai a haka , sannan ya ce ta cire hannunta ciki, ta cire aka dauke 'ko'kon daga gun
Hannu Malam Shafi'u ya d'aga sama yana addu'a yana kuka
Shi dai Aliyuu yau yana ganin abin mamaki, ita ko Baba Laure ta saba ganin wannan lamarin tun tana karama
Bayan ya gama wannan addu'a ya aje carbin a gefe ya kalli Baba Laure yana cewa.
"Wallahi aike ne , sai dai mu munfi karfin duk wani àljani , da ikon Allah da manzonmu Muhammadur...."
Baba ta girgiza kai
Mikewa ya yi ya debo wani kullin magani guda biyu, ya mikawa Baba.
"Ku karbi wannan, saboda tsarin jikinta ga duk wani shedani, sannan a ja mata kunne ta dage da addu'a."
Tasa Hannu biyu ta amsa tana cewa.
"To malam."
"Sannan kuma zatai cuta mai tsanani sosai, daso samu ne yau ku koma Bachin, sai dai in baku koma ba babu matsala, amma idan aka koma zai fi."
Baba ta ce .
"In Sha Allahu kuwa daga nan sai gida."
Ya kallesu yana cewa ku je waje ku jira ta
Su baba suna fita minti biyu, me yayiwa Salma Allah masani , ta mike ta fito idanunta a bude hannayenta sun dawo daidai.
Kuka ta fashe dashi yayin da suka had'a ido da baba Laure, Salma ta zube kasa ta sume .
Bayan kwana biyu
Bauchi
Alhamdulillah alhamdulillah alhamdulillah, sai dai godiyar Allah, Salma a halin yanzu tana shan jinya Sosai da sosai, domin yanzu haka jini ake kara mata