← Book details Marubuciya Book One Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 1 OF 19

Sashe 1

Marubuciya Book One Complete Hausa Novel · about 8 min read

*MARUBUCIYA*✍️
Na
Autar Marubuta
_________________________________________
Bismillahir rahmanir Rahim.
Da sunan Allah mai rahma mai jin kai,
Zan fara wannan labari mai suna MARUBUCIYA✍️
Wanda na sadaukar da wannan labarin ga marubuta....👇

Gageren labari ne , kuma kagaggene daga alkalamin Fatima Abdallah kano
(Autar marubuta ✍️)

Bayan dogon lokacin dana dauka banyi typing ba yanzu na dawo, sai dai inajin alkalamin nawa yana da'kirewa🤭

Tooo Allah ya bamu sa'ar duniya da lahira ✌️☺️

*SADAUKARWA GA Marubuta masu tsaftataccen alkalami*🥰✍️

Masu YouTube na baku damar karanta wannan Littafin 👌🙏kar a yi kuskuren canza mini duk abin da aka gani a wannan labarin ✍️

A yi hakuri masoya wanna lokacin ma babu editing❌
~Ba labari ba ne mai tsayi~

MARUBUCIYAR .....
Gubar rayuwata
Kawar karuwai
Dajin mutuwa
Fatima da zarah
Mahaukacin so
Dangin dalas...🥂👇

*AUTAR MARUBUTA CE*✍🏻👼🏻
🌹__________🌹_________🌹__________🌹_________🌹
_Faduwar wani tashin wani_
_Yau ake yi, gobe sai labarin_
_Burina Rayuwata, rubutuna dan masoyana_
_Cikawa da imani fatana_🤲🏼
<><><🌹><><><>🌹<><><>🌹<><><><>🌹<><><><><>🌹<>

Ku yi mini subscribe 🥰🥂🙏 Something big is coming....😌
https://youtube.com/@fatimaismailabdullahi?si=l3dnPNRKygK5lG4g

Page 1&2

"A hankali yake shafa jikinta yana wani irin murmushi, lokaci guda ya fara cewa gaskiya baby...".

Salma ce ta mike zuwa gaban 'yan aji ta fisge littafin a hannun wata budurwa dake karanta littafin a gaban yan ajin .

Kowa ido ya zuba mata ganin yadda take huci , amma babu wanda ya iya cewa komai , sai wata budurwa sa'arta wacce ita ce marubuciyar labarin.

"Ke Salma dallah bama san hauka mene haka wai."?
Cikin fusata tai maganar

Wacce aka kira da Salma ba tare da annuri ba ta kalli mai maganar tana cewa .
"Haba dan Allah Hadiza, wannan wanne irin littafi ne , to wallahi abin ya isa haka , wannan ai iskanci ne da rashin mutunci, kuma a cikin islamiyya, to wallahi zan sanarwa da malam Auwal ."

Cikin fuskar rashin mutunci Hadiza ta mike ta Sha gaban Salma ta fisge littafin tana cewa .
"Aikin banza , ai ni na dade da sanin bakin cikin da kike mini , saboda kinga ba a karanta littattafan ki ."

Murmushi Salma tayi ba tare da taso ba , kana ta ce .
"Allah sarki ."
Kawai ta koma gurin zamanta kusa da wata aminiyarta zainab ta zauna.

"Aikin banza aikin wofi , hassada ta yi wa mutum yawa."
Hadiza ta karasa maganar tana neman gurin zama .
Zainab ce ta kalli Salma tana cewa.
"Salma shi yasa baba yake hanaki rubutu saboda marubutan batsa da sukai yawa, suke bata muku suna , tunaninsa abin da kike yi ke nan."

Ajiyar zuciya Salma tai tana cewa.
"Wallahi haka ne Zainab, ni kuma gaskiya ina da buri a cikin duniyar marubuta, sai dai baba yana bani matsala."

Tana karasa maganar sukaji karar kararrawa alamar an tashi , hakan yasa kowa ya mike tare da jakarshi a hannu wasu a kafad'a.

"Zainab ki sauri dan Allah muje ki bani hadisin nan , kin san malam Naziru idan ban masa aikin nan ba , bazai barni ba ."

Salma tai maganar yayin da suke fita daga get din makaranta.
"Haka ne wlh ai ba shi da kirki ,mi sauri kan a kira magari ba ."

Suka fara tafiya cikin sauri , kamar yadda Zainab ta bukata.
"Allah ya kawo mu lokacin da zaki waya Salma, kodan ki zo online ki ga irin littattafan da Hadiza take yi na marasa mutunci, ni wlh bama na iya karantawa."

Salma ta ce .
"Hmm!."
"Ai ki bari kawai Yaya Umar yana son sai min waya kwanan nan ."
Ta karasa maganar tana tuntu'be da wani dutse kamar zata fadi .

Dariya Zainab tai tana cewa.
"Ai kodan soyayyar shi yasai miki."

Salma ta ta'be baki tana cewa.
"Wacce soyayya kuma bayan muna gida daya."
Ta karasa tare da jefa mata harara .

Hadiza cikin fushi sosai tabar islamiyya suka nufi gida ita da kawarta Ruma .

"Ai wallahi Ruma na tsani Salma,bana san ta wlh , munafuka ce ta karshe bana kaunarta ."

Ruma tai murmushi tare da cewa .
"Haka ne , ammma ki dena damuwa da ita mudai a cigaba da rubuta mana littattafai muna more duniya, idan badan haka ba ai wani abin ba sani zami ba , tunda dai ko a islamiyya ba a Mana filla filla 'baro 'baro yadda zamu gane , sai dai aita damun mu da wani wankan wajibi wankan tsarki ."

"Kuma ke mene naki na damuwa Hadiza, ke fa Hadiza RM sunanki , ita kuma Salma Aminu, a suna ma naki yafi dadi bare littafi."

Sannan Hadiza ta samu tai murmushi

Har yanzu Salma bata samu ta isa gida ba , sakamakon tana tsaye kofar gidansu Zainab tana jiran fitowarta ta kawo mata Littafin Hadisi

A lokacin wani farin gaye kirar yaran hutu ya tsaya gaban Salma yana cewa .
" 'yan mata adon gari , kwana biyu."
Wani takaici Salma taji ya rike mata zuciya, ta kalleshi tana cewa.
"Lfy lau. Ammma dan Allah bakajin kiran sallah ake ka tafi inda ya dace ."

Farin saurayin me suna Kalifa ya ce .
"Haba Salma, bafa na samun damar ganiinki , kuma kinsan irin san da nake miki."

Lokacin Zainab ta fito rike da wannan littafin ta mikawa Salma, kana Salma tai godiya Zainab ta ce mata "Saida safe."
Sannan ta shige ba tare da ta ce da wannan gayen komai ba .

Salma ma ta juya ta nufi hanyar gida.

Baban Salma ne da yayanshi Yusuf, dawowarsu daga masallaci ke nan
Yayan nashi yake cewa.
"Har yanzu Salma wai bata dawo ba ."
Yake tambayar Yaya Umar da shima shigowarshi ke nan.

Ansa ya ba shi tare da cewa .
"Eh baba ammma nasan tana hanya ."

Sallama Salma tai tana shigowa cikin gidan ta na hada ido da yayan babanta taji gabanta ya fadi.....

Bayan Hadiza ta isa kofar gidansu ta hangi wata vabbar mota cike da kaya a ciki , hakan yasa ta karasa da sauri cikin mamaki , mahaifiyarta dake ganawa da mai motar ta fara tambaya.

"Mama me yake faruwa ne Ina zamu haka ."?

"Shiga mota kawai Hadiza, babu lokaci yau sai kwanan sokkoto mun bar kano domin bamu da kowa ."

"Mama wannan wanne irin tashi ne haka fisabidillahi, sai ka ce ana korarmu na shiga uku."

Mahaifiyarta kawai ta shige gaban motar , yayin da shima driver ya shige , ganin babu yadda Hadiza zata yi , ta kama motar ta shiga kusa da mahaifiyarta cikin bakin ciki.
Sannan driver yaja mota cike da kaya suka tafi .

Tunda Salma ta shigo ta durkusa gabansu tana ta kuka , sakamakon irin maganganu da Alaji Yusuf yake yi .

Malam Aminu ba shi da kowa sai wannan yayan nashi Alaji Yusuf, suna zaune lfy sosai , sai dai Alaji Yusuf yafi mlm Aminu rufin asiri domin har yaje ya zama Alaji.

Irin girmamawa da malam Aminu yake da ita , hakan yasa yake daukar duk maganar yayan nashi Alaji Yusuf, hakan yasa ma Umar ya zo ya zauna gurin malam Aminu har ya kammala karatunsa , yadda yaji dadin zama da kuma yadda yake son Salma yasa har yau bai koma gida ba .

Kuma Salma take sharba sosai , sai dai mahaifiyarta babu yadda zata yi ne , ammma bata san wannan hali na Alaji Yusuf.

"Tom ai ba lefinki ba ne , domin tuntuni nake cewa ka bani yarinyar nan ta dawo gidana da zama, duk ga sa anninta nan su Karima da Husna , ammma kaki ."

Cikin fusata da fada Alaji Yusuf ya cigaba da cewa "To in Sha Allah komai ya kare , gobe ki shirya kayanki tsaf Umar ya kawo ki."

Kuka Salma ta sake rushewa dashi tana kallon mahaifiyarta.
Babanta malam Aminu shi ne ya ce .
"To mene abin kuka kuma, kin san cewa bama san wannan rubutun da kike yi , karya da gaskiya da shedanci , ammma bakya ji ."

Umar ne da ransa ba ya masa dadi ya kallah kanin babanshi yana fad'in .
"Baba wallahi wannan abin da Salma take bafa abin sabo bane ko ...".

Kafin ya karasa maganar babanshi ya dakatar dashi da cewa .
"Baki daya Umar nawa kake da har kasan duniya, mu muka ga ga jiya muka ga yau , duk iskancin da ake a fim kala kala su waye ke rubutawa in ba marubuta ba , to bazai yiyu yarinya ta zo tana jaa mana zagi ba ."
"Wanne irin iskanci ne basa yi duk aita lalata tarbiya."
Ya sake kallon malam Aminu yana cewa."Wai har da marubutan matan aure, tsabar isgili to rubutu dai Salma ba a wannan zuri'ar tamu ba ."

Ya mike tsaye tare da sake kallon Salma yana cewa
"Gobe babu fashi Ina sauran ku ."
Ya nad'e malum malum ya fice , mahaifiyarta na cewa "A sauka lfy Allah yasa haka ne yafi alheri."
Salma ta sake bushewa da kuka .

07040805269
WhatsApp only
Autar marubuta ✍️

MARUBUCIYA
Na
Autar marubuta
________________________________________

*SADAUKARWA GA Marubuta masu tsaftataccen alkalami*🥰✍️

Masu YouTube na baku damar karanta wannan Littafin 👌🙏kar a yi kuskuren canza mini duk abin da aka gani a wannan labarin ✍️

A yi hakuri masoya wanna lokacin ma babu editing❌
~Ba labari ba ne mai tsayi~

MARUBUCIYAR .....
Gubar rayuwata
Kawar karuwai
Dajin mutuwa
Fatima da zarah
Mahaukacin so
Dangin dalas...🥂👇

*AUTAR MARUBUTA CE*✍🏻👼🏻
🌹__________🌹_________🌹__________🌹_________🌹
_Faduwar wani tashin wani_
_Yau ake yi, gobe sai labarin_
_Burina Rayuwata, rubutuna dan masoyana_
_Cikawa da imani fatana_🤲🏼
<><><🌹><><><>🌹<><><>🌹<><><><>🌹<><><><><>🌹<>

Ku yi mini subscribe 🥰🥂🙏 Something big is coming....😌
https://youtube.com/@fatimaismailabdullahi?si=l3dnPNRKygK5lG4g

Page 3&4

Bayan Alaji Yusuf ya tafi Salma ta mike ta shige daki ta cigaba da kuka , duk yadda Umar yayi domin ya rarrasheta taki , domin tasan idan ta koma gidan Alaji Yusuf burinta na zama marubuciya tabbas sai dai mafarki.

Haka tai ta kuka tana sunbatu kala-kala har akai kiran sallar isha'i
Ko abinci bata iya ci ba ta shige daki ta rufe , mahaifiyarta abin yana damunta sai dai babu yadda zata yi , domin komai wuya tafi son Salma a kusa da ita .

Anan cikin gidan Alaji Yusuf kuwa .
Karima ce zaune sai had'a gumi take rike da waya a hannu , da gudu Husna ta shigo tana cewa.
"Wallahi Aunty Karima ga babana ."
Chapter 1 · 0% Book details