Sashe 11
Marubuciya Book One Complete Hausa Novel · about 8 min read
Aliyuu ya matukar rame sosai , ko dan irin abin da matarshi ke yi masa , domin tana tunanin a karshe tabbas zai ce yana son Salma, har yakai ya aureta, wannan lamarin take gudu yasa take yin abin da take
Kimanin kwana 3 Aunty Hauwa tana jaraba kiran wayar Salma, amma shiru ,domin ta samu ta maida komai nata bayan tasai waya a Dubai, Allah yasa komai tana aje shi a email kamar yadda ta koyawa Salma.
Bayan yayan baban ta ya tabbatar mata hajjiya Aisha ta tashi ta siyar da gida , kana ta kori Salma kamar yadda Suwaiba take sanar dashi.
Hankalin Aunty Hauwa ya matukar tashi sosai, har shugaban kungiyar Lafazi tai wa magana amma ya ce shima number Salma bata tafiya, online ma babu labarinta.
Washe gari da safe jigum Aliyuu ya yi , domin an shigar da Salma ana mata aiki yaso ya sanar da mahaifiyarshi wannan lamarin , sai dai tana cann wani kyauye a katsina nertwork ma babu , idan taje ta yi wata biyu ko 4 kafin ta dawo .
Allah dai ya baki lafiya Salma
Yana zaune sai ga Dactor din ya fito, shigarsa da fitowarshi bai ci ace ya yi wannan aiki ba , hakan yasa da tsoro Aliyuu ya mike tsaye.
"Dactor meke faruwa."?
"Biyoni office."
Abin da ya ce ke nan, bayan Aliyuu yabi bayanshi suka shiga office suka zauna.
"Likita me yake faruwa dan Allah."?
Kafin ya fara bashi amsa , ya yi ajiyar zuciya tare da fad'in.
"Ammm Malam Aliyuu, zan maido maka da kudadenka ,saboda wannan yarinyar ciwonta bana asubiti bane , hakan yasa ban yi mata aiki ba ma."
"Likita kamar ya kuma." Da damuwa Aliyuu ya tambaya
"Eh kamar dai shafar àljanu ne , saboda a halin da ake ciki yanzu, hannayenta duk biyun, sun tsaya cak , basa aiki ."
"Tom ashawarce a koma gida a yi magani saboda duk asubitin da zaku je , Tom zasu ci kudin ku ne kawai."
Durkusar da kai Aliyuu ya yi , bayan likitan ya karfafa masa gwiwa ya tashi ya koma wajen Salma.
Yana shiga tana zaune hawaye sai kwarara suke a idonta , ya dubi hannayenta
Yatsunta duk guda goman wasu sun lankwashe kamar zasu karye, wasu kuma suna tsaye cakk , baki ya rike sakamakon wani kuka da ya ke ce masa , jin hakan ya tabbatar wa da Salma ya shigo inda take .
"Allah yana jaraftar bayinsa ta duk inda ya so , ki yi hakuri Salma irin taki kaddarrar ke nan, gida zamu koma zamu nemi mai magani ."
Cikin kuka kamar mace Aliyuu yake mata wannan maganar
Bayan su karasa gida, Fatima tana zaune ta kara wayarta a kunne tana sauraran wani Littafi
Sallama Aliyuu ya yi , amma bata ko kulasu ba , yarinyar data rako Salma ya nuna mata dakin Salma ta shige da ita , kana ta fito ta tafi , Aliyuu yana ciro naira 50 yana bata .
"Yanzu rashin mutuncin ki yakai haka Fatima, mu shigo ko kallo bamu isheki ba."
Duk da ya yi wannan maganar ko a jikinta, volume din Littafin ta karo .
"Fatima da zarah kashi na 57 , mai sauraro mun tsaya daidai gunn." Hannu yasa ya zaro wayar ya wurgar da ita saida ta rabe gida biyu .
Wani gigitaccen kuka Salma ta fashe dashi sakamakon yadda taji Fatima tana sauraran Littafin ta , amma gata cikin gidanta ba tare da tasan ita ba ce .
Irin rayuwar da Salma suka ringa yi ke nan cikin wannna gidan har kimanin wata biyu, sai Fatima ta gadama zata taimaka wa Salma da wulakanci, Aliyuu yasha danko mata masu aiki domin su kula da Salma, amma basa zama , saboda Aliyuu ba ya iya biyansu
Karfe 11 na dare Aliyuu ya rufe shago ya dawo, bayan ya yi wanka ta kawo masa abinci.
Ba tare da ya bude abincin ba ya kalli Fatima da cewa.
"Ina kika je dazu , na aike ki gidan Baba ne."
Ajiyar zuciya tai kana ta ce .
"Tom naga dai Baba ta dawo jiya,lefi ne dan naje ña gashsheta , ta ce kuma karka fita koina ka jirata da safe tana zuwa."
Ya mike ya shige daki yana cewa."Dauke abincin ki."
Gombe state Akko local government
Yayan baban Aunty Hauwa ne shida matarshi har wajen 11:29 sai hira suke matar tashi ce take cewa.
"Tom ni ai ban yi mamaki ba , dan hajjiya Aisha ta yi haka ."
Mijin na ta ya ce
"Hmm tom ai ke abin da baki sani ba ,duk wannan baya damun Hauwa'u, wannan yarinyar Salma da ba a san ina take ba , shi ne babban tashin hankalin Hauwa'u, ta ce mini kullum saita kira number ta ko Allah zaisa a samu , wani karin abin ma ta ce ba yanzu zata dawo ba , sai nan da wata 4, wani aikin ya kuma bullo musu ."
Matar tashi ta ce
"Allah sarki Hauwa, Allah dai ya bayyana yarinyar ko hankalinta ya kwanta."
Ya ce .
"Amin ."
Washe gari da safe misalin karfe 8, bayan Aliyuu ya yi wanka ya tsaya jiran mahaifiyarshi.
Ba zato yaji sallamar ta a kunnuwansa , da firgice ya mike ya fice yana amsa sallamar yana cewa.
"Sannu da zuwa Baba."
Baba da idanunta taji kwalli , irin mutanen nan ne da suka ga yau suka ga jiya , idanunta a bude .
"Ki shigo ciki baba.".
Aliyuu ya fad'a yayin da Fatima ke fitowa
"Ba zama nazo ba Aliyuu, ina son yanzu ka kori yarinyar daka kawo gidanka take tsiyata ka , kake ramewa , dube ka ."
Ta nunashi da hannunta jajir yasha kunshin tsofaffi
Dogon numfashi Aliyuu yaja yana cewa.
"Baba ki yi hakuri mana , wallahi duk abin da Fatima ta zo ta fad'a miki ba gaskiya bane ."
"To mene ne gaskiya, me yasa kai baka zo ba , tun shekaran jiya na dawo , ammma babu kafar ka cikin gidan me yake faruwa."?
Saida Aliyuu ya yi nannauyar ajiyar zuciya yana kallon matarshi, sannan ya ce .
"Baba , dan Allah ki zauna mi magana zaki fahimce ni ."
Tsawa ta daka masa da cewa.
"Ina wasa da kai Ali, wa ce ce wannan yarinyar kuma tana ina."?
Murmushi Fatima tai tare da nuna farin ciki.
"Abin da yake faruwa Baba, wannan yarinyar bata da lafiya tsawon watanni 3 yanzu ke nan."
Aliyuu suna tsaye kemm ya gama bawa mahaifiyarshi labarin Salma tun a ranar da ya ganta kofar gidansa, har zuwa wannan ranar."
Salma dai tana daki tana kuka tare da tunanin idan tabar nan ina zata nufa a wannan mawuyacin yanayin .
"Ina yarinyar take ."
Baba ta tambaya bayan ta gama sauraran labarin ta .
Da hannunsa Aliyuu ya nuna mata dakin Salma, kana Baba ta taka ta shiga dakin, suka bita a baya .
MARUBUCIYA ✍️
Na
Autar marubuta
________________________________________
Page 27&28
"Assalamualaikum."
Baba ta fad'a tana shiga cikin dakin
Idanun Salma kamar mai gani cike da hawaye ta amsa sallamar
Baba ta dubi hannunta ta dawo ta dubi idanunta
"Innalillahi wa innailaihir rajiun."
Abin da ta fad'a ke nan ganin yadda Aliyuu yake bata labari lamarin duk ya wuce nan .
"Ba kwa gyara mata daki , dubi sai zarni, barinta kuke tai Kashi da fitsari anan ."?
Tai tambayar tana kallon Fatima
murmushin farin ciki ne ya rufe Aliyuu ganin yadda mahaifiyarshi ta fahimta, domin a kullum ita ke fad'a masa ya yi adalci ya yi taimako tabbas zai ga cigaba a rayuwar shi .Gashi kuwa bata ba shi kunya ba
Kusa da Salma ta matsa tare da d'ago ta suka fito waje, kai tsaye ta wuce ban daki da ita , ruwan zafi ta samu ta wanke Salma tass har kanta saida ta wanke , sannan ta debo kayanta nan ma ta wanke su, bayan ta gama ta share dakin nata , ta yayyafa ruwa ta goge shi, sannan ta shiga dakin Fatima ta dauko turaren wuta ta kunna cikin dakin Salma.
Duk Aliyuu yana tsaye yana bin mahaifiyarshi da kallo ta gama wannan aikin, domin ta matukar faranta masa rai sosai ba kadan ba .
Bayan duk ta gama wannan ta maida Salma daki, ita kanta taji dadin jikinta sai murna take tana godiya.
Hatta wajen sana'arshi Aliyuu bai iya fita ba , saboda wannan yanayi
Baba ta zauna dakin Salma, Aliyuu ma ya shigo tare da Fatima tana ta fishi .
"Bazan iya dena godiya ba , na gode sosai Baba."
Salma ke nan
Murmushi Baba tai tana cewa.
"Babu komai yarinya, ai duk wanda ya taimaki wani , to shima Allah bazai barshi ba , sannan ni suna na Baba Laure wato mahaifiyar Aliyuu, saboda haka ina nan zan kula dake harki samu lafiya."
Jin hakan yasa Salma ta fashe da kuka
Aliyuu ne ya rarrasheta ya kwantar mata da hankali
Jimmm Baba Laure tai tana kallon Salma
"Baba ko akwai wani abin ne."?
Inji Aliyuu
Baba Laure ta d'ago kai tana cewa.
"Dama kin ta'ba yin irin wannan abin ne ko yaya."?
Salma tana share hawaye ta ce .
"A'a Baba, lokaci guda abin ya sameni ."
Jin amsar salma yasa ta kalli Aliyuu.
"Yanzu wanne maganin ake yi."?
Cikin karfin gwiwa ya ce .
"Baba wani magani ne , saboda munje asubiti har guda biyu , amma sun ce ba ciwon asubiti ba ne ."
Baba ta girgiza kai tana cewa.
"To babu ko shakka wannan sihiri ne akai wa wannan yarinyar."
Gaban Aliyuu faduwa ya yi .
"Sihiri kuma Baba, me wannan yarinyar ta tsarewa wani ."
Baba ta ce .
"Aliyuu mu muka san duniya babu inda bamu shiga ba , saboda haka ina tabbatar ma wannan sihiri ne aike ne akai mata."
Wani iri Salma taji a ranta , to waye zai mata wannan abin, babu wanda yasan da zaman ta, tunanin da take yi ke nan
"To mene abin yi yanzu."?
Aliyuu ya tambayi Baba Laure
Girgiza kai Baba tai kafin ta ce .
"Akwai wani babban malami a Katsina naga irin yadda yake aiki sosai kan irin wannan matsalar, indai ya yi maka magani baka warke ba , to tabbas cutar ajali ce ."