Sashe 13
Marubuciya Book One Complete Hausa Novel · about 8 min read
Irin yadda Fatima take ganin ana kulawa da Salma sai duk tsantsar kishi yake damunta, domin tana ganin karshen wannan lamarin to Aliyuu auren Salma zai .
Bayan an cire mata wannan Karin jini bacci ne ya kwashe ta , ba ita ta farka ba sai karfe 9 na dare, abin yana matukar bawa Salma mamaki, wai idanunta sun dawo daidai, hannunta ma babu abin da bata yi dashi , duk da cewa tana cikin jinya Sosai amma idan ta dubi yadda take tana jin dadi ta gode Allah.
Bayan ta tashi tashi aka bata ruwan zafi tasha, kana aka soya mata kwai kamar yadda ta nuna tana bukatar ci .
Har kowa na gidan ya yi bacci, amma bata iya baccin nan ba , farin ciki da mamaki, bata ta'ba zaton zata tsinci kanta cikin wannna yanayi ba .
Washe gari da safe , Baba Laure kamar wacce ake kora, tai wanka ta hado kayanta , tana gama karyawa ta ce yau sai gida , tsakar gida ta fito rike da jakar kayanta, hakan yasa duk suka fito
"Baba yanzu fa karfe 8:45. Dan Allah ki bari rana tayi , ina nan ina gidanki." Cewar Aliyuu
Baba ta ce .
"Tom ai kaji mene ka ce , ina nan ina gidana, daman jinyar wannan yarinya ce ta zaunar dani."
Ta nuna Salma
"Yanzu kuma jiki Alhamdulillah zan koma zuwa gobe ko jibi nazo naga jikin nata ."
Salma durkusa wa tai gabansu tana cewa."Baba hakika kun yi mini abin da bazan ta'ba mancewa ba , kuma kun yi mini sanadin farin cikin da bazan ta'ba gushewa ba , bani da abin da zan gode muku , Allah yabar zumunci ya bani ikon saka muku ."
Murmushi Baba Laure tai tana cewa."Karki damu Salma, ki ci gaba da kula da kanki, idan kinji sauki kuma sai Ali ya kawoki gidana."
Salma ta kalli Aliyuu tana murmushi da fad'in.
"In sha Allah kuwa zan zo Baba."
Baba ta ce .
"Masha Allah, yarinya mai hankali da tarbiya, kowa zai so kizo a sirikarshi ko yarsa."
Salma ta sunkuyar da kai.
Wani mashi Fatima taji ya sokar mata zuciya, sabuwar kiyayyar Salma taji ta sake samun guri a zuciyarta
Nan Baba tai sallama dasu kana ta wuce gidanta
Salma shigewa daki ta yi ta samu guri ta zauna
"Idan har sihiri akai mini wannan abin ya faru dani , to wane ne ? Na baro gida , kan karamin dalili,kamar dai mara hankali."
Maganar da take cikin ranta ke nan sai ga Aliyuu ya shigo , matarshi Fatima dake biye dashi ta tsaya kofar dakin
"Salma ya jikin."?
Salma cikin girmamawa ta kalleshi da cewa.
"Da sauki Yaya Aliyuu."
Ya zura hannu a aljihunansa yana cewa."Allah ya kara lafiya."
Wata kifat din Tecno ya zaro ya mika mata, kana ya mika mata sauran SMS dinta guda biyu da ya shigo dasu .
"Ga wannan wayar second ce , ki yi hakuri da ita sai kisa layukanki ciki ."
Hannu biyu tasa ta karba tai godiya tana cewa.
"Na gode Yaya, Allah ya saka da gidan aljanna."
Sannan ya fice ya tafi
Cikin farin ciki Salma ta bude wayar tana saka layukanta ciki
Cikin yanayin fusata Fatima ta shiga kichin ta dauko wuka , kai tsaye ta fad'a dakin Salma.
MARUBUCIYA ✍️
Na
Autar marubuta
________________________________________
Page 31&32
Salma tana d'ago kai ta ganta , da sauri ta mike tsaye tana jaa da baya .
Idanun Fatima jajir tamkar wacce ta fita a hayyacinta .
"Wato kin zo gidana , ki hanani farin ciki, kin yi cuta an miki magana, an sa miki jinin mijina, mahaifiyarshi tana yabonki a gabana, ya sai miki waya , abin da ya rage ki aure shi kooh."
Salma da matukar tashin hankali take ja da baya tana cewa.
"Wallahi Aunty Fatima ba haka bane , babu komai tsakaninmu saii.."
Dakatar da ita tai tana d'aga wukar kamar zata caka mata
"Kafin na yarga biyar , ki kwashe kayanki ki bar wannan gidan , idan baki fita ba wallahi saina kasheki Salma." Jikin Salma na rawa tai sauri ta zura hijabi, kawai tai waje babu ko takalmi sai wannan wayar a hannunta.
Tana nishi da ajiyar zuciya ta fito ta tsaya "innalillahi wa innailaihir rajiun. Wannan matar kodai tana da àljanu, ko takalmi bata bari nasa ba ."
Salma tai maganar tana haki, bakin titi ta nufa , duk ta rame tayi wani irin tsayi, tunanin ta kawai yanzu ta je ta hau motar Kano
Ringin din waya take ta ji tare da ita , amma ta kasa sanin daga ina ne , sai daga baya ta lura ashe akwai waya a hannunta, ta dubi fuskar wayar yayin da akai kira biyu babu amsa .
Kafin ta cire fuskar ta kan wayar sai ga wani kiran yana shigowa
Kara wayar tai a kunne kamar mai jin tsoro
"Hello."
Muryar mace taji tana cewa.
"Salma Salma."
Salma ta ce ."Eh ni ce waye."
Babu zato ba tsammani ta ji an ce ."Aunty Hauwa ce Salma kina ina ne ."?
Wani rasss taji a ranta da faduwar gaba "Aunty Hauwa ke ce ."
Kawai ta fashe da kuka
Wani farin ciki Aunty Hauwa taji ya rufeta, ko tsayawa rarrasheta batai ba ta cigaba da cewa.
"Kina ina duk inda kike ki taho Salma na , na dawo ."
Cikin kuka da matukar shauki Salma ta fara mata magana."Ina Bauchi Aunty amma gani nan yanzu zan taho , sai dai hajjiya Aisha ta siyar da gidan."😭
Murmushin farin ciki Aunty Hauwa ta sake yi tana cewa.
"Na sani Salma ki hawo mota ki taho idan kin zo zan miki kwatancen sabon gidanmu."
Salma ta share hawaye tana cewa" To Aunty amma babu komai a gurina babu kudi wallahi yanzu ma daga wani gida aka koroni bani da lafiya."
Ajiyar zuciya Aunty Hauwa tai kana ta ce .
"Tom ki samu wani ya kawoki idan kun zo sai na bashi kudin, idan bai yarda ba kice za a ninka masa ."
Da sauri Salma ta nufi tasha kamar zata fad'i, sam ta mance ma babu takalmi a kafarta, mutane kuwa sai kallonta suke , daga taje gurin wannan mai motar sai taje gun wannan, haka ta samu wani ta ce Gombe zai kaita ita kadai , da kyar ya yadda sai da ta hadashi da Allah da annabi sannan ya ce ta hau , suka tafi.
Matukar shauki da farin ciki take ji kamar tai fiffike ta sauka a Gombe, sam ta mance ma bata da lafiya, haka suka ringa tafiya har suka fara shiga birnin Gombe
Wajen karfe biyu Aliyuu ya shigo gida , ganin takalmin Salma zube a kofar dakinta, yasa shi mamakin me yasa bata fito ta ce masa sannu da zuwa ba kamar yadda ta saba
"To ko dai jikin ne."?
Ya tambayi kanshi
"Salma."
Yaji shiru
"Salma."
Fatima ta fito a daki fuskaantar babu annuri
"Na koreta ta tafi inda ta baro, tunda nan dai ba gidan ubanta bane ."
Wani yammm Aliyuu yaji maganar kamar da wasa, ya leka takin nata .
Sai dai ga komai nata nan , hakan yasa bai yarda ba
Ganin bai yarda ba ya sake fusata Fatima tana cewa.
"To wallahi na koreta babu ko takalmi, shegiya matsiyaciya , harda wani sai mata waya , daga nan kuma ka ce zaka aureta ko."
Da sauri Aliyuu ya juyo tare da mamaki sosai. "Wai dan Allah da gaske kin koreta, baki da hankali ne Fatima, mene ta tsare miki."
Yayo kanta da jajayen idanu kamar zai daketa
"Saboda ba gidan ubanta bane, ba kuma na mijinta ba ."
Jin zancen shirmen dake fitowa daga bakin Fatima ya sake bakanta masa rai .
Ganin karya 'bata lokaci yasa ya fice da gudu, neman Salma ya shiga yi lungu da sako ko Allah zaisa ya ganta , haka har yaje tasha yana ta tambaya, nan ya samu wasu suke tabbatar masa ta hau mota zuwa Gombe kuma tun dazu ne, yanzu baza ta gaza zuwa ba .
Bakin ciki da takaici ne ya turnike masa zuciya, cikin kasala ya nufi gidan mahaifiyarshi
Baba Laure tana zaune gama cin abincinta ke nan ya samu guri ya zauna bayan sun gaisa . "To ko jikin Salman ne , mene yake faruwa."?
Ta tambaya domin ta ganshi a wannan yanayi.
Sai da ya sauke ajiyar zuciya, sannan ya fara cewa. "Wallahi Baba shigata gida ke nan yanzu, wai Fatima ta kori Salma tsabar rashin mutunci."
"Aliyuu ban gane me kake magana ba , dazu fa na baro gidan , kamar ya ta koreta me tai mata ."?
Cewar Baba Laure da ita ma labarin bai mata dadin ji ba
Aliyuu cikin yanayin rashin walwala ya ce ."Baba gaske nake miki, yanzu ma daga Tasha nake , an ce mini ta hau motar Gombe, yanzu ma taje."
Baba ta rike haba tana cewa."Innalillahi wa innailaihir rajiun meke damun Fatima, wannan wanne irin rashin hankali ne , yanzu ya za ai."?
Aliyuu ya maida mata da cewa.
"Babu yadda za ai kuwa Baba , domin ni ko number Salma bani dashi ."
Baba ta girgiza kai.
"Wannan matar taka ko 'yar banza wallahi, an yi shasha sha."
Aliyuu ya zame ya kwanta bisa wannan tabarma
Anan kuwa Salma da driver suna tsaye suna jiran ganin ta inda Aunty Hauwa zata bullo
Wata mota Salma ta ga ta nufosu blue mai bakaken murfi .
"Motar Aunty Hauwa ba blue ba ce ."
Cewar Salma tana sake hangawa
Bayan motar ta tsaya ko gilashi ba a bude ba , kawai aka bude kofar motar .
Da gudu Salma ta nufi Aunty Hauwa ta rumgumeta da matukar kewa da farin cikin yadda ta ganta , amma tun da farin Aunty Hauwa abin data fara lura dashi Salma ta rame sosai babu ko takalmi kuma a kafarta.
Driver da ya kawo Salma ya yi murmushi yana cewa. "Kai ai dah raina wannan yarinyar nake , ashe yar masu kudi ce . Bari naje a sallame ni ."