Sashe 14
Marubuciya Book One Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ya matsa kusa yana wata far'a
Hawaye har sun kawowa Salma, ta kalli wannan driver tana cewa."Aunty ga wanda ya kawoni , duk cewa suke baza su zo wata Gombe ba , shi ne ya taimaka mini . "
Jin haka yasa ya yake hakora
"Allah sarki, mun gode bawan Allah."
Cewar Aunty Hauwa tana zura kai a mota , kudi ta ciro kimanin dubu 30 ta mika masa, cikin murna yasa hannu ya karba ya gamsu shimm ya yi godiya.
Hakan yasa Salma suka shige mota suka fara tafiya.
Rufe idanu tai tana wata nannauyar ajiyar zuciya, yadda tai kewar sanyin motar Aunty Hauwa yasa ta tuna farkon haduwarsu, har lumshe ido take tana jin cewa tabbas duk kan wahalar ta ta kare .
Aunty Hauwa kamar tasan tunanin da take , ta kalleta tana murmushi kafin ta ce ..
"Salma wayata aka sace mini sam ban kula ba , har saida muka je Dubai , ki gafarta mini."
Jin hakan yasa Salma ta bude idanunta.
"Aunty na sani , domin kuwa Anas shi ne wanda ya sace miki waya bayan ya rakoki, har gida ya zo da ita , sannan suka koreni suka siyar da gidan ."
Aunty Hauwa ta sha kwana , sannan ta kalli Salma tare da maida hankali zuwa tukinta tana cewa. "Daman Anas ne ya sace mini waya , lallai yaron nan , ai yanzu zancen da nake miki hajjiya Aisha tana cann an kulleta, domin tunda na dawo na shigar da ita kara, dukkan duniyar mahaifina ta dawo gurina ."
Jin hakan ya sa ran Salma sanyi , ta sake furzar da iska
Wani gida Aunty Hauwa tai parking motarta bai kai wancen girma ba , amma yafi wancen kyau sosai da kayan more rayuwa, gidan a bude yake suka sa kafa suka shiga .
MARUBUCIYA ✍️
Na
Autar marubuta
________________________________________
Page 33&34
Suna shiga ciki , sabuwar yar aikin Aunty Hauwa dake zaune falo tana kallo, ta sake rissinawa tana cewa. "Sannu da zuwa Aunty."
Aunty Hauwa ta kalleta tare da zama a kujera tana cewa."yawwa sannu Farida, fatan kin dorawa Salma ruwan wankan da nace ."
Cikin girmamawa Faridan ta ce ."Na dora Aunty, har abinci ma an gama ."
Ta ce "yawwa."
Salma tai murmushi sannan ta nemi guri ta zauna , yayin da Farida take shigewa ciki . Ajiyar zuciya mai zafi Salma ta sauke ."Aunty wannan gidan ya yi kyau sosai." Ta fad'a tana duban koina
Aunty Hauwa ita ma ta murmusa tare da fad'in."Tom Salma kije ki fara wanka , ki ci abinci sai kiyi sallah."
"Tom Aunty."
Salma ta fad'a tana bin hanyar da Farida tabi , ba tare da tasan ina ne a cikin gidan ba , bayan Salma tai wanka , ta saka wata atamfar Aunty Hauwa, sannan ta fito falo ta saka sallaya ta fara sallah, daidai lokacin data idar da wannan sallar, ita kuma Aunty ta gama cin abinci
Shiru Salma tai tayi zuruu , hakan yasa Aunty cewa. "Salma ga abinci nan." Ta nuna mata kular dake gefe tare da ruwa da lemo
"Gaskiya kin rame sosai Salma." Saida Salma tai murmushi ta ce . "Ai Aunty nayi kiba ma , nasan yanzu Yaya Aliyuu hankalinshi yana tashe shi da Baba Laure."
"Su waye su , baki fad'a musu zaki dawo bane , sannan ina babbar wayarki , kullum ina kiranki Salma, ammma shiru , kuma ke baki neme ni ba ."
Aunty Hauwa tai magana cikin damuwa, zama Salma ta gyara kana ta ce ."Hmmm Aunty ke nan, na yi zatan mutuwa zan wallahi, ashe zamu sake haduwa."
Aunty Hauwa tai dariya tana cewa. "Salma wai mene ya kai ki Bauchi to."?
Jin wannan tambayar yasa Salma ta fara bata labari , tun daga ranar data sa kafa ta tafi Dubai, har zuwa wannan ranar
"Innalillahi wa innailaihir rajiun, Salma makancewa fa kika ce." Aunty Hauwa bayan ta saurari duk labarin abin da ta ce ke nan.
"Hmmm Aunty ke nan, harda kuturta ma kuwa."
Girgiza kai Aunty tai kafin ta ce .
"Abin mamaki tom wane ne zai miki sihiri Salma, gaskiya su Baba Laure sun yi kokari, in sha Allah zamu kai musu ziyara da zarar aiki ya ragarmin."
Ta sake muskutawa tana cewa. "Ikon Allah Salma, gaskiya kina shan wahalar rayuwa, amma in sha Allah yanzu ta kare , ko yaushe na kira wayarki a kashe , Allah sarki."
Salma ta sunkuyar da kai kasa tana murmushi
"Tom ki ci abinci Salma ni yanzu zan fita wani aiki, duk abin da kike bukata ki yi wa Farida magana." Ta karasa maganar tana mikewa tsaye
Salma ta ce .
"To Aunty a dawo lafiya."
Har ta kai kofar falon sai ta juyo tana cewa.
"Idan na dawo kuma da dare ,zamu je shopping daga nan sai ki siyo waya da laptop din ki ."
Jin dadin hakan yasa Salma ta washe baki tana cewa.
"Na gode Aunty a dawo lafiya."
Sannan ta fice ta tafi
Ajiyar zuciya Salma tai mai matukar girma, sannan ta jawo wannan abincin ta fara ci .
Bayan kwana biyu
Alhamdulillah Salma dai sai farin ciki, a halin yanzu tana zaune dakinta tana danna laptop, har an yi kiba an yi kyau .
Aunty Hauwa ce ta shigo ta zauna, hakan yasa ta aje duk abin da take yi tana fuskantar Aunty da cewa.
"Aunty lafiya. Naga jikin ki duk a mace ."
Aunty Hauwa tai murmushi tana fad'in. "Kai Salma baki ga daidai ba , daman ina so na sanar dake akwai wani babban shago dana siya, tom akwai abaya a ciki , atamfofi da sauran duk kayan mata , to Salma babban shago ne , akwai ma'aikata , ina so gobe ki shirya muje , domin zan mallaka miki shi ."
"Me kika ce Aunty."?
Cewar Salma
Aunty Hauwa tai murmushi tare da mikewa tsaye tana cewa. "Ai kinji duk me na fad'a, kuma bana son godiya." Tana gama maganar ta fi ce
Ai Salma ji take kamar ba ita ba ce , irin wannan babban magana, tom sai dai mu ce Allah ya tabbatar da alheri, aiko washe gari da safe , suka shirya suka tafi wannan babban shago , aka nunawa Salma komai , sannan Aunty ta wuce office
Anan kuwa Hadiza ce a online.
Bude datarta ke nan ta ga sabon update na cigaban Littafin HIJIRA na Autar marubuta
Yadda ta ga ana posting dinshi a koina take mamakin yadda wannan abin ya faru .
Kai tsaye ta nufi Facebook shafin Autar marubuta
"Alhamdulillah masoyana na dawo , cikin ikon ubangiji bayan doguwar jinya , na yi kewar ku sosai."
Abin da ta gani ke nan, kwana daya da rubutawa
Hankalin ta ne ya tashi ganin wannan lamarin, like dubu biyar akai wa wannan Post na Salma, banda comments marasa adadi , zazzafar ajiyar zuciya tai , tana cewa."Kutumar u..."🤭
Cikin mamaki take sanar da mahaifiyarta, yayin da Umma take tambayar ya za ai , Hadiza ta ce abar mata komai a hannunta
Karima kuwa kullum tana sauraran Littafin Fatima da zarah da ake yi a gidan redio, Littafi ne mai yawan gaske , domin kuwa har yau ba a kammala ba , wayarta ta lalace hakan yasa Karima bata WhatsApp, sai idan an karbo daga wajen gyara
Sunan Autar marubuta ya yi shura sosai, hatta a masana'antar kannywood saboda irin fina finai da take rubutawa, sai dai ana kawo mata gayyata sosai daga gidajen television domin hira da ita , sai dai Salma bata amsar wannan bukata, ta ce akwai lokaci
Sir Sadiq Abubakar yana matukar farin cikin yadda Salma take tare dasu har yanzu, ita ma Aunty Hauwa ba karamin alfahari take da Salma ba, sai dai duk yadda zatai alfahari da ita, to Salma tana ninka wannan adadin tana alfahari da Aunty Hauwa
Tana cikin falonta, gefe aje da shayi, tana rubuta wani fim , Aunty Hauwa ce ta kwala mata kira tana daga falo , hakan yasa Salma tashi ta nufi falon, zama ta yi tana cewa.
"Aunty meke faruwa."
Aunty Hauwa ta ce .
"Gaskiya Salma na yi mamaki sosai, ki dubi adadin ribar da kika samu 2 millionaire Salma, cikin kankanin lokaci, Allah yayi wa rayuwar ki albarka, sai dai daga yau duk abin da aka samu kar naji labarin, domin sirrin ki ne ."
Dariya Salma tai tana cewa. "Kai Aunty."
Ita ma dariya ta yi tana cewa.
"Sannan kuma an kirani daga gidan redion Kano Salma, akwai abokin aikina a can , ya ce kuma sun nemi hira dake , amma baki amince ba , tom dan Allah Salma ki amince ."
Saida tai ajiyar zuciya mai zafi, sannan ta ce .
"To Aunty, ai duk abin da kika ce mini wajibi na aikata, kinfi karfin wannan, su ne mutanen farko dazan fara hira dasu ."
Aunty Hauwa ta ce .
"Yawwa kanwata , Allah ya kara Basira da lafiya da nisan kwana, sannan kuma tare zamu je kanon , daga nan zamu biya gidan yayan baban nan naki ."
"Saboda nima zan yi kwana uku bana aiki a lokacin."
"Tom Aunty."
"Amma Aunty ina so daga nan zamu je Bauchi, domin ganin su Inna, ina so na saiwa Yaya Aliyuu mota."
Murmushi Aunty Hauwa tai tana cewa.
"To Salma rigima, banda abinki ai ni Baba Laure ya kama ki yiwa wani abin. Ammma tunda haka ne , akwai tsohuwar motata, sai a bashi , ita kuwa Baba Laure zuwa hajjin bana ki shirya zuwa da ita ." Ta karasa maganar tana dariya
Ita ma dariya sosai Salma tai , kafin ta ce ."Tom shi ke nan Auntyna. Allah ya saka da alheri na gode ."
Aunty Hauwa ta ce ."Babu komai ai Salma, mahaifina yabar mini dukiya mai yawa, zan yi amfani da ita domin gina lahirarsu da tawa. Sannan kuma yau zan bada akai motar Kano, idan munje sai a dauka danke baki iya mota ba ."
Tai dariya tana cewa."Aunty banda gori ."
bayan Salma ta koma daki , ta tsaya ta yi jimmm
Cikin zuciyarta take cewa.
"Tabbas lokaci ya yi dazan fadawa Aunty Hauwa gaskiya koni wace ce, domin na gaji da yaudarar ta, Allah yasa ta fahimce ni ."
Taji wasu hawaye