← Book details Mahreen Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 17

Sashe 6

Mahreen Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Agaban table din ta tsaya tana karewa office din kallo saida ya danyi rubuce rubucensa sannan ya dago a tsaye ya ganta kamar an dasa ta phone dinta take bubbugawa akan lip dinta tana kallon wani wuri have a sit ya fada bata motsa ba ki zauna ya sake fada still bata motsa ba kansa ya dafe ya zuba mata Ido kamar ba zaiyi magana ba yace mahreeen kamar bayaso dagowa tayi idonsu cikin na juna why are you trying to give me a headache , "mee! hararar ta yayi sannan yace akwai wata ne bayan ke sau nawa ina maki magana kinyi shuru sorry I don't think you are talking to me Cox u haven't mention my name zuba mata Ido yayi dan ji yayi kamar ya maketa saboda haushi adan tsawace yace nace ki zauna ko kika min tsaye a Ka bata rai tayi ba a min tsawa Maher really ya fada yana juyi akan kujerar sa I'm your superior here not ur cousin you don't have the right to address me informally kujera taja ta zauna ba tare datace komai ba shuru office din yayi na dan wani lokaci sannan yace your name batare data kalleshi ba tace mahreen ishaq abdallah sunan ya maimaita har saida ta dago suka hada Ido ta dauke kanta meya kawoki nan , kallon Ka raina min hankali ta watsa masa kafin tace aiki , "ke ba law kika karanta ba meye hadinki da hukumar DSS ba tare data tambayeshi ya akayi yasan ita lawyer bace ta bashi amsa da I earned both my first degree in law and my masters degree in defence and security studies, how old are you ? This question is not relevant here ta fada tana daure fuska kamar wadda aka aikowa da mutuwa , tabe baki yayi tare da dage kafada irin I don't care din nan sannan yace wancan shine part dinki a office din nan and wancan toilet ne yana gaba fada ta mike zata fara tafiya cikin fada fada yace did I ask u to go I haven't finished juyowa tayi cikin masifa itama I have told you before don't shout at me I'm not your daughter although I will work under you, that doesn't give you the right to control me , I also want to remind you that I'm not going to work here permanently hope you Gerrit Ido cikin Ido suke kallon juna idonsa ya maida Kan hannun ta data matse spec dinta sosai kamar zata balle shi saboda masifa sannan ya sake dubanta juyawa tayi tafara tafiya yace mahreen kamar baza ta tsaya ba sai kuma dai ta tsaya ba tare data juyo ba tace lemme be.
shuru yayi yana nazarin yarinyar there's something peculiar about her I need to know more about her.

Tana fita taciro p cap dinta ajaka ta saka sannan tayi waje can wani waje data ga da kujeru karkashin wata bishiya nan ta karasa ta zauna ,duniyar tunani ta fada dole ta nemi mafita indai haka aikin nan yake dole tafara aiwatar da aikinta tun wuri ta rabu da wanna jarabar dan baza ta zauna mutum yana bat umarni ba kamar ubanta saida taji zuciyar ta tayi sanyi sannan ta tashi ta koma yaji shigowarta amma bai dago ba wucewa tayi Inda yace part dinta ne ta zauna kafarta ta dora kan table din sannan tafito da wayarta Kiran husna tayi suka gaisa ahankali take maganar har suka gama , dagowa yayi ya zuba Mata Ido kafar yabi da kallo kamar bata taka kasa sannan ya maida kallon sa gareta dole yasan komai da wurwuri domin take taken yayi yawa to me ma yakawota nan kuma mai take taqama dashi da har take irin wanna abubuwan, sarauta wata zuciyar taba shi amsa to ai shima jikan sarkin ne meysa sai ita yasan idan yace kiranta zaiyi wata sabuwar rigimar ce shi kuma baya son surutu da yawa pistol ya dauko sabuwa a drawer office din ya hada mata komai ya cikata da bullet sannan ya nufi table dinta a kujerar gaban table din ya zauna ya dora bindigar Kan table din dagowa tayi taga kafarta yake kallo saukewa tayi tana cigaba da abinda take dauki yace yana mata nuni da bindigar dan tura kujerar baya tayi sannan ta bude locker dake gaban table dinda kafa dan yatsa tasa ta dago bindigar ta wurga cikin locker din hmmm ya sauke wata boyayyar ajiyar zuciyar sannan yace ba anan nace ki ajje taba ki dauka ki tafi da ita gida taki ce amma kiyi taking care, okay tace kawai a ina kikayi karatu wanne daga ciki tabashi amsa both Australia and Russia why did u assume you wouldn't work here permanently ? Cox that's not my ambition , " and why do you choose it right now ? this is my personal plan and it's none of your concern baice komai ba yayi shuru can kuma yace there's a case I'd like your help with , come over when you are ready to hear the details ya fada Yana tashi ya koma Kan table dinsa saida tadau wasu lokuta ya ma dauka baza tazo ba sannan ta tashi ta karasa bayani ya fara mata sosai ta nutsu take sauraran sa har ya gama bayanin sannan ya mika mata file din mikewa tayi ina fatan kin fahimta yea and I will go through the information again good ya fada ita kuma ta wuce.

1:30pm ya shiga yayi alwala sannan ya fita yayi sallah Inda ya barta nan ya sameta ke bakya sallah ne ya fada , Bani da hijabi saida ya harari kayan jikinta sannan ya zauna waya ya dauka yayi dan danne danne sannan ya ajje kusan 30 minutes miss rabi ah ta shigo sai falli take rike da wata leda a hannun ta gashi sir ta fada pointing mahreen yayi da hannu miqa Mata karasawa tayi tace gashi from where ta tambaya sir Maher kallon sa tayi taga hankalin sa ma baya kansu okay thanks tace ita kuma ta wuce tana hararar ta budewa tayi taga jilbab ne aciki black colour tashi tayi tayo alwala sannan ta dau pray mat dinda ta gani ta saka hijabin ta tada sallah koda ta idar saida tayi addu a wa iyayenta da ya yanta sannan ta mike come and take your lunch kallon table din tayi leda biyu ta gani iri daya I'm not starving , bai sake cemata Kala ba ta cire hijabin ta linke ta maida a ledar sannan ta linke pray mat din ma ta maida Inda ta dauko abubuwanta ta hada a jaka ta saka p cap dinta ta gado ta dauki key din motarta sannan ta dauki wanna file din daya bata tayi hanyar waje where are you going wrist watch dinta ta duba it's almost 3 , and so , " I'm going to my office , office ya nanata yana dagowa yeah I'm going to our chamber whom do you ask for permission maimakon ta amsa masa saita maida masa tambayar what's your closing time ? I'm the one asking the question here not you dan yatsina fuska tayi I'm leaving now set your questions aside I'm going with or without permission and that's final, " do u know our rules ? They are for those staying long term tana gama fadar haka tayi waje wayar sa ya jawo ya rubuta message ya tura Kira ne ya shigo wayar da dagawa yayi da fadin yeah ita tare da katse Kiran.

Tana fita chamber su ta nufa saida ta nutsu tabi baya nan dake cikin file din da ya bata daki daki sannan ta tsunduma kogin tunanin yadda zatayi gaskiya ta bayyana tabbas tasan Abdul hameed shine makashin iyayenta but a yanzu bata da evidence dole ta shiga jikin ya yansa dake gidan da haka ta yanke shawarar zuwa gida domin ta shirya ta koma masarauta tana samun baya nan data keso zata bar can din .

Aunty ummi ta nuna rashin amincewarta da komawar mahreen can din amma dole dole ta tada bori akan sai taje haka ta barta amma da sharadin ba gaba daya ta koma ba murmushi tayi kawai tare da girgiza mata Kai Imran ya shiga rudani saboda barin mahreen gidansu badan komai ba sai dan shishshige matan da ayman yake yi amma ba yadda zaiyi ya san tunda tace sai taje sai taje din haka ta har hada duk abinda ta san zata bukata sannan ta nemi aunty ummi tai mata transfer wasu kudade a acc dinta.

Komawarta masarauta kamar a kunnen Abdul hameed aunty amarya kuwa cewa tayi abu yazo da sauki husna ta shiga rudani sosai baza ta sake bari akashe mahreen ba saboda tasan itama Allah saiya kamata da laifin boyewa datayi tunda har da saninta.

TWO WEEKS LATER
Chapter 6 · 0% Book details