← Book details Mahreen Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 17

Sashe 16

Mahreen Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Washe gari tana tashi ta duba time 5:09pm ta gani ganin dakin bakowa yasa ta mike dama tana fashin sallah wanka ta shiga ta fito ta shirya sannan ta fita parlour shima shuru sai hadimai ne daketa hidima suna ganinta suka zube suna kwasar gaisuwa hannu kawai ta daga masu ta shiga kitchen ta zuba juice a cup sannan tafita garden ta kofar baya Maher ta gani zaune ya zubawa waje daya Ido duk yayi rama jikin ta ne ya karayin sanyi harta karasa taja kujera ta zauna tare da cewa good evening sau daya ya kalleta ya dauke Kai Yana kokarin tashi Maher ta Kira sunansa slowly tsayawa yayi shi bai tafi ba shi bai juyo ba sai kuma tarasa mai zatace tafiya ya fara har ya fice daga wajen cup din juice din ta daga ta buga da bango zuciyar na wani irin zafi wayarta ce tayi Kara ko dubawa batayi ba ganin an ki de na Kiran yasa ta daga ba tare data duba sunan ba cikin masifa tace wai waye ne yake damuna Imran kuwa a zuciyarsa cewa yayi nasan zaa ri na ba tana tare da wanna yaron ba watakil ma ya hure Mata kunne ina waje ku fito kawai ya fada kashe wayar tayi ba tare data amsa ba ta tashi ta koma ciki.
a dakin ta samesu sun dawo nawal ce tace mahreen ya Imran yazo yana waje yana jiranmu bata tanka mataba ta dauki hijab ta makala sannan tayi waje what's wrong with her manira ta tambayi nawal I don't know too ta fada da mamaki meya bata mata rai haka kuma daga ina take da wanna tunanin suka fito granny da fitowarta parlour Kenan suka Mata sallama nawal maiya samu yar uwar taku naga ta fito kamar zata tashi sama , whl mu ma haka ta shigo mana mun barta tana bacci mukaje part din Ammi shine dawowar mu muka Tarar bata nan sai kuma gashi nan ta shigo ranta abace , Allah ya kyauta Ku gaida mamanta ku ita kuma wanna ina zata ta tambaya tana nuna manira husna ce tace wai part din Ammi zata koma tunda mu tafiya zamuyi , au kaura zaku mun duka Kenan to ai ni duk Wanda yaci tuwo dani miya ya sha zaa zo a sameni ne duk dariya sukayi har manira da bata san Mai grannyn ta fada ba sannan suka fice a mota suka samesu sallama suka yiwa manira ta wuce part dinsu su kuma suka shiga mota.

Fitowa tayi cikin Shirin fita yace ina zaki ne love ? zanje na aje aikin ne kamar yanda na ma alqawari murmushi yayi cikin jin dadi to ko kefa my love adawo lpy take care of yourself for me wucewa tayi ba tare data sake magana ba.

tunda ta shiga office din ta hangoshi shida miss rabi ah suna magana ganin shigowarta yasa ya canja hirar daga ta aiki zuwa wata hirar daban itama miss rabi ah wanna damar tayi amfani da ita ta fara zuba masa labari murmushi kawai yake dukda bai Kai zuci ba, sosai taji zafin ganinsu a haka wanda har hakan ya kasa boyuwa a fuskarta karasawa tayi ba tare da tayi magana ba ta dora masa takardar akan table ta juya tsintar muryarsa tayi Yana fadin takardar miye ne wanna din? resignation letter ce , to ai bani keda alhakin karba ba sai kije wajen sir JB juyowa tayi cikin dacin rai ta warci takardar saida takusa bakin kofa yace wa miss rabi ah dear bita ki karbo takardar tashi tayi cikeda jin dadi ta bita dan karbo takardar a maimakon ta bata takardar saita hada harda IV bikin su tace gashi kya hada masa dashi sannan tabar wajen cikin sauri ta karasa ta shiga mota kifa kanta tayi akan steering tayi shuru ta rasa Mai yake Mata dadi saida tayi kusan five minutes tukun tasamu ta tada motar ta fita a harabar wajen.

Miss rabi ah tana komawa tace gashi wanna kuma tace abaka ta bashi IV din, file din dayake Mata magana akai dazu ya mika Mata zaki iya tafiya cike da farin ciki ta wuce dan yau ta samu fuska wajen Maher , IVn ya dauka Yana kallo yayyaga wa yayi sannan ya mike ya zuba a dustbin safa da marwa ya fara Idonsa cike da hawaye zuciyarsa tafara masa nauyi abubuwansa ya dauka ya bar office din.

YOUNG WRITER

MAHREEN

END 91-----100

Shirye shiryen biki ya kankama Inda ya rage saura kwana uku a daura aure da yake sai an fara daura aure tukun na ayi sauran event din yayin da amarya take kwance ba lafiya ko abincin kirki taki ci anyi anyi aje asibiti taki dole haka suka hakura suka zuba Mata Ido, Ammi taso ta dawo wajen ta har a gama bikin amma aunty ummi ta hana acewarta ai itama yartace ba sirika ba ganin maimartaba yasa baki yasa aunty ummi hakura da in an daura aure zata koma fada har sai an gama events din saita tare a gidanta.

A bangaren Maher kuwa tunda yaga shirye shiryen da ake a masarauta na bikin mahreen ya shiga daki ya kulle kansa ya kashe wayoyinsa anyi neman duniya an rasa shi sosai iyayensa suka shiga tashin hankali especially abba wanda yasan kwanan zancen wasa wasa har ranar daurin aure ba Maher ba labarin sa , Ayman ne ya shigo part din dan daukan wani abu a dakin Maher zuwa yayi ya jijjiga kofar a kulle Allah yasa suna raba spare key daukowa yayi ya gwada cikin sa'a ya bude can ya hango Maher karshen gado Yana fidda numfashi da kyar da sauri ya karasa Yana masa magana ganin baa cikin hayyacinsa yake ba yasa ya fice da sauri fada ya nufa acan ya samu mahaifinsa janshi yayi gefe ya fada masa abinda ke faruwa komawa yayi shima sannan ya sanar da maimartaba shi kuma suka tafi shida Ayman domin kaishi asibiti.

Abangaren mahreen tunda ta tashi yau da ciwon Kai da zazzabi mai zafi har suma take nawal ce tafita da gudu ta sanar da aunty ummi halin da ake ciki driver tasa nawal din takirata Mata don Kai mahreen asibiti sannan tabukaci sana da nawal din su tsaya da baki ita da husna kuma su kaita asibitin , ahanya take Kiran Imran take shaida masa shima cikin tashin hankali yace zai same su acan.

MASALLACIN FADA

2:00pm daidai bayan an idar da sallar jumma a aka fara sanar da an daura auren MAHER KHALED ABDALLAH da amaryarsa MAHREEN ISHAQ ABDALLAH Akan sadaki dubu Dari biyar sannan aka sanar da daurin auren IMRAN MUKTAR AYUB da amaryarsa MANIRA KHALED ABDALLAH Akan sadaki dubu dari biyu , duba na kai wajen Imran kwallar data tarun masa a Ido ya dauke Yana amsar gaisuwar mutanen da suke masa murna.

Abangaren majinyata kuwa da suke hospital Ayman ne ya shiga dakin da aka kwantar da Maher idon sa biyu amma idanunsa a rufe karasawa Ayman yayi Yana dariya angon mahreen sai a tashi cuta ta kau bude Ido yayi akan ayman dan neman Karin bayani ,videon ya masa playing awayarsa daidai lokacin da ake am batar an daura auren MAHER da MAHREEN ,Mai hakan yake nufi Ayman taya hakan ta faru murmushi yayi za kaji komai abakin Mai martaba Amma ba yanzu ba , "Ayman maisa zakuyiwa mahreen haka bani takeso ba Imran takeso ta fadamin da bakin ta shin wani irin kallo kukeso ta min mai son kansa ? dariya ayman ya saki da fadin ai duk jirgi daya ne ya kwasoku domin ita mahreen din ma yanzu haka tana cikin asibitin nan an kawoka da kadan itama aka kawota kuma I'm sure itama dalilin dayasa aka kawoka shi yasa aka kawota , " Ayman Kana nufin mahreen ma tana cikin irin halin danake ciki kwarai kuwa Maher ai..... Maganar sace ta tsaya ganin husna ta shigo da gudu tana kuka tana nuna masu hanyar waje menene Ayman ya tambaya mahreen ta bashi amsa ai kafin ta karasa bayanin Maher ya fisge Karin ruwan da ake masa sai ganinsa sukai abakin kofar da sauri husna takarasa fita ta nufi room dake opposite da nasu suka rufa Mata baya abinda ya faru kuwa shine farkawar ta Kenan husna tafara tsokanarta da an daura an daura ta Zama matar ... .bata Karasa ba numfashin mahreen yafara sama da kasa shine dalilin dayasa ta rikice ta fada dakin Maher .

Ko da suka shiga ta sake suma Ayman ne yafita da sauri Dan Kiran doctor, doctors biyu ne suka shigo cewa sukayi su fita Maher ne yace shi ba zai fita ba dakyar doctor rukayya ta samu ya fita Amma a kofar dakin ya tsaya .

Kusan 40 minutes suka fito dashi suka fara cin Karo doctor rukayya ce tace ta farka Amma munsa mata oxygen kafin numfashin nata ya daidaita yanketa yayi ya shige ciki gaban gadon ya karasa ya kamo hannun ta ya hada da nasa yace mahreen dagowa tayi ta zuba masa Ido kokarin cire oxygen din take ya riqe hannun rufe Ido tasakeyi hawaye na zuba ta gefen idonta mahreen open ur eyes and see me ni ne Maher dinki ur husband Ido tasake budewa sosai tana kallon sa yace yes I'm ur husband dani aka daura maki aure bada Imran ba su Ayman ne suka shigo shida husna ina wayarka Ayman Mika masa yayi ya bude videon sannan ya nuna mata sake lumshe idonta tayi Ayman ne yace husna taso kiga muyi waje .

Ganin numfashin ta ya fara daidaita yasa ya zare oxygen din sannan yatemaka Mata ta zauna sai a lokacin ya lura da yadda jini yake zuba ta wajen cannula dinda aka samasa cireta yayi gaba daya sannan ya karasa ya dauko tissue ya danne wajen karasawa yayi ya dale gadon da take zaune kanta ta dora Kan kafadar sa shi kuma Yana Mata magana a hankali shigowar su aunty ummi ,Ammii da abba yasa yai shuru kokarin raba jikinta da nashi take amma bai bada damar hakan ba murmushi irin nasu na manya abba yayi sannan ya dubi aunty ummi ai inajin kawai a sallamesu ko tunda naga sun samu sauki , "hakane barin ga doctor din.
Chapter 16 · 0% Book details