← Book details Mahreen Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 17

Sashe 4

Mahreen Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

mahreen aunty ummi takira sunanta cikin rashin jin dadin abinda tayi kallon aunty amarya tayi tace evening, "evening din uwarki nace eveni....... Shigowar Abdul hameed ya hana ta karasawa kusa da matarsa ya karasa ya zauna Yana fadin ashe kunshigo nan aunty ummi ce tayi murnushin karfin Hali da fadin eh whl , mahreen da zuciyarta ta taso jin ta zagi mommyn ta , cire spec din idonta tayi ta kalli wanda akace kanin kakanta kuma makashin iyayenta tace tell your wife to get back into her sense sannan ta kalli aunty amarya this is the first and last time you will disrespect one of my parents in front of me, " owooo you are showing me that u lack morals and respect, husna ce ta shigo ta gaishesu sannan ta zauna Baba baki mukayine eh e-h ya fada kamar adan rikice sannan ya nuna mahreen jikar Mai martaba ce kuma yar ishaq Wanda suka rasu shekaru biyu da rabi daya wuce , they died or were killed ta fada a dan tsawace tana binsa da kallo dan ta fara loosing control ,rikicewa yayi eh eh aka kashe su mantawa nayi amma ai dama lokacin su yayi dan daba haka ba baza su mutu ba cike da tausayi husna take kallonta ganin an maidata marainiyar karfi da yaji ko uba ka rasa ya zakaji balle kuma harda uwa da kuma ya yanta Allah sarki may Allah have mercy on their pure soul mahreen may Allah grant them jannah and expose all those involved in their killing, wata muguwar harara iyayen suke aika mata kamar zasu rufeta da duka duk abinda suke mahreen na lura dasu amma tayi kamar bata gani ba kallon husna tayi suka hada Ido alama tai mata da number ta itama sign ta mata na bari su tashi girgiza Kai mahreen tayi sannan ta mike ta karasa wani table karami da aka daura littattafai akai pen ta dauka ta rubuta number ta kananu a yar karamar paper ganin duk sun zuba mata Ido yasa ta yayyaga takardun saita barbaza su akan table din dagowa tayi ta dan wurgawa husna pen din paper data rubuta number ta dauka sannan ta karasa a fakaice ta wurga Mata takardar sannan ta kashe Mata Ido taya ta karbi pen dinta paper tasake yagowa ta koma Inda ta tashi ta zauna ta daura kafa daya Kan daya duk ita suka zubawa Ido wani rubutu tayi sannan ta Mike ta dauki bag dinta aunty ummi let's go, " ohk dama yanzu zamu wuce ta fada tana sauke ajiyar zuciya sallama suka masu mahreen ce taje gaban kujerar su aunty amarya wani kallo take jifansu dashi cike da tsana sannan ta sunkuya kamar zasu hada goshi da aunty amarya I will show you that I lack moral and respect ta fada tana wani kankance idanuwa sannan tafara tafiya ball tayi da mug dinda ke gaban kujerar tasu take ya tarwatse sake juyowa tayi ta kallesu sun zuba Mata Ido in shock kamar zatayi magana sai kuma ta fasa ta kalli mug din dayayi pieces sannan tayi waje anan tayi joining dinsu dan dama basu yi nisa ba Ayman ne yake janta da magana ba komai take amsa masa ba domin yanzu tana bukatar time tayi tunani akan wanna lamarin shiko Imran haushi ne yakama shi saida suka kusa mota ayman yace have you finished studying sister ? yea! which course ? criminal law tabashi amsa a takaice wow I am also a lawyer juyowa tayi daidai lokacin zata shiga mota mika masa wayarta tayi insert ur digits here karba yayi yasa mata sannan yayi flashing awayarsa ya mika mata nata wayar karba tayi ta rufe kofar suka wuce.

YOUNG WRITER

MAHREEN

PAGE 21---30

MAHER

sai 11pm ya dawo part dinsu ya wuce wanda ya kasance shi da Ayman ne masu mallakin part din a parlour ya sameshi yana ta dube duben littattafai irin nasu na lawyoyi a kujera ya zube yana fidda pistol din da ke bayan wandonsa ya aje akan center table , "kadawo bros Ayman yace yana dagowa , " Bari kawai tun dazu naso dawowa sai kuma mukaje wani investigation kuma har yanzun da nake fada ma ban kammala binciken ba, " wanna aikin anya baya ma yawa kuwa Maher kaje nan kaje can , hmmm kawai yace Ayman kuma ya cigaba da fadin dazu yarinyar uncle ishaq sunzo, " uncle ishaq dai wanda yarasu ? eh dazu sukazo da auntyn ta Kana fita suna shigowa ko itace wata marar kunya mai shade, " dariya ayman yayi dukda baisan me ya hadosu ba amma ya bashi dariya yace kwarai itace amma fa kasan miye bruh yarinyar tana da abin al ajabi da daure Kai bakaga yadda tayiwa grandfa Abdul hameed ba da aunty amarya abin ya dauremin Kai sosai sai kace wasu abokan gabarta Maher daya nutsu yana sauraron sa yace mai tayi tho? kasan dokar gidan nan dama idan dai kaje part din manya to akasa zaka zauna sai Kaine ma da kake karya dokar to ita ma halinku daya yadda baka shiri da aunty amarya itama haka amma kusan nata yayi worst saboda bakaji yadda ta dinga maida masu magana ba bata da tsoro ko kadan.......... nan ya kwashe duk abinda ya faru ya zayyane masa shuru yayi can kuma yace baka tunanin akwai wata a kasa kuwa Ayman nifa inaga haka kawai baza tayi musu haka ba ko dan girmansa a matsayin sa na kanin kakanta , "Nima gsky nayi tunanin hakan amma tunda munyi exchanging numbers sannu a hankali zansan komai kuma tunda ita ta fara neman number na ma kaga kamar tana da magana dani Kenan , mikewa Maher yayi yana daukan bindigar sa yace kamin sending number din ta ta, " ohk yace kawai.

Abangaren aunty amarya da Abdul hameed kuwa mahreen tana fita itama husna ta tashi Dan taje tasa number da mahreen ta rubuta Mata nan tayi Musu Saida safe ta shige , Abdul hameed ne ya juyo Yana fuskantar ta fiddausi munfa kashe maciji ne amma bamu sare kansa ba wani murmushi tayi haba Alhaji muka Kawar da manyanta ma bare ita karamar kwaro karka damu zan sa a kawar mana da ita kawai dan karta kawo mana matsala muji da wa annan biyun ma na wajen Khalid da suka zame mana karfan kafa, husna ta manta da Jakarta a parlourn hakan yasa ta juyo domin dauka taji abinda ya girgiza tunaninta da sauri ta boye bayan labule tareda saurin danna recording Abdul Hamid ne ya cigaba da magana taya hakan zata kasance fiddausi kashe wanna yarinyar fa a yanzu ba karamin aiki bane dan daganin ta tsagera ce batada tsoro nisai nake ganin ma kamar ta gano wani abun , "haba mana Kai kuwa karkabar kanka ya kulle mana Ka barmin komai a hannuna kamanta wace ce ni kenan na dade fa ina doraka a hanya tun wancan lokacin damuka yiwa shi Mari gayi kurciya muka sa akayiwa Khaled allurar poison kuma a karshe Ka Kai shi ishaq din da iyalansa barza u saboda gudun matsala yanzu kuma wanna yar karamar kwaron ce zatasa Ka firgita ai kawai itama binsu zatayi kuma suma wanna Maher din da ayman indai aka kasa daga minsu daga kasarnan to Suma kawai kashesu zansa ayi kaga sarauta dai dole hannun Ka zata dawo wata dariya yasaki shegiya fiddausi akwai brain fa saisa nake sonki kina daurani Kan hanya , husna da tayi Saving din recording dinta wayarta tayi Kara da sauri suka juyo waye anan abdul hameed ya tambaya Yana mikewa haba Alhaji kafiya tsoro fa wayatace tayi Kara kagan ta can ta fada tana nuna masa wayarta dake charge kusa da curtain dinda husna ta buya ajiyar zuciya ya sauke Yana kallon ta ni mamaki nake yadda Ka iya kashe har mutum uku ahakan da wanna shegen tsoron kamar farar kura , baza ki gane bane fa, " amma kasan dai bawanda zai shigo idan ba kiransu nay iba husna kuma ta shiga bacci dan haka Ka kwantar da hankalinka fa .
Chapter 4 · 0% Book details