← Book details Mahreen Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 17

Sashe 14

Mahreen Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ko da ayman ya fada masa abinda mahreen din tace yi yayi Kamar bai ji ba can kuma ya yunkura ya fito hannunsa zube a aljihu har ya karaso ya koma ainahin Maher din sa dan ba alamun wasa a tattare dashi Imran ne ya mika masa hañnu domin su gaisa ba tare daya kalle shi ba ya daga masa hannu alamar salam sannan ya juya wurin mahreen din sauri nake je ki canja Kaya fita zamuyi, " Imran ne yace ha a Malam yaza kazo ka sameta sannan kace ta tashi ta canjo Kaya kufita ko ance maka bata da ma fadi ne zaman kanta take a duk lokacin data ga dama tafita aduk lokacin da taga dama ta dawo sai a lokacin ya daga Ido ya dubesa a wulakance idan ina magana da ita ka dena tsoma min baki kuma inada iko da itane sai sa nace ta tashi taje ta canjo Kaya ko kana da ja , " Kai awa zakace Kana da iko da ita ni nan ni ne mai iko da ita saboda ni ne mijinta wanda zata aura nan bada jimawa ba , wani kallon tara saura kwata yai masa yana ebansa a sheqale ya watsar miji oh really to bari mugani taku daya ya kara tare da kawata fuskarsa da murmushi cikin wani salo yace my princess tashi kije ki canjo Kaya karkimin wanna banzar shigar kiyi shiga ta mutunci kinji na baki five minutes mikewa tayi a fusace Imran yace lilly idan har na isa dake koma ki zauna itama cikin daga muryar tace imrannnnn stop it meye hakan wai kakeyi ne ta karashe tana wucewa ciki , yatsu biyu ya sa a baki tare da yin wani siririn fito yana murmushi tare da juya kwayar idanunsa kamar wata mace tho ya kaga Wasan ya fada yana wucewa ya bar Imran din daya kasa wani kwakwaran motsi.
mota ya koma ayman ne yace mai ya faru naji kuna ta hayaniya ko kallon sa baiyi ba idon sa na kofar fitowa daga falon aunty ummi ganin haka yasa Ayman Jan bakin sa ya sa kwado ya kulle dukda ba hakan ya so ba dai .

Shiryawa tayi cikin dubai abaya black mai golden stones ajikin veil din datayi rolling dashi an rubuta sunanta da stones din ta dauki jaka da takalmi black samun kanta tayi da cewa aunty ummi zata masarauta ta dawo dukda bata san ina zasuje din ba sannan tai wa su husna sallama ta fita tana fitowa ya sha gabanta, mahreen wai me kike nufi dani ne miye tsakaninku da har ina mijin da zaki aura namiki umarni ki ki bi , Imran yaka Mata Ka gane dan Kana mijin dazan aura ai ba aurena kake yanzu ba nifa ba yarinya bace nasan me nake, " ohk haka kikace , cikin tabbatar wa tace naam haka nace Imran , "to shikenan zanyi wa tufkar hanci , ka hada harda baki ma ta fada tana wucewa ta bude back seat ta shiga yaja mota suka fice.

YOUNG WRITER

MAHREEN

PAGE 81---90

PALACE

Bayan sun shiga sun mika gaisuwa Ayman yace wa waziri suna da magana da maimartaba , sallamar mutanan fadar akayi sannan yace dasu sarki na sauraren Ku bayani suka fara masa tare da kunna masu duk wasu audio.
Sarki mai adalci da tawakali ya girgiza da jin abinda kaninsa ya aikata masa uwa daya uba daya akan Mulki ya nakasta masa ya ya da duk duniya bashi da wa anda yake kalla yaji dadi saisu cike da bakin ciki yace wa Maher Allah yakaisu ranar zaman kotun.

Duk wasu evidence daya kamata Ayman da mahreen su tanada sun hada domin so suke ranar da aka hau kotu a yanke hukunci kawai duk wasu maganganun sirrin da Abdul hameed yayi a waya mahreen ta tantancesu, sun bawa Abdul hameed damar daukan lauya haka kuwa akayi yayi wa lauyansa magana tare da masa bayani cewa karya ne shi bai aikata duk abinda suka ceba, ko da mahaifiyar Maher taji labari ta girgiza dama ta dade tana zargin furar da jakadiya ta dama ranar amma kasancewar batada hujja yasa tayi shuru kuma jin halin da ake ciki akan hargitsin da Abdul hameed ya kawo a masarauta yasa bata gayawa su Maher improvement dinda aka samu akan rashin lafiyar mahaifinsu ba , dan likitoci sunyi aiki sun qone ragowar gubar dake jikinsa sannan suka bada tabbacin zai kai one zuwa two weeks kafin ya farka amma suna da hope idan ya farka zai tashi lafiya.

Abangaren Imran kuwa daddysa da aunty ummi ya samu kan cewa sun daidaita da mahreen akan zasuyi aure shine yazo ya sanar masu ganin yadda suke sai basu bukaci jin ta bakin ta ba Inda daddynsa yace abari idan aka gama case din nan sai suje har wajen maimartaba suyi magana cikin farin ciki ya tashi ya tafi da fadin Allah yakaimu.

COURT

Cike take makil tako ina ka juya mutane ne waziri shiya wakilci Mai martaba can cikin lauyoyi na hango Ayman da mahreen suna ta hada takaddu rigistra ne ya Mike ya Kira shari ar su mahreen sannan yamikawa judges din su uku dake high table file din , judge din na tsakiya shi yace ina lauyan masu Kara Ayman da mahreen ne suka Mike sannan akace ina lauyan mai kare wanda ake Kara lauyan Abdul hameed ne ya Mike daidai lokacin da aka shigo dasu Abdul hameed da aunty amarya da chiroma da jakadiya Maher ne da yaransa guda biyu abayansu waje ya nema ya zauna , nan aka fara karanto laifin da ake zargin Abdul hameed dashi karyata wa yayi da cewa sharri ake masa shi bazai yi haka ba judge ne yace to ku kunji ya musa shin kuna da hujja mahreen ce ta Mike ina da ita hujja ya me girma me shari'a takawa tayi gaban Abdul hameed audion sa ta bude masa saida ya gama ji sannan ta karasa ta mikawa registra shi kuma ya kunnawa judges din duk suka saurara tukun aka kunna masu hotonsa tare da su chiroma da matarsa kuka ya fashe dashi da cewa na amince na aikata whl amma sharrin shaidan ne kuma da sharrin Matata ya fada Yana pointing aunty amarya ita ta jefani a bala'i , alhaji sharri zaka mun ni fa bansan komai ba muhawara ce ta barke a tsakaninsu har saida kotu ta tsawatar masu, kansu chiroma da jakadiya aka koma ba musu suka amsa yaran da suka tura ranar domin kashe su husna tare da yaran da suke tare da Abdul hameed a ranar daya kashe iyayen mahreen tambayoyi aka masu suka amsa lauyan Wanda ake kara ko kanada ja akan hujjojin da kuma bayanan da lauyoyin masu Kara suka bayyana cike da sanyi jiki yace bani da ya Mai girma mai shari a.

kotun ce tayi shuru na wasu dakika sannan Mai shari'a yace according to Section 319 of the Nigerian Criminal Code .
Subject to the provisions of this section of this Code, any person who commits the offence of murder shall be sentenced to death dan haka kotu ta yankewa Abdul hameed Umar Jamil hukunci kisa ta hanyar harbi da bindiga sakamakon rashin wahalar da shari a da baiyi ba kotu ce tayi tsit sannan judge yaci gaba da magana kotu kuma ta yankewa fiddausi auwal magaji hukuncin zaman gidan Kaso na tsawon shekara goma tare da horo Mai tsanani sannan kotu ta yankewa jakadiya daurin rai da rai sakamakon yunkurin kisan Kai datayi ta hanyar saka wa uban gidanta guba a abinsha sannan an yankewa chiroma shekaru bakwai gidan yari tareda Tarar 500,000 nan kotu ta dau hayaniya ,asaurara masu shari'a suka fada sannan aka koma Kan yaran nasu shekaru bibbiyu aka yanke masu tare da Tarar dubu dari dari sannan masu shari ah suka buga guduma duk mikewa akayi har saida suka fita sannan mutane aka fara maida zance mahreen ce takarasa wajen husna dake kuka ta dago ta rungume itama hawayen taji suna neman zubo Mata saboda tuno da mahaifanta da tayi aunty ummi ce ta karaso ta hada su duka ta rungume hakika husna kinyi sadaukarwa Kuma ubangiji shi zai maki sakayya da mafificin alheri hakika zan rikeki kamar yadda zan rike nawal kinji ahaka duk suka firfita waje .

fitowa akayi zaa tafi dasu Abdul hameed husna ta karasa wajensu "Baba kayafe min hakika banyi hakan dan na tsane ku bane idon Abdul hameed cike da hawaye yace baki min komai ba husna kuma na yafe maki domin taimako na kikayi dan nasan idan naje lahira azabar sai tafi haka gwanda amin anan duniya kuma nayi nadama ina fatan Allah ya karbi tuba na Allah yamiki Albarka yabaki miji nagarih wanda zai Kula dake inaso ki rokarmin yaya gafara ya yafemin kinji yana gama fadi aka tasa keyarsa mama tace tana riko kafadun aunty amarya juyowa tayi mama kiyafemin murmushi tayi ba komai husna Allah ya yafe mana mama fishi kike dani Dan Allah mama kiyi hakuri kiyafemin kema, ko daya ba fishi nake ba dama ko ba yanzu ba asirin mu sai ya to nu domin rana dubu ta barawo rana daya tak ta mai Kaya dan haka Allah ya miki Albarka ki Kula da kanki kirike sauran yayunki da hannu bibbiyu sannan ki dauki matar babanki lamya kamar ita ta haifeki kinji nasan bata da matsala zata Kula dake itama wucewa akayi da ita aunty ummi ce ta jata sannan suka shishiga mota direct masarauta suka wuce , ranar cikin jimami aka yita sai dare suka komo gida.

TWO WEEKS LATER
Chapter 14 · 0% Book details