← Book details Mahreen Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 17

Sashe 17

Mahreen Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ana sallamarsu direct fada suka nufa Ko da suka koma Maher kafarsa kafar mahreen har saida Ammi ta korashi tukun ya fita , washe gari akayi sa lalle Sunday kuma aka shirya mother's eve Inda da antashi kuma angwaye zasu kwashi amaren su su tafi Maher a masaurauta zai fara zama kafin ya gyara gidansa.

Mai martaba ne ya aiko yana son ganin Maher da mahreen , Yana kokarin shiga dakin Ammi ta fito ina zuwa kuma tace dashi dan shafa kansa yayi Ammi dama Mai martaba ne yace yana son ganin mu kallonsa ta tsaya yi dan dariya yayi Ammi baki yarda dani bane Allah da gaske nake kuma ki kirashi kitambaya, naji to jeka, to Ammi ai tare yace muje , naji jeka zan turo ma ita juyawa yayi ya fita ita kuma ta koma dakin lace ta dauko Mata skirt da riga sai babban mayafi ki shirya yanzu mijinki Yana waje Yana jiranki Mai Martaba na neman Ku to tace sannan ammin ta koma wajen bakinta.

Tunda tafito yazuba mata eyes sau daya ta kalleshi tayi kasa da kanta harta karaso bude Mata motar yayi saida ta shiga ya rufe sannan ya zagaya ya tada motar suka bar part din shuru ne ya ratsa motar har suka karasa fada kokarin bude kofa take yace a a madam tsaya mana bude wa yayi ya fito sannan ya zagaya ya bude Mata rankwafowa yayi ya gyara Mata veil din sannan ya mika Mata hannun sa kallon sa tayi yayi murmushi hannun nata ta daura saman nasa sannan ta fito tare suka jera cikin fada , fadawa nata Mika masu gaisuwa acan suka samu abba sai manira da Imran da alama su ake jira, karasawa sukayi suka gaishe da maimartaba sannan suka gaishe da abba Musabaha sukayi shi da Imran sannan yakoma ya zauna kusa da mahreen data sunkuyar dakai kasa abba ne yafara magana kamar haka nasan Kai Maher da mahreen da kuma ke manira zakuyi mamaki da yadda kukaji abun wato abun daya faru shine ana baifi saura awa biyar a daura auren ba wanna yaro dan Albarka ya fada Yana nuna Imran yazo nan fada ya bukaci yin magana dani da Mai Martaba duk da a lokacin ni ina cikin kidima halin dakai Maher kake ciki gashi kuma Kana kokarin rasata gaba daya hakan nazo nan fada muka zauna abun daya fara fada shine ya bar maka mahreen nan muka tambayeshi dalili yake ce mana a lokacin mahreen tana asibiti kuma rashin lafiyar saboda Kaine kamar yadda kaima kake asibiti ta dalilinta dan haka shi ya sadaukar da soyayyar dayakewa mahreen saboda farin cikinta sosai naji dadin hakan Wanda har yasa nace in har bazai takura ba na bashi auran yata manira bai min musu ba ya amince da Allah yasa hakan shi yafi alheri nan na samu mama Fulani da amminku na fada masu Amma na nemi a boye maki ke manira har sai na fada maki da kaina to kunji dalilin , Maher ne ya Mike ya karasa wajen Imran ya rungume shi nagode Dan uwa nagode da sadaukar war dakamin Allah yakara zuminci murmushi yayi shima bakomai dan uwa kuma sirikina shima murmushin yayi kafin Mai martaba yayi gyaran murya duk nutsuwa sukayi nasiha ya musu sosai sannan ya basu umarnin tashi Imran ne ya musu sallama ya fita abba ne yace manira ta tashi ta bishi cike da kunya ta Mike ta bishi juyowa yayi wajen Maher naji Ayman yace ka nemi visa zaku tashi a satin nan eh abba in sha allah, to Masha Allah Amma inaso kasani a nan masarauta zaka zauna nasa an gyara ma part guda naji amminka tana cewa wai kace daka gyara gidanka zaka koma to ban aminceba kansa akasa yace to abba yadda kace haka zaayi , to Allah yamuku Albarka da ameen suka amsa sannan suka tashi suka fito.

Juyowa yayi jin kukanta da baya ya dawo sunshine kukan na miye kuma oh nagane tsohuwar soyayyar ce ta motsa ko ya fada yana juyawa dan cigaba da tafiya a dan fusace ta baya yaji ta rungumoshi I'm so sorry ba abinda kake tunani bane ta fada cikin kukan juyowa yayi yace is okay daina kukan to yaja hannun ta dan ganin Ido yayi yawa a wajen .

8:00pm

Manira da mahreen na hango cikin wata alkyabba ta alfarma yan bikine suke ta shige da fice awajen hall din nawal naga ta fito a motar ganin Imran ya doso su magana sukayi Naga ya karasa ta gefen manira ya fito da ita wasu ganin motoci ne guda hudu suka Shigo filin ta farko Ayman ne da husna suka fito sauran kuma abokan Maher ne wanda rabin su Ayman ne ya gayya to su, Ayman dinne ya zagayo motar da Maher yake yace bros inaga fa kaikadai ake Jira ,sun karasone ya tambaya eh inajin ma mahreen dince kawai a motar take jiranka fitowa yayi ya fara takawa zuwa motar ya rankwafa ya kamo hannayenta duka dagowa tayi suka hada Ido gira ya dage Mata gira fitowa tayi kafarta ce ta dan gurde tayi baya zata fadi ya tarota ta fada kirjinsa rikeshi tayi gam dan ta tsorata har saida ya dagota hular alkyabbar ya daga my sunshine you look so gorgeous amma Mai kwalliyar tayi kuskure ka dan tissue ya zaro a aljihunsa ya kamo habarta jan bakin da aka samata maroon ya gogeshi tas bata fuska tayi sorry baby kinfi kyau a haka maida mata hular yayi sannan ya kama hannun ta suka gara tafiya nan shima Imran yafito da manira daga motarsa , amaren ne suka fara shiga Inda husna ta tsaya gefen mahreen nawal ta tsaya gefen manira dama ba wasu friends bane dasu saida suka shige tukun Suma angwayen da friends dinsu suka jera suka wuce , anci an sha anyi games tsakanin amare da angwaye sai wajen 12:30 aka tashi angwaye suka dauki amaren su suka wuce.

Suna Shiga part dinsu ta zame hannunta ta zauna a parlour dakinta ya nuna Mata sañnan ya wuce tashi tayi ta shiga nan taga akwatuna guda 24 da alama na lefe ne kayan jikinta kawai tarage ta watsa ruwa ta fada gado.

kwana biyu tsakani ya shigo dakin zaune take akan gado tana faman latsa waya wata karamar vest ce a jikinta sai wando Wanda da kadan ya wuce guiwarta kallo daya ya Mata ya kauda Kai tun ranar da suka dawo daga dinner sai yau suka sake haduwa bakin gadon ya zauna good afternoon tace kasa kasa murnushi yayi noon my sunshine dama zuwa nayi nafada maki ki shirya kayanki anjima zamuyi tafiya flight din 9 zamubi idan an idar da sallar laasar zamuje kiyiwa aunty ummi sallama, Tom Allah ya kaimu ameen yace ya Mike ya fita .
3:30 ta tashi ta Shiga wanka hadawa tayi da alwalar sallar laasar doguwar Riga tasa da hijab tayi salla sannan ta cire rigar tayi shafe shafenta akwatinta na gida Wanda jiya su nawal suka kawo Mata ta bude atampa ta dauka dinkin doguwar Riga tasa sannan ta gyara kanta mayafi ta dauko da jaka da takalmi ta ajje gefe ganin har yanzu Bai shigo ba yasa taja akwatunan lefenta ta Fara hada abubuwan bukatarta Wanda zasuyi tafiya dasu tana gama shiryawa yana shigowa cikin farar shadda da alkyabba Baka hannun sa rike da wata alkyabbar irin tasa black Amma ta Mata ce sorry nayi delay ko karbi kisa zamu Fara biyawa fada sannan zamuje part din Ammi da kuma wajen granny da nace saimun dawo Amma Naga yanzun zai fi kawai ,mayafinta ta dauka tayi rolling tare da karbar Alkyabbar tana Dan yatsina fuska Jin nauyin ta murmushi yayi Nima basan Sawa nakeba nauyi takemin a jiki ,ganin ba daidai tasa ba yasa ya gyara Mata sañnan ya Riko hannun ta suka fito bude musu gidan Baya akayi Saida tafara shiga ya rufe sannan yazagaya ya Shiga shima fada suka Fara zuwa tun daga bakin kofa ake Mika masu gaisuwa har suka Shiga cike fadar take da mutane hakan yasa ya Kara Jan hular alkyabbar Dan rufe fuskarta sosai Saida suka Mika gaisuwa wajen sarki sannan suka gaishe da waziri Basu Dade ba suka fito sashin granny suka biya Saida suka taba Yan wasanni na Kaka da jikokinta sannan sukayi part din Ammi Wanda sai kusan magrip suka samu suka fito a gidan aunty ummi ya ajje ta yace zaije masallaci yayi salla idan ya dawo zai kirata, a lokacin daya kirata kuwa kamar zatayi kuka haka ta tashi ta fito bayan aunty ummi tasake Mata nasiha Mai ratsa jiki , jiki a sanyaye tafito suka tafi, suna komawa gida kayansu suka dauka sukayi airport a Dubai suka yada zango satinsu biyu suka wuce umrah sannan suka yada zango a paris (france) apartment guda ya kama masu Zama suke Mai cike da farin ciki da walwala.

7 MONTHS LATER

Mahreen ce zaune Akan kujera Sanye take da mini skirt da half vest tayiwa gashin ta style ta daure Shi a gefe popcorn takeci hankali kwance duba nayi wajen Maher dayayi matashi da cinyar mahreen Yana karanta Mata wani novel Mai abun dariya sosai take jin dadin novel din Dan sai dariyarta take cike da nishadi Dan tsagaitawa tayi sannan tace moonlight wai yaushene tafiyar tamu ne naji Kayi shuru kasan idan bamu jeba Ammi da aunty ummi baza suji dadi ba tafada cikin shagwaba lakace Mata hanci yayi sunshine kinfiya rigima fa Nima da nafiso sai babyna ya bayyana kansa tukun yafada Yana shafo karamin cikinta da baifi three months ba, nidai a a ban yarda ba bikin Ayman fa da husna ga na nawal kuma gsky Bai kamata ba murmushi yayi Wasa nake maki har nayi booking flight a week dinda zaa Fara bikin zamuje saboda banaso kiyi nisa Dani Amma fa ko bikin nawal aka Fara saidai kije ki dawo Amma Banda kwana nifa nafijin dadin nan Dan haka nan zamu tattaro mudawo gaba daya koya kikace abinda kace haka zaayi my man tafada tana shafa kansa mikewa yayi sunshine I want to feel my baby's warmth ya fada Yana daukanta cilak sukayi daki.

TAMMAT BI HAMDULILLAH

anan na kawo karshen novel Dina Mai suna MAHREEN kuci gaba da bibiyar novels Dina domin fadakantar nishadantarwa da kuma ilmantarwa taku har kullum YOUNG WRITER .
Chapter 17 · 0% Book details