← Book details Mahreen Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 17

Sashe 15

Mahreen Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Imran ne ya matsawa mahreen cewa taje ta ajje aikinta na DSS tunda burinta ya cika kuma ga magana har taje gaban mai martaba gashi ba a wani ja auran ba aka saka wata uku masu zuwa , "bazan ce zan ajje aikin nan yanzu ba gsky Imran, "to sai yaushe ne dear inaga dama iya waadin dakika dauka daga burin nan naki ya cika zaki ajje mesa yanzu kike son canjawa murmushi tayi karka damu Imran nama alqawari kafin auren zan ajje aikin, " ni fa dear ya kamata a canja min sunan nan , " ummm karka damu akwai lokaci ta fada can kasan zuciyar ta kuwa batajin wani son Imran kawai dai tasan ya Mata halacci kuma bashi da wani aibu amma ita tarasa me sa batajin sa a zuciyarta ta , kanta ta daga sama tana kallon yadda iskar hadarin farkon damina ke kadawa karar text ne ya shigo wayarta dubawa tayi Maher ne yace kina ina ne sunshine sunan ta sake maimaitawa sunshine reply ta masa da gida , inaso inzo in ganki a fakaice ta kalli Imran dayake danna waya shima tuna abinda ya faru tayi rannan hakan yasa ta tura masa Kai Kana ina ? love garden, ohk wait for me there, hopefully there's no problem, yea kawai ya tura Mata kallon Imran tayi sannan tace inaso naje naga granny na dan kwana biyu ban leqa ba kamar zaice suje ya kaita sai kuma dai yace adawo lpy take care , okay tace sannan ta koma ciki after dress ta dora sannan ta fito, da map tayi amfani dan zuwa Inda ya fada matan.
tana fita ta kirashi kwatanta mata Inda yake yayi tana karasowa ta zauna , murmushi ya mata ai na dauka baza kizo ba gira daya ta daga maisa tho zanqi zuwa, " umm to nagode ya jikin abba ta tambaya da sauki alhamdulillah shuru sukayi na dan wani lokaci sannan yace mahreen naam tace tana bashi full attention dinta saida ya nisa sannan yace mahreen kina so na , shuru tayi kamar me tunani kafin tace kaman ya bangane ba, I mean kina so na zaki aureni , "whl har yanzu ban bangane Inda Ka dosa ba Maher wace irin magana kake ne , wani zazzafan numfashi ya fezar mahreen ina sonki kuma ina so in aureki mu rayu cikin aminci , "ni kuma bana sanka Maher ban taba ma kallon irin san da kake magana akai ba ina sonka a matsayinka na cousin dina kuma jini na , karya kike mahreen kina so na ya fada Yana Mikewa, itama mikewa tayi nace ma bana san ka Imran nake so kuma Shi zan aur.... Bata karasa ba ya bige mata baki karya kike mahreen kalli cikin idona kice min bakya so na baza ki aureni ba sannan me sa kika taremin bullet ranar nan in har da gaske bakya son nawa meysa baki bari bullet ya sameni ba kinga mahreen karki cuci wanna zuciyar data cika da begenki ki nutsu muyi magana ta fahimta ki bar wani zancen imran karkice ko dan kina zaune gidan su baza ki iya cewa bakya sansa ba , "wai Kam ko Ka kurman ce ne Maher nace ma Imran nake so kuma Shi zan aura nan da three months kasan dai bakyau nema cikin nema ko kuma kasan magana har taje gaban manya ya kakeso Ka hargitsa min tunani ne, "ko daya mahreen kin kasa banbance SO DA KAUNA kinason Imran amma ni zuciyar ki take kauna ga hakan a idonki me sa zaki karyata me sa zaki hana zuciyar ki abinda take kauna haba mahreen ki bar wanna wasan dan baki san yadda nake ji bane da baki fada min wanna maganar ba dan Allah in wasa kike ki bari zuciyata zata iya bugawa hañnun ta yakamo ya dora daidai saitin zuciyar sa mahreen please kitaimaki wanna zuciyar hannun ta ta kwace ta rufe bakinta dashi duka hawaye suka fara ambaliya a fuskar ta da sauri ta juya gudu gudu sauri sauri ta hada ta fice ko ganin gabanta sosai batayi haka ta karasa mota ta fige ta a guje sai gida bata shiga ciki ba saita zagaya baya saida taci kukan data rasa na miye sannan ta wanke fuskarta a tap ta shiga gida lokacin an fara Kiraye Kirayen sallar magrip.

TWO DAYS LATER

zuciyoyin nan biyu sun shiga wani hali especially Maher daya tabbatar mahreen na neman yi masa nisa tunda gashi ya tabbatar nan da wata ukun ne aurenta duk ya rame ya fita hayyacinsa , sai kuma ya samu Kira daga Ammi cewa su zo tana nemansu da gaggawa cikin tashi hankali yake tambayar ta ko wani abune ya faru ba komai ku de kuzo kawai cikin wani tararrabin ya sake fadawa ba bata lokaci ya sanar da Ayman suka shirya tafiya tare da sanarwa grandparents nasu zasuje duba mahaifinsu ne .

Suna zaune bayan an gama masu screening ya dauko wayarsa yana so ya kirata kuma me ma zaice mata da haka dai ya yanke shawarar kiranta har sau biyu bata dagaba sai ana ukun ne ta daga hello!, inaji tace, cikin dacin rai da kuma dacin maganar da zai fada ya lumshe idon sa dama na bugo ne na tayaki murna Allah ya sanya alheri zanyi tafiya watakil kuma kafin na dawo kinyi aure Allah ya baku zaman lpy yana gama fada ya katse wayar yana dafe kirjin sa da yakeji kamar zuciyar sa zata fito, abangaren mahreen ma hakan ce ta kasance wani Abu taji ya tokare Mata makoshi so take tayi kuka ta kasa pillow ta kankame tana runtse Ido tare da sauke wasu tagwayen ajiyar zuciya.

Abun da suka Tarar a Egypt shiya kusan shafe rabin bakin cikin da Maher ya taho dashi abbansu suka samu zaune manira na gefensa tana basa labari Ammi kuma tana hada masa shayi sunyi farin ciki sosai ganin abbansu ya tashi daga paralysis kuma yana magana saidai takawar ne har yanzu batayi karfi ba sati biyu da zuwansu aka sallame su daga asibitin gidansu dake nan Egypt suka koma .

yanzu ma zaune yake shi da abbansa yana matsa masa kafafunsa manira da Ammi kuma suna kitchen Ayman kuma ya fita , abba ne ya dafa kansa son miye matsalar murmushin karfin hali yayi ba komai abba mai ka gani ? Maher karka boyemin damuwarka ko da banida lpy ina gadon asibiti mun saba sharing komai tare dukda baka fadamin marar dadi amma komai zakayi ko kayi saika labarta min dan haka kafadamin abinda yake damunka nisawa yayi sannan yace abba Dama....... Zayyane masa komai yayi dan jim abban yayi sannan yace karka damu Maher idan mahreen matar kace bata da miji sai Kai idan kuma ba matar Ka bace to Ka qaddara dama haka Allah ya tsara girgiza masa Kai kawai yayi ba tare daya sake cewa komai ba.

wata biyu sukayi sannan suka shirya dira Nigeria domin yiwa mutane bazata dan dama basu fadawa kowa tashin abban ba ,kwana kwana Maher ya fara dan baya son dawowa Nigeria yanzu amma abbansa ya kasa ya tsare tare zasu dawo hakan Kuwa akayi abba ya tuso keyarsu suka dawo manira cike da farin ciki take dan ita batasan Nigeria ba tun tana 1 year aka tafi da ita Egypt.

Mahreen mahreen kina ina mahreen ce tafito daga daki har wani yar rama tayi naam aunty ummi, kije kicewa su husna su shirya anjima zamuje sannu da zuwan kanin mahaifinki , sun dawo ne ? eh kuma ance ya warke ma, Allah ya Kara lpy tace tana komawa ciki jiki a sanyaye duk ta zama wata iri .

Bayan magrip suka shirya nawal ce ta kalli mahreen tab yau dai inajin zaai ruwa da kankara yau kece zaki fita da hijabi mahreen bata kulata ba tayi waje, a parlourn grandmother dinsu duk suka samesu har Mai martaba mahreen da Imran sune abaya tunda suka shigo idonsa na kansu Amma sai yayi kamar wayarsa yake dannawa gaishe gaishe aka fara abban su Maher ne yace zo nan daughter zo ki zauna nan kusa dani Kan mahreen akasa ta karasa ta zauna satar kallon Maher tayi taga ya kauda Kai can kuma ya mike ya fice a zuwan zai amsa waya Mai martaba ne ya bukaci abar mahreen anan ta kwana Imran kamar ya hadiyi zuciya saboda shi ganinsa dan ta hadu da Maher ne Amma ba yadda zaiyi dole haka ya dauki aunty ummi suka tafi domin husna ma cewa tayi zata zauna itama nawal tace za akawosu gobe tare aikuwa raba dare sukayi suna hira da manira dan ma ita mahreen din tana da damuwa saisa duk a takure take .
Chapter 15 · 0% Book details