← Book details Mahreen Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 17

Sashe 2

Mahreen Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Kamar yadda suka shirya hakance ta kasance Abdul hameed da kansa ya shirya ya shiga cikin tawagar thugs dinsa suka dirarwa gidan dan uwan nasa wai dan karma yaran su samu matsala sai sa zaije da kansa, cikin dare suna bacci suka shiga gidan bayan sun gama da masu gadi parlourn gidan sukawa tsinke zama yayi yasa yaransa su fito masa da duk wanda ke gidan haka aka fito da ishaq da matarsa an sa masu bindinga aka yana kuka yana fadin me na maku kuke neman raina ni da iyalaina mommy tace in kudi kukeso kufada zaa baku ko nawa ne wani ne daga cikin yaran ya daka mata tsawa da cewa idan ta sake magana saiya fasa kanta shuru tayi tana kuka mahreen data buya bayan ya'yan ta tana kuka suka dakawa tsawa wadda saida taku san tafiya da numfashin ta , Abdul hameed ne ya zaro bindiga a aljihunsa ya nufi ya Sadiq yana zuwa baiyi wata wata ba ya saita brain dinsa ya sakar masa alburushi Karan Harbin nai ya rikita mahreen ta riqo hannun Abdul hameed din a gigice fisgewa yayi da karfi har hannunsa na fita daga safar hannun da yasa, Kan dan uwanta tayi tana kuka mommy ce ta taso tana mai ya maku baisan hawa ba bai san sauka ba kuka kasheshi sakar Mata harsashi yayi a zuciya sannan yakara Mata a forehead daddy da yayi suman zaune yana hawaye gaba daya komai na jikinsa ya daina aiki na wucen gadi, cewa thug din nasa yayi suyi waje shima yayi wajen kofa kamar zai fita sai ya juyo yasakarwa ishaq din bullet shi ma mahreen ce tasaki wani ihu ta mike tana masa wani irin kallo ko ina na jikina sa a rufe yake idonta ne ya sauka Kan hannunsa dayake rike da bandiga kurawa hannun Ido tayi kafin ta maida Idon ta zuwa kansa Ido hudu sukayi kallon kallo kafin ya juya ya fice ita kuma tayi kan iyayenta tana kuka ganin fa basa numfashi yasa ta dauko waya tana Kiran aunty ummi saida tai mata misscall 5 tukun ta daga cikin muryar bacci amma jin abinda mahreen din take fada mata bata san lokacin da ta wartsake ba ko da sukazo aka sake tabbatar da sun mutu tunda mahreen ta suma bata san in da kanta yake ba sai da akayi uku sannan ta dawo hankalin ta to yanzu kwana shida Kenan da rasuwar tasu .

BACK TO STORY

Bayan bakwai Mahreen ta dawo gidan aunty ummi da zama ta dawo wata so silent dan abu kadan ne ke Hassala ta a yanzu bata jin akwai abinda take tsoro ciki kuwa harda mutuwa .

A masarauta ma an jimama mutuwar ishaq ciki kuwa harda Abdul hameed daya nuna mutuwar ta bigeshi husna tayi kuka jin cewa sun aikata har wata zuciyar na che mata ta tona masu asiri tunda tana da evidence amma tana tsoro.

An hana a sanarwa Khaled rasuwar dan uwan nasa kasancewar halin da yake ciki, Maher da Ayman da sukayi tafiya Germany har su mahreen sukazo sukayi zaman duba abbansu basa nan saida bayan sun tafi suka je sai kuma yanzu da aka fada masu mutuwarshi suka dawo jin yadda mutuwar tazo taso sa Maher shakku amma kuma kawai sai ya watsar Ayman yaso yin bincike akai a matsayin sa na lawyer Amma Abdul hameed ya nuna cewa binciken bashi da amfani tunda har sun mutu ba dawowa zasuyi ba , su Ayman sunso ganin mahreen su Mata gaisuwa ita kuma a lokacin baza ta fito ba haka suka hakura sukace a fada mata suna Mata taaziya.

Bayan six months da faruwar hakan mahreen tacewa imran tanaso takoma school cikin lallabi yace mata a ina takeson tayi (Dan yanzu lallaba ta suke especially ma shi ) ba tare da wani fargaba ba tace masa russia jim yayi kamar bazai amsa ba saikuma yace Mata wani course ne take so defence and security studies tabashi amsa a takaice , but mahreen irin wanna aikin ba irin naki bane , " ni da nake lawyer ai ba aikin zanyi ba kawai ina san course dinne, ko da suka tuntubi aunty ummi taso hanawa amma yadda mahreen din ta taurare yasa suka kyaleta tare da nema Mata admission ta tafi .

YOUNG WRITER

MAHREEN

PAGE 11--20

TWO YEARS LATER

Wata matashiyar budurwa na hango ba zaa kirata doguwa ba kuma ba zaa sata sawun gejerubace ba , ba fara bace amma light skin gareta mai daukar Ido tana da dogon hanci da idanuwa dara dara wanda suke zagaye da zara zaran lashes haka eyebrow ta gazar gazar batada kiba kuma ba siririya bace a dire take irin su ne ake Kira da figure 8 sanye take da ash din jeans Wanda yabi jikinta sai black top data dora wadda zata Kai guiwarta daga baya kuma takai har kasa ta yane kanta da karamin veil sai P cap data sa ta janyota gaba sosai ta yadda ta rufe rabin fuskar ta a yau ta diro naija da gudurin fara aiki a hukumar DSS dakuma yin aiki a matsayin ta na lawyer sabanin yadda ta tafi da cewa baza tayi aiki a matsayin dss ba idanunta ta daga tana kallon airport din wayarta dake Kara ta dauko a jaka Imran sunan daya bayyana Akan screen din wayar dauka tayi daga daya bangaren naji ance hello mahreen I haven't seen you yet and ur flight landed 15 minutes ago, where are you ? I'm coming kawai tace sannan tafara tafiya Kana kallonta zakasan jinin sarauta Yana gudu a veins dinta daga yadda take tafiya .
tana fita tagan su nawal ce ta fara hangota da gudu taje suka rungume juna welcome back home sister murmushi ta mata taja kumatun ta how are you doing ? I'm doing good buh I missed you Imran ne ya karaso Lilly ya fada juyawa sukayi direction din da yake murmushi yasakar Mata welcome back Lilly , thank you bruh, ' so let's get home Cox ummi is so eager to see you , I missed her so much wlh, really ya fada tare da daga mata gira yeah tace kawai tayi gaba suka rufa Mata baya .

Tafiya sukeyi amma ita ta Lula cikin wata duniyar tunanin har saida Imran yace Lilly you haven't gisted me about your studies hope you did it successfully idonta akan titi tace alhamdulillah buh I'm so exhausted right now later in sha allah, "ohk no problem ur wish is my command, ahaka suka karasa gida ba wanda yakara magana a cikinsu.
cikin farin ciki aunty ummi ta tarbe ta bayan sun zauna take tambayar sana bata zo ba (Sana tayi aure bayan tafiyar mahreen kuma ba gari daya suke ba)har 1am suka Kai suna hira sannan suka shiga bacci koda ta shiga daki ba bacci tayi ba tunane tunane take ta yanda zata shawo Kan aunty ummi ta yadda da abinda takeso a karshe dai ta yanke shawarar samun Imran domin yi mata jagora ta samu aiki a hukumar DSS tare kuma da fara aiki a matsayin ta na lawyer domin ta hakan ne burinta na daukan fansa zai cika da wanna tunanin bacci yayi awun gaba da ita.

THE NEXT DAY

Zaune take a garden sanye da sweet pant da top long sleeve sai P cap dinda ta kifa a fuskarta kanta ma kallon sama kafarta daya akan table din wajen tana girgizata kadan kadan Imran ne ya karaso wurin da fadin helloo lilly dagowa tayi sannan tace ah Imran I need to discuss something with you kujera yaja ya zauna sannan yace go ahead dear I'm all ears, dan muskutawa tayi sannan tace you know when I was going to Russia I told aunty ummi I wasn't going to work as a DSS girgiza kansa yayi yana bata duka attention dinsa saida ta sake nisawa tukun tace so now I have changed my mind I want you to take me to any DSS headquarters, I'm eager to start my work early, and after that Ina son fara aikina matsayina ta barrister but I prefer to work independently, without being under someone's control, and please I'm not requesting for advice and I'd like to keep this matter confidential between us between us tana gama fadar haka ta maida P cap dinta a fuska nisawa yayi yana tsinewa wa'anda suka kashe mata familynta da wargaza farincikin ta yarinya mai saukin Kai da Wasa da dariya amma yanzu duk ta zama somehow sai ahankali a fili kuwa cewa yayi ohk I will check and get back to you , great kawai tace jin bata sake magana ba yasa shima ya tashi ya tafi .

AFTER ONE WEEK

Imran yayi duk abinda mahreen tace kuma an mata komai kasancewar documents din karatun ta Bana nan bane yasa cikin sauri suka amsheta a babbar headquarter DSS ta jahar sannan ya sama mata office awani chambers din lawyoyi bai fadawa ummi aiki data samu a headquarter dinba shi dai yace mata ta bukaci ya kama mata office zata fara aikin ta a matsayin Barr.
Chapter 2 · 0% Book details