← Book details Mahreen Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 17

Sashe 11

Mahreen Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Imran ta samu a parlour da alama zaman jiranta yake karasowa tayi ta zauna tana fadin oh allah na nagaji kallonta yayi dama I'm just waiting for you , I can see she ai then what's up ? fadamin gsky abinda ya faru har aka harbeki ? shin shi doctor Maher din zai ma karyane Hala ajiyar zuciya ya sauke yana kallon hanya sannan yace nayi tunanin ko garin aikine ? nop ! sai kuma tace do you know what labarin abinda husna ta fada Mata ta bashi ta Kara da cewa kuma in sha allah everything has come to an end number Abdul hameed ta binciko awayarta tun ranar da husna tasa mata bata Kara bi ta kanta ba sai yanzu wanna number inason kaje kasa abincikomin duk wani list na calls dinda ke shige da fice da text messages zan baka letter cewar daga headquarter dinmu ne Ka wakilceni saboda abubuwan dake gabana dayawa bazan samu time ba kaji ko jinjina Kai yayi kamar wani danta yace an gama madam sai kuma yace to alhamdulillah tunda gashi burinki ya kusa cika sai kuma me next ? babu komai tace tana maida hankali kan wayarta, sai ki ajje wanna aikin kiyi aure kallonsa tayi wani aikin Kenan daga ciki ? aikin zaryar nan mana , "zanyi aure Amma ba yanzu ba , "to maisa ba yanzu ba mai kike Jira you are going to be 23yrs fa haba , "nayi tsufa Kenan ? nop ni ba abinda nake nufi ba kenan ai idan ma ba fada kikayi ba ba wanda zaice kinkai 23ye din , " then what's ur problem imran ta fada tana maida wayarta jaka ta zuba masa eyes gyara zama yayi sannan yace mahreen kinsan tunda kuka dawo nan na daura Ido akanki naji na sami Mata nayi kokarin bayyana maki kuma wanna abun ya faru ganin kin shiga rudu yasa na jinkirta daga baya kuma kika tado da tafiyar nan dan haka yanzu lokaci yayi dazan bayyana maki domin Nima na gaji da boye boye ajjiyar zuciya ta sauke Imran ba irin namijin da zaaki bane kuma ya bata muhimmiyar gudun mawar da baza ta iya mantawa da ita ba amma batajin tana masa son aure dan haka tace karka damu Imran zanyi tunani akai kaman zaiyi kuka yace wani tunani kuma murmushi ta masa gaggawa daga shaidan ne jinkiri kuma alheri ne Imran tunda nace kaban time kadan Kara hakuri mana tana fada ta mike ta wuce daki.

8pm daidai ta gama shirin ta yau atampa tasa dinkin skirt da riga Wanda yayi mutukar shiga da surarta bata daura dankwali ba sai mayafi data yafa kawai tadau jakarta ta fito a parlour ta samu Imran da daddynsa suna kallo wayarta ce tayi Kara tana dauka yace ina waje fa dakin aunty ummi taje tai Mata sallama sannan ta dawo parlourn tace wa daddyn zataje masaurauta amma ba Kwana zatayi ba adawo lpy yai Mata Imran ne yace Lilly dare baiyi ba kuwa ? don't mind Maher na waje Maher ya maimaita da mamaki ganin ta canja shigarta kuma tace tare da Maher zasu fita shin masarautar zasuje ko kuma wani wajen shima cewa daddyn sa yayi Yana zuwa sanna ya dauki dan makulli ya bi bayanta.

Tunda ta fito ya zuba Mata Ido wani kyau yaga tayi masa kodan ta canja shiga ne yau data san yadda kayan Hausa suke karbarta data ajje wanna shigar tata ta yahudu da nasara tana karasawa ya bude mata kofa ta shiga idonsa akan Imran daya ke tsaye kofar parlourn jan motar yayi suka fice ba wanda yace da dan uwansa komai a maimakon taga yayi hanyar masarauta sai taga yayi wata hanyar daban batayi magana ba sai tsintar muryarsa tayi Yana cewa waye shi ,wa kenan Wanda nake ganinku a asibiti tare ya fada kamar bayaso, oh wai Imran kake nufi shine babban Dan aunty ummi he's so kind ba shida problem dan kallota yayi sannan ya maida kansa titi meysa yake bibiyar ki to , bibiyata kuma like how ? kalli mirrorn gefanki cikin mamaki take kallon motar tabbas motar Imran ce kallosa tayi ya akayi kasan shine kallonta yayi ya dauke Kai ba tare da yace komai ba daidai nan wani security ya bude gate din wani gida shiga yayi da motar yayi parking , inane nan ? in mun shiga kya gani ya fada Yana ficewa itama fita tayi ba tare da tsoro ba tabi bayansa wasu thug boys ta gani a parlourn da alama abige suke suna ganin su suka fara boye kayan shaye shayen su suna Kiran sai oga Allah yakara lpy bai wani kulasu ba ya Mika masu hannu alamar subashi wani abu key dayan su ya Mika masa sannan yayi gaba itama binsa tayi suna zuwa ya bude dakin wani dan dattijon mutum ne ya bayyana duk an masa jina jina tana ganin sa ta gane shine na hoton data gani tare da su aunty amarya kofar ya rufe bayan ta shiga sannan ya karasa gabansa kujera ya janyo da kafarsa sannan ya nuna Mata da hannu alamar ta zauna karasawa yayi gaban chiroma daya girgiza da ganinsa kaganeni ya tambaya Muhammad ma-maher maika keyi anan murmushin gefen baki yayi na zo ne kafadamin yadda akayi kasawa abbana poison a abinci cikin firgici yace a a whl bani bane bansan da zancen nan ba ohk baka daku ba Kenan barin kirasu a a dan Allah tsaya zan fada whl zan fada ma gsky juyawa yayi wajen mahreen da hannu yamata sign data danna recording sannan ya fara tambayar sa meysa kasawa abbana poison a abinci whl bani bane Muhammad nima sani akayi waye ya saka? alhaji Abdul hameed ne da matarsa ina zaman zamana sukazo suka cusa min raayin daba nawa ba kuma ya bani kudade masu tsoka da cewa idan na aikata zai bani fiye dasu shi yabani poison da cewa na kaiwa jakadiya ta zuba a abincin alhaji Khaled tareda bata kudi Mai yawa a furar dayakesha duk dare wadda takasance ita take damawa anan tasa masa saidai kash a daren bai wani sha sosai ba saisa bata kasheshi ba saidai illar datayi masa wanda har yanzu Bai dawo hayyacinsa ba sunso mutuwa yayi Amma jin babbar illar data masa yasa sukace ya Zama minor bazai yi wani tasiri ba kuma whl nayi nadama ya fada yana rushewa da kuka, hotonsu shida Abdul hameed da aunty amarya ya bude awayarsa ya nuna masa sannan yace kasan dai wanna hoton bana da bane meya Kara hadaku kuma duk kuka tsallake ko ina kuka shige har dakinsa cikin rudewa yace a a -a a whl kamar daga sama yaji tsawar Maher zaka fadamin ne ko yaya ? dan Allah Kayi hakuri ohk baza kafada ba Kenan zan fada zan fada karkayi gigin yimin karya domin haka na barazana ga rayuwarka ya fada Yana daga masa rigarsa Inda ya hango bindiga soke jikinsa ne ya dau rawa, kirana sukayi akan sunaso akawar da maimartaba Inda sukeso na jawo waziri cikinsu saboda waziri shine na kusa da maimartaba tunda aka nadashi tare suke shi yake bashi shawara anan nake chemusu waziri baze bada hadin kaiba saidai su nemi wata hanyar shine sukace idan har banbi umarninsu ba na kawo masu cikas to sai sun tona min asiri awajen waziri , wani asiri Kenan ? cikin kuka yace wata tsohuwar alaqata ce da amaryar waziri , Kenan da Kai akaje aka kashe uncle da iyalansa ? whl Allah kaji na rantse ma Muhammad bansan komai akan hakan ba sai daga baya da nake tuntubarsa da zance shine yake cemin shine kuma idan nayi gigin fadawa wani abakacin raina, shiwa Kenan Ka tuntuba? alhaji abdul hameed juyawa yayi wajen mahreen data dora kafa daya Kan daya ta zuba masu Ido da hannu ya nuna masa tayi saving record din, hakan tayi sannan ta mike ganin shima yayi hanyar waje , tare suka fita karbar duk wani Abu da aka kamo chiroma dashi yayi sannan sukayi waje suka shiga mota suka wuce masarauta still Imran na biye dasu Inda ita kuma ta kule da hakan karfa yaga dan yace Yana sonta yayi amfani da haka yaga kamar har tazama matar sa ne da zai dinga wani binta duk Inda zataje dole ma ta shata masa layi.
Chapter 11 · 0% Book details