← Book details Kawar Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 31

Sashe 8

Kawar Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Mahaifinsa Arch. Prof. Bello Rafindadi, dan asalin shiyyar Rafindadi ne ta jihar Katsina, shine (Chancellor) na farko na Jami’ar Umaru Musa ‘Yar Adua, sanda aka budeta.
Mahaifinsa Prof. Bello Shi ya zaba masa tafiya Jami’ar Ahmadu Bello, yana kammala karatun sakandirensa a Barewa College, babu bata lokaci ya samu admission, don shima Baba Prof. can yayi nasa digirin na farko, sauran kuma a UDUS, Baba Bello yana da burin dan shi Zayyan ya karanci abinda shima ya karanta ya samu daukaka, arziki, shuhura da cigaba mai yawa akan profession din, watau “Architecture”.
Burinsa tun a lokacin shine Zayyan dinsa ya gajeshi akan komai da yake kai, kasancewarsa Da namiji tilo daya mallaka cikin tarin ‘ya’yansa mata.
**** ***** *****
Jim kadan bayan ritayarsa daga aikin gwamnati, Baba (Prof) Bello Rafindadi, ya koma harkar contract na zanen gidaje da ginasu da bada hayarsu, harkar da ake kira (Real Estate) irinna zamani a manyan biranen kasar nan.
Baba Bello ya samu tsundumawa a wannan harkar ne ta hanyar amininsa Arch. Murtala Babangida Masari, wanda shi ya jima a harkar (Real Estate) da gwamnatin Najeriya, Alh. Murtala bai taba aiki a jami’a ba, sai a harkokin real estate. Alh. Murtala Ya tara arziki mai yawa a real estate business.
Baba Bello yana yawan cewa.
“Zayyan gashi dai shi daya a gabansa tilo, amma daya ne tamkar da dubu”.
Kasancewarsa ya taso namiji daya a cikin ‘ya’ya mata biyar, yasa Zayyan ya tashi da dabi’ar yawan tausayawa ga mata, duk inda ya ga mace babba ko yarinya yana girmamata, in da halin taimako yana taimaka mata, ya iya hakuri da halayensu sannan duk dabi’un mata na rauni da kyuya Zayyan ya sani, ya kuma iya tafiyar dasu, tunda gabansa da bayansa duk ‘ya’ya mata ne a dakin Mama Fatu. Mace daya tal da Baba Bello ya aura a lokacin rayuwarsa.
Har Mama Fatu ta gama haife – haifenta wato ta iso (menopause) bata taba yin tsarin iyali ba, Zayyan kuma bai samu kani namiji ba, sai kanne mata uku.
**** ***** *****
SHEKARA TA 2012
Itace shekarar da ya hadu da Safiyyah. A wancan lokacin, wajejen shekarar ta dubu biyu da goma sha biyu, mawuyaci ne ka samu yarinya mai kananun shekaru mai kamun kai da tsare mutuncin gidansu a jami’ar Ahmadu Bello, kamar Safiyyah Usman Dandume, wadda ake kira Safiyyah Dandume, ta shigo jami’ar da shekaru goma sha bakwai kacal. A halin yanzu kuma ta shiga level 2 tana neman cika sha tara.
Safiyyah Dandume, ta riga ta siffanta kanta da dabi’u na kamun kai a idon kowa, da suttura ta mutunci, ta hanyar yin kyakkyawar shiga ta kamala, don haka mazan banza shakkar dosarta ma suke, haka kawayen banza don babu fuskar neman kawance da ita, a cikin ‘yammatan dake tashen kokari a karatu a tsangayar ‘Architecture’ Safiyyah Usman Ladan, tayiwa kowacce yarinya a department din zarrah, ta yiwa tsararrakinta da abokan karatunta da yawa fintinkau wajen maida hankali ga abinda ya kaita, in akayi jarrabawa ta karshen zango da (CGPA 4.50) take fita. Kullum addu’arta da fatanta shine cikawa Malam alkawarin data daukar masa, na cewa karatun jami’a bazai sa ta canza dabi’un ta da halayenta masu kyau daya riga ya santa dasu ba.
Kai shi bama wannan labarin da yake yawan ji akanta bane abinda ya fara attracting dinsa ga Safiyyah ba, irin saurin maganarta dinnan (in’ina) da take masa dadin ji, Safiyyah ga ga sassanyan kyau, ga rangwada irin ta ‘yammata, wata irin rangwada ta halitta Safiyyah keda ita cikin Hijabi, komai nata Zayyan ya rasa mai yasa, ko ba mai kyau bane shi kyau yake masa, ya kuma burgeshi, ya kara kawatar da ita a zuciyarsa.
Bai manta ba. A ranar da ya fara ganinta Safiyyah a kule take, kuma a harzuke da malamin labirare dinsu, amma duk da haka tana kokarin shanye harzukarta, saboda cewa da yayi bai gane in’inarta ba, so take malamin labiraren ya dauko mata wani littafi daya shafi abinda take karantawa, tana so zata zauna a labirare tayi Assignment, ta fada har sau biyu amma mutuminnan yace wai ya kasa gane me take fada da gangan da iya shege, kyakkyawan bakinta kawai malamin labiraren ya kurawa ido, sabida saurin bakinta na halitta mai hade da hardewa da tangardar harshe.
Shikuma Zayyan dake bayansu yana jira ta gama shima ya karbi nasa, tun bata rufe baki ba shi ya gane me tace, ko don shima littafin da ya zo nema din kenan?
Yana jin su itada malamin labiraren suna magana, Safiyyah tana kara cewa bazata maimaita ba, shikuma librarian yana faman cewa “Na’am?? Hajiya sake fade inji?”
Hakan ya tunzura Safiyyah taji haushi sosai, har kwallah ta cicciko a idonta, ta kwanta a kasan kwayan idanun nata, kiris take jira ta zubo akan kundukukinta, a can baya Malam mahaifinta kullum da safe yana karanta ayar;
“Rabbish’rahly sadry, wa yassirly amry, wahlul uqdatan min lisany, yafqahu qauly…..”.
Yana tofawa a ruwa yana bata tana sha sanda tana yarinya, shine ma ta samu saukin in’inar, amma duk da haka abin bai tafi gabadaya ba, saidai ya ragu sosai. Tunda har in ka saba da ita data fada zaka gane.
Tausayinta Zayyan yaji ya kama shi, ganin tana neman barin wajen cikin kufula, ya tuna wani abokinsa a sakandire mai suna Saleh Wangara shima haka yake da in’ina (stammerer), sai ya samu kansa da yanke shawarar saka musu baki, wanda hakan ba halinsa bane shiga maganar da bada shi akeyi ba.Amma kwarai yarinyarta bahi tausayi.
Zayyan sai ya samu kansa yana maimaitama malamin labirare me yarinyar nan take cewa, cikin nitsatstsen lafazin Ingilishinsa.
Ganin cewa yarinyar ta zo wuya har tana hadiye hawaye da kyar, tana kuma kokarin barin wajen don haushi, ba tareda an bata littafin ba.
Kawai daga bayanta taji mutumin dake tsaye a bayanta yace ma Librarian din cikin nutsuwa; Tana son ka bata.
“Architecture, Form, Space, and Order” na (Frank Ching, 1979)”.
Abinda bakinta ya kasa fada correctly.
Kuma abinda ta fada din kenan a zahiri, sak babu bambanci, shida bada shi take maganar ba, tsaye kawai yake a bayanta, yana jira ta gama ya karbi nasa, ya gane furucinta, amma librarian dinnan don yasa ta tayi ta maimaita magana yana karewa dan kyakkyawan bakinta da motsin siraran labbanta da suka sha ‘wetlips’ mai santsi kallo, suna sassarfa da hardewa da juna, wajen yin furuci shiyasa yace wai bai gane ba.
Aka dauko littafin aka miko mata, kamar tace a mayar ta fasa, sai kuma ta kasa musamman da suka hada ido da wanda yayi mata ‘speech interpretation’ din. Kallon da yake mata na lallashi ne, mai nuna cewa kada ta yi fushi, ta amsa tayi karatunta.
Sai tayi masa kallon Rahma itama. Ta kuma kasa tankwabe lallashin dake cikin idanunsa. Ya fahimci hakan, sai yayi mata murmushi na Sanya salama. Yace.
“ki karba ko?”
Ya tsareta da kyawawan Katsinawan idanunshi, hakan yasa sai ta kasa kin karba, domin zai zama kamar ta gwasile wannan taimakon nasa da kulawar nasa ne.
A hankali ta amsa, bakinta na kokawa da halshenta wajen motsin fizgo kalmar.
“Na - gode sosai fah!”.
Sai tasa kai ta wuce su, zuwa ainahin cikin dakin karatun, kai tsaye Safiyyah ta wuce zuwa wata corner a can kuryar library din, inda a can ta saba zama duk sanda ta shigo cikin dakin karatun.
**** **** ****
Chapter 8 · 0% Book details