Sashe 16
Kawar Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read
AURENSU
A
hankali Zayyan ya kara lumshe idanunsa, ya cigaba da tariyo abubuwan da suka faru dasu bayan nan shi da Safiyyah. To cut it short, yayi nasarar samun auren Safiyyah (at a very tender age) daga shi har ita suna tsakiyar shekarun kuruciya, in her teens shikuma in his twenties.
Irin auren nan na mutanen da ga ‘ya’yansu, da ake kira AUREN GATA shi mahaifinsa Baba Bello yayi masa da Safiyyah kamar yadda ya alkawartawa Mama, cewa zai masa auren gata, to ya cika wannan alqawarin, domin Baba shi yayi masa komai na hidimar auren nan including lefe, wanda Malam yaki yarda a kawo yace can in sun hadu a gidan auren su ya bata amma ba a gidansa ba.
A kullum sanda Baba yake raye, yana kara jaddada masa da ya rike Safiyyah da amana, 'yar masu dattaku ce itace asalin 'yar manyan mutane, kuma matar rufin asirinshi ce. Baba Bello ya kan ce “na saka himma na aura maka itane bisa ganin dacewarta da kai da nagartar gidan data fito, da kuma uwa-uba karfin sonta dana gani a tattare da kai, ba tareda na jira lokacin da ya dace ace kayi aure yayi ba”.
Baba ya kara ce dashi "ya aura masa ita da wuri ne don kada ta kubuce masa.
Domin mata irin Safiyyah da suka fito daga tsatson kwarai tamkar allura cikin ruwa ne wato na mai tsananin rabo ne”.
Bazai taba mantawa da ire-iren wadannan kalaman na mahaifinsa akan Safiyyah ba, masu sawa kullum yake kara ganin darajarta da kimarta a bayan ran Baba. Yake kuma girmama kowanne kankanin al’amarinta.
Da amincewar mahaifin Safiyyah da nasa dari bisa dari aka daura aurensa da Safiyyah... aure mai dimbin tarihi. A wannan lokacin da tunaninsa ya zo nan, murmushi ne ya kubce masa daga kwancen da yake, sakamakon tuno wani abun da ya faru bayan daurin aure.
Wato tun daga lokacin da aka daura musu aure sai Safiyyah ta canza masa, ya rasa gane kanta, duk ta damu, ta shiga kunci marar dalili.
Har ta kai da cewa ta rokeshi kan bata shirya tarewa ba, tana so ya roki Malam da Baba a bata lokaci, saboda gabadaya auren da yuwuwarsa yazo mata ne bagatatan, bata yarda da yiwuwar komai ba sai data tabbatar ya tabbata din. Wato an daura shi, tunda gashi har Malam da Limamin garin Dandume da ya zama Alwalinta sun kirata sitting room din Malam na soro a ranar bayan an watse, sun damka mata sadaqinta na aure a hannunta.
A baya Safiyyah kallon komai take kamar wasan film, wato daga haduwar ta da Zayyan har zuwa gajeruwar soyayyarsu sun faru kamar kiftawar ido, zuwa daidaitawar iyayensu, zuwa maganar auren data bullo duk bata yarda dasu ba sai bayan ta tabbatar an daura mata auren shaidu sun shaida, tun daga nan ta shiga damuwa, ta fitini kanta ta fitineshi shima da rokon alfarma na rashin son tarewa yanzu.
Da farko tace masa ya roki a barta sai ta gama jarrabawar karshen zangon da zata fara, ta huta ta nutsu bayannan, duk ta dauka Zayyan zai ce a’ah, ganin yadda yake ta dokin tarewar tata, tunda Malam yace biki ba’a gidansa ba saidai in ta tare suyi can a gidansu, amma sai taji kawai ya amsa inda ya ce mata cikin lallashi da tausasa kalami.
“sophie, kinsan burina kawai in mallake ki mu rayu tare ko, daga wannan banida wani sauran buri a duniya sai na fatan gamawa da iyayena lafiya.
Kuma gashi Allah ya cika min wannan burin, alas! Ya mallaka min ke Safiyyah, bada tsumi ko dabara ta ba.
To gaggawar me zan yi kuma a kan tarewarki, ai anyi mai wuyar, don haka ki kwantar da hankalinki ni ta fannina “no haste”, na baki damar tarewa a gidana a duk lokacin da kika shiryama hakan.
Zayyan will be patiently waiting for you to come (Zayyan zai jira isowarki cike da hakuri)”.
Daga ranar da aka daura auren su ne ya soma kiran ta da suna “Sophie”, ya cire mata suna “Hijabie”, don a cewarsa yanzu babu sauran Hijabi a tsakaninsu!.
Wasa-wasa har ta gama jarrabawarta Safiyyah tana dojewa tarewarta, Malam da Ammi ma basu matsa mata ba, don wani zazzabi zazzabi ta soma a tsaitsaye, irin na sabon aure.
Kannenta da Ammi kadai ke zuwa saye sayensu a kasuwa na 'yan kayan dakinta da kayan kitchen, da suka tsara za’a yi mata daidai karfinsu.
**** **** ****