Sashe 13
Kawar Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
min kai ko a rabani da kai, kai kadai dinnan namiji danake dashi a cikinsu? To bada ni ba gada makabarta. In ka ganni a lahira kaini aka yi. Kai kenan kwalli dayan da Allah ya bani a matsayin da namiji, maimakon ka kawomin matar da zan yi alfahari da tinkaho da ita da iyayenta kai kuma ka samu ta sakawa a gaban mota, a kara maka karfi, wadda zan dinga zuwa da ita a gidan biki ina nunawa kawayena a matsayin surukata, yarinya ‘yar hutu da za’a cika mana gida da duma-duman ‘royal furniture’ a dinga bamu kujerar Makkah duk shekara nida kai, da yayyenka, ba tare da la'akari da namu samun ba, a kuma baka gwaggwaban jarin da zaka kafa kanka kafin ka samu aikin yi, sai ka bige da kawon diyar gidan alaramma?”. (A saninsa wannan shine mafarin rashin kaunar Mama da Safiyyahrsa. Domin tun ba’a kai ga auro Safiyyah ba, ba’a kai ga an zauna da ita anga kalar halinta ba, kasancewarta diyar Alaramma da yace kadai gidan da ba mamora (ta bakin Mama), yasa Mama tun tashin farko ta tsani zancen aurenta, ta kuma ki jinin asalinta, ta gwasile shi nan take, ta sassage masa gwuiwa a kanta. Haka Mama ta cigaba da sakin maganganu na ba’a da raini da shagube ga zabinsa, irin wadanda zasu sa shi kansa yaji Safiyyah ba ajin aurensa bace, amma ina! Baffan Mama ya riga ya kamu iya wuya, maimakon hakan sai ji yake Safiyyah tana kara kawatuwa da kwanciya masa a rai, tana kara burgeshi tareda kara nabba’a a birnin ransa. Hatoon dake gefe shame-shame a kwance, amma tsaf ta kafa kunnenta a kansu tana sauraronsu shi da Mama, tun tana gintse dariya da ganin yadda Yaya Baffa ya muzanta a gaban Mama, har a karshe tace me zatayi ba fashewa da shaqiyyar dariya ba! Ganin Yaya Baffa yanata karkarwa don Mama tace diyar Alaramma ba cikin zuri’arta ba. Hatoon bata san sanda ta dinga tilliqa dariya ba harda kwarewa, jin Mama na cigaba da sakin maganganu na wulakanci da nuna rashin aji (class) ga zabin da yayi. Yana fama da kalaman Mama yana kuma kara fusata da jin yadda Hatoon ke babbaka masa dariyar shakiyanci daga kwance, ya san jinsu take da kunne daya, ita Hatoon abinda ya bata dariya da Mama tace wai “diyar Alaramma ko? To ba dai a gidana ba Baffa, haka kawai a saka min sunanka a katon mimi (minjaye) a shanyemin kanka tas, azo ana ce min saidai in haifi wani tunda ya auri ‘yar Alaramma, bayan already na iso menopause, ba nida wani Da namijin sai kai kadai kuma Baffa. Hatoon tace a ranta (don ta san bata isa ta fada a fili yaji ba) musamman ganin yadda yake mazari da kumburin nan, in ta sake ta fada a fili ko Mama tayi kadan ta kwaceta a hannun Yaya Baffa yau. “Kai amma su Yaya Baffa an sha kasa! Aji (class) ya fado kasa warwas! Duk kwalisar nan tashi da kwarewa a daukar wanka, ya kare a ‘yar gidan alaramman kauye, ‘yar kauyen Dandume, shi dama ya cika kwashe-kwashe, ko abokansa in an duba za’a ga ‘ya’yan talakawa ne mafi yawansu, duk a wurinsa suke nema, kai cikin abokansa na shiyyar Rafindadi har da na Allah ya baku mu samu. Mama ta tsefe shi ta taje tas, akan matan duniya ‘ya’yan masu hannu da shuni dana ‘yan boko dana ‘yan kasuwa dana ‘yan siyasa sun kare ne a cikin jihar Katsina? Da zai tsallaka ya dauko mata diyar alaramman kauye? Tace kuma ita bama rashin wadatar gidansu yarinyar ne damuwarta ba, kamar yadda za’a mallake mata shi da maluntar da bata san kowacce iri bace, haka kawai. Yo ai ita ko wacece zata auri Baffa sai wadda iyayenta suka ci suka tada kai, saidai taci riba da ita, ba dai ta zama ‘yar kallo a gun matarsa ba. Ko tna ji tana gani a mayar mata dashi saniyar tatsa ba. Tace to idan matan Katsina sun kare ne Baffa, ita zata nemo masa, in kuma kyau ya hango, to ya bari ta samo masa Barumiya. Diyar asalin ‘yan boko kamar nashi iyayen, ko wadanda suka fisu naira da boko. Tace ita sam! Bata son kwashe-kwashe da jogane-jogane irinna zubar da aji da barar mata da class cikin kawayenta. Idan kuma kyau ne ya debo shi a Dandumen, kowa ya san babu mai kyawun kabilar fulanin Rumawa a fadin jihar Katsina. Suna tsaka da haka Baffa yaki cewa komai akan fadace fadacen Mama, sai ga Bello ya dawo gidan, daga wata tafiya da yayi ta aikin ginin titina a jihar Jigawa. Duk da a gajiye yake kamata yayi ya haye samansa kai tsaye ya samu hutu, amma kumfar bakin Mama yaja hankalinsa sosai don har kofar gida ana jiyo tashin fadanta, ya san Mama ta saba fada akan abinda bai kai ya kawo ba amma ganin yadda Zayyan yayi durkushe tsumumu gaban Mama, yayi tsugunno kamar na mai neman gafara yanata zufa, ita kuma Mama tana sake surfeshi, kamar zata hada da kai masa duka, Zayyan ya dukar da kai kawai, ko dagowa bai yi ba, sai digar gumi yake daga goshinsa zuwa kan yatsar kafarsa, lallausar fatar bakinshi dake zagaye da gashin bakinnan da ake kira (quarter million) tana raurawa tana hardewa sabida tashin hankalin da kalaman Mama suka saka shi, wadanda a takaice suke nufin Mama bata amince masa ya nemi auren Safiyyah ba, tayi watsin Allah tsine da zancen sabida Safiyyah bata yi daidai da ra’ayin matar data ke so ya aura ba. A lokacin da shikuma bakidaya zuciyarsa ta gama matowa a kan Safiyyah. Dukkan burinsa na yanzu ya dora shi ne kacokam akan mallakarta ta hanyar auren sunnah, Mama tana ta fada da mita kamar ta kara da arar wani bakin, ta inda take shiga bata nan take fita ba, ta kara da cewa “yaushe ka isa auren ne ma Baffa? Ko aikin yi baka da shi? Kuma baka karbi kwalin masters dinka a hannunka ba har yanzu? Uban waye zai ciyar maka da matar? Haka kawai zaka je ka wani rakito aure gidan Alarammomi da jira suke kaima ka basu, to shekarun naka har guda nawa suke da suka isa daukar dawainiyar mata da danginta?” “Shege ne shi da bashi da Uba?” Baba Bello ya karbe zancen yana shigowa. Tun kafin ya nemi jin ba’asin zancen abinda yace da Mama kenan cikin fushi, wanda da wuya ka ganshi cikinsa indai akan Mama Fatu ne. Mama ta shiga koro masa bayani cikin takaicin da har a furucinta zaka ji shi, tace. “yanzu saboda Allah Baba! Zayyan ya rasa inda zai je ya nemo aure sai gidan Alarammomi, irin masu bada karatun buzu a zaure, a kauye kuma fa!”. Budar bakin Baba Bello sai cewa yayi “kai masha Allahu amma, da wannan kyakkyawan zabi na Zayyan, tsatso nagari irin albarka kenan, tsatson malamai magada Annabawa”. Mama sai ta saki Baba galala! Tana kallon Baba cikin haushi. Don da wuya ta nuna bata son abu Baba ya so shi. Baba Bello ya dauko gangar wa’azi ya soma bugawa Mama Fatu, bayan ya sallami Zayyan kan ya tashi ya basu wuri, cewa hakan data yi ba hanyar da zata yi confronting al’amarin bane, idan ‘ya’yanta sun kawo zabin da bai yi mata daidai ba. Yace ko ganin yarinyar nan baki yi ba, baki yi bincike akan dabi’u da halayenta ba, balle su iyayen nata da kika rainawa matsayi, kawai daga ance diyar malamai sai ki ari wani abu daban ki yafa! Ya Subhanallah Malamai fa aka ce! Masana ilmin Allah da Manzonsa masu hani da mummuna da umarni da kyakkyawa, wallahi Fatima kiji tsoron Allah bansan yaushe kika koma haka ba. To so kike kenan ya dauko miki diyar makada da mawaka in bai dauko diyar masu karantar da Al’qur’ani da Sunnahr Ma’aiki ba? Ina laifin Zayyan anan Hajiya Fatima? Maimakon ki godewa Allah da ya nutsar miki dashi, wannan yaron duk rawar kan samarin zamaninnan bazaki sameshi a ciki ba. At 27, kina cewa bai isa aure ba, alhalin yana so yayi auren, idan ‘ya’yanku suna so su yi aure kuma kuna da halin yi musu Allah da Manzonsa sunyi umarni da muyi musu, hakan ya nuna yana so ya kame kansa ne, ya tara iyali karkashin sunnah baida ra’ayin sharholiya, kuma da diya ta mutunci ‘yar masu albarka. Don wauta da son zuciya sai kice a’ah! Sabida wani ra’ayi naki na daban marar muhimmanci? Wani lokacin Hajiya Fatimah kina bani mamaki, don wani sa’in in kika yi wani abun na rashin kan gado, akan son duniya da girmama abin duniya sama da nagarta, wallahi sai in ga kamar bake ba, wani abun in kikayi sai inga ko Hatoon da bata son zuwa islamiyyah saida duka, bazata iya yin kamarsa ba, don rashin tsinkaye da rashin waiwayen dake cikinsa”. “Baba!” Yadda ‘ya’yansa ke kiransa, bashida zafi ko kadan amma yau ya sille Mama tas da soso da sabulu, sannan yace tasa a ranta auren diyar Alaramma an yi an gama ma, sai idan su suka ce bazasu baiwa dan sa Zayyan ‘yar su ba, ko yarinya tace bata sonsa. Yace “kuma auren ma na gata zan yi masa, ba sai na jira samun aikinsa ba, zan masa komai a matsayinsa na Da namiji daya tilo da na mallaka a rayuwata”. Baba bai bata lokaci ba, sati daya da wancan zuwan na Zayyan gidansu Safiyyah yasa Zayyan din a gaban mota ya raka shi har gidan Malam Usman a Dandume. Kuma koda suka je ma a lokacin daukar karatu magidanta suke yi a gaban Mallam. Saida suka zauna aka kammala aka yi addu’a tare dasu. Malam yana ganin Zayyan ya shaida shi, kuma kamanninsa da dattijon da suke tare yasa nan da nan ya gane mahaifinsa ne. Da girmamawa da mutumtawa da far’a irin ta Malam ya baiwa Baban Zayyan hannu suka yi gaisuwa irinta manya, sannan Baba yace ya zo da kansa ne nemawa Zayyan iznin auren yarinyar wajensa, don kamar yadda Zayyan ya gaya masa, ta san da shi, makarantarsu daya, kuma ita ta bashi iznin ya zo ya gabatar da kansa ga mahaifinta. Ya kara da cewa “kayi hakuri Malam ban turo wakili ba nayi rashin kawaici