← Book details Kawar Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 21 OF 31

Sashe 21

Kawar Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

zai shiga baya wuce limit din da ya san Sophie bazata iya dauka a lokacin ba, wannan shi yafi komai samo masa kanta nan da nan, ta yarda dashi akan hakuri da hadiye sha’awa dari bisa dari, zata iya bugun kirji tace shi daban yake, wato ya bambanta da sauran mazan da Aunty Dije ke bada misalin rashin hakurinsu akan matansu a cikin gida bayan aure. Zayyan ya kasance namiji mai tsananin wayau da hikimar iya sace zuciyar matarsa.... A hankali yasan yadda yayi yasa tsoron nasa ya fara barinta, har ta zama addicted da yawan sumbar da yake mata, da nau’ikan romancing dinsa kala-kala da yake yawan aika mata a ko’ina suke cikin gidansu, har a kitchen bai barinta, bai raba ta da jikinsa, ta zama addicted to his touches, koyaushe har jirace take daya sumbacetan, ko ya rabi jikinta ko yaya ne. Da haka soyayyar su ta aure ta bunkasa, ta soma zama flamboyant. Hatta wanke wanke Safiyyah nayi Zayyan na dauraya, yana aika mata kiss a kasan wuyanta yana zuba mata hira, wannan ba damuwarsa bace wai don ya tayata aikin kitchen (as long as) Safiyyah zata daina tsoronsa da aka saka mata. Da kyar yake iya fita yanzu, ko ya fita cikin makaranta baya jimawa. Sallah ma shi yake musu jam'inta, sai yace wai tafi lada. Duk don kada ya fita yayi nisa da Safiyyahrsa. Hutun sati uku office suka bashi na aure. Gashi ba wuya a wurin Allah har ya lamushe su, cikin kulawa da tattalin Safiyyah da inganta rayuwar aurensu da soyayyah mai wuyar samu. Ranar da Sophie tayi kwana ashirin da daya da tarewa ne wato ranar da hutunsa ya kare yace ta shirya ya kaita Katsina ta gaida Baba Bello da Mama Fatu. **** **** **** Hausawa suka ce wai komai nisan jifa kasa zai fado. Kuma sannu sannu bata hana zuwa saidai a dade ba’a je ba. Sannan suka ce wai komai wayon amarya….. watarana irin wannan……na zuwa!!! Ranar mai dimbin tarihi a garesu ta kama Asabar ce, kuma ta karshen wata. Don haka ana sanitation a gari, wanda yasa basu fita kofar gida da wuri ba, sai wajen karfe goma na safe. Safiyyah ta shirya tsaf cikin wata makubar Egyptian Jilbaab dinta. Ta kawo bungles ta zubawa hannun hagunta ta fito tsaf da ita, kamar baqar balarabiyar Saudiyyah. Tun jiya yayi musu shatar Taxi da zata kaisu har Katsina, mai taxi ya iso kofar gidan ya kirashi yace ya iso yana waje. A daren ranar Safiyyah tayi wa Mama dambun nama mai dan yawa da cake da (milk doughnut), tun Asubah ta tashi tana karasa aikinsu, ko Zayyan bai san aikin me take tayi a kitchen tun duku-duku ba. Da suka yi sallah barcinsa ya koma. Saida gari yayi haske ya tashi yayi wanka a gurguje, ya dauki wata dakakkkiyar shaddarsa fara sol, getzner. Ya fesa turaren sa dayake amfani dashi tun na lokacin wato UltraViolet (Men) samfurin Paco Rabanne. Har sun fito zasu shiga mota bayan Zayyan ya saka kwanukan data shirya abubuwan da zata kaiwa Mama a ciki a bayan motar. Sai Safiyyah ta tuna tayi mantuwa. Ba wani abu ta manta ba cajar wayarta ce da kayan kwalliya data sayawa autar Mama (Hatoon), tayi excusing dinsa ta koma cikin gida, tana komawa daki ta sunkuya a kasan kujera tana neman charger dinta. Da Safiyyah ta juya baya tana tafiya kamar wanda akayi wa wahayi a wannan lokacin sai kawai ya ya samu kansa da dagowa a slow ya kalli bayanta… tana takawa bayanta yana kadawa dari da sittin, dari da saba’in, duk da cikin jilbab take, kirjinnan ya ciko kamar zai fashe, don har wata ‘yar kyakkyawar kiba Sophie ta kara a gidansa cikin sati uku, saboda samun kyakkyawar kulawarsa da soyayyar mijin da bai son ta wahala, duk wani aikin energy zai karba yayi mata, tafiya take cikin wannan takun nata mai kamar na mage mai yanga (cat-walk). Zayyan ya hadiyi wani whalallen miyau, ji kake, muqut, cikin tasowar sha’awar da bai taba ji ba a rayuwarsa. Amma a haka ya basar ya maida kai ga wayar hannunsa yace a ransa “yarinyar nan kin dade kina cin lokacin ki a kaina. Ko maza nawa ne irina masu sadaukar da farin ciki da jin dadinsu, ga samun kwanciyar hankalin matansu? Sai kuma wani irin bakon tunani ya zo masa, na idan suka mutu a hanya fa shi ko Safiyyah, ba tareda ya taba tabbatar da sunnar Manzo data rataya a wuyansu ba shi da ita, kawai sabida gudun zuciyar matar tasa? Wannan fa ya tashi daga neman hadin kanta da kwanciyar hankalinta, ya koma kamar shakkarta yake yi?? Shin Safiyyah zata rabu dashi ne idan ya dabbaqa sunnar aurensu? Ko sakinsa zata yi? A gidansa fa take. Iyakaci tayi fushi dashi duk ranar da hakan ta faru. Sai wata sabuwar sha’awa da fitina mai tsanani da bai taba ji ba akan Safiyyah suka zo suka rinjayi duk wani tunani da ‘self-control’ da ya mallaka a lokacin. Yayi kokarin ya shanye komai har suje Katsina su dawo, amma ina! Al’amarin nema yake ya zama out of his control a cikin taxi. Ya kasa sukuni sam a zaunen da yake, sai muskutawa yake yana sake muskutawa. Da yaga haza, wato zaayi abin kunya in Safiyyah ta fito sai kawai ya fito daga motar, ya fidda kayansu daga bayan motar ya sallami Mai taxi da kudi masu kauri, yace yayi hakuri sun fasa tafiyar sai wani satin ya dawo suje. Ya dauko kayan girkin nata ya mayar matasu kitchen daya bayan daya. Sophie na dagowa daga leka kasan kujera tana neman charger taga Zayyan tsaye a bayanta kamar sojan badaqqare, har sai da jikinsu ya gogu da na juna garin dagowarta. Ganinsa a bayanta unexpectedly yasa Safiyyah ta dan tsorata, musamman ganin yanayinsa na lokacin, saida gabanta ya fadi, mummunar faduwa domin ta dauka wani abun ne ya faru a irin kallon da yake mata, ta soma kokarin magana cikin in’inarta…. “Ah! Zay...,yan.. Habi-by…. Lafiya dai ko? Ai da ka jirani yanzun….zan.. Yanzu zan fitoooo... ". Sauran maganar makalewa tayi a makoshin Safiyyah, sakamakon irin rungumar da Zayyan ya kai mata intensely, ba shiri ta hadiye sauran abarta, domin idanun Zay--yyan dinda ta kasa karasa ambatar cikakken sunansa yau saboda firgita, sun tashi daga na normal Habiby dinta data sani mai lallabata, ya fito mata a namijin zakinsa sak! Yanayinsa ya nuna muraran cikin yanayi na matsananciyar bukatuwa yake da ita, yanayine da ita dai ta kasa fassarawa, don bata taba ganinsa cikin kwatankwacinsa ba. Wani yanayi ne da ko me zata ce, kuma ko zata yi yau don son ya daga mata kafa… zuwa wani lokaci, hakika ba zaiyi wani tasiri ba. A lokacin nan Zayyan ya hautsine mata ya koma mata a namijin Kure, wadanda basa ji basa gani a lokaci irin wannan. Ko daga yanayin hot kisses dinsa na yau, wanda ya sha bambam dana kullum wajen daukar zafi, Sophie ta san yau dai ta kare mata, karyarta ta kare a hannun dan mutanen Rafindadi, shima tasa ta kare, wanda hakan yasa ta tausayawa kanta da kanta tun kafi mai afkuwa ta afku... At the same time, Zayyan yayi kokarin dan hadawa da lallashinta, yana kuma bata baki da tausasan lafuzza na cewa hakan bazai cutar da ita da komai ba, duk cikin son da ya samu kansa da yi mata ne, yana kokarin cimma burin gangar jikinsu. Amma shima zufa yake. Shi kansa baya cikin hayyacinsa, kamar wani wanda aka yiwa wahayin lallai-lallai ya amshi sadaqinsa a yau, kuma a yanzu, da farar Safiya, in ba haka ba zai iya rasa ransa. A cikin kalamanshi na ranar da Safiyyah zata iya tunawa har cewa yayi ta yi masa alfarma, ta bashi dama (koda ta iya yau ce kadai) domin ya gwada mata girman son da yake mata a aikace. Manyan idanunsa da suka canza launi suka kuma kankance sun gama gaya mata manufarsa ta yau mai kankat ce, ba sauran ragayya a tsakaninsu. Koda bai fayyace da fatar bakinsa ba, emotions dinsa sun gama nunawa. Jin saukar dumin hawayenta kan kafadunsa, gabadaya sai ya shiga damuwa, da kyar ya iya cewa “Sophie, kiyi hakuri kinji, kiyi min alfarmar yau kadai, haka rayuwar kowacce mace ta gada ba rashin so bane, ba rashin tausayi bane, shine cikar manufar hakikanin son da nake miki. Shine kuma hanyar da zata bamu zurri’a tsarkakakka mai albarka nida ke. Ji nake yau in ban sameki ba mutuwa zanyi Nana Safiyyah!” Shima sai nasa hawayen suka digo a gadon bayanta. Kalamanshi sun bata tsoro. Kuma koda ace Zayyan bai furta hakan da bakinsa gareta ba, idanunsa da rawar da jikinsa keyi wajen shige mata, sun gaya mata yau mai rabata da Habiby sai Allah kadai, wanda ya kulla wannan zazzafar soyayyar tasu. Duk wata sha’awa da ya tara ta wata da watanni, duk wani feeling daya dade da zama tamkar gyambo ko tsatsa a gangar jikinsa da zuciyarsa, sai yau ya samu suke ‘healing’ daya samu Safiyyah yadda yake so a kan gadon aurensu. Maganganunsa na karshe kafin ya maidata cikakkiyar matarsa da zata iya tunawa shine da yace “tayi hakuri” and he mean it. Ba abinda zai iya mata a lokacin bayan ban hakurin. Zayyan yace tayi hakurinnan sau ba adadi yafi cikin carbi, tun tana kirga adadin ban hakurin har ta daina, because he cannot speak any fluent language today, sai baragada, irin wannan; “I neeed yhuhh badly today…I am so so - sorry Sophieeeeeee”. Gabadaya yau Habiby umarnin jikinsa da zuciyarsa kawai yake bi, ba abinda take so yayi ko ya bari ba…. Duk wani uzuri da kauda kai da kawaici ya gama yi mata su a can baya. Yayi mata bajinta da sadaukarwar da maza matasa kamarsa da yawa bazasu yiwa amarensu ba, musamman wadanda suka aura da gumin soyayya. Dole kanwar naki, Safiyyah yau tayi saranda! Ba dogon musu ta mika wuya ga bautar aure bautar Ubangiji. Zayyan ya zama mijinta na hakika yau, kamar yadda ya taba ce mata a soron gidansu watarana zai zama .... In bata manta ba ai dama ya taba ce mata bazasu dawwama a haka ba tunda ba auren Yaya da kanwa suka yi ba! Ya kuma taba cewa “akwai ranar
Chapter 21 · 0% Book details