← Book details Kawar Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 25 OF 31

Sashe 25

Kawar Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Safiyyah na level two a lokacin da sukayi aure. Kullum tare suke shiga makaranta in ta rigashi tashi ta jirashi har sai ya tashi ya goyota a bayan LIFAN dinsa su dawo gida tare. Rayuwar sa da Safiyyah ta cigaba da tafiya a haka gwanin ban sha’awa ga duk wanda ke gefensu, zaka shaida cewa rayuwar aurensu cike take da so da kauna na hakika zallah, wanda babu karya ba kuma kwadayin duniya a cikinsa, suna masu yawan tausayawa juna, da taimakekeniya a tsakaninsu, ta fannin karatu da hidimar gida, har zuwa shigar Safiyyah level three. Zayyan shi ya cigaba da daukar nauyin karatunta bayan aurensu. Da yawan abokan karatun Safiyyah basu san ma tana da aure ba, balle alaqar aure dake tsakaninta da Assistant Lecturer mai tashe a tsangayar zane-zane; Yaya Brainlliant Architect, Zayyan Bello Rafindadi. Saboda babu wata alama da zata nuna maka cewa Sophie tayi aure yanzu, tunda dama kowa ya riga ya santa ne da shigarta ta kamala wato hijab ko jilbab da kowa ya santa cikinsu. Da wannan kalar ‘dressing’ din ta riga ta suffantu, tun shigarta jami’ar Ahmadu Bello. To da tayi aure ma ba abinda ta canza illa shi Zayyan dake koraffin Hijabin ya daina burgeshi yanzu, don har a cikin gida fama yake da ita akan ta saka masa suttura irin wadda yake sayo mata ya kawo mata, amma saidai ta boyesu a kasan akwati. In kayan kwalliya ya sayo ya kawo mata kuwa don tayi masa kwalliya a gida to su Rayyah da Sabah da Rayha take aikewa Dandume. Har rannan wani coursemate dinta mai karambani da shishshigi mai suna Balarabe ya kasa shiru yake tambayarta, shin ko Zayyan Rafindadi biological Yayanta ne? Don yaga suna tafiya gida tare yanzu kullum, yana goyonta akan Lifan dinsa. Ko kusa bai kawo aure a tsakaninsu ba, sabida Zayyan nada iya taku, baya bada wata kafa da zaka gane akwai alaqar aure tsakaninsa da Safiyyah Dandume, sai ta karatu a makaranta. Ita kanta a makaranta “Malam” take kiransa, sai sun dawo gida zaka ji ya koma “Habiby”. Safiyyah tayi murmushi tace da dan ajinsu Balarabe "eh, Mallam Zayyan Yayanta ne, kuma Malaminta ne". Bata kuma kara tofa komai akai bayan wannan ba, aka wuce wurin, wato aka bar zancen a haka. Amma shi dai Balarabe ya digawa abuna yar tambaya, don in ba Yayanta bane a kamala irin tata, bazata yarda ta dinga hawa bayan Lifan dinsa ba Don haka take karatunta lafiya ba idon 'yan ajinsu a kanta, musamman da Zayyan din baya daukar 'yan level three. Level 1&2 yake dauka. Library kuma bata fasa zuwa ba, ta wuni tana karatu acan da ‘Pink Travel Mug’ dinta na shan ‘hot coffee’. Allah ya sani she is addicted ga shan coffee, yana bude mata kwanya sosai. Musamman a lokacin da jarrabawa ta kusanto, ko in zata yi assignment, tana can library da pink travel mug dinta mai cike da hot coffee, to acan Zayyan yake samunta ya dauketa su wuce gida. Har Kano Zayyan ya kaita sada zumunci wajen Yayarsa Zubaina, amma basu kwana ba, sun yi zumunci da ita da iyalanta suka dawo Zaria a ranar. Sosai Safiyyah ta kwantawa Yaya Zubaina a rai, ta yaba da hankalinta da kamalarta, Zubaina ta kasa shiru har sanda zasu tafi ta kira Zayyan zaure kafin su wuce, ya dawo shikadai, sai ta rike hannunsa tana murmushi tace. “Gaskiya Baffan Mama, ka gama yin dacen mata, ga kyau ga nutsuwa ga cikar addini, ka riketa da kyau, kaji Baffa? Domin na hango maka mace tagari anan, wadda dukkan alamu sun gama nuna ta fito daga babban gida na tarbiyyah da addini, wadda zata baiwa ‘ya’yanka irin tarbiyyar da akeson ‘ya’yan musulmi su samu, a tareda Safiyyah”. Zayyan ya gyada kai yana murmushi, ya kara jin son Yayarsa Zubaina, ita kadai ce ta yabi Safiyyah a danginsa, su sai dai suyi mockering dinta da diyar Alaramma ko ‘stammerer’. Sai kace fitowa daga tsatson Alaramman ba abun alfahari bane ko in-inar ita ta baiwa kanta. Yace. “Nagode Yaya Zubaina. Na san you will always stand with me, akan duk abinda na kawo nace inaso. Ko da kuwa ke abun bai yi miki ba zaki tayani son shi, da kula dashi. Ke kadai ce kika yaba da Safiyyah a cikinku. And I truly appreciate. In sha Allah zanyi duk yadda kika ce akan Sophie, zan riketa amana, zamu rufawa juna asiri mu zauna lafiya”. Da aka kwana biyu kuma ya kaita gidan Yaya Zubaidah a Batsari. Tarbar ta sha banban tsakanin ta gidan Zubaina data ta gidan Zubaida, ko daga ruwan pure water biyu da aka ajiye mata akan plate aka shanyata a falo aka ce za’ayi magana da Baffa cikin daki, bayan daga nesa suka zo ko abinci bata basu ba, sai Baffa data janye uwardakinta tana masa korafin Baban su Amal ya hanata aikin da takeyi. Sabida yadda Mama ke yawan kiran Safiyyah diyar Alaramma yasa itama Yaya Zubaidah tuni tabi ta raina ajin Safiyyah tun kafin ta ganta. Nan Safiyah ta gama gane ‘clear difference’ na halayen ‘ya’yan Mama, biyu sun biyo Baba Bello sak a komai (Zayyan da Zubaina), hudu sun kwashe Mama Fatu tsaf (Zubaidah, Zahra, Zaytoon da Hatoon). Safiyyah a wannan dan tsakanin da take karatun digirinta na farko a Zaria, Zayyan na aikinsa na Lecturing, suna yawan zuwa Katsina gaida iyayensu, duk kuma sanda suka je Katsina sai sun shiga Dandume, sun shiga shekara ta biyu da aure yanzu, ta gama fahimtar halin dangin mijinta tsaf, don basa wata daya Zayyan bai kaita cikinsu ba. Musamman lokacin da Baba Bello ya kwanta wata ‘yar jinya. Baba ya jima yana fama da larurar suga da hawan jini, amma basu taba kwantar da shi ba sai a wannan lokacin, kuma Zayyan ke kula da zarya da shi a asibiti, kullum yana hanyar asibiti dashi, don haka da aka baiwa Baba kwanciya don samun (bed rest) sai yayi tunanin maido Baba asibitin koyarwa na ABUTH kawai don dai yafi samun damar kula dashi da kansa, in yana kusa dashi saboda aikinsa, ya kuma ragewa kansa zirga-zirgar da yakeyi tsakanin Katsina da Zaria. Sai hakan yasa takalihun abincin Baba da ake yi masa na musamman irin na masu ciwon suga a zaman asibitin ya dawo wuyan Safiyyah, ita ke kula da yi masa tsaftataccen abincin da ake masa na musamman, kullum ita keyi safe, rana da dare ta kai asibitin da kanta, to anan ne suka cakude da dangin Zayyan suke wuni tare har dare, wani lokacin Zahra da Zaitoon su kan biyota gidanta su kwana, da safe suyi wanka su koma asibiti tare, don autar Mama Hatoon na makarantar kwana har a lokacin. A dan tsakaninnan kaf! Sophie ta gama banbance halin yayye da kannen Zayyan a kanta, dukkansu dinnan ra’ayinsu ya tafi daya dana mahaifiyarsu Mama Fatu akan rashin dacewar aurenta da Zayyan. A wurinsu ita ba tsarar aurensa bace, kamar wata alfarma aka yi mata da aka aureta, in ka cire mai saukin halin cikinsu Yaya Zubaina. Babu mai kallon kanta da gashi. Abin mamaki ko a fuska Zubaina kadai ke kama da Baba Bello, dukkansu da kyakkyawa Mama Fatu suke kwasar kama har Zayyan din, kuma ita kadai take da halinsa na accommodating kowa ya rabeta, irrespect of social status. Safiyyah ta fahimci ‘yan uwan Zayyan da mahaifiyarsa sun raina ajawalinta, suna ganin bata isa ya aureta ba, kamar ajinta yayi kadan da auren Zayyan dinsu, matsayinta bai kai da auren dan uwansu/dan ta ba, balle ta samu matsayin shigowa cikin su ta hada kafada dasu a matsayin surukarsu/matarsa. Ta kan tambayi kanta to ko mai yasa ahalin Mama suka raina ajawalinta haka? Ita bawulakantacciya ba? Daga bisani ita da kanta ta gane sabida ita ba ‘yar masu kudi bace, kuma ba ‘yar gayu gangariya irinsu ba, ko daga yanayin sutturarta sun raina mata, wadda tasha bambam data ‘ya’yan Mama da abokan huldarsu. Har ila yau, a wannan zaman ne ta fahimci tsakanin Zayyan da Zubaina akwai fahimtar juna mai kyau fiyeda tsakaninsa da babbar Yayarsu Zubaida. Zubaina kamar ba sakuwarsa ba, tunda kowa ya san sako da sako ba’a shiri. Amma su shiri suke kamar aminai. Zubaina ita Zayyan ke bi a haihuwa, wato ita ta saki nono ya kama. Ita kadai ke taya shi son Safiyyah bilhaqqi, take kuma girmama tushenta, asalinta da nasabarta, saidai kuma ita a nesa take, ko jinyar Baba da akeyi yanzu sau daya ta samu Malam Mahi mijinta ya barta tazo, kuma bata kwana ba a ranar ta koma. Zubaina ce kadai bata samu ilmin zamani mai zurfi a cikinsu ba, kuma bata aikin gwamnati, don daga sakandire aka yi mata aure, mijinta kuma baya ra’ayin ta cigaba, sai ya bata jari take sana’ar poultry, amma hakika Zubaina tafi Zubaida kyakkyawar alaqa da kowa. Zubaida kuwa babbar ma’aikaciyace a Batsari Local Government. Su kam su Zubaida, Safiyyah kan fada a ranta, duk an tsotso hali daga Mama, na raina mutanen da basu kaisu a status na rayuwa ba, halinta ba wanda suka bari sai ma wanda suka dara ta. Abin nufi, ‘ya’yan Mama kullum suna kallon kansu da matsayin mahaifinsu da shaharar sunansu a Katsina, cewa su iyalin Bello Rafindadi ne, kamar diyan gwamna haka su Zahra ke jin kansu, in kai ba kowa bane a Katsina, iyayenka basu yi suna kamar nasu uban ba, kuma basu taka wani matsayi a boko ba, to 'ya'yan Mama da ita kanta basa wata alaqa mai dadi da kai. Ta gane wannan halinsu ne na cikin jini, akwai girmama abun duniya da daukaka sama da asali da nagarta. Don haka Safiyyah ta zama kamar wata ‘yar karere a cikinsu, saboda yadda suke wareta gefe su manta da ita a wurin a zaman asibitinnan, kamar wata ‘yar aikin Mama haka suka dauketa. Don haka sosai Safiyyah ta kama kanta daga shiga sha’aninsu. Bayan ritayar Baba Bello daga jami’ar Umaru Musa, kafin ciwon nan ya ci karfinsa, Arch. Bello ashe ya tara duniya a boye, domin ya koma ya kutsa sosai cikin sha’anin (Real Estate Business). Baba Bello ya samu arziki ya kuma samu budi mai yawa akan harkar zanen Estate da ginasu da bada hayarsu cikin dan lokaci, ya samu alkhairi akan real estate nan da nan, har fiyeda
Chapter 25 · 0% Book details