← Book details Kawar Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 28 OF 31

Sashe 28

Kawar Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kalamansa ne da support dinsa suka raineshi, har ya zama jarumin da ya zama. Yanzu kuwa da Baba ya tafi ya barshi, ya tabbata ya tafi harda jarumtarsa. Sabida haka ba wani abu na farantawa ko wata soyayya da wani ko wata zai nuna masa yanzu da zata hana shi damuwa da rashin Baba da yayi. Saidai ya kalleka kawai. Har sai bayan zuwan Malam Usman ne ya dan samu canjin yanayi kadan. Da safe suna karya kumallo, ya kalli Safiyyah, sai ya ga itama duk ta rame saboda damuwar da yake ciki, kamar ma ya fita kuzari yau, ya sa hannu a habarta yace “Sophie”, sai ta dago a hankali ta dube shi sai ga kwalla fal! A kwance cikin idonta. Zayyan yasa yatsarshi manuni ya tabo kwallar ta idasa gangarowa, yayi mata murmushi yace “haba Sophie na, ban sanki da saurin karaya ba, in duk muka karaya wa zai cigaba da karfafa wani? Kiyi hakuri dani kinji, kici gaba da karfafani, ni nasan situation dina ba mai wucewa bane in har zan tuna Baba. But I always pray that it will come to pass idan ina ganin ki a tare dani cikin walwala”. Ya fadi hakan ne da ya yana tuno wasu kalaman Baba Zayyan akan Safiyyah, watarana suna hirarta yace dashi “Zayyan ina fada maka ka riketa da kyau, wannan matar kwarai ce, kada ka bari ta kubuce maka, ita kadai ta isheka rayuwar duniya kamar yadda Mamanku ta isheni, ni nasan ‘yar baiwa ce, tsatson albarka mai iya tattalin farin cikin mijinta, ko a fuskarta mutum zai karanci kaunarka, ka tattalata ka sata farin ciki kullum wallahi kadara ce ita babba gareka”. Sai yaji murmushi ya subuce masa. Yana shafa habar Sophie yana fadin “Sophie diyar Babanta, Baba Bello, I truly love you!”. Murmushin da Safiyyah ta dade bata gani daga gareshi ba, watakila tun kafin rashin Baba rabon da taga murmushinsa. Yace. “Zan wuce Katsina yanzu, amma bazan kwana ba in sha Allah, ki daina damuwa kinji Sophie na? Everything will be alright da karfin tawakkali. My mood will be restored soon, idan wannan shine damuwarki. Zan yi kokari in dawo Habiby dinki da kika sani, kin ji Sophie?” Safiyyah ta kusa shidewa don farin ciki, domin taji dadin kalamansa sosai, ta kasa boye jin dadin data yin ta hanyar fadawa jikinsa ta rungume shi, ta sumbace shi saman lips dinsa yayi maza ya kwaci kansa yana dariya yace “kada ki karya min alwalar walha” tace ba damuwa sai ka daura wata, nasan wannan ta riga ta kwance. I have no idea na yadda nayi missing my man anan wurin…”. Ta fada tana rufe idon da ya bashi dariya, har yana tantama anya Sophien shi yau take masa wannan soyayyar? Safiyyah sarkin kunya sarauniyar ustazan Dandume? Inama ta dore da hakan, da ya zama dan sarki. Amma ya san mawuyaci ne ta dore din, kunya a jininta take. Da kyar ta bar shi ya tafi, don sai da aka yi alwala mai dalili, sannan ta bashi sakon gaisuwarta ga Mama dasu Zaitoon, ta rako shi har kofar gida. Safiyyah bata koma gida ba sai da ya hau okada (babur) din da zata kai shi tashar da zai hau motar Katsina. A farkon shiga unguwar Rafindadi ya sauka daga kan Achaban da ya dauko shi daga Tasha, ya taka a kafa, da dan nisa kadan kafin ya isa gidansu, sannu kan hankali yake takawa don isa zuwa kofar gidansu. Ya sauka tun daga dan nesa da gidan ne don kawai ya motsa kafarsa, don ya dan dade bai taka ta sosai ba, hakan yasa ya samu damar da ya gaggaisa da jama’ar unguwarsu. Suna kara yi masa ta’aziyya. “hakika Baba Bello na kowa ne, Allah yabamu hakurin jure rashinsa” yadda ‘yan shiyyar Rafindadi da suka hadu a hanya suke yawan fada masa kenan. Tun daga bakin kofar gidansu da ya sako kai ya shigo cikin harabar gidan, Zayyan ya kara gayawa kansa “lallai bangon gida ya fadi!” kamar yadda Mama tace. Wato Baba Bello ya barsu. Ya subhanallah! Meyasa yayi wannan dadewar bai zo gida ba ina tawakkalinsa da imaninsa suka je suka barshi? Saboda da shigowarsa harabar gidansu yaga hatta fulawoyin gidan kansu, da grass carpet duk sun fara bushewa, kamar an shekara ba’a basu ruwa ba, alamu ne na rashin samun kulawa kamar da. Abin mamaki ma’aikatan gidan sun fara watsewa wai ace daga rasuwar Baba, ko arba’in ba’a yi ba, ko a tunaninsu an daina biyansu ne yanzu, oho! Ko kuma don ya dade bai zo Katsina ba? Mama kuma ya san bata tasu take ba a wannan lokacin da take cikin alhini da Takaba. Maigadin Baba Malam Ilyasu ne kadai bai tafi ba. Ko dama can shi dan amanar Baba ne. Busassun ganyaryaki duk sun cika harabar wajen ba’a share ba. Hakanan yake jin kararsu duk takun da yayi suna bada kara rakakas-rakakas na bushewa. Wannan abu ya yiwa Zayyan ciwo. Yace yau gidansu ne za’a maida kango as early after the demise of Baba? Malam Ilyasu na gaisheshi bai ko amsa ba don bacin rai, kawai zuciya ta kawo shi wuya, ya fara fada ta inda yake shiga bata na yake fita ba akan Dattijon, har ya manta da shekarun Baba Ilya. “Baba Ilya, yaya akayi aka bar gidan haka babu shara, sai kace bola? Yaya aka yi shukoki suka mummutu haka ba kwa basu ruwa da taki ne? Motocin Baba ne sukayi irin wanan kura haka? Saboda babu Babana ko? Saboda ba’a biya ku kudin wannan watan ba? Ko babu mutane da suke rayuwa a cikin gidan ne?” Nan Malam Ilya ya sadda kai, ba ciwon fadan da yaron ke masa yaji ba, a’a ya san feeling dinsa na yanzu, kamar baya cikin hayyacinsa yake maganar. Shima sai kewar Alhajinnasu ta zo masa har saida ya share kwalla, da kyar ya dafa kafadun Zayyan yana lallashinsa, yace masa “kayi hakuri Zayyanu, inna kira wayarka bana samunka, Hajiya kanta tace bata samunka a waya wai ta rasa lambar maidakinka cikin wayarta, naso in gaya maka Habu ya koma garin su tun bayan bakwai, wato mai kula da shukokin gidan, shikuma Umaru mai wankin motoci da share-share shima yace ya samu wani aikin don haka ya tafi, Bala direba kuwa ko sallama bai yimin ba na daina ganinsa”. Zayyan yace a ransa “dan adam kenan! Babu komai, it is well. An gode”. A fili kuma yace “kuma da babu Habu ba Umaru ba Bala a gidan, saboda su butulallun Allah ne, kai sai ka kasa share harabar gidannan ko sau daya?” Shi bai san ba su Habu kadai ba, duk ma’aikatan cikin gida mata ma sun ware, don Mama tace bata bukatar kowa, Ankudi kawai tace ta zauna to itama tace zata ganin gida kafin sadaqar arba’in amma har yau bata dawo ba. Daga cikin gida Mama ta jiyo tashin sautin Zayyan yana magana da Baba Ilya cikin fada-fada, take cema Hatoon “ke duba min ki gani naji kamar muryar Baffana yana fada a waje, jeki gano min shi da waye? Dama ashe Baffa ya iya fada haka?” Hatoon ta leka ta taga ta ganshi, tace da Mama “ai kuwa shine. Baba Ilya ne maybe ya taka sawun barawo”. Ya tako zuwa cikin gidansu yana gayawa kansa sai yayi da gaske, ya kuma tsaya tsayin daka don ganin gidansu bai mutu ba, a rashin Baba Bello. Dole ya dinga zuwa akai kai, fiyeda baya don tabbatar da lafiyar gidansu, lafiyar kannensa data mahaifiyarsu, da bukatunsu na yau da kullum. Yayi sallama a falon Mama Fatu, Maman ta amsa daga zaune akan sallayarta, bata dade da idar da sallahr azahar ba ya shigo, ta ce. “maraba lale da Baffan Mama, kuma Baffa daga zuwa sai fada? Kai da waye halan? Waya taba min Baffana magajin gida haka?” Zama Zayyan yayi, yana ajiyar zuciya, ransa yana sanyi da ganin Mama, da kalaman maraba da take yi masa cike da murnar ganinsa, bai ce komai ba, sai sauke ajiyar zuciya yake yana kallon Mama cikin tausayi, ganin yadda duk kibar nan tata ta jin dadi ta zaizaye rana daya yasa yaji zuciyarsa ta dada tsinkewa, gabadaya ta rame, alamu ne na har yanzu bata wartsake daga dukan da rashin Baba Bello yayi mata ba. Idanuwanta duk sun yi ciki sun kankance don yawan kuka, Mama ta koma yellow kamar mai ciwon shawara daga fara, kuma jajazir din Barumiyarta. Gidan da kullum zaka samu kowa cikin annuri ana raha da wasa da dariya, a shiga nan a fita can, walwalar gidan data mutanen gidan duk ta kaura yanzu, tabbas Uba shine jigon gida, don haka Mama Fatu kam ta ga mutuwa irin wadda bata taba gani ba, saboda Baba Zayyan dinnan shikadai ta sani ta kuma rika a duniya a matsayin komai nata, bata gajiya da fadawa ‘ya’yanta “Bello ne uwarta shine ubanta” tunda bata tashi tareda iyayenta ta san dadinsu ba sai nasa, shine kuma danginta don ba abinda dangi suka kulla mata a rayuwarta, tun tana karama iyayenta suka rasu, aka rasa mai daukarta sai wata kanwar mahaifiyarta a Rumah, ya kuma aureta ne da kananan shekarun da basu fice goma sha biyar ba. Sun yi zama na kauna da soyayya abar buga misali ita dashi da ‘ya’yansu, na kusan shekaru arba’in da doriya. Zayyan yasa farin hankacinsa yana share fuskarsa da tayi jajawur da gumi, hawaye ya digo masa. Mama ta taba ce ma Zubaina. “Wannan shine hawayen Zayyan na farko data yi witnessing a shekarun girmansa”. Ko ranar da Baba ya rasu, Zayyan yafi kowa jarunta da nuna dakiya, amma a yau ganin yadda gidan mahaifin nasa ma neman mutuwa yake yi ya jefa shi cikin wani hali na jin mutuwar Baba Zayyan fiye da kullum. Da kyar Mama ta samu ya saki ransa suka soma gaisawa, tace ina Safiyyah? Yace a ransa yau wace rana Mama ta tambayeshi Safiyyah? Ya gaya mata tana lafiya tana kuma gaisheta. Yayi fatan Allah yasa Mama ta fara son Safiyyah ne saboda rashin Baba Zayyan, tunda ta san yadda shi Baban yake sonta kamar ‘yarsa, in ta cigaba da nuna rashin kauna ga Safiyyah abin zaiyi masa yawa. Sunyi hirarraki masu dama ranar, Mama tace “dama inata jiran zuwanka tunda kaki ko waya ka kunna,
Chapter 28 · 0% Book details