← Book details Kawar Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 31

Sashe 10

Kawar Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

labarin cikin wahalar in-ina kara sonta yake yi, bai iya ya bari ta gama bashi labarin ba ya katseta. “Hijabie, ina son zuwa gidan ku fa!”. Safiyyah ta dubeshi da dan mamaki da dan tsoro a idanunta, saida yaji tsigar jikinsa ta tashi, tace “gidanmu? To me akeyi a gidanmu Mr. Library?” Ta bashi dariya sabida tsakaninta da Allah ta shiga damuwa da jimami. Don ta san halin Malam sarai, sanadin haka zai iya katse karatun, don wannan ba shine alkawarin data daukar masa ba kafin ya barta tazo makaranta. Zayyan ya samu sa’a mai ban mamaki a kanta da ita kanta take mamaki. Yayi magana cikin sauti na kwantar da hankali, ganin yadda kalamanshi suka sa ta shiga rudu, yace, “Safiyyah, mu zama frank da junanmu, zumuncinmu nida ke mai ma’ana ne a wurina, mai nufin yada kyakkyawar yabanya, kuma shine abinda zai kawo ni gidanku gaban iyayenmu”. Safiyyah ta gyara zaman hijab dinta a kanta, ta langabar da kai tace “idan kuma Malam yace wanene kai? Ko meye tsakaninmu idan kaje me zan ce masa? Ka dai bari sai na sanar dasu a gida tukunna, don Babana Malami ne babba, baya bari azo masa gida haka kawai babu dalili”. Zayyan ya kankance ido yayi mata wani shanyayyen kallo da bai taba yi mata ba, yace “ai nima ba hakanan zan zo ba Hijabhie, ba haka kawai ce zata kawo ni gaban Malam ba, banza tana kai zomo kasuwa ne? Safiyyah stop kidding and joke apart pls, Hijabi na dake ajiye a gidansa nake so in dauke abina. A takaice zan iya cewa soyayyah ce ‘yar gaske, wadda ta dabaibaye ni, da neman irinsa mai albarka zai kawoni gidansa. In kika ga kare na sunsunar takalmi ki tabbata dauka yake so yayi Safiyyah!?" Safiyyah ta rufe ido da hannayenta da suka sha adon jan lalle, taji kunya matukar gaske ta lullubeta, rana ta farko da wani namiji da zuciyarta ta riga tayi na’am dashi ya furta mata kalmar SO a tsanake, tace cikin jin nauyi da farin cikin da take kokarin dannewa, don gabadaya sai yau tasan ashe itama ta fara kamuwa da son dan ‘little gentle’ saurayi Zayyan din, ba haka kawai zuciyarta da ruhinta suka sake dashi cikin dan kankanin lokaci ba, SO ne gangariya, dan asali na hakika Allah ya gittar a tsakaninsu. Don haka cike da jin kunya Safiyyah ta sunkuyar da kai tana kokarin hada kalmar da zata bashi amsa wadda bazata nuna eager dinta ko amincewarta farat daya ba, tace a hankali. “Amma dai ka fara bari in sanar a gida first, cewa kana so kazo ka gaida Malam, in yaso ya baka iznin zuwan, saboda kafin Malam ya barka ka zo wajena fa sai ka je ka fara samunsa takanas, ka zuba gwuiwa a kasa ka gabatar da kanka da dalilin zuwanka, ya baka yardarsa, da lokacin da zaka dinga zuwa, wannan shine, bisa tsarin gidanmu. In ba haka ba zuwanka kai tsaye zai zame min matsalar da zata iya yin sanadin karatuna”. Zayyan dai ya fahimci ya zo gida na mutunci da tarbiyyah irin wanda yake fatan samarwa ‘ya’yansa. Kuma aka ce labarin zuciya a tambayi fuska, ko daga idanunnan na Safiyyah masu nuna yawan jin kunyarsa yanzu, da jin nauyinsa tuntuni, yau kuma gabadaya sun kara canzawa da yawan kaucewa haduwar idanunsu. Uwa Uba, amsar da ya samu daga gareta yanzu, ya san Safiyyah tayi na’am da shi dari bisa dari ko bata furta kai tsaye ba. Don haka shikuma bai yi kasa a gwiwa ba, ranar Juma’ah kwana uku da yin wannan maganar tasu, bayan an sauko daga masallaci ya sake daukar wanka na musamman, daman dai shi Zayyan kowa ya shaida ma’abocin iya daukar wanka ne, ga iya sanya hula a kan goshinsa, ya dauki karin hular Zanna Bukar da ake yayi a lokacin, da karin gugar shaddarsa ta yayi, ya fesa turare sannan ya fito daga dakinsa ya nufi cikin gidansu, nan yayima Mama sallama kan zai je unguwa, har Mama tana tsokanarsa ko daurin auren babban amini Habibu zai je ne? Irin wannan kashe hula a goshi Baffana? Murmushi yayi bai ce komai ba, don abu na karshe da Mama zata kawo a ranta shine Zayyan dinta zai iya kallon wata mace da sigar soyayyah balle har yace yana so, sabida kamewarsa da dattakunsa na halin manya irinna mahaifinsa, ya fita ya kama hanyar Dandume a motar haya bayan ya rufe dakinsa dake BQ na gidansu. A ranar Safiyya na gida tazo yin hutun karshen mako, tunda bata da lecture ranar Juma’ah tun sassafe ta kamo hanya ta taho gida, kasancewar a Zarian tana zama ne a hannun Antinta Dije dake aure a Tudun Wadar Zaria. To kusan duk bayan sati biyu zata taho Katsina a ranar Juma’ah, ta dawo Zaria Lahadi da yamma. Zayyan koda kuskure bai gaya mata a wannan satin zai zo ganin mahaifinta ba. Don haka ita kanta bata san da zuwansa ba ko alama. Tama manta da zancen da sukayi dashi kwanaki uku da suka gabata. Tun daga zauren farko da ya iso Safiyyah ta shaki wani kamshin turare data yiwa farin sani amma ko kusa bata kawo shi bane a zauren gidansu, har cikin gidansu turaren Zayyan ne mai dadin kamshi na Ultraviolet (Paco Rabanne), Zayyan Bello ya iso gidan ne ta hanyar bin adireshin da Safiyya ta kwatanta masa tun daga tashar Dandume aka dauko shi a babur har kofar gidan, don haka bai sha wahalar samun gidan Alaramma Usman Ladan ba. Kasancewar mahaifinsu Safiyya sananne ne kuma fitaccen malamin addini a ciki da wajen garin Dandume, don haka Zayyan yana sauka a tasha yayi tambaya sai aka hadashi da mai babur ya dauko shi, bai sauke shi a ko’ina ba sai kofar gidansu Safiyyah. Da yake yammaci ne na Juma’ah magidanta na unguwar ya tarar tare da Malam din, suna daukar karatun yammacin Juma’a yadda suka saba, kowanne magidanci da irin littafin da Malam yake karantar da shi. Zayyan sai ya shige cikin daliban malam masu daukar karatu ya zauna ya saje dasu abinsa, duk da shine kadai yaro matashi a cikinsu, saika rantse dalibin malam ne saboda yadda ya nutsu yana sauraren karatun da Malam ke badawa. Malam na lura da bakuwar fuskar, mai zubin kyawun fulanin Rumah daya cakude da kamannin ‘yan Rafindadi ma’abociyar kuruciya a cikinsu, ya ga kuma shi bashi da littafi a gabansa amma ya tattara hankalinsa ya nutsu yana sauraronsu. Hakan yasa lokaci zuwa lokaci Malam na daga ido yana kallonsa yana cigaba da bada karatu. Bai kula shi ba, har sai da ya gama da dalibansa gabadaya. A karshe aka yi tamabayoyi akan darussa daban daban da aka karantar, sannan aka yi addu’a ga iyali da al’ummar musulmi da kasar bakidaya, aka shafa tare, yadda Malam da dalibansa suka saba kullum, kowa ya soma kokarin saka takalminshi don barin zauren gidan Mallam. Shi kam Malam har lokacin yana zaune akan buzunsa yana musabihar sallama da dalibai masu ficewa, Zayyan yana zaune gefe a inda yake tun shigowarsa, bai yi niyyar tashi ya karasa gaban Malam ba, kuma bashida niyyar tafiya. Ya rasa ta ina zai fara, gabatar da kan nasa ko gaida Mallam din? Kamar yadda Safiyyah ta gaya masa ko waye Babanta, yaga har fiyeda hakan, yaga dattaku da tarin ilmin addini, don gabadaya kamilin dattijon Malam Usman wanda fuskarsa ke cike da farin gemu zagaye da farin saje yayi masa kwarjinin da ya hana shi ko motsi. A hakan kuma duk da alamun tsufa mai nagarta dake tareda Mallam, wanda bai yi yawan da za’a kira shi tsoho can ba, sai farin gemun da ya nuna shekaru sun tura, duk da hakan Alaramma yana dan diban kama da kyakkyawar diyarsa Safiyyah sosai. Har saida Malam ya gaji da sauraronsa yayi magana don yana so ya shiga cikin gida, yace dashi cikin mutuntawa da tausasawa. “Samari, ina fatan lafiya? Ko zan san daga ina kake? Ban wanye da kai sosai ba, kuma naga kai baka dauki karatu ba”. Zayyan ya muskuta ya gurfana gaban Mallam, kamar mai neman gafara, yayi ta maza kansa a sunkuye cikin kunya yace, “Allah gafarta Mallam ni Danka ne, sunana Zayyan Bello, nazo daga unguwar Rafindadi ta nan cikin Katsina, musamman don in gaisheku in samu albarkarku, in kuma gabatar da kaina a matsayin mai So da kauna ga irinku dana tsinta a jami’a mai albarka, wato diyar wajenku Safiyyah, wanda nake fatan ya kaimu ga zama abu guda, cikin yarda da amincewar ku, da sanya albarkar ku. Idan Mallam yayi min izni, ina so na saka kai ga fara neman aurenta”. Ya kara dukar da kai cikin dar-dar, na fargabar amsar da zai samu daga dattijon. Malam Usman ya dubi Zayyan wanda kansa ke sunkuye, tsantsar hankali da ladabin da ya nuna masa, da nutsuwar dake tattare da zancensa, sannan appearance dinsa bai nuna duniyanci ba, a’ah appearance ne na samari masu tarbiyya da kula da addini ya gani a tare da Zayyan, sune kuma abinda suka dauki hankalinsa matuka akan yaron, suka canza tsohon tunaninsa nan da nan suka juya kudirin daya dade dashi a ransa bai taba gayawa kowa ba. Ga yaron da kyawun fuska dana kirar jiki irin na zaratan mazan Rafindadi son kowa. Masha Allah dashi. Mallam ya nisa sannan yace “samari na ji bayanin ka, madallah da hankali irin naka da baka tare Safiyyah a hanya da maganar soyayya ba, a’ah sai kayi tunanin ka zo gare ni, ni mahaifinta ka nemi iznina. Wannan ya nunamin kalar tarbiyyarka. Da wannan halin kwarai daka nuna na ladabi da sanin girman iyaye, ni kuma na baka iznin ka dinga zuwa ganin Safiyyah sau daya a sati, idan ta zo nan gida hutun karshen mako da take zuwa har ku daidata kanku. Samari ban yarda ka dinga tareta a wurin karatunta ba, yin hakan karya dokata ne, sai a nan gidansu kadai, kodayake ta kan yi sati biyu bata zo ba, amma dai in har ta zo gida, na yarje maka ka dinga zuwa wajenta, anan zauren na yarda ku dinga zantawa, idan kuka daidaita kanku na kuma gamsu da nasabarka, to ni bani da abin cewa sai binku da kyakkyawar addu’a da fatan alkhairi”. Dattakun mahaifin Safiyyah da wannan tsaftatattar Malanta
Chapter 10 · 0% Book details