Sashe 29
Kawar Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
in gaya maka sakon Babanku Alhaji Murtala. Zuwansa har biyu kenan bai sameka ba, kan maganar dukiyoyin Babanku dake hannunsa da wadanda ya sani dake hannun Lauyansa dama wadanda ke Banki, yazo ne kan batun, don yanaso zai tattarosu a raba gado ranar sadaqar arba’in, a raba marigayin da wannan nauyin”. Kamar yadda ya riga ya sani Arch. Murtala shine babban aminin Baba Bello, kuma kamar Ubangida yake a gareshi a harkar Real Estate, shi ya fara budawa Baba harkar ya shigeta sosai da taimakonsa, bayan ritayarsa daga aikin gwamnati, saboda Alh. Murtala yanada connections sosai da gwamnatin tarayya, da kuma gwamnatin jihar Lagos. Arch. Murtala Babangida Masari, abokin Baba Bello ne tun na kuruciya (childhood friend) wanda tun zamanin makarantar sakandire suke tare, kuma sukayi karatun jami’a shima tare a fanni guda, don haka lokacin da Baba yayi ritaya sai ya jawoshi jikinsa ya tsundumashi a harkar da yakeyi ta kwangilar gine-gine da zanen gidaje. Zayyan yace da Mama cikin raunin murya da karaya. “Kamar ana jiran matsawar Baba har an soma zancen raba gadonsa? Hakan bai yi wuri ba saboda Allah Mama?” Mama tace “umarnin Allah ne ai na raba gado cikin lokaci, ba umarni na bane, ba kuma na Babanku Murtala ba, don a raba mamaci da nauyinsa, ba don komai ake rabawa da wuri ba ai don amfanin mamaci ne, ba kuma ni nace dashi azo a raba din ba, balle kace na fiya kankanba”. Kafin Zayyan ya samu abun cewa sai Hatoon ta fito daga daki, ta gaida shi, ta wuce kitchen ta zubo abincin da Mama tayi yau, ta dawo cikinsu ta zauna gefe tana ci, Mama tayi mata kallon takaici tace. “Shi Yayanku da yayi sammako yayi doguwar tafiya tun daga Zaria baki ga ya kamata ki bashi abincin ba? Hatoon, na rasa irin hakalinki, yaushe zaki girma ne? Kullum sai kin nunawa mutane halinki na rashin da’a da sanin yakamata da zaisa aga laifina wajen baki tarbiyya kike jin dadi ko? Cikinki kadai kika sani. amma na dan uwanki ko oho ko?” Karo na farko da zai iya cewa yaga Mama tayiwa Hatoon dinta fada, kuma a kan abinda ya kamata. Kullum saidai tayi laifi in an yi yunkurin yi mata fada ko gyara ta tare mata. Yau dai yanata ganin sauyi a tareda Mama yayi fatan Allah yasa ta dore. Yana matukar son ace halin uwarsa yafi na kowa kyau. Ganin yadda Hatoon ta zumburo baki, dama aka ce icce tun yana danye ake tankwara shi….. Hatoon zatayi shagwabarta yadda ta saba sai suka hada ido da shi, irin kallon da ya sakar mata yasa ba shiri ta mayar da bakin data zumburo ya koma daidai, daga yadda taga yanayinsa zai iya marinta yau, don haka ba shiri ta tashi da sauri, ta koma kitchen din ta zubo masa Sinasir, Waina da miyar ganyen alayyahu da tantakwashin Sa, da Mama tayi. Ta kawo gabansa ta lallaba ta ajiye ta gudu dakinta bata kara fitowa ba. To dai da yake yana jin yunwar da gasken gaske, shiyasa ya yarda da tayin Mama, ya mike ya wanko hannunsa a sink din falo, ya dawo ya zauna, ya yiwa Sinasir da wainar nan kyakkyawan ci, ko babu komai Mamansa ce tayi da kanta. Yayi kewar girkinta sosai, don Mama ta iya girki na gargajiya, yana ci suna hira da Mama, hirar da suka jima basu yi irinta ba, yace zai je gidan Baba Murtala din cikin satinnan ya same shi har Lagos din. Haka ya wuni sur tare dasu har la’asar yana Rafindadi, har su Zahra suka dawo daga makaranta suka sameshi a gidan suka sha hira shida su, abinda bai cika yi dasu ba a baya, amma yau ya zauna cikinsu ya saki jiki da fuska ya ji damuwar kowaccensu da sha’anin karatunta, ya basu abinda suke bukata don tausayinsu yake ji su duka in ya tuna yanzu sunansu marayu, musamman sanin yadda Baba ke kula dasu, kafin yamma tayi ya juyo Zaria. Sai dare can ya iso gida. Ya koma Zaria da kyakkyawan kudurin ba zai sake nisa dasu Mama ba, hakika suna bukatarsa a kusa dasu, domin yaga yadda rashin Baba ya ragaita su. Ya barwa ransa in sha Allah ba zai kuma jimawa bai zo garesu ba. Ya tafi da tausayin Mama fal a ransa, da damuwar ganin su Zahra duk sun rage karsashi da kidifiri, wannan fallin nasu na gayu da iyayin ‘yammatancinsu duk babu shi yanzu, walwala kanta ta kaura a gidan Mama da ‘ya’yanta. In ka dauke Hatoon babu wani mai walwala a cikinsu. To kafin ma Zayyan ya saka ranar zuwa Lagos gun aminin mahaifinsa Baba Murtala shi ya zo da kansa har Zaria ya same shi tareda Lauyan Baba Barr. Abba Gana Shattima. Sun tattauna extensively, an kuma tattaro dukiyoyin Baba na gida dana banki da wadanda ke hannun Baba Murtala wadanda Zayyan kansa bai san dasu ba, don haka ya sha mamakin jin abinda Baba ya bari ya kuma jinjina amana irinta Baba Murtala don shi ko sau daya Baba Bello bai taba gaya masa yanada dukiya mai yawa cikin dukiyar Murtala ba. Ya kara jin gudun duniya ya shigeshi, da tsoron tara dukiya. Mutuwa mai tonon asiri! Ashe har Estates Baba Zayyan ya gina ga gwamnatin tarayyah da ba’a kai ga biyanshi kudin kwangilarsa ba, sai yanzu da ya rasu, Baba Murtala ya tsaya tsayin daka yayi fafutuka aka biya magadansa. Baba baya tattauna harkokin business dinsa da shi dan sa Zayyan saida Baba Murtala kadai, ko mai yasa? Ko don ya san baya ra’ayin business din? Zayyan a lokacin bai takura kansa da dogon nazari akan dalilin da yasa Baba Bello baya gaya masa samunsa ba, a take ya baiwa kansa amsa don ya dade da sanin doctrines din Baba Bello fiye da kowa; Shi ya san ba don komai Baba yayi hakan ba sai don yafi so ya koyi dogaro da kansa, ta hanyar amfani da ilminsa bada dukiyar da waninsa ya tara ba. Kuma alhamdulillah Baba yayi nasarar tsayar dashi akan kafufunsa, ta hanyar bashi ilmin addini dana zamani, don tuni ya tashi daga Asst. lecturer zuwa cikakken lecturer a ABU yanzu. Aka tattara dukiyar baba Bello waje daya da taimakon mai shari’a da lauyansa aka rabawa iyalinsa gadonsu bisa tsarin addinin musulunci. Inda kamar yadda addini ya tsara shi ya tashi da kason da ya rubanya na ‘yan uwansa mata. Mama kuma ta karbi tumunin takabarta. To bayan gama rabon gadon ne Mama ta tara yaranta mata duka suka yi (closed door meeting), suka amince da shawarar da Mama ta kawo musu. Mama ta kira Zayyan a washegarin ranar data zauna da yaranta mata, suka zauna daga ita sai shi, bayan sun gaisa yaci abincin data aje masa ta tabbatar ya samu nutsuwa, sai tace masa. “Baffana, nida ‘yan uwanka Zubaida, Zubaina, Zaitoon, Zahra da Hatton, mun yanke shawarar damka maka ragamar komai namu a hannunka, wato mun maido kason kowaccenmu hannunka, a sake cure dukiyar nan waje daya in yaso ka cigaba da juyata kamar yadda Babanku ke yi a harkar Real Estate. Da sauri ya dago ya dubi Mama a rikice, ta bude ido sosai tace “Eh, haka nake nufi ka bar aikin gwamnati, muna son a matsayin ka na Da namiji kai kadai a cikinmu ka dora mana daga inda Babanku ya bari”. Ta soma matsar kwalla da gefen hijabinta. Tana cewa “ni ban ga me kake samu a koyarwar nan ba, ni ban saba da wahala ba haka ‘ya’yana, dole ka taimaka mana kada rashin Babanku yasa mu ragaita, kaga dai dukiya in ba juyata ake ba bata da albarka, nan da nan za’a nemeta a rasa. Ni dai ka ajiye aikin gwamnati, kazo ka zame min Bello Rafindadi tunda dai ga jari ya bar mana”. Zayyan a wannnan lokacin sai ya karaya, har fiyeda kima, irin abunda yake gudu kenan tun rasuwar Baba. Ya san duk nauyin gidansu kansa zai dawo. Mama ta manta kama da wane bata wane. Dama har lokacin cikin dimuwar yawan dukiyar da Baban ya bari yake. Yana ganin bazai iya da wannan nauyin da Mama da ‘yan uwanshi ke son dora mishi ba. Arch. Bello Rafindadi, bayan kasancewarsa tsohon dan boko tofa rikakken dan gwagwarmayar kasuwancin gine-gine ne. Baya taba tsugunnawa a waje daya, duk inda ya samu kwangilar zane ko gini zai je yayi a cikin Nigeria. Shikuwa ya riga ya san kansa cewa shi malamin makaranta ne, wanda samunsa duka ya ta’allaqa ne ga albashinsa na wata. Bai taba mafarkin zama irin Babansa a harkarsu ta kasuwanci ba, ko zama dan gwagwarmayar neman kudi kamar Baba Bello, wanda ba abu ne mai sauki da zai iya ba a halin yanzu. Da karyayyar zuciya da kuma sanyin murya Zayyan yace da Mama cikin bijirewa. “Mama naji bukatarki data ‘yan uwana mata, amma ina baku hakuri, wannan wani nauyi ne mai girma kuke son dora min da bazan iya dauka a halin yanzu dana samu Rauni a zuciyata ba, tunda nauyi ne na dukiyar marayu kin ga, ina tsoron wani abu ya samu dukiyar ‘yan uwana a hannuna saboda tsautsayi ko sakaci na, tunda kinga ba wai na iya harkar bane, ban kuma taba gwadawa ba. Ni a ra’ayina da dai kin bar kowaccen su ta juya dukiyarta da kanta, tayi sana’ar da take so da kasonta, nikuma zan taimaka musu da shawarwari da goyon baya duk sanda suka bukata”. Amma Mama tace “a’ah, sam ban yarda ba, ni da kai kanka da su ‘yan uwan ka mata duka abu guda ne, ba kuma ‘yan Uba kuke ba balle kace min zasu zargeka, hadin kanku nake so a duniya tunda baku da wanda yafi muku junanku, shiyasa nace a hade komai wuri daya a damka maka. Da a samu riba, da ayi asara duk daya ne a wajenmu, indai dukiyar nan a hannunka take Baffana bamu da haufi kaji?!”. Zayyan ya buga ya raya akan bazai iya ba, Mama Fatu ma ta kafe akan bakanta. Tace “zamusa kafar wando guda nida kai in ka ki jin maganata”. Don haka da damuwar wannan maganar da sukayi da Mama ya juyo Zaria a ranar. Har yace sai ya kai kararta gun Baba Murtala. ***** ***** **** Kwana biyu kullum Safiyyah cikin